Advertisement
*_Mamuhgee 34_*
********************
Suna shigowa gidan farhat tafara tarbonsu da gudu ta fada jikin afia tana Dan bayyanarda tsoronta afili tace”
Afia mum tazo tana ciki tundaxu da kuka fita……
NURU data jefa qafarta Palo ta tsaya cak Jin abinda farhat tafada zuciyarta na dakatawa na ‘yan mintuna kafin ta daga fuska tana kallon cikin palon da Babu kowa ta danne tashigo tareda nufar dakinsu direct tana shiga ta sa sauke ajiyar zuciya ahankali tareda fitarda numfashi ta nufi table din dake
tsakiyar sofas din dakinsu ta ajiye shopping bags din hannunta ta zare qaramin gyalen dake kanta ta cire kayanta ta dauki towel ta nufi toilet tayo wankanta tareda alwala ta fito tashirya cikin riga da wando dogo marasa nauyi tazo ta tayarda sallah har lokacin afia Bata shigo dakinba.
Advertisements
Saidata idar da sallah tayi adduointa ta miqe ta kwashi bags din tasaka cikin wardrobe ta dauki hula tasaka akanta ta fice zuwa kitchen neman abincin tana Dan Jin yunwa.
Kodata fita Palo farhat na zaune ita kadai tana ganin NURUn ta taso tana cewa’
Aunt yunwa nakeji.
Da kulawa ta waiwayo ta kalleta tareda Kama hannunta suka nufi kicin tana cewa”
Sweetie Nima yunwa nakeji muje muga me Fana ta dafa.
Suna Shiga ta dudduba taga tuni angama jere komai a dining ta dauko musu melon drink suka dawo dining din suka zauna tafara zubawa farhat kafin tazuba suka faraci tana kallon yanda farhat din keci alaman taji yunwa sosai ta zuba Mata drink din a cup ta miqa Mata tana cewa”
Advertisements
Sweetie tunda Kika dawo school bakice abinci bane?
Gyada Mata Kai kawai tayi tana cewa”
Dana dawo mum Sarah zata kawomin saiga mum shine tace ta ajiye komai taje ayi Mata gyaran dakinta daganan banci komaiba.
Murmushi NURU tasaki tana cewa”
Shikenan yanzu kici abincin bazan qara Bari kiji yunwa hakaba Inshallah baby.
Suna cikin ci wani sabon qamshi ya doso dining room din Wanda ta tabbatarda kila lailah ce ke zuwa Dan haka saita dauki ruwa Tasha dama tagama saita miqe tana cewa farhat”
Sweetie nagama idan kingama kisameni Palo muyi kallon cartoon.
Juyawa tayi daidai shigowan lailah sanye cikin wata straight doguwar riga data tafi daidai tabi jikinta kanta a daure da band tana zuba kamshi hankalinta kwance tashigo tana ganin NURUn ta tsaya kallonta daga qasa zuwa sama sbd NURUn riga da wandone ajikinta dasuka sake maidata yarinya qarama sbd rigar Kamar shimi take sai wandon daya wuce gwiwa sosai Amma bekai qasa ba,
Fuskarta ta kalla taga yanda take wani maiqon kyan fata da gyaran datake samu tareda nutsuwa datake ciki datake qarawa mutum kyan fata.
Kallonta NURU tayi fuskarta Babu wani sauyi akai tace”
Barka da zuwa.
Kamar lailah bazata amsaba saidai ta dakata tareda juyowa ta kalli NURUn tace”
Karki sake zuwa dining cin abinci dagani sai ‘yayana da mijina muke hawa dining a gidan Nan
Idan ada kina hawa yanzu nadawo banason tarkacen da hayaniya ki tsaya inda bazan ganki ba kafin me MALEEK din yadawo kisan matsayinki.
Tana Gama fadar hakan ta wuce ta nufi dining din tana cewa farhat ta tashi taje takira Mata fana tazo tayi serving dinta.
Aje spoon farhat tayi ta sauka daga kan dining din ta nufi dakin mum Sarah tafada Mata sbd Bata taba bi ta hanyar kicinba taje bangaren masu aikinsuba tunda take.
Daga gurin mum Sarah sidadawa tayi Takoma dakinta Bata koma dining ba.
NURU kuwa tunda Lailah tagama maganganunta ta juya ta fice Bata ce kalaba ta nufi Palo tayi zamanta tana kallo tana gani farhat tazo ta wuce dakinta batai yunqurin bintaba sbd gudun mum dinsu tace Kuma ga wani salon saitaci gaba da kallonta tana kallo afia ta fito ta nufi dining fuskarta ba wani walwala da alamar itama mum din batai Mata da Dadi ba.
Tana Nan zaune lailah tagama tafito ta wuce sama batareda ta lura da NURUn a Palonba datayi magana kila.
