UBAYD MALEEK 24

Advertisement

 

Mamuhgee 24_*

Saida safe dukkaninsu sukasan farhat batada lafiya Koda suka Isa dakinta tana zaune jikin dad dinsu Yana zaune bakin gadonta sanye da black jallabiya ta maza me tsananin taushi sai kyallin maiqo takeyi alamar ta masu abun duniya ce.

Itace agaba ashigowa kafin Afia Amma tana ganinsa tayi slow afia ta wuceta tana qarasa dayan gefen ta farhat din ta zauna tana cewa”

Gud morning dad,

Farhat bakida lafiya bamusaniba mum Sarah ke fada Mana yanzu da safen Nan.

Advertisements

Dago fuskarsa yayi dake fayau dinta sai wani daukan ido take ya kalleta da idanuwansa Wanda itama daidai shi ta sata kallo suka hada ido tayi saurin sauke idonta muryarta da wani irin salon sanyi dabata saniba tace”

Barka da safiya.

Har lokacin kallonta yakeyi 

Tasake dagowa ta saci kallonsa suka sake hada ido sai kawai tunanin ganin dayayi Mata jiya da daddare kusan Babu komai a jikinta take wata matsananciyar kunya ta mamayeta batasan lokacinda ta rufe idoba ta fita da gudu Kamar karamar yarinya.

Da mamaki afia ta dago ta kalli kofar kafin ta juyo ta saci kallon dad dinta da bataga alamar ma yasan da NURU tashigo bare tace kofar yake kallo ta maida kallonta kan farhat tana cewa”

Sorry baby aunt NURU taje Sanyo kayane sbd batasan dad na Nanba ta taho da sleeping dress ajikinta shine Takoma ta sauyo nasan kin matsu tazo gurinki ko baby?

Gyada Kai farhat din tayi tana kwantawa jikin afia din tace”

Advertisements

Afia I saw mum yesterday a school dinmu she was there before I fainted……

Da sauri AFIA ta dago ta kalli farhat din tareda kallon dad dinsu da sauri shima saidai ko Gama juyowa batayiba ya miqe ya fice kamarma baiji me farhat taceba afia tabi bayansa da kallo kafin tadawo da kallonta kan farhat cikin mamaki tace”

Baby dagaske Kinga mum?

Gyada Kai tayi tana kallon afia din tace”

Eh naganta tazo kafin ta iso gurina I fainted daganan shikenan saidai Naga dad kawai.

Wani yawu afia ta hadiye kafin ta ta danne mamakinta da farin cikinta tana miqewa tace”

Ok baby Bari naje naturo Miki NURU tazo tayi Miki wanka da brush saita Baki abinci akwai abinda zanyi yanzu na gaggawa ok baby.

Wucewa tayi ta fice da sauri ta nufi dakinsu ta janyo doguwar riga tasanya akan kayan baccin jikinta ta dauki wayarta da sauri ta fice ta nufa library dinsu Dan Yin waya.

Doguwar kimono NURU ta doro akan kayan jikinta na bacci kafin ta wuce ta nufa kicin ta hadawa farhat Dan guntun breakfast sharp sharp ta dauko a qaramin faranti ta nufa dakin tana adduar Allah yasa ya fice.

Ganin baya dakin yasata qarasowa da wuri ta ajiye tray din tana cewa”

Sweetie kiyi hkr bamu San bakida lfy ba,jiya ma anan nayi wanka Amma banluraba sbd hankalina yatafi wani gurin dabam na……kasa qarasawa tayi tana sake tunano abinda yafarun sai kawai ta sauya zancen da sakin qaramin murmushi tana cewa”

Ok sweetie muje ayi brush kizo ga breakfast sai asha magani.

Tayar da ita tayi suka nufi toilet din suka shige.

Harsuka gama komai har wanka da Shirin farhat din kafin suka fito zuwa nasu dakin itama NURU tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga suka fito Palo ta kunna Mata cartoon takoma ciki tayi Shirin makaranta tazo ta fice har lokacin afia Bata shigowaba tanacan.

