Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako,mazan su da matansu,alherin Allah yakai muku a duk inda kuke,nayi tawassali ga Annabi Muhammadu (SAW),Allah kai ruฦo da hannayena dan alfarmar ahalin manzon Allah (SAW)*
Advertisements
_Bissimillahirrahmanir raheem_
_wannan littafin nawa ฦirฦirarsa nayi banyishi dan wani ko wata ba,duk abinda kaga yayi dede da rayuwarka arashine_
_wannan daban yake da sauran,salonsa na dabanne,akwai abun dariya,zazzafar soyayya,tausayi,ฦiyayya,da ษumbin danasani,karku bari abaku labari,kubishi sannu a hankali dan kwashe darasin dayake tafe dashi_
_surbajon ce de har yanzu,salo da basirar duk nata ne,nice da kaina ba saฦo ba,ga me_
*Ummu Aymana*
*Surbajo*
*Kano to jiddah*
Advertisements
*Karen bana*
*Sanadin kidnapping*
*ฦan karuwa*
*Cin Amana Ko Fansa*
*Giษaษo ba Shege Bane*
*Allah Gatan Bawa*
*ฦณar Bautar ฦasa*
*Aure Da Haihuwa*
Da de sauransu.ku kasance da wannan banufiya domin ci gaba da samun nishaษi.๐
*1*
“Zahra’u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce,tun ษazu su hanne ke tsaye suna jiranki,bana son sakarcin banza fa”cewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar zaman tsakar gida tana ษaure nono a ledar siga.
Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra’u tace “Inna do Allah Do Annabijjo,ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali,ke bakisan in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba’a yi?”
“aykin kawai,yo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini,se asarar kuษin siya miki da nike yi”cewar inna daga wajen da take zaune.
Fitowa tayi daga cikin bukkar tana gyara ษamarar da ta ษaura a ฦugunta,ko ina a fuskarta kwallliyace irin ta fulani.
Laษษanta shafe cikin jan janbaki,yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyar ba.
“kede Inna kinada matsala,bakin ki be taษa faษin alkha’iri,se sharri,ni ษoramin mu tafi”ta ฦarasa maganar cikin turo ษan ฦaramin bakinta gaba.
Gammo ta ษora sannan ta ษora mata kwaryar nonon akanta,ta miฦa mata ledar viva da aka sa ludaya da ฦorai aciki,ta juya gun su Hanne dake tsaye zaman jiranta tayi murmushi kumatunta suka lotsa,siririyar hushiryarta ta bayyana atsakanin fararen haฦoranta masu kyan tsari,tace “na ษata muku lokaci kuyi haฦuri,mu tafi kar mu sake ษata wani lokacin”
Murmushi sukai mata,sannan suka rankaya suka fice bayan sunyiwa inna sallama.
Tafe suke suna hirar su ta yau da kullum,ษaya daga cikinsu Me suna haule tace”wai duk ฦawancen nan namu muna aure inba riga ษaya muke ba se ya ragu ko?”
Dariya Zahra’u tayi sannan tace,”Allah ya kyauta,ni aradu ko birnin sin naje aure bazan dena ฦawance daku ba,bare ma dukanmu muna ruga ษaya ba inda zamu”
Hanne ce ta amshe zancen da cewa”ni Auran ma tsoro yake ban,kunga de Ma’u kamar abun arxiฦi Rabi’u ya Aureta amma ku dubi wulaฦancin da yake mata yanzu”
“shiyasa na shiga makaranta dan bazan yarda namiji yamin wulaฦanci ba,”cewar Zahra’u tana murmushi.
Da wannan hirar tasu suka ฦarasa fitowa daga cikin dajin falgore inda rugarsu take,suka miฦo tsawon titin zuwa inda barikin sojojin dake cikin dajin yake,sabida ankawo sababbin sojojin da ake ba training gurin acike yake da mutane kamar kasuwa,dan motocima in sun zo gurin da ฦyar suke wucewa sabida yawan sojojin.
Basu jima da zuwa ba kowa kayanta ya ฦare sabida ฦarancin abincin gurin,a hannu a hannu ake siyan duk wani abun ci na gurin.
gurin me saida burodi suka ฦarasa kowa ta sayi guda ษaya sannan suka juya cike da farincikin sun sayi burodin da zasu ci yau agurin alibidin sunan Zina,wata ฦawarsu data haihu.
Karo suka ci da wani matashi sanye da wandon sojoji,hannunsa riฦe da bindiga,se riga tshits army green da hular sojoji,ba laifi kyakkyawane,raษewa sukayi zasu wuce ta gefenshi yayi sauri yasha gabansu yace yana murmushi,
“don Allah kuyi haฦuri mu baฦi ne anan,kuma abinci mukeso mu ci,isowar mu kenan daga Abuja,amma mun rasa”
Harara Zahra’u ta galla masa sannan tace”amma dan baฦin hali ay kuna gani muka kawo tallan nono, in yunwar kukeji me ya hanaki siya?”
Murmushi yayi dan ya fahimci yarinyar akwai tsiwa,cikin taushin murya yace”Bamu lura bane ฦanwata,ayi haฦuri”
“to yanzu me kukeso muyi muku,tunda mude ba abinci bane bare ku cinyemu”cewar Zahra’u batare da tsoron komai ba,dan ita ba ฦaramin abu bane ke firgitata.
“in anan kuke don Allah ku taimaka mana, kuษin cefane zamu baku ku dafo mana abincin ku kawo mana nida abokina,”
Shuru sukayi sannan hanne tace”gaskiya rigarmu da nisa nide bazan iya zuwa gida in dawo ba”
“yo inba wahalalle ba waye zeje gida yadawo nan”cewar haule.
“don Allah ku taimaka abokina yanada lalurar gyambom ciki be jure yunwa don Allah ku taimaka ku yi mana kamin yafara jin yunwa wallahi zamu biyaku ladan yi”cewar matashin kamar zeyi kuka.
Zahrau tsintar kanta tayi da tausayawa abokin nasa,sabida itama tana da lalurar gyambom cikin tasan azabar ziwon,dan haka tsintar kanta tayi da cewa
“kawo kuษin,zan dafo muku,sede muna da nisa zaku iya jira?”
Da sauri matashin ya gyaษa mata kai,sabida tun ษazu yake neman wanda ze dafo musun amma be samu ba,ga abokin nashi shegen taurim kai shiba jure yunwa ba amma ko ze mutu baze ci abincin siyarwa ba,shiyasa duk yabi ya damu.
Hannu yasa a aljihu ya ษebo kuษin dashi kanshi besan adadinsu ba yabata,juya kuษin take a hannunta tana mamaki,amma batace komai ba ta ษauka da yawa suke so, dan haka ce mishi tayi”zan kawo ma insha Allahu ka tsaya a bakin titi de inda zan ganka da wuri”
Godiya yay mata sosai sannan yace”mu haษu kawai anan,zefi sauฦi,sunana Capt Jameel Ahmad zan jiraki anan”
Bata ce komai ba suka juya suka wuce ita da ฦawayen nata,wanda gaba ษaya haushinta sukeji,cikin fushi hanne tace.
“nufinki de bazaki gidan sunan ba ko?shiyasa kika amshi girkin gardawan da baki sani ba”
Batare da damuwar komai ba aranta tace”dan bakusan ciwon ulcer bane da kuma kun tausaya kun musu,nide zan musu sabida Allah”.tana kaiwa nan tai gaba ta ฦyalesu a baya.
Muje zuwa.
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings