UBAYD MALEEK 23

Advertisement

 

_Mamuhgee 23_*

Abdul-rahman (sudais) is a  young boy who’s so passionate about putting the Holy Qur’an into memory. Please help this little boy grow his YouTube channel *ABDUL-RAHMAAN* you got nothing to lose in sha Allah thank you and Jazakumullah khair🙏🏻

Do subscribe please

Advertisements

****************

Kodata fito kasa zuwa dakin farhat tayi sbd gabaki daya kafafunta sunyi sanyi toilet dinma tana fitowa ta zube kan gado a kife tana sauke ajiyar zuciya a jejjere Dan Kamar har lokacin tanajin dumi da softness na hannunsa akan mararta.

Bude kofar da akaine yasata Dan juyowa ahankali taga afia ce ta tashi zaune da sauri tana cewa”

Princess tadawo.

Dariya afia tayi tana qarasowa ta aje shopping bags din dake hannunta tace”

Harkinji sauki kenan?

Waskewa NURU tayi da cewa”

Advertisements

Eh” tajawo kayan tana budewa Dan mantar da kanta tunanin abinda yafaru din.

Duk abinda take buqata afian tasiyo Mata ta tashi ta tattara kayan tasa musu su a inda suke aje kowanne tayi sallah tazo ta zauna suna duba wani sabon Francie’s program na likitoci da lawyers tareda engineers a laptop.

Sai la’asar lis tayi wanka ta sauya cikin White three quarter da farar top me laushi ta fita tayi dakin farhat afia tabi bayanta da kallo sbd kusan kome NURU tasaka kyau yake Mata inama ace Imran dinta tafara aura dashine zata more rayuwa sbd yanda yake Sonta Amma dad dinta bazata taba samun so agaresaba har abada sbd mum ce kawai a zuciyarsa.

NURU na shiga dakin farhat ta taddata itama sanye da fararen qananun Kaya tana jiranta har ta fidda kayan drwing din Nan suka baje suka fara.

Sai bayan magriba suka gama 

Farhat ta dauka da gudu taje nunawa dadynta ya duba Masu idan sunyi daidai Amma bayanan kusan so uku tana komawa bayanan ta karba wayar  NURU ta saka numbernsa dake cikin kanta ta Kira Bai dagaba tukuna ta hakura anan dakin sukai sallarsu suka kunna cartoon suka baje abinsu adakin suna kallo Saida lokacin cin abincinsu na dare yayi suka fito zuwa dining suka zazzauna sukaci suka koshi suka shige anan dakin farhat NURU tayi barci Bata koma nasu ba Dan dama hakan takeyi wani lokacin.

Qarfe goma Sha biyu da mintuna ya nufo dakin farhat din wadda kusan kullum idan haryana gida saiyazo ya dubata da daddare sbd qarancin shekarunta musamman yau dayasan saitayi nemansa sbd zanenta yaduba Mata Dan haka ya nufa dakin Kai tsaye ya bude yashigo tareda rufe kofar har zai kunna wuta gudun kada ya tadata yasa Bai kunna dinbaya qaraso bakin gadonta tareda zaunawa bakin gadon ya Kai hannu yakunna bedside lamp kadan haske ya ‘dan bayyana yana waiwayowa yaganta itace kwance abakin gadon farhat na quryar gadon ya sauke sahirtaccen numfashi Yana kallon kayan baccin jikinsu itadai farhat komai iri daya riga da guntun wando royal blue bacci suke duk su duka hankali kwance.

Dan qara rage hasken wutar yayi sbd kaman hasken zai damesu yajanyo musu bargo ya lullubesu ko Gama janye hannunsa baiyiba NURU tasa kada ta yaye lullubin Dan dama Bata cikason rufaba cikin bacci.

Fuskarta yayiwa kallon minti biyu ya dauke Kai tareda Miqewa ya nufi hanyar ficewa harya taba kofa zai fita saiya tsaya tareda Dan rufe ido ya bude tunanin Dole wani daga cikin masu aiki zasu tadasu da asuba yasashi dawowa yasake Jan bargon ya rufa Mata saidai Yana dauke hannu takai hannu cikin baccin zata yaye yakai hannu zai danne hannuwansu suka sauka atareda nashi akan nata Wanda Kai tsaye yasata bude manyan idanuwanta dake cikeda bacci ta dagosu.

Kasa yadda tayi da abinda tagani tasan mafarkine kawai take Dan haka saita juya hannunta tasanya tafin hannunta tana sake tattaba hannunsa Dan Jin tsananin taushinsu ta lumshe ido baccinta na fizgarta har lokacin tafin hannuwansu na hade.

Dan sarquwa yayi da yawu kadan yasaki Dan qaramin tari Mara dogon sauti Wanda yasata bude idanuwanta duka da qarfi tareda zaburowa daidai motsawar farhat sai yayi saurin dafeta Takoma kwance sbd kada ta tada farhat ga farhat din da surutu zata iya jeho wani zance akan hakan.

Kallonsa takeyi face to face akaro na farko a rayuwarta zuciyarta na harbawa a tsorace yayi Mata kallo daya da idanuwansa da yau suka shiga daidai cikin nata take taji jikinta ya sake gabaki daya sai kawai ta sake a jikinsa ya hadiye wani mugun yawu a maqogaransa Wanda yasata kallon moqoshinsa sbd yanda Adams apple dinsa yayi sama yayi qasa ta maqoshin nasa.

Miqewa yayi tsaye yaraba jikinsu sbd asthma dinsa dayakejin kaman zata tashi ya juya ya fice adakin yabarta kwance Bata iya ko daga hannunta sbd mutuwar jiki saidai ido databisa dashi cikin wani irin yanayi na kunyane ko na menene ta Bata saniba illa dai Abu daya data tabbatar ayau shine kyawun da Allah yabasa Wanda ko rabinsa ‘yayansa Basu daukoba cikin yama manyanta kenan…daganan baccinta ya watse har kusan asuba Bata samu baccinba gashi gobe tanada zuwa makaranta Dole ta rintse idanuwanta Dan tayi baccin Kona Dole ne.

Qarfe shida ta farka ta sauko gado tashiga toilet tayo alwala ta tada farhat sukai sallah ta fice.

Tana shiga dakinsu ta tada afia sallah kafin ta fito ita ta fice zuwa kitchen aikin breakfast.

Tana gamawa ta jere a dining takoma daki tayi wanka tashirya cikin black riga da wando ta doro doguwar kimono fara akai ta daura black scarf me kauri tafito sukayi breakfast itadasu afia da farhat suna gamawa kowa yaje ya dauko jakarsa suka fito.

Da Mr Omar suka fara cin Karo tsaye jikin motar dazasu tafi da ita makaranta tareda sabon driver cikin girmamawa yana Dan taudasa harshe cikin sakin fuska yace”

Gud morning Mrs MALEEK.

Gud morning princess.

Kallonsa AFIA tayi Jin abinda yace itadai NURU sidadawa tayi ta wuce Jin  kalmar tamata girma ta shige mota tana kunna wayarta da Imran yahanata sakat da kira saigashi tana kunnawar kiransa na shigowa ta dannata silent tana Dan kallon gefen Mr Omar dake tsaye idanuwansa kuwa quru akan wayarta tana juyowa ya dauke Kai Yana cewa”

Adawo lafiya.

Suna barin gidan ta sauke ajiyar zuciya tareda daukar wayar data kusa katsewa cikin sanyi da rawar murya na rasa abin cewa da damuwa tace”

Hello im ka……da wata gigitacciyar ajiyar zuciya ya katseta yana cewa”

NURU labarin aurenki Bai kasheniba duka ya kashe rayuwata gabaki daya amma rashin daukan wayarki zai kashenine sbd…..

Da siririyar murya tayi saurin katse zancen da cewa”

Kariga kasan komai Im tayaya zan iya daukan wayanka yanzu inajin tsoron hakan.

Kasa danne abinda yakeji yayi cikin wata wahalalliyar murya idanuwansa na cikowa da hawayen zafi da ciwon da zuciyarsa kemasa ya bude Baki dakyar yace”

NURU shin da gaske kin auri MALEEK sbd wlh nakasa ji nakasa yarda da komai inason ji daga bakinki Dan kuwa nasan nikadaine a zuciyarki nakasa yadda da hakan NURU na…..

I’m sorry im bansan mezan iya cewaba Amma dai koma menene gskiyan shine aure dai andaura Wanda Koda bada son Rainaba Dole zan kiyaye dokan aure Dan Allah im kayi hakuri komai yafaru ne kaman daga sama,nasani kana tsananin Sona haka Nima Ina……shiru tayi Idanuwanta na cikowa da wasu irin hawayen karyewan zuciya sbd Jin sautin kukansa dake fita ahankali cikin karyewa da zuciyarsa keyi taji zuciyarta ta karye itama hawayenta na gangarowa takasa karasa mganar ta kashe wayar sbd kukansa reras dake ji cikin qaramin sauti.

Kasa cewa komai afia tayi tanajinsu sbd tausayinsu datakeji musamman im Wanda tafi kowa shaida irin so me girma dayakewa NURUn.

Farhat kuwa riqo hannun NURUn tayi tana kallon hawayen daya gangaro Mata tace”

Aunt NURU meya samu uncle Imran din Naga kina kuka.

Dauke kanta tayi tana goge hawayenta da tissue ta Dan qaqalo murmushin yaqe tace”

Ba komai kafiyansa kalau he’s just missing you princess farhat.

Murmushi tayi tace”

kema Yana missing naki ko??

Shiru sukayi Babu Wanda yasamu damar cewa kalaba har suka Isa aka ajeta suka wuce Dan su sunada Dan nisa.

Suna isa makarantar Kai tsaye ladies washroom ta nufa ta nutsar da kanta tareda bude kanta kwakwalwarta tasamu damar haddace abinda take nanatawa kanta na cewa tanada haqqin auren wani akanta yanzu dokar Allah na kanta.

A dauki mintuna aciki kafin ta samu ‘yar nutsuwa ta gyara fusakrta ta fito tana duba wayarta dake ringing ga mamakinta saitaga numbern ta Ethiopia ce Kiran daga gidane kenan da hanzari ta dauka tana tafiya cikin sa’a kuwa padima ce cikin tsananin farin ciki tace”

Hey padima hw are you??

Dif padima tayi sbd batasan abinda NURUn tafada meyake nufiba tana danne baqin cikinta tayi kasa da murya cikin tsananin damuwa tace”

Nuru kina lafiya kuwa?

Ya gida?

Yasu farhat?

Lafiya kalau kowama Yana lafiya,yayasu abal da meryam Ina ammi?

Sake qasa da murya tayi tace”

Lafiyansu kalau nuru.

Kefa padima kina lafiya dai ina?Kuma Yaya jikinki?

Antabo Mata inda take jira sai kawai takasa riqe kukan ‘dacin ran datakeji tsawon kwanaki cikin qaramar sheshekar kuka tace”

NURU wlh bansamu saukiba Ni kilama ciwon ajaline abun yamin tsanani Kuma Babu wani magani dasu abal ke bani hasalima haryanxu fushi sukeyi Dani tun kan maganar cikin Nan da Babu nidai Dan Allah NURU kitaimekeni inason gyara rayuwata sbd Nima na faranta ran iyayenmu.

Sanyi jikin NURU yayi ta danyi shiru na seconds kafin ta sauke numfashi me zafi asanyaye tace”

Padima kidaina kuka Inshallah Zaki samu lafiya bazan Bari wani Abu yasamekiba da yardan Allah,

Yanzu Ina makaranta idan nakoma gida zanyi shawaran zuwanki na tambayi AFIA muji idan da hali sai jekadi takawoki Nan anemamiki lafiya.

Da qaramar muryar kuka tace”

Ngd sosai NURU Dan Allah kadaki manta ayi magana da wuri kada abin yayi qarfi fiyeda da.

Tana kashe wayar tafara tunanin Yaya zatayi yanzu da wannan sabuwar damuwar Kuma,da haka ta shiga class.

Qarfe biyar saura suka dawo amatuqar gajiye Dan ko zama batayiba ta aje Jakarta ta tareda zare kimono dinta ta nufi dakin farhat dan wanka take tsananin buqata da fitsari dayake neman matsarta gashi AFIA tarigata shiga toilet bazata iya jiraba.

Tana Shiga dakin farhat bata ciki Kai tsaye ta tube tareda janyo qaramin towel din farhat ta daura tafada toilet.

Ajiyar zuciya ta sauke lokacinda ruwa masu dumi suka sauka jikinta sbd yau Bata zauna sosaiba sbd zuwanta biyu kotu yau ga damuwar padima data Imran Amma yanzu taji sauki komai datayi wankan Nan.

Farhat yau da zazzabi tadawo daga school sbd bayan drwing din da jiya aka bawa kowa yayo yau games sukayi ita tana cikin masu football Wanda yadata haki da yawa Amma sbd ba qura asthmanta be tashiba saidai ta kwaso zazzabi me qarfi Wanda tun a school tayi collapsing aka Kira MALEEK Koda suka Isa ta farfado Amma Kam tanajin jin zazzabi sosai siadai yanzu zazzabin ya sauka gabaki daya saitasamu bacci ya dauketa Dan hakane yasa Koda suka dawo gida da ita ganin su afia basanan yasa yatafi da ita samanshi yanzu ta balcony daya hango dawowarshi saiya daukota ya dawo da ita dakinta danta samu kulawa gurinsu afian sosai.

Fitowa tayi tana gyara zaman towel din farhat dayayi Mata kadan tana sauke ajiyar zuciyar nustuwar data samu tana qarasowa tsakiyar dakin taganshi tsaye bakin gadon da farhat ke bacci wata mummunar razana tayi ta damqi towel din da qarfi Jin zai sabule Mata ta sake dagowa da sauri ta kallesa cikin tsananin tsoro.

Tsabar rudewa rigarta dake gefen gadon ta nufo da sauri zata dauka kafin ta iso yabar gurin batareda yabari ta qaraso gurinba ya fice dakin gaba daya Dan towel din ko Gama rufeta baiyiba sbd qanqantarsa.

Zamewa tayi bakin gadon farhat tana kallon kanta tareda dafe goshinta tanajin wani irin yanayi na damuwa.

Zarar kayanta tayi ta fice da sauri ta fada dakinsu ta Sanya kaya tayi sallah ta zauna gefen afia batareda tace komaiba ta zurfafa tunanin wani Abu dayakasa fita cikin ranta afia na lure da ita Amma batace Mata kalaba.

##MAMUH#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like