Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*8*
Advertisements
A harabar gidan yayi parking,tun kan ya gama tsayawa Hajiya da Muhammad suka fito,cike da damuwa yafito daga motar,sannan yayi umarnin da a ษaukota akaita boysquater dake gidan.
Ba musu masu tsaron lafiyar tashi suka ษauketa kamar yadda ya buฦata,ba hajiya ba hatta Muhammad ya kaษu dajin warin da takeyi,haka aka wuce da ita ciki.
Jummai da Asabe Masu aykin gidan hajiya ta kira bayan sunzo tace”ku kwashi kayan wanka maza kuje kui mata wanka,ku tabbatar da cewa komai na jikinta kun wanke ganinan zuwa”
Amsawa sukayi da sauri suka wuce aywatar da abinda tace.kallonta takai gun Muhammad wanda gaba ษaya Babu annuri a fuskarsa tace”Muhammad bari inje in dubata bazan jimaba zan dawo”
“Mummy wannan warin fa ze iya cutar dake,gaskiya da aba direba ita yakaita asibiti,nan akwai matsala”ya faษi cikin yanayin damuwa.
Advertisements
“karka damu bari in dubata ba abinda ze sameni”ta faษi sannan ta juya ta bi bayan su jumman.
Se a lokacin Muhammad ya ฦarasa gun mahaifinshi yana murmushi ya ษan rusuna yace “sannu daddy”
Dafoshi yayi yana murmushi yace “Yauwa ษan gidan daddy ya hanya,ya kuma hajiya da jikin”
“hanya Alhmdllh,hajiya kuma ta warke sosai”
Daga haka suka shiga ษan taษa hira kaษan suna jiran hajiya ta fito suji in agidan zata diba mara lafiyar ko asibitin zaa tafi.
Hajiya lokacin data shiga toilet ษin kusan kukane yakusa kwace mata ganin yadda gaban mara lafiyar ke shirin lalacewa.
Safa tasaka sannan ta tara ruwa me zafi,tasa detol,sannan ta tsomata acikin ruwan ta fara wanke gurin,wayyo Allah na gurin yauฦi yake gashi har wani kore kore yake,ga uban wari.
Hajiya na fara wankewa tsananin azabar da zahra taji yasa ta farkawa daga suman da tayi ta kwalla wata ฦara.
A gigice Daddy da Muhammad suka nufi boysquater ษin,sede suna shiga jummai ta dakatar dasu a falo ta hanyar shaida musu wanka ake mata.
Kimanin awa guda Hajiya ta kwashe tana sauya ruwa tana wanke gurin Zahra kuka take iya ฦarfinta tana kiran sunan Allah.
Kan kace me tuni wannan azababben wari ya tafi se ษan wanda baa rasa ba,doguwar riga ta marasa lafiya hajiya tasa mata sannan suka ษaukota zuwa ษakin da hajiya ta ware domin kula da marasa lafiya na gida,ba abinda babu aciki.
Kan gado ta ษorata,sannan ta fara wanke duk inda taji rauni sakamakon bigeta da mota tayi.seda tagama tsab sannan ta buษe gaban nata ta kawo fitilar likitoci ta haska,sosai tausayinta ya kamata,wannan sashin ba ษangarenta bane shiyasa bata fahimci ko matsalar menene ba.
Kashe fitilar tayi sannan ta rufeta,tasa jummai ta kawo mata abinci,ayko kamar tsohuwar mayunwaciya haka takecin abincin har ta cinye tasha ruwa,
Magunguna hajiya ta bata,sannan ta kwantar da ita ayko kamar jira bacci yayi awon gaba da ita,sosao tausayinta ya taษa zuciyar hajiya,yarinya ฦarama amma ta haษu da matsalar taษin hankali,dan atunaninsu su dika mahaukaciyace.
Falo ta dawo gun su muhammad da Alhaji tace cikin damuwa “Alhaji ni nayi nawa,sede yarinyar nada matsala a al’aurarta,shine nake ganin ko de A kaita Hammad Hospital ne,kaga can akwai kayan ayki zata fi samun kulawa,tunda can dama na ษangaren mata ne”hajiya tace cike da damuwa.
“wanne irin Hammad hospital,menene zaay mata acan wanda ษanki Muhammad baze iyaba,ko kin raina kwarewarsa ne,da har kike cewa akaita wani guri bayan ga abu agida”cewar Alhaji yana duban Muhammad.
“Mummy zan dubata ingani insha Allahu baze gagara ba,abinda zaay mata a wancan asibitin nima shi zanyi insha Allahu”cewar Muhammad.
juyawa hajiya tayi yabita abaya zuwa inda Zahra take kwance tana bacci.
Safa yasaka a hannu sannan ya kunna fitilar likitoci ya matsa da ita gabanta hajiya ta buษe masa gaban na zahra.
A Hankali ya duฦa yana kallon gurin,yasa hannu ya ruฦo wannan tsoka dake lilo itama ya ฦare mata kallo, tsawon mintuna arba’in ya kwashe yana karantar gurin sannan ya ษago ya cire glass ษin fuskarsa,sosai damuwa ta bayya na a fuskarsa idanunsa sukayi ja,tsigar jikinshi har tashi take yace “mummy fyaษe aka mata,kuma a ฦalla ya kwashe watanni da yi matan,kuma anji mata ciwo agurin,wanda sanadin hakan ta kamu da yoyon fitsari,ga infection me ฦarfi daya kama gurin wanda in baayi da gaske ba ze iya rikiษewa yakoma cancer”
.Salati mummy tayi sannan tace”oh ni jamaa yaushe zasu fara tsorom Allah ,yarinya ฦarama a haike mata wannan wanne irin cin zarafine”
“mummy muje inyi list na abinda zaa buฦata,dan akwai buฦatar ayi mata ayki yau ษinnan ayi mata plushing ษin infection ษin sannan a ษorata akan magani”cewar Muhammad bayan ya cire safar dake hannunsa ya wanke Hannunsa suka fito ransa Aษace ya rasa dalili,ko kaษan baya ฦaunar akawo masa yara an musu fyaษe ransa ษaci yake ji yake da ze ga wanda ya aykata musu ba makawa seya kasheshi .
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings