Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*don Allah masu cewa asa su agroup ษinnan kuyi haฦuri ni bana adding,haka kuma bana tura novel private,iyakacina posting a group,kar ki buฦaci ษaya daga ciki ban miki ba kiji haushi,pls*
Advertisements
*3*
Har dare Hammad haushin Jameel yake ji,dan shi a duniya ba abinda ya tsana irin a faษawa stranger yana da ciwon ulcer,aganinshi kallon mayunwaci za’a masa.
Haka suka ci abincin se cika yake yana batsewa.
Koda gari ya waye,basu wahala ba cincin sukai ta ci da dublan.
Wajen azahar Hammad yafara jin yunwa,duk yadda yaso ya daure ya kasa dole ya isa ga Jameel wanda shima tun ษazu yake kallon hanya yanaso yaga ta ina zata ษullo.
Advertisements
“ya kamata fa kasamo wasu yaran abasu kuษin suje su girko mana abinci ni yunwa nakeji”hammad ya faษi sanda ya isa ga Jameel.
“karka damu nasan yarinyar jiya zata dawo,tabani tabbacin hakan,mu ษan jirata kaษan”Jameel ya bashi amsa cike da kulawa.
Hammad Juyawa yayi ya nufi cikim tantinsu,Bayan yaba Jameel ษin wayarshi ya riฦe masa.kamar jira yana barin gurin Zahrau ta ฦaraso gun Jameel ษauke da kwaryar nononta,ษaya hannun kuma ledar abincin data dafo musu,shinkafa da wake dafadukan manja taji alayyahu da albasa se ฦamshi take.
Murmushi tayi tace”duk da baku buฦata ba amma na dafo muku wannan,sabida me ulcer nan”ta faษi tana miฦa masa ledar da kular abincin take.
Da Sauri ya amsa yace”mungode sosai wallahi,shima yanzu yagama tambayarki,nace baku zoba tukunna”
Murmushi tayi batace komai ba,Wayar da Hammad ya miฦo masa ya riฦe masa ya ษaga yasa camera yace”yakamata muyi hoton tarihi ko ฦanwata?”
Zahra’u murmushi tayi batace komai ba ya fara ษaukarsu hotuna,tana dariya wani tana murmushi,har seda yagaji ya dena ษaukarsu selfie ษin.
Kwanikan jiya ya bata,dan dama suna ajiye agefenshi,sannan ya ษauko kuษi masu yawa ya bata yace”ki ajiye wannan agurinki ki dinga yo mana girkin,in sun ฦare ki sanar dani zan ฦara miki,sati uku zamuyi anan mu tafi”
Amsar ฦuษin tayi tana murmushi,ta juya tabar gurin ta ฦarasa inda suke siyar da nonon.
ฦaukar ledar Jameel yayi ya nufi gun Hammad,da hanzari,dan yasamu yaci abincin.
Ganin jameel da abincin sosai ran Hammad yayi masa daษi,matsowa yayi kusa dashi yana murmushi duk fushin da yake ya huce,yace”ta zone yarinyar?”
“Kana baro gurin tazo wallahi,yarinyar akwai kirki ga sanin ya kamata,kaga yau tun kan musa tayi tayo mana”
“naga alamar hakan”Hammad yace sanda ya ciko cokali da abincin ya danna abakinsa.
Lumshe ido yayi yana tauna abincin gashide ba nama akasa ba amma daษin abincin ya wuce inda yake tsammani.
Jameel na janshi da hira ko sauraronsa bayayi ya maida hankali kan abincin seda yaji yacika cikinsa tab sannan ya ajiye cokalin.
Kamar daga sama suka fara jiyo ฦarar harbe harbe da guje gujen mutane ana ihu.
A hankali suka fito daga tantin ga mamakinsu ankashe mutane da dama agurin musamman ฦดan talla da suka zo.
Harbin ne yafara yo ษangarensu,da gudu suka nufi bayan wani dutse,hankali atashe,Jameel a firgice ya kalli hammad yace”ฦดar filanin nan data dafo mana abinci tana gurin can,bari inje in taimaka mata kar wani abu yasameta”
Yayi yunฦurin zuwa harbin ya yawaita dole ya tsaya,guri yayi guri domin tankokin yaฦi aka fito dasu daga cikin barikin aka fara ษarin wuta tsakanin sojoji da ฦณan bindigar da suka kawo hari garin,dan tuni sun shiga cikin rigagen sun ฦona komai sun kashe mutane,shine suka dawo nan bakin titin.
A gigice Jameel yaja hannun Hammad suka ruga da gudu zuwa cikin jejin domin su samu mafaka,sede ฦarar da jameel ษin ya kwalla ce tasa Hammad tsayawa ya waiwayo yaga me ya samu aminin nasa,
Wayyo Allah harbinsa akayi agadon baya,rungumeshi yayi suka faษi tare,ya tallafoshi yana ฦarajin kiran sunanshi,”No!!!!!!!! Jameel !!!!!!!! wake up!!!!”!!”yana ihun jijjigashi,Jameel wanda idonsa ke shirin lumshewa a hankali yace”ka kula da ฦดarfilanin nan Hammad”yana kaiwa nan yafara salati jini na fitowa ta bakinsa.
A gigice yake jijjigashi amma ina jikinshi ya riga ya saki.
Ihu Hammad yake iya ฦarfinsa yana jijjiga aminin nasa,yana kiran sunanshi,amma shuru,
Harbin da ake yowa ta ษangarenshine yasa ya miฦe da gudu,ฦauke da Aminin nasa a kafaษa ya ฦara nausawa cikin jejin,zuciyarshi na masa zafi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings