MAKAUNIYAR KADDARA 47

Advertisement

 

*Page 47*

………..Cike da ɗokin zuwa ganin mmn sadiq dasu Aliyu Zinneerah ta 

shirya cikin wando da riga na parkistan red and white, sai gyale red 

Advertisements

data naɗa a kanta wanda ya fiddo mata ƙyawun da fuskrta ta ƙara. Kayan 

sun zauna mata ɗas a jiki kasancewarta mace mai mulmulallan jiki da 

ƙyawun surarta ta ƙuruciya. Babu wani kwalliya a fuskarta, amma ta saka 

lipstick kaɗan da yayma lips ɗinta ƙyau, dan tanada lips masu ƙyau da 

tsarinsu ya fita sosai yanda suke ɗaukar jambaki kamar wata babyn roba. 

Takalmi tasa mai ɗan tudu da igiya, sai side bag ɗinta ƙarama. A yanda 

Advertisements

tai ƙyau dolene ka kalleta ka sake kallo, ga ƙamshi tana bazawa dan 

Zinneerah gwanace wajen ɓarnar turare, idan ta samu batai masa da sauƙi. 

Ƴar jikkar data zuba kayanta kala biyu da tsarabar chocolates ɗin su 

Abdul ta ɗauka, dama hajiya iya ta fice ita tana falo tuni.

       Hajiya iya kawai ta samu a falon itama tana ƙoƙarin fita, samarin 

gidan tun bayan breakfast suka fice, hakama ƴammatan, su Jamal kuwa 

batasan ina suka dosaba. Hajiya iya dake ƙoƙarin fita tace, “Inno kashe 

tvn nan ki taho nasan Moddibo nacan ya cika da hasahinmu”.

     Da to Zinneerah ta amsa tana ɗaukar remote, bayan ta kashe tvn ta 

gyara labulolin sannan ta fito, ƙofar ta rufe dan masu aikin Hajiya iya 

basu dawoba, maybe sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Tafiya ta fara 

cikin nutauwarta tana ƙoƙarin ɗaura agogo data ɗakko a tsintsiyar 

hannunta da dosar inda ta hango Hajiya iya da Mommy tsaye da alama harda 

ita zasuje. Idonta bai lura da AK ba sai da tazo dab dasu tana ɗagowa da 

shi ta fara tozali yana ɓullowa daga ta gaban motar waya a kunnensa 

alamar magana yakeyi. 

     Kallon nata yayi dai-dai da saukar nasa idanun a kanta. A take ƴar 

sakewar data hango akan fuskar tasa ta ɓace ɓat, ya tsuke fuska yana 

mata kallon data nema kifawa saboda harɗewa da ƙafafunta suka shigayi. 

Saurin maida kanta tai ƙasa tana cigaba da takowa ranta fal nauyinsa da 

kwarjini, sai mita take a ranta kuwa. (Haka kawai bakama mutum komaiba 

yayta hararka, shi wai baya ganin waɗanan idanun nasa manya da ƙarfinsu 

yay yawa suna tsorata mutane)…….

     Da wannan tunanin ta ƙaraso Mommy dake kallonta tana ambaton, 

“Masha ALLAH ɗiyata irin wannan ƙyau haka”.

    Ƙasa Zinneerah ta ƙarayi da kanta tana murmushi, hakama Hajiya iya 

murmushi take tana kallonta itama. A bazata sukaji AK ya saki tsaki, 

cikin faɗa-faɗa yace, “K! Koma kisa hijjab”.

   Ba Zinneerah ba hatta su Mommy sai da suka dubesa, shiko ya fuske ya 

buɗe murfin motar ma a fusace ya shige abinsa. A sanyaye Zinneerah ta 

juya zata koma dan shi ba abin wasanta bane, waɗandama suka girmeta da 

shekaru masu yawa a gidan sunabin dukkan dokarsa balle ita ƴar jiya. 

Dakatar da ita Hajiya iya tayi ganin yanda tai ƙwalƙwal da idanu kamar 

zatai kuka, ta kamo hanunta tana matsawa saitin driver da yake zaune. 

