Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*2*
Advertisements
Gudu-gudu sauri-sauri Zahra’u ke tafiya zuwa gida,dan azahar ta kusa,
Tana shiga gida bukkar innarta ta shiga da sallamarta.
“wai har kun siyar?”cewar inna bayan ta amsa sallamarta,
Murmushi Zahra’u tayi sannan tace”wallahi inna mun siyar,yanzu ma wasu sojoji ne,suka roฦeni in dafo musu abinci,yunwa sukeji gashi suna da me ulcer acikinsu,shine na dawo in musu”daga haka ta kwashe komai ta faษa mata,gami da bata kuษin.
Sosai inna ta tausaya musu sannan tace”Allah miki albarka Batulu na, daษina dake akwai tausayi, maza zo kije ki cefano abinda yadace ayi sauri ayi musu”
Daga haka miฦewa sukayi suka fito tsakar gida,inna ta bata kuษin cefanen ta tafi.
Advertisements
Kamin la’asar sun kammala komai,abinci lafiyayye bame cewa daga rugar aka girkoshi,domin,harda,cincin,dublan,duka masu jimawa basu lalace ba kasancewar can cikin garin falgoren Zahra’u tazo cefanen,shiyasa tasamu komai.kasancewarta ฦดar makarantar gaba da primary,kuma ษangaren sciece yasa ta iya komai,sabida food and nutrition da ake koya musu.
Ga kaji da zabbi da suka soya musu rabi da mangyaษa,rabi kuma da manja sabida me ulcer shima yasamu yaci,suyar sosai tayi kyau.a ledoji ta juye sannan ta zuba abincin a kular abincin baffanta,
A babbar roba ta zuba komai sannan tayi gammo ta ษauka,inna ta bata canjin dubu biyar daya rage tace ta mayar musu,amsa tayi sannan ta juya ta nufi barikin.
Kusan mintuna arbain ta kwashe tana tafiya kamin ta iso bakin titin,sannan ta ฦarasa gurin da sojojin ke tare.
Inda sukayi dashi zasu haษu nan ta ฦarasa,ga mamakinta yana tsaye agurin yana jiranta,yana hangota ya taho da sauri ya tarbeta yana murmushi.
Kama mata kayan yayi ta sauke,sannan tace”kuyi haฦuri wallahi gidanmu da nisa ne shiyasa”
Murmushi yayi yace”Ko kaษan baki buฦatar bamu haฦuri,mune yakamata muyi hakan,mungode sosai,Allah saka miki da alkhairi,”
Canjin ta miฦo masa tace “ga canjin ku inna tace in dawo dashi,kuma tace tanawa abokin naka me ulcer ya jiki dafatan Allah ya bashi lafiya”
Sosai wani jin daษi ya bayyana a fuskarshi,aranshi ya yaba da tarbiyyarta,cikin murmushi yace”ki maidawa inna kuษin kice mungode”
Fafur taฦi amsar kuษin,duk yadda jameel yayi da ita ฦin amsa tayi dole ya maida kuษin aljihunsa,
“gobe in munzo talla zan tafi da kwanukan”tace sanda take ฦoฦarin tsallaka titi domin ta koma gida.
Sallama sukayi ta tafi,jameel yabi bayanta da kallo yana yaba natsuwarta da hankalinta.
Duฦawa yayi ya ษauki,robar abincin ya nufi tantin da suka haษa na tempol sabida ruwa da rana,kamin ay musu izinin shiga cikin barikin.
Zaune yake daga ฦarshen tantin,yana latsa wayarshi,hannunshi ษaya,riฦe da bindigarsa,
Farine sosai yana da ษan faษin fuska kyakkyawa ajin farko,sede ko kaษan ba fara’a fuskarsa.
Sanda jameel ya shigo tantin,a yatsine ya ษago kyawawan idanuwansa ya kalleshi sannan ya amsa sallamarsa.
Robar abincin ya ajiye akusa da shi sannan ya shiga ciro kayan dake ciki,
Buษe ledar soyayyun kajin yayi,sosai yayi mamakin ganin harda wanda aka soya da manja,
ฦamshin abincin ne,yasa ya ษago kansa da sauri yana bin ledar da kallo,da sauri ya matso kusa da jameel,yana faษin”kunyi waya da mummy ne?”ya tambaya cikin zaฦuwa.
“me ka gani”jameel ya tambaya.
“itace kawai take soyamin kaza da manja sabida ulcer ta,shiyasa nayi zargin kunyi wayane”
“ko kaษan,wannan wasu nasamu suka dafo mana,daga cikin garin nan,ka matso kaci abinci kasan tunda mukazo baka ci abinci ba tun ษazu hankalina be kwanta ba sabida baka ci abinci ba”
Tausayin jameel ษinne yakamashi ganin yadda yadamu dashi fiye da kansa,yasan duk ฦoฦarinnan yayine domin shi.
Ba musu ya matso yasa hannu ya ษauki cinyar kazar yasa abakinsa,daษin daya gauraye bakinsa sosai yatafi dashi,zagewa yayi yaci abincin sosai dan wannan girkin ma yafi na mommynsa daษi.
Bayan sun gama cin abincin,su cincin da dublan din duk acikin jakun kunansu suka saka,sabida taimakon gaggawa,abincin kuma rufe sauran sukayi,sabida dare.
Se a lokacin suka samu natsuwa,Jameel ne ya dubi abokin nasa yace cike da kulawa”Gaskiya Hammad yarinyar nan ta iya girki,ba me cewa ita ta girka,ji abinci don Allah sekace a birni”
Cikin rashin fahimta,Hammad ya kalleshi,yace”dama yarinyace ta dafo abincin?”
“eh yarinya ce dan bata wuce sa’ar su surayya ba,ma’ana bazata wuce 14 to 15 years ba,nono suke siyarwa na roฦeta ta girko mana”
Sosai abun yaba Hammad mamaki dan shi de in ze iya tunowa ba ya jin ko gas surayya ta iya kunnawa bare ayi zancen dafa ruwan zafi,to taya yarinya sa’arta za’ace har tafi mummynsa iya girki,ta ya?
“Dan haka in munyi settling komai zan bita inga gidansu,dan mu dinga zuwa cin abincin can gidansu mudena sata wahalar kawo mana”jameel ya faษi yana kallon Hammad ษin.
“ba damuwa “Hammad ya faษi yana nazarin zancen.
“innarta ma tace aymaka sannu gameda ulcer da take damunka “jameel ya faษi yana murmushi dan yasan bazasu wanye lafiya ba.
A fusace Hammad ya dubeshi yace”Au kace bara kaje kayi da ciwon dake damuna,amma wallahi ka cuceni kuma ba inda zani wallahi bazan je gidan nasu ba”ya faษi sanda ya miฦe ya fice daga tantin.
Muje zuwa
Surbajo for life
GIPHY App Key not set. Please check settings