TAYI MIN KANKANTA 9

Advertisement

 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

  *TAYI MIN ƘANƘANTA*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*Zahra Surbajo*

Advertisements

*9*

A daren duk abinda ze mata yayi mata,iya azaba zahra tasha ta,duk wanda yaganta seya tausaya mata,haka ya gama komai,sannan ya barota kwance kamar matacciya.

Ɗakinshi ya wuce kai tsaye kan kujera ya faΙ—a yana maida numfashi,wayarshi tayi Ζ™ara da sauri yakai idonsa gurin,Amininsa kuma babban likitan mata na asibitin Hammad Hospital,shi ke kiransa.

Ɗagawa yayi ya kara wayar a kunne yace “ya kake?”

Daga can Ι“angaren ya amsa masa “kaganni wallahi se yanzu zan bar office,tun safe ina asibiti har na gaji,”

“munyi Ι—aya kenan,nima yanzu fitowata daga wani aykin gaggawa kenan?”

Advertisements

“Wallahi da naso in shigo gidanku yau sabida gobe weekend,inaso in je falgore dubo Ζ΄arfillon nan inga ko zaa dace,to se kuma ayki ya riΖ™eni,dama so nike in ce ko zaka rakani”

Murmushi muhammad yayi me sauti sannan yace”na gaida na Ζ΄arfillo,Allah de ya yanke maka wannan wahalar,”

Dariya dukansu sukayi,sannan daga can Ι“angaren yace “aboki bazaka gane bane,wallahi ina matuΖ™ar tausayawa yarinyarne shiyasa”

“Na jima da fahimtar hakan,kaga in Allah yasa ka ganota kuma kaga tayi kalata kaga shikenan seka aura min ita,adena cemin gouro”muhammad yafaΙ—i yana dariya.Dan yasan ya tsokano abokin nasa,ilai kuwa bece komai ba ya kashe wayar.

Wata dariyar muhammad yayi sannan ya ajiye wayar ya miΖ™e ya shiga wanka dan jikinshi duk ciwo yake,danma mummynsa na gurin tana taimaka masa.

Tsawon watanni biyu zahra ta kwashe Muhammad ke kulawa da ita,zuwa yanzu Ζ™afa tasamu tana tafiya kaΙ—an kaΙ—an.

Sosai take samun kulawa agurin mummy,safe darana da yamma ita ke mata wanka,ga ruwan zafi datake yawan sata aciki ta zauna.

Zahra farinta yasoma dawowa ga wata Ζ™iba da tayi kamar ba mara lafiya ba,yanzu komai takeso tana samu,sede ba uhm ba uhm uhm ido kawai take binsu dashi ko wanne lokaci.

Yau zaune suke ita da hajiya a falo tana bata kankana tana sha,Muhammad ya shigo falon,bayan sun gaisa da hajiya ya dubi zahra sannan yace “hajiya jikin yarinyat nan da sauΖ™i,yakamata akaita asibitin mahaukata aduba lafiyar kwalwalwarta,shurun tayi yawa”

Kamar jira yana saukewa zahra cikin muryar marasa lafiya tace”lafiyata Ζ™alau ni ba nahaukaciya ba ce”

Ba muhammad da hajiya ba hatta daddy dake Ζ™oΖ™arin shigowa falon yayo mamakin maganarta.

Muje zuwa

Surbajo for life.

Leave your vote

-4 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

TAYI MIN KANKANTA 3

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *don Allah masu cewa asa su agroup Ι—innan kuyi haΖ™uri…

TAYI MIN KANKANTA 32

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *To sabon sauyi acikin tafiya,😊akwai sabon novels Ι—ina dazan saki…

TAYI MIN KANKANTA 20

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *nace muku bana adding mutane a group,kuma bana tura novel…

TAYI MIN KANKANTA 10

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *10* Advertisements Murmushi mummy tayi ta dafo kanta tace “Ι—iyata…

TAYI MIN KANKANTA 1

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako,mazan su da matansu,alherin Allah…

TAYI MIN KANKANTA 6

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *6* “Ζ΄arfillo!!!!!!!!!”ya ambata da Ζ™arfi sanda ya farka a gadon…