Sai guraren goma ta miqe ta nufi dakinsu tayi tayi duk abinda zatayi tazo gefen afia ta kwanta tareda rage hasken dakin sosai tanajin motsin afia din wadda da Alama batai bacci ba kwancen kawai take.
Bata Jima da kwanciyarba bacci ya dauketa Bata farka ba sai bayan asuba har gari yafara haske ta tashi tana miqa ahankali ta wuce toilet tayo brush da alwala tafito ta tada sallah.
Bayan tagama ta miqe ta nufa dakin farhat ta tada ita tayi sallah kafin tafara Mata Shirin makaranta suka Gama ta fito ta nufa kicin ta hada Mata breakfast dinta sukaci tare kafin aka tafi Kai farhat din school itakuma takomawarta daki ta kwanta ta shige bargo ta Dora sabon bacci cikin kwanciyar hankali.
Har Rana tayi Fana na aikin abincin safen aikin yaki karewa sbd kalolin abincin da lailah tasaka a daddafa din Wanda tasaba idan zataci abinci tafison ayisu kalolo daban daban sbd taci Wanda taga tanada raayinshi sukuma yanzu sun Saba aikin abincin gidan akan kaida akeyinsa tunda NURU tafara Aiko a kicin din gashi tun bayan tafiyar maleek NURU ta cire hannunta a aikin abincin iyakacinta ci idan anyi kamar kowa.
Koda ta farka ta bude idanuwanta taga afia zaune a dakin tanashan Cocoa Krispies da Madara ta mamaki take kallonta tana tashi zaune tace”
Afia yanzu da Rana kike Shan Krispies nagama bakyashansa be damekiba.
Kallon NURU afian tayi tana Kai spoon bakinta tace”
Yunwa nakeji ne sosai kodana tashi kaman naci Rami acikina sbd jiya da daddare banwani ci abinci ba juice kawai nasha bayan hakama ace haryanzu a gidan Nan ba’a Gama breakfast ba sai kace wasu celebrities dakecin abinci akan lokacinda suke zabarwa kansu bazan iya jiraba.
Murmushi NURU tayi tana cewa”
To kodai fana batada lafiya ne da aikin yakaita haryanzu?
Pass 11 fa.
Sanin dalilin hakan yasa afia batace komaiba taci gaba dashan abindake gabanta tana cewa idan nagama asibiti zanje Nanda 4 days zamu fara zuwa session training dinmu yaushe ne naku?
Tana saukowa gado ta nufi mirror tana cewa”
Namu sai next week Nanda kusan 10 days ma Amma Nima may b kwanakin Nan nafara lekawa court din.
Toilet ta nufa tashige tana cewa idan kinfita zanmiki texting din sunan wani littafi kizomin dashi idan Zaki dawo.
Wanka tayi tana fitowa daureda towel tana goge kanta da ruwa yadan jiqa ta alamar afia din ta fita ta nufi mirror kenan zata zauna aka shigo dakin ta Bata waiwayoba ta cikin madubin taga lailah wadda takusa hadiyar zuciya ganin NURUn a Haka sbd fatarta dake wani irin daukan ido sbd zamanta fresh ta kanne tareda dan yamutsa fuska ta kalli cikin dakin taga afia Bata Nan ta maido ta kallonta kan NURU dake abinda ke gabanta tace”
Karkicemin anan dakin kuke zama tareda afia?
Waiwayowa NURU tayi ta kalleta sai tace mata”
Barka da shigowa”tayi skipping wancan tambayar tana kokarin dauko Kaya tasaka ajikinta.
Sake kallonta lailah tayi tana cewa”
Wane irin toshewar Kai ne zaisa ki zauna a dakin AFIA bayan dakunan dake gidan Nan gasucan kusa Dana Sarah Amma kinzo nan kin gwamutsa ta Yaya mutum biyu zasu zauna daki daya a matse wani na shaqan numfashin wani wannan masifa ne cuta na shigowa ciki.
Wannan karon tsayawa NURU tayi kallonta sbd tasamu fahimtar me mum dinsu afian ke nufi Dan dai ita abin yafara gundurarta Matar tacika tsirfa.
Fara hasala da kallon da NURU ke Mata Kamar wawuya lailah tayi tace”
Ba’a kallo Haka idan Ina magana ba sa’arki ke magana ba Matar uban gidankice ke mgn.
Hakan data fada yasa NURU kallonta gabaki daya saidai har lokacin Bata ce komaiba kafin ta juya ta dauki kayanta tafara sanyawa lailah taqara harzuka sbd ganin Kamar NURUn ta maidata hauka kawai takeyi saita dauki towel din afia ta riqo hannun NURUn dashi tajawota ta fito da ita dakin tasawa dakin key ta zare ta kalli NURUn tana Dan yamutsa fuska tace”
Next time idan Ina mgn saiki saurareni da kyau,
Kije dakunan dake kusadana Sarah ki dauki daya wannan banason tarkace ko gwamutsetse atareda yarana ciwo zai iya shiga.
Wucewa tayi tabar NURU a tsaye daga ita sai towel tayi shiru batareda tace komaiba har lokacin sai kawai ta juya ta nufi dakin farhat tashige Allah yasa tanada wasu Kaya adakin na farhat saita Sanya duk Dana shan iska ne saita fito taje kicin ta dauko drink da biscuits tadawo daki taci tayi sallah ta haye gadon dakin tana juya wayarta tanason kiran jekadi Amma saita fasa ta ajiye wayar.
Sai yamma afia tadawo ta tararda dokar mum dinta ta girgiza matuqar gaske ta kalli mum din zatayi magana mum din tayi Mata wani kallo tana numa Mata kofa sbd batason dogon zance bare hayaniya.
Koda afia ta fito dakin farhat ta nufa Kai tsaye sbd tasan NURUn na can tana shiga ta taddasu zaune kan kujera suna game da farhat hankalinsu kwance suna dariyarsu.
Wani iri taji na rashin Jin Dadin abinda mum dinta tayi Amma bazata iya take maganartaba sbd duk yanda take kaunar NURU mum dinta mum dintace saita kasa shigowa ta juya zata wuce NURU data lura da ita kalleta tace”
Charger na kawai nake buqata a dakin sai laptop Dina.
Tsayawa afia tayi tareda juyowa ta kalli NURUn taga ba damuwar komai akan fuskarta ta dake itama tace”
Ok zan Aiko mum Sarah takawo miki.”tajuya ta tafi tabar gurin suka cigaba da abinda sukeyi zuciyar NURUn a dake Taki Bari abinda takeji ya rusata.
Koda dare yayi daqyar NURU ta iya rintsawa sbd dokokin lailan sunfara tsauri sbd ko dining din suna Gama cin abinci aka rufesa
Mum Sarah duk hankalinta ya tashi NURUn ta nuna Mata bakomai kadata damu Takoma daki ta kwanta.
Washe gari bayan tafiyar farhat school ma haka tashiga wani sabon cin zarafin ta daure dai Bata cewa komai bare ta tanka qarshe dai futa tayi taje restaurant taci abinci dagacan tace driver ya wuce da ita wani guri acan ta wuni sai qarfe bakwai tadawo gidan tana dawowa ta shige sbd komai na gidan da doka da iko sundawo qarqashin Lailah tadawo da duk qaidojinta da kaf masu aikin suka Santa dasu cikin kwana biyu ta dawo LAILAH MALEEK dinta Dan kuwa tani kowa yasake shiga taitayinsa.
NURU kuwa tsananin yafara Mata yawa Dan kuwa ko ruwan gidan Idan bana toilet ba batada ikon ganinsu bare tabawa Kullum tana daki idan taji yunwa ta fita taje taci abincinta qarshe dai abin duniya ya isheta sbd cin zarafi da ikon lailah yayi yawa Dan yanzu drivernma ta hanashi sake daukan NURU Dan Haka kwana biyu tana daki ga ciwon Mara tun jiya daya sakota gaba sai kawai ta sayi ticket din komawa gizah ta waya.
Tana kwance ciwon mararta yafara tsananta Mata ta tashi zaune riga da wandon baccin safene a jikinta qananu tun na safe Bata tashi tacireba tana dungule cikin gashi yau weekend ne farhat na gida duk taqara hanata sakat da hayaniyarta shiyasa duk Bata cikin nutsuwarta.
Tashi zaune tayi ta kalli farhat tace”
Farhat kije kifadawa mum Sarah takawomin tea me lemon.
Tashi farhat din tayi ta fita da gudu taje tafadawa mum Sarah ta jira Dan agama su taho dashi tana Taya mum Sarah fira.
Mum Sarah duk hankalinta ba kwanceba ta hadawa NURUn tea din tareda sabon cupcakes datayi yau da safen ta hado Mata a qaramin tray ta miqawa farhat din tana cewa”
Farhat ki riqe da kyau kije ki kaiwa aunt dinki kafin mum dinki tafito ko.
Karna farhat tayi ta fito tana tafiya ahankali sbd kada ya zube ta nufi hanyar Palo zuwa dakinta
tana kaiwa tsakiyar Palo sukai kicibis da mum dinta tafito cikin shigar Kuwait gown tana kamshi fuskarta taji kwalliyarta kamar ko yaushe sirrin kyau sai fita yake a fuskar.
Firgici da tsoro yasa farhat sake tray din ya zube Mata gabaki daya a qafa tasaki wani razanannan ihun da duk yasa kowa fitowa