“Haba Moddibo aimata haƙuri tunda ta rigada ta fito, ai kaga gyalen ya 

rufe mata jiki, kuma naga daga mota sai gida”.

       Shiru yay kamar baiji mi Granny ta fadaba, sai da ta ƙara leƙasa 

tana faɗin, “Oh nima yarfin daka iya zakamin?”.

    Idanunsa da suka canja launi ya ɗago ya dubi Hajiya iyan, “Amma 

Granny …….”

      “Dan ALLAH ai nace”. Tai saurin katsesa dan tasan shegen taurin 

kansa da dagiya akan abinda duk ya kafama sharaɗi. Badan yasoba ya ɗauke 

kai daga kallonta yan yima motar key. Murmushi Hajiya iya tayi da duban 

Zinneerah. “Kinga zagaya can kusa dashi ki zauna Inno, mu saimu zauna 

baya da Mommynku”.

      Kamar Zinneerah ta fasa ihu taji, dan yanda taga fuskarsa batai 

zaton ya haƙuraba, kawai dai yayi shirune dan Granny ɗin. Amma yata iya, 

dole ta zagaya tabi umarni. Zama tai maƙure jikin murfin mota, zuciyarta 

na mata hasashen ko ina little yake? Dan tayi tsammanin dashi zasuje 

itakam. Yanda AK ya figa motar da ɗan ƙarfi yasata saurin dubansa, sai 

dai da sauri ta ɗauke idonta ganin wani shegen harara daya watso mata 

laɓɓansa na motsawa tamkar mai magana komai son cewa wani abu amma ya 

gagara furtawa.

        “Kai malam wlhy karka zubar damu, dan idan ka kasheni banga sake 

ganin ɗan inno ba ALLAH ya isa mai kishin tsiya”. Hajiya iya ta faɗa da 

iya gaskiyarta tana zazzagama AK masifa. Dariya Mommy ta sanya ganin 

yanda AK ɗin ya hararo Hajiya iya ta mirror.

    Zinneerah kanta sai da zancen hajiya iya ya bata dariya, amma sai 

tai murmushi kawai tana kauda kanta gefe, dan zuwa yanzu ta fahimci 

Yayansu da Granny ba’a haɗuwa ba’ai faɗa ba. Kuma itace mai takalar 

faɗan shi kuma yayta mazurai, idan kuma ya magantu ya rama sau ɗaya yay 

mata banza.

      A nutse yake tuƙin cike da ƙwarewa da bin dokoki, sai da suka hau 

titi sosai ya fara amsama Mommy maganar da take masa daga can baya, 

hajiya iya na tayata. Zinneerah dai bakinta gum, sai strawberry sweet 

ɗin dake bakinta take ta faman juyawa tana kallon hanya, tana jiran taji 

ya tambayeta ina suka dosa taga ya ɗau hanyar anguwar kai tsaye. 

Mamakine ya kamata sai dai babu damar magana, sunyi kusan rabin tafiya 

taga ya gangara dasu wani super market, sai da ya samu waje yay fakin 

sannan yay magana batare da ya kalli kowa a cikinsu ba. “Mommy muna zuwa 

Please”.

        Cike dajin daɗi tace, “A fito lafiya”. 

    Hajiya iya kam baki ta taɓe da ɗauke kai tana maganar da su dake 

gaba ba jinta sukeba. “Muje”. Ya faɗa yana buɗe murfin ya fice. 

Zinneerah bata fahimci da ita yakeba sai da Mommy tace, “Ɗiyata fita 

kuje ku dawo kinji”.

     Sai da Zinni taɗan waro idanunta waje, tace, “Mommy amma…..”  

     “Maza kije karyayi faɗa”.

Mommy ta katseta kafinma tace komai. Dole Zinneerah ta yunƙura ta fita 

zuciyarta na dukan goma-goma. Idanunta kuwa harsun tara ruwa. Ina ita 

ina shiga irin wannan wajen da Yayansu, itakam yau tana cikin abba-tuwa, 

shikenan ya samu damar dazai cimata uwa akan ƙin bin maganarsa na saka 

hijjab duk da Granny ce tai bell nata dai. 

      Koda ta fito da birkitattun idanunsa ta fara cin karo, ga 

fuskarnan kamar zatai aman abinda kecin ransa. Ƙasa tai da kanta tana 

ƙoƙarin haɗiye rauninta dake son bayyana. Ta fiske abinta da takowa inda 

yake a hankali batare data sake yarda sun haɗa ido ba. Tana isowa wajen 

ya miƙa mata handkerchief ɗin hannunsa, “Kwashe wannan abun na bakinki”.

    Idanunta dake tara ruwan hawaye ta ɗago ta kallesa. ya zuba mata 

hararar data sakata amsar handky ɗin babu shiri, cikin ɗan tura baki ta 

fara kwashe ɗan janbakin dabai taka kara ya karya ba. Handky ɗin ta miƙa 

masa tana ƙoƙarin haɗiye kukanta. Batare daya amsaba ya raɓata zai wuce 

da faɗin, “Idan baki shiga hankalinki da saka wannan janbakin ba saina 

tsinke waɗanan lips ɗin da haƙori mtsoww”.

        Duk yanda Zinneerah taso daurewa kasawa tai sai da ta bisa da 

kallo mamaki ƙarara akan fuskarta. Ganin bata biyosaba ya sakashi 

tsayawa cak. Da sauri ta nufesa saboda fahimtar dan ita ɗin ya dakata. 

Jerawa sukai a tare gwanin sha’awa, dan yanda yake tafiya babu garaje 

haka itama take tafiyar, amma kasancewar abinda ya faru tana tsoron sake 

laifi ya ƙara hanzarta tata tafiyar, sai suka samu daidaito dashi dan ya 

fita kuzari da tsaho.

      Shigarsu wajen ya sake bayyana ɓacin ransa a saman fuska ganin 

yanda mutane ke ɗan kallonsu jefi-jefi, a bazata kawai taji ya ruƙo 

hannunta cikin nasa mai taushi da ƙamshi tamkar nata ɗinma, dan zuwa 

yanzu ta fahimci jin daɗi ke kawo irin wannan baiwar ga fata bawai 

shafe-shafe ba. A kusan tare ita da shi suka lumshe idanu saboda jin 

sabon al’amarin dake saukar musu a gangar jiki da magudanar jini, ya 

sake damƙe hannun da ƙyau yana ƙoƙarin dai-daita kansa gudun kar ayi 

abin kunya.

    Zinneerah kam ai murus bakinta ya ƙara mutuwa sai sama da ƙasa da 

numfashinta keyi tana ƙoƙarin fisgosa da ƙyar. Haka tanaji tana gani ya 

shiga zagayawa dasu yana ɗaukar abubuwa da sakawa a basket ɗin da ɗaya a 

ma’aikatan wajen ke biye dasu da shi. Itama kuma sai yanda budurwar ke 

kwarkwasa da wani iyayi a gaban Yayan nasu ya bama Zinneerah haushi ta 

shiga hararta ta gefen ido tana faman yamutse fuska.

      AK bai fahimci halin da take ciki ba sai da sukazo wajen biyan 

kuɗi, har lokacin yana riƙe da hannunta tamkar ance za’a ƙwace. ATM ya 

ciro a aljihun wandon getzner shaddarsa ash zai miƙa budurwar data 

tayasu takai hannu zata amsa cike da yauƙi, caraf Zinneerah ta kawo 

hannu ta amsa daga hannunsa tana wani juya ido da sake miskile fuska.

    Yanda tai ɗin ya saka wata dake kusa dasu kwashewa da dariya ita da 

ƙawarta. A fili tace, “Wlhy yarinya kin birgeni, adana abinki kar ƴan 

shishshigi suyi miki wuff da shi”. 

     Sarai Zinneerah ta jita, amma sai ko kallon inda suke bataiba tama 

ɗauke kai gefe. AK ma da sarai yajisu bai nuna yajiba, sai dai ya ɗan 

dubi Zinneerah ta gefen ido maganar ƴammatan na masa kaikawo a zuciya da 

ƙwaƙwalwa. 

     Koda aka gama saka musu a leda budurwar bata daddaraba duk da 

yarfatan da ƙawayenta sukayi da Zinneerah ta sake kai hannu zata ɗauka 

ledar Zinneerah ta rigata ɗauka da faɗin, “Don’t worry, thanks”.

     Kasa haƙuri AK yayi yanzu kam sai da ya ɗan dubeta, mi zuciyarsa ta 

ayyana masa oho sai gashi da sakin wani malalacin murmushi yana sake 

damƙe hannunta dake cikin nasa, daga haka ya jata suka fito yana mamakin 

miskilancinta da kame kai tamkar ba ƙaramar yarinya ba.

         Zinneerah na ganin sun fito ta fara ƙoƙarin zame hannunta a 

nasa, shima babu musu ya saki tare dayin gaba abinsa. Sai dai kuma 

abinda sukema gudun su Granny, kuma sun gani. Dan Granny dake bama Mommy 

labarin da Zinneerah ta bata akan zuwanta katsina aikatau tun bayan 

fitarsuce ta fara hangosu. Ta taɓa Mommy tana faɗin, “Auta kalla 

mutanenki”.

       Ɗago kan Mommy yayi dai-dai da sakin hannun juna da sukayi, dan 

haka ta murmushi kawai da faɗin, “Inna tarkon nan naki fa mai ƙarfine, 

dan na ƙaramin damƙa yayma ɗana ba, yana dai ƙoƙarin nuna halin nasa na 

basarwa ne”.

      Baki Hajiya ita ta taɓe da cewa, “Ai sai yayma ubanda baisan 

halinsaba. Ni tuni na harbosa ai. Itace dai na kasa gane kanta dan itama 

gidan miskilancince, bansan yanda gidan nasu zai kasanceba an tara masu 

shegen baƙin rai da miskilanci. Shiyyasa banason a faɗa mata har sai ta 

tare suje can su ƙarata”.

     Dariya Mommy ta sanya har su Zinneerah suka iso wajen, sai da suka 

shigo mota ta haɗiye abinta tana musu sannu. Duk amsawa sukai yana tada 

motar, daga haka sai gidan mmn sadiq da Zinneerah taita mamakin tayaya 

ya sani?.

    ★★

  Tarba suka samu maiban mamaki daga mmn sadiq da maman halima. ashe 

hajiya iya ta sanar musu da zuwan nasu, shiyyasa mmn sadiq datai niyyar 

zuwa dubata yau dole ta haƙura. Zinneerah kam ai tuni ta faɗa jikin mmn 

sadig tana murnar ganinta ita da mmn halima. hakan datai har sai da ya 

bama AK mamaki dan baiyi zatonta hakaba. Kasancewar Abba na gida yana 

jiransu a falonsa aka sauke AK, su Hajiya iya kuwa da mmn sadiq keji 

kamar ta goya suna a sashenta. 

        Duk yanda mmn sakina taso nuna halin nata garesu saita kasa. Dan 

wani cika mata ido sukai dole ta kama kanta harda zuwa ɗakin mmn sadiq 

gaishesu. Ai kam sun amsa mata da fara’a da mutuntawa, hakan da sukai 

kuma sai ya ƙara musu kima a idonta da shakka. Mmn halima ma cike da 

girmamawa tazo ta gaidasu, Hajiya iya nata sanya mata albarka dan bata 

manta da fuskartaba taje mata gaiauwar Inno.

        Saboda zuwa nan hajiya iya dama taƙi cin abinci, dan ta taho da 

shirin cin abincin gidan ɗiyar tata. Aiko taji daɗin samun masa da mmn 

sadiq tai musu, sai gashi daga ita har Mommy sunci sosai suna godiya. 

hakan yasa Mmn sadiq ƙara jin daɗi da nutsuwa. Dan koba komai ai sun 

bata kimarta. Zinneerah kam tuni tana sashen mmn halima ta barsu dan su 

sake da kuma kasancewarsu manya a gareta.

    Da wannan damar mmn sadiq da baƙinta sukai hirar zuminci da 

tattaunawa game da labarin da Zinneerah ta bama hajiya iya da kuma 

abinda ya faru akan zancen little da maganar ɗaurin aurenta. Harma da 

shirye-shiryen tariya da a take mommy ta tabatar musu ita ta gama shirya 

komai rana kawai suke jira insha ALLAHU.

    Hawaye sosai mmn sadiq keyi har sai da hajiya iya ta shiga 

lallashinta. 

     Sai da akai sallar la’asar Abba ya shigo gaida su hajiya iya tare 

da AK da shima yaci masa sosai dan yana sonta, ya kuma sha zoɓo shima. 

Sun gaisa cikin mutunta juna, suka ɗan ƙara tattaunawa har zuwa kusan 

biyar da rabi sannan sukai haramar tafiya.

    Sai kuma ga Zinneerah tai ƙwalkwal da idanu na kewar hajiya iya da 

zatayi duk da dai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata koma. Sau biyu suna 

haɗa ido da AK da tuni ya shige mota ta mirror ɗin waje, daga ƙarshe dai 

ta matsa daga saitinsa tana ɗaga musu hannu.

    Tafiyarsu da mintuna basufi talatinba su Sadiq suka dawo gida. Ganin 

Zinneerah suka haukace da murna suna tambayarya ina little ɗinsu?, su 

dai sunyi kewarsa dan ALLAH a dawo musu da abinsu. Dariya kawai take 

musu dan ita dai wannan ba huruminta baneba ai. Tunda batasan yaje canba 

itama ganinsa tayi.

     Bata samu zama da mahaifiyartaba sai dare bayan yaran sunyi barci, 

kasancewar ɗakin mmn sadiq ɗin zata kwana suka sami damar yin hira, 

yayinda mmn sadiq ketama ƴar tata nasiha a kaikaice akan aure da 

muhimmancinsa da darajojinsa. Ita dai Zinneerah saurarenta kawai takeyi 

bawai fahimtar dalilin yinsuba. Sai dai suna shiga kwakwalwarta tana 

kuma ƙoƙarin adanawa da fatan yin aiki dasu a duk sanda ƙaddara ta 

tilasta mata yin aure dan bata kawosa a lissafinta sam. ita kullum 

lissafi da budget ɗinta akan karatune mai zurfi kawai.

     Washe gari ma bayan tafiyar su Abdul skull sake zaman hira tayi da 

mamanta. A yau ɗinma hirar ta kasance kusan duk nasiha da dabarun zaman 

gidan aure koda da kishiya. Harma dai takai abin ya fara bama Zinneerah 

mamaki amma saita danne a ranta kawai.

     Karfe huɗu dai-dai sai ga Ni’ima da driver sunzo ɗaukarta, jitai 

kamar ta fasa kuka. Amma jin mmn sadiq tace zasuje taron biki Danya kuma 

harda ita nanda kwanaki tara yasa taɗanji daɗi a ranta har fuskarta ta 

nuna. Bayan ta gama matse-matsen hawayenta ta shirya suka wuce ɗauke da 

madaidaicin botikin gullisuwa da mmn sadiq ɗin tai musu.

          Koda suka iso gidan cike da murna suka tari juna dasu Bahijja 

daketa mata ƙorafin basusan zataje wajen mama ba da sun bita. dan sai da 

su Mommy suka dawo suka sani. Haƙuri ta basu kawai, daga haka suka shiga 

hidimar cin gwullisuwa kuma.

         Ana idar da sallar magrib hajiya iya tai baƙuwa. Bayan sun 

shiga ɗaki kusan awa ɗaya aka kira Zinneerah, kai tsaye hajiya iya tace 

mata ta shirya zasu tafi da baƙuwar gidanta. Mamaki ya kama Zinneerah, 

amma ganin yanda hajiya iya ta fiske dole itama ta shanye mamakin nata.

     Bayan ta shirya Hajiya iya ta jata gefe tai mata ƴar nasiha da 

gargaɗin duk abinda akai mata a inda zataje kartai jayayya, karkuma tai 

wasa wajen koyon komai ɗin. Ta amsama hajiya iya da girmamawa ita dai 

tana matsar ƙwalla, dan hankalinta ya tashi jin wai sati ɗaya zatai 

acan, a hakanma hajiya fadi take waje ya ƙure ba haka tasoba.

      Zinneerah naji na gani ta tafi tabar su Meenal tana hawaye suma 

sunayi tamkar masu rabuwa har abada. Hajiya iya kanta sai da taji 

kewarta, to amma wannan shine kawai gatan da zatai mata ta miƙata wajen 

kwararrun mata ta fannin sanin gyaran jiki da wasu sirrika irin su 

hajiya Falmata su gyara mata ƴar jikallen tata. Dan idan tai dubi da 

abinda ya faru da kuma kishiya irin Farah saita ƙara jin wannan shine 

gatan.

      Koda suka iso gidan hajiya falmata bata tsaya sanyaba saboda 

gargaɗi da sharuɗɗan hajiya iya akan irin salon gyaran da take buƙata 

aima Zinneerah ɗin, itako hajiya falmata dama aikinta kawai ta sani 

batasan wasaba. Musamman ma aiki irin wannan na manyan mutane kamar su 

hajiya iya da suke alaƙa tun zamanin ƙuruciya ba abinda zatai sanya 

bane. Dan haka tun a ranar ta fara gyara Zinneerah daga isowarsu gidan 

ko hutawa batama bari sunyi zaman yiba. Tun Zinneerah na kallon abin 

wani iri hardai ta fara jin yana shiga jikinta da sha’awarsa ganin yanda 

ta fara canjawa da ƙamshi mai kama jiki da gogewar fata a cikin kwana 

biyu.

       Babu abinda ke damunta sai kewarsu Jamal da hajiya iya dan ko 

abinci da ake bata na musamman ne. Hajiya Falmata kuwa nata aikinta da 

koya mata abubuwa kai tsaye har kunya na neman kashe Zinneerah da ganin 

hajiya falmata zata iskantar da ita shekarunta basu kai ba. A ranta kuma 

tana mamaki yanda ake mata magana mai kama da harshen damo akan aure da 

zamantakewarsa. Ta rasa wannan dalili itakam, takumayi alwashin bazata 

tambayaba zata cigaba dabi da ido da kuma saurare.

      A Ɓangaren su Hajiya iya kuwa Zinneerah na barin gidan aka ware 

fara tsare-tsaren biki da maganar invitations dan hajiya iya da Baffah 

fa shiri suke gagarumi kodan ƙular dasu Mammah dake can hotel suna jiran 

tsammani daga mai bincike, AK kuwa daketa ƙoƙari akan aikin shinkafarsa 

yana sane dasu, dan tuni yasa aka bincika masa inda suke, ya kuma shirya 

ɗaukar mataki akan Farah data bijirema maganarsa. 

     Akan gyaran gidansa kuwa Dr Mahmud da Huzaifa ne tsaye akai duk da 

gidan bama taɓa zamansa Farah tayiba. Garamashi yankan zauna lokacin da 

yake shigowa ƙasar a munafunce.

     Ranar da Zinneerah ta cika kwanaki huɗu wajen Hajiya falmata lefen 

da Momie ta haɗa gudunmawarta ya iso, sai kuma ga Adilah da Mahma daga 

london suma sun iso da nasu kayan lefen, dan AK na sanar da ita komai 

bai ɓoyeba, takuma bashi goyon baya ɗari bisa ɗari. 

     Zokaga yanda Adilah ke murna da farin cikin kasancewarta cikin ƴan 

uwa. mahma kuwa abinci kawai taci anan taɗan huta ta nema inda su Mammah 

suke, dan bata son ita kanta su san da maganar auren har sai ranar 

tariyar insha ALLAHU…………..✍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like