Tsaye take cikin libry din idanuwanta sunyi jajir sbd tsananin baqin cikin dake mamaye da zuciyarta ayanxun datake waya da mum dinta cikin tsananin sanyin murya da sarewa tace”

Haryanxu Babu ‘yayanki acikin ranki kenan?sbd wani burinki na duniya mum kike fadar haka? Tayaya kike tunanin dad zai iya rayuwa ahaka for how long kikeso yayita jiranki?mum please ki……

Cikin iko da muryarta me taushi ta katse afia da cewa”

Zandawo wa MALEEK Amma ba yanxuba haryanxu akwai abubuwan dake gabana,afia kinada naci akan zance daya koyaushe bayan nace Miki zandawo Amma ba yanzu ba idan akwai abinda yafi cancanta yanzu dakiyi shine ki raba maleek da yarinyar daya aura Kuma tabar gidan gabaki daya sbd matuqar tananan koya saketa bazan iya dawowaba infact inason sauyin gida tunda harta zauna a wannan gidan koba komai idan haryanzu kunason aikinta zaku iya zama da ita acan Amma dai Ni Kam a sauyamin gida musamman farhat da lalurorinta sunyi yawa yau ciwo gobe lafiya….

Cikin mamaki,takaici da baqin ciki daya Gama kashe afia tabude Baki tace”

Mum shin akan abindake gabanki kika watsar da ‘yayanki musamman Yar qanqanuwa Kamar farhat harkina cewa lalurarta yayi yawa?

Ciwone fa atareda ita Wanda Allah ne ya Dora Mata ba ita tadorawa kantaba, badan NURU ba da yanzu dukkanin mu munshiga wani hali and now kina cewa akoreta?a koreta kokuma mubita can mu zauna kenan kin yafemu?

Mum inasonku keda dad duka saidai I’m sorry to say this to you yau nafi son dad ayanzu fiyedake da duk wani tunaninki Dan kuwa koba komai shi yasan haqqinmu ‘yayansa akanshi Yana bamu Dan haka mum tunda haryanxu Bakida mijinki da yayanki aranki inaga zaifi idan na karbi hakan na runguma nakuma amince Dan kuwa na tabbatarda dana amince da hakan tuntuni da bazan cutatu hakaba,

Na lalata rayuwar mutum uku sbd hope din Zaki dawo saidai Ashe mafarkinane kawai….hawayen baqin ciki me tsanani ne suka gangaro Mata ta kashe wayar da qarfi tareda wurgi da ita sbd Jin mum din na cewa”

Afia ke yarinyace haryanxu bazaki ganeba Dan haka please don’t call again idan Baki shirya daukan abubuwan dazan fada mikiba.

Kuka me qarfi ta sake tareda daukar wayar taqara kwadawa da qasa tana qoqarin sulalewa qasa cikin kuka taji hannuwan dad dinta duka biyu ya riqota Yana kallon kyakkyawar fuskarta ya girgiza Mata Kai ahankali ya bude Baki cikin muryarsa me nutsuwa da dadin sauti yace”

AFIA MALEEK karki manta ke ‘yar maleek ce jikar kaleeb our beautiful and brave lioness and you know wat thats means right princess??

Da jajayen idanuwanta ta dago ta kallesa zatayi mgn yace”

Ya Isa haka banason Jin komai all I want from you shine ki maida hankali akan karatunki ki Gina career dinki da kanki.

Sakinta yayi tareda juyawa zai fice saikuma ya dakata batareda ya juyoba ya bude Baki wannan karon cikin cikakken iko da bada umarni cikin sautinsa me daidaita nutsuwarta yace”

Wannan shine Karo na karshe daza’a Kuma maganarta acikin gidan Nan.

Karo na karshe.

Gyada Kai tayi tana sawa ranta batada uwa araye daga yau itama sbd dukkanin inda take tunanin mum dinta yau ta kai limit Dan Bata taba daukar uwa zata iya yafe har yayanta ba datake ikirarin Bata buqatar farhat sbd tacika ciwo, wannan kalmar ta rusa duk wata sauran hope datake dashi akan mahaifiyarsu.

Fitowa tayi tana shigowa Palo ta tararda farhat zaune apalon tana kallon cartoon cikin walwala abinta tana ganin afia din tasake murmushin farin cikin ganinta tana cewa”

Afia bakije makaranta ba kina inane tun dazu?

Aunt NURU ta tafi ta dauka kintafine.

Kasa magana afia tayi tausayin qanwarta me tsanani na shigarta har batasan sanda hawaye suka ciko Mata idoba suna gangarowa ta qaraso ta zauna gefen farhat din tareda rungumeta jikinta tanajin tsananin so da kaunar yarinyar tareda tausayinta,tayaya uwa zatace Bata buqatar ‘danta sbd wani ciwo na harbawa da Allah ya sako Masa,

Ta Yaya mum dinsu zatace Bata buqatar farhat?

Kamar farhat din tasani saita lafe jikin afian batace komaiba hawayen afian Bata sauka kan jikinta sun Jima ahaka kafin Afia ta zame tareda Miqewa yayi daki ta rufe kanta tana wani irin kuka me ciwo da baqin cikin rayuwa,

Babu abinda Allah be basuba najin dadin duniya sai rashin uwa tagari da soyayyar uwa da Basu samuba kwata kwata,

Suna cikin ni’imar dukiya me yawa,

Mulki na sarauta me girma,uba nagari da soyayyarsa,ilimi na Boko Dana addini,kyawun jiki Dana fuska taredana zuciya daidai gwargwado Amma uwa Basu samu komai daga garetaba bayan dawainiyar daukan ciki da haihuwa duk cikinsu Babu Wanda yayi shekara yanashan nononta take zaresu tabarwa masu aikisu sune komai nasu tayaya zasu qarar da soyayyar uwa.

Sai yamma NURU tadawo tun apalo ta sake tabbatarda farhat ta warware Dan da gudu ta tarbeta suka fada kan kujera cikin murna take bawa NURU labarin yau dad yafita da ita Amma Basu dadeba suka dawo.

Miqewa NURU tayi tana cewa”

Iyye yau Daddy ya kyauta Mana sweetie taje yawon datake so.

Duk da haka fa aunt NURU alqawarin mu Yananan fa dakikace Zaki kaini yawo har wani qasa daban.

Hanyar daki suka nufa tana cewa”

Eh banmantaba saina gama karatu idan zanje Vegas attaching papers Dina na Gina career Dina dake zanje Inshallah sweetie.

Tsalle tasaki tana cewa”

Yes yes my Lewa 

Suna shiga daki afia na zaune tayi wanka sanyeda gajeran wando da shimi tana aiki da laptop tana ganinsu ta sake fuska tana cewa NURU”

Welcome baby.

Thank you princess”NURU tace tana zare kayan jikinta tana fadawa Afia zancen dasuke da farhat suna dariya.

Wanka tayi tazo yayi sallah ta Sanya qananun kayan Shan iska itama tasha coke daya ta Dan kwanta sbd ta Dan gaji Kuma batajin yunwa Dan taji snacks a wani coffee shop.

Tana bacci wayarta tadauki ringing afia dake zaune ta kalli wayar saitaga sunan padima.

Murmushi tasaki sbd tasan padima abakin NURU Amma Basu taba gaisawaba Dan haka ta dauka Kai tsaye tareda cewa”

Assalm alaikm padima ānichī gini inidēti neshi? (ya kike ya gida/hw are you doing and family).

Tsit padima data Kira da Dan qungun  kukanta tayi Jin muryar afia wadda takeda tabbacin itace ‘yar maleek da ake fada Dan haka saita Dan saita murya cikin girmamawa da kulawa da sautin muryarta daya tabbatarda tayi kuka tace”

Lafiya kalau alhmdlh li’iliti.

Ya karatu da hidima?

Murmushi me sauti afia tayi tace”

Ba hidima saidai karatu shima munatayi inshallah munkusa gamawa, NURU na bacci yanzu saidai ko Zaki sake Kira anjima kokuma idan ta tashi saina fada Mata ok?

Dan kame kame padiman tafara tana cewa”

Eh baza’a tada ita bane yanzu da magana zamuyi me mahimmanci ne?

Kai tsaye afia tace”

Aa baza’a tashetaba yanzu dai lokacinda ta tashi dakanta kokin manta Matar maleek ce?

Koma yayane bazan tashetaba saita tashi da kanta matuqar ba lokacin sallah bane kawai ya isa yasa na tasheta sai idan dad ne dakansa yake nemanta which kuma is not possible for now dai.

Wani Abu padima taji yataso Mata kamar zata ashararo ashar ta danne tana cewa” Sabala ibilis cikin ranta.

Wato NURU har matsayin nata yafara kaiwa haka tun wuri.

Jin shiru yasa afia cewa”

Ko da akwai matsale ne a gida?

Kifadamun zanyi maganan da ita idan ta tashi.

Shiyafi komai sauki ‘yar maleek padima tafada cikin ranta tareda sauke wani wahalallen numfashi tana karye murya zuwa rawa rawar son kuka tace”

Dama nafada Mata maganar rashin lafiyan danake fama dashine abin yafara tsanani anyi magani anan gida baiyiba shine tace zata kaini Inga likita anan ko za’a dace.

Da mamaki a bayyane afia tace”

Anan Kuma?

Tun yaushe ne ciwon?

Tsawon shekara”padima tafada tana hawaye.

Gyara zama afia tayi tana cewa”

Shekara daya ciwo ajiki shine NURU Bata taba fadaba.?

Menene matsalar?

Ciwon zuciyane yanzu nakai Ina amai da tarin jini wani lokacin.

Innalillahi padima meyasa bakuje ko English hospital na can ba.

Shiru padima tayi tana hawaye da shehekar data sake bawa afia tsoro tafara Mata tambayoyin akan yanda takeji da kalar jinin datake gani tana nazartawa da ‘dan nata ilimin na likita da Bata qarasa zamaba.

Girgiza Kai tayi cikin jimami da tausayawa tareda tsoro tace”

Padima this is serious yakamata kiga likita cikin gaggawa gaskia.

Kuka padiman tasake fashewa dashi tana cewa”

Bansan Yaya zanga likitaba Dan Allah li’iliti ki taimakeni NURU takasa taimakona banason na mutu yanzu.

Ki taimakeni ki kawoni gurinki ki kaini gurin likita Dan Allah.

Shiru afia tayi ciki rasa sanin abinyi Nan take Sadai koma menene batada ikon kawo padima Nan take Dole saidai NURUn ce zatace akawota tukuna akawota din sbd kawo mutum Kai tsaye gidan MALEEK wani aikine Dan kuwa sai ankaita gizah an tantance kafin akawota gidan MALEEK Wanda yanzu Kam NURU ce kawai takeda ikon kira gizah tafada tanason akawo Mata padiman.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda nutsuwa cikin son fahimtarda padiman tace”

Kiyi hkr padima Inshallah Zaki samu lafiya Amma yanzu dai Ni inshallah zan nema appointment na babban likitan da Zaki gani anan Amma maganar zuwanki zanyiwa NURU magana idan ta tashi saita Kira inda za’a kawo ki anan din.

Nagode sosai Allah yaqara girma ina gaida NURUn idan ta tashi.

Katse wayarta tayi tareda wurgi da ita tana jerowa daga afia din har NURU zagi sbd Sam sunqi hawa yanda takeson suhau su rikice da tausayinta yazama basa tunanin komai saina tausayinta tasamu Isa qasar.

##MAMUH#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like