Advertisement
ππππππππ
*TAYI MIN ΖANΖANTA*
ππππππππ
*Zahra Surbajo*
*6*
“Ζ΄arfillo!!!!!!!!!”ya ambata da Ζarfi sanda ya farka a gadon asibiti yana laluben ta,faΙowa yayi daga kan gadon yana ihun kiran sunan ta.
Advertisements
Da sauri sojojin dake kula dasu suka zo suka riΖeshi,dambe yake iya Ζarfinshi yana kiranta,”Ζ΄arfillo kina ina,ki zo nan kusa dani,kar kimin nisa,don Allah kiyi magana injiki,kitaimakeni kiyi magana mana,nace kiyi haΖuri,ko baki yarda dani bane,nace zan kula dake,zan Ιaga darajarki fiye da ta kowacce mace me gata”sambatun da Hammad yake kenan sanda ya farka a asibiti.allurar bacci aka masa ko zaa samu sauΖin sambatun.
A can sansanin Ζ΄an gudun hijira ko masu kawo sadakar abincine suka zo dan haka kowa da gudu yaje ya hau layi,banda Zahra wacce cinyoyinta ke mata mugun ciwo,zaune take ta kife kanta akan guiwowinta tana kuka,
Haka aka gama rabon abincin ita bata samuba,se hanne ce ta sammata nata.shima daΖyar ta iya ci sabida bakinta Ιaci yake mata.
Haka suka kwashe tsawon kwanaki uku,Zahra zuwa lokacin bata iya ko tafiya sede rarrafe,ga wani ruwa data rasa ko na menene dake bin cinyoyinta.tayi kukan tayi kukan har ta gaji.gashi ba suturar arziΖi ke garesu ba haka take zaune Ζuda na bin ta.hanne kanta yanzu ta gujeta sabida warin da zahran take.
Duk sanda zaa kawo abinci zahra bata samu sabida Ζyamarta da akeyi,hakan ne yasa take fita daga sansanin da rarrafen taje,bakin titi tayi bara dan ta samo abinda zata ci.cikin ikon Allah kuma tana samowar seta koma gefe taci ta Ιoye sauran.
Acikin sati biyu duk wanda yaga Batulun inna bazece ita bace,gaba Ιaya ta sauya,tazama abar tausayi.
Advertisements
Acan kaduna ko,lamarin na hammad ba sauΖi,dan gaba Ιaya kwakwalwarsa tasamu matsala,a birkice yake,arana seya kira Ζ΄arfillo yafi so dubu,kuma yana dukan duk wanda yazo kusa dashi.
Hakanne yasa aka nemo iyayenshi sukazo aka basu shi domin suje su nema masa lafiya.
Allah sarki,a ΙaΙΙaure aka sashi a mota sabida dukan da yakeyi,shima seda aka masa allurar bacci sannan akai nasarar fita dashi.
Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Hammad,me hamshaΖin me kuΙine,wanda sunanshi ya kewaye ko ina a Ζasar nan harma da Ζasashen Ζetare.Ζ΄aΖ΄anshi biyu Hammad da Surayya,se matarsa hajiya maryam,dukansu asalinsu Ζ΄an gombe ne.
Alhaji ba abinda yakeso a duniya sama da Ιansa Hammad,duk wani buri nasa na duniya akan Hammad ya Ιorashi,lokacin daya ga halin da Ιan nasa yashiga kuka yake da idonsa kamar Ζaramin yaro.dan shi dama a dole yabar Hammad ya shiga aykin soja,dan kawai ya nuna yana sone.
Hammad matashine Ιan kimanin shekara 30 da haihuwa,bayan kammala karatunsa na secondry,mahaifinshi oxford university ya tura shi inda ya karanci gynocology,wato likitan mata,inda yasamu sakamako me kyau bayan kammala karatun.
Lokacin daya dawo gida nigeria,seya samu Ζasar na cikin yanayi na fama da rashin tsaro,ana kashe mitane basuji ba basu gani ba,wannan dalili ne yasa Hammad da Amininsa jameel suka faΙa aykin soja,wanda mahaifin hammad yasaki Ζ΄an mazan kuΙi aka basu manyan muΖamai,bayan sun samu horo na musamman asansanin sojoji dake NDA kaduna. sunason taimakawa Ζasarsu da dukkan Ζarfinsu.
Wannan kenan.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings