Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*7*
Advertisements
*Bayan shekara ษaya*
“Modibbo ษiyata zata mutu a sansanin ฦดan gudun hijira,kataimaketa!!!! kataimaketa!!! kataimaketa!!!!!!!!!”
A Razane ya farka daga baccin da yake,wani gumine ya karyo masa me zafi,gudun AC dake ษakin ya ฦaro,sannan ya samu guri yazauna yana tunani gameda mafarkin da yake yi da Hauwa ฦanwarsa,wacce sanadin faษan da akayi a garinsu yasa ta ษace wanda sunyi cigiya har sungaji.
To shi wannan mafarkin da yake da ita me yake nufine,yau kusan kwana uku kenan seyayi mafarkin,ษiyarta to dama ta haihune ko ya abun yake,a iya saninshi hauwa nada matsalar rashin haihuwa,kuma mijinta ankasheshi a faษan da akayin.
Haka de yayi zugum shi kaษai a ษaki yana tunani,to shi wanne sansanin ฦดan gudun hijira zashi,?taya ze iya gano ฦดar da be san kamanninta ba,?to bama wannan ba shin mafarkin gaskiya ne?wainnan tambayoyi sune ke yawo a kansa da ya rasa amso shin su.
Haka ya kwana be runtsa ba,da gari ya waye bayan yayi sallar asuba ษakin matarsa ya nufa,
Advertisements
Da faraarta ta taso ta tarbeshi,bayan sun gaisa ne,tace cike da kulawa”Alhaji naga kamar kana cikin damuwa?”
“Hajiya kwana biyu ina cikin damuwa,hauwa kullum se tazo amafarkina tana cewa in taimaki ษiyarta,a sansanin ฦดan gudun hijira ni na kasa gane kan wannan lamari wallahi”ya faษi cike da damuwa.
“ka kwantar da hankalinka baban Muhammad,wataฦila akwai wani abu me muhimmanci gameda mafarkin nata nide ashawarata da ka fara duba sansanin ฦดan gudun hijirar kagani ko wani taimako suke buฦata yasa hauwan ke zuwa ma a mafarki”
“kema kin kawo shawara hajiya,zanyi hakan in yaso duk week end na dinga zagayawa guraren da ฦดan gudun hijirar suke,dan abun akwai ษaure kai wallahi”
Haka de suka gama jajantawa modibbo ya miฦe ya fice zuwa ษakinshi,wanka yayi ya kimtsa sannan ya dawo dinning suka ci abinci,agurin cin abincin ne yace “Munyi waya da Muhammad ษazu ya shaidamin ฦarfe biyu na rana zasu iso, kuma hajiya babba jikinta da sauฦi,shiyasa ze taho,ki tanaji komai,ni zan fita,zan jima kan in dawo”
murmushi Hajiya tayi sannan tace”lalle Muhamnad yaci saa da hajiya babba ta barshi yataho,ita da tace se ta masa aure sannan ze dawo”
Dariya sukayi irin ta girma sannan yace”hala ta masa matar ne shiyasa tabarshi yataho”
Miฦewa yayi yana kallon agogon hannunsa yace”hajiya bari in ฦarasa office,zamuyi waya,in kuma naga da lokaci zan ษan leฦa sansanin ฦดan gudun hijira dake nan kusa”
A dawo lafiya tay masa sannan ya fice da hanzari,bodygurd ษinsa suka mara masa baya.
ฦarfe huษu modibbo ya baro office,bayan yayi sallar la’asar,kai tsaye wani gidan abinci ya nufa, domin yaci abinci kamin ya wuce sansanin ฦดan gudun hijirar.
A kan idon Zahra motocinsa suka faka,tana can ษayan gefen titin,da ษan saurinta ta taho tsallako titin dan tasamu tayi bara agunsu ko zasu taimaka mata,dan kwananta biyu yau bata ci abinci ba,agalabaice take ga ulcer ta data tashi,yanzu ko gabanta ya koma ciwo,yana fitar da wani wari me ษaga hankali,ko giftawa kayi ta gunta se kaji warin,shiyasa duk inda tayi ake korar ta,hakanne yasa take samun kan bola tayi zamanta,gudun kar akoreta.
Cikin rashin sani mota tayi ciki ciki da ita lokacin da take ฦoฦarin tsallakowar.
ฦarar burkin motar ne,yaja hankalin mutane da dama, ciki harda modibbo dake ฦoฦarin shiga gidan abincin.
Da gudu me motar daya bugeta yabar gurin be tsaya ba.
A Hanzarce Modibbo yayiwa bodygurd dinshi umarnin su ษauko wanda aka buge susa a mota,
Hakan sukayi,sede warin da takeyi ne,ya hanasu kuma shiga motar da sauri suka ja baya har modibbo ya ฦaraso.
Warin shi kanshi ya ษaga masa hankali,shiyasa be tuhumesu me ya hanasu shiga motar ba.
Tsayawa yayi shima yana nazari kamin ya ciro waya ya kira matarsa kasancewarta likita,tana ษagawa yace”Hajiya akwai emergency yanzu wani ya buge wata mahaukaciya kuma ya tsere,in kaita asibiti ne zaki je yanzu ko in kawota gida?”
“Gaskiya ka kawota gida sabida muhammad be daษe da dawowa ba bazan iya fita in barshi ba,amma in kukazo naga yanayin lalurar dole se anje asibitin semu tafi”.
Yana kashe wayar ya faษa motar da kansa yaja,da gudu suka shiga sauran motocin suka mara masa baya zuwa gidan.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings