Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*10*
Advertisements
Murmushi mummy tayi ta dafo kanta tace “ษiyata sauฦi yasamu kenan?”
Murmushin itama zahra tayi ta sunkuyar da kai ฦasa,
Daddy ne ya ฦaraso gurin ya zauna sannan yace”dama wannan lokacin nake jira kuma gashi Allah ya kawo mu,zamu so ki sanar damu ko ke wace ce,dan musan taya zamu taimakeki ki koma ga danginki”
Hawayene ya zubowa zahra tasa hannu ta goge,sannan tace”ni bani da dangi,baffana yayi hatsari ya mutu,innata ฦดan bindiga sun kasheta,tade taษa shaidamin muna da ฦดan uwa a gombe,kawu modibbo amma sun bar gomben kuma batasan inda zata gansu ba”
Kallon kallo suke tsakanin hajiya da Alhaji,bakinsu har rawa yake gun jefo mata tambayar”ya sunan innar taki na Aynihi?”
“hauwa’u sunanta”ta basu amsa.
Advertisements
Rungumota hajiya tayi jikinta tana hawaye tace”tunda nake kallon fuskarki naga kamar nasanki,amma na kasa gasgata hakan,ashe ko ikai fuskar hauwa nake gani ataki fuskar,Allah mungode maka”
Daddy sosai yake murna da ganin ษiyar ฦดar uwarshi,hotunan inna nada ya nunawa zahra ayko murmushi take tana faษin”innata ce wannan dama kunsanta”
Daddy ya gabatar mata da kanshi da iyalinshi a matsayin dangin nata yamata bayanin komai,ayko itama kuka tasa najin daษin ganinsu.
Shide Muhammad abun koma masa yayi kamar a film,daga neman shawarar akaita gidan mahaukata shikenan abu ya juye ta komo ฦดar uwarsa.
Basu bar falon ba se da dare yayi sosai anata hira,sosai daddy yasaki jiki da zahra wacce yake kallo amatsayin sauran danginsa da suka rage masa a duniya.
Washe gari da safe bayan muhammad ya duba zahra,cire safar hannunshi yayi ya janyo kujera ya zauna yana fuskantarta,ita de tunda ta fahimci shine ke dubata kunyarshi takeji,da ฦyar take iya haษa ido dashi.
“zahra kin bada labarin komai naki,amma baki sanar damu wanda kuma ya miki fyaษe ba?wanda a matsayinmu na ฦดan uwanki zamu so musani”muhamnad yace cikin tattausar murya.
Hawayene ke biyo idonta a hankali tace”na barshi a matsayin sirrina,don Allah karka kuma tambayata”ta faษi cikin kuka.
Taษe baki yayi sannan yace”bazan kuma ba,amma kisani in ni baki faษa min ba dole zaki faษawa mijinki ay”yana kaiwa nan ya fice daga ษakin.
Hankalin zahra yayi ฦololuwar tashi jin furucin muhammad,tabbas dole zata sanar da mijinta wannan mugun labarin,duฦar da kanta tayi ฦasa tana kuka me tsuma zuciya.
A haka mummy ta shigo tasameta,sosai hankalin mummy yatashi janyota tayi jikinta tashiga tambayarta abinda yafaru,cikin kuka zahra tace”mummy yanzu rayuwata a haka zata ฦare kenan,bazan taษa aureba,in ko zanyi auren dole sena cewa mijina anmin fyaษe? inde hakane nida aure har abada”ta ฦarasa maganar cikin kuka.
Tausayintane ya kama mummy ta shiga rarrashinta da duk wata kalma me daษi,da ฦyar tayi shuru.
Mummy ษakin daddy taje tasameshi yana shirin fita,ganinta cikin yanayin damuwa ne yasa ya nemi guri ya zauna yace”hajiya lafiya kuwa?”
Cikin damuwa tace”Alhaji yarinyar nan na cikin damuwa gameda fyaษen da aka mata, baka ganin akwai buฦatar a binciko ko waye a hukuntashi sannan asa shi dole ya aureta?”
Shuru Alhaji yayi na ษan lokaci sannan yace”nemo ko waye beda wani amfani,fyaษe de anriga an mata,ba abinda ze sauya hakan,kuma ni modibbo inde na isa da Muhammad to tabbas shine ze auri Zahra,dan shi kaษai ze rufa asirinmu”
Mummy itama ta gamsu da bayanin na alhaji,dan haka kwarin guiwa ta ฦara bashi kan ฦudirin nasa,sabida Allah yasani tana tausayin zahra matuฦa.
Alhaji be samu zama da Muhammad ba seda dare bayan ya dawo daga gun ayki.
Lokacin daya sanar dashi hukuncin daya yanke akanshi da zahra muhammad kaษanne beyi fitsari a wando ba sabida firgici,bakinsa har rawa yake yace”daddy don Allah kayi haฦuri kabar maganarnan,nifa bana sonta,gaba ษaya zahra nawa take da har zaay batun aurenta,ni tayi min ฦanฦanta daddy pls”
Yafaษi kamar zeyi kuka.
“muhammad ba shawara fa nake nema ba,hukuncin dana yanke nake faษa maka,wannan duk raayinka ne,ba nawa ba,nan da wanne lokacine zahra zata iya warkewa gaba ษaya” daddy ya buฦata cikin haษe rai.
Jikin Muhammad a sanyaye yace “wata guda”
“nasa lokacin auranku nan da watanni biyu masu zuwa,na ษauke maka komai,kaje ka fara shiri”daddy ya faษi sannan ya miฦe yabar gurin.
Muhammad na zaune kamar wanda aka dasa,yama rasa me zeyi yaji sanyi aransa,da ace ze iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.
A Hankali ya miฦe ya nufi ษakinshi jiki a sanyaye ya faษa gado yana nazari,shide gaskiya tayi mishi ฦanฦanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaษen da aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ฦatuwa ne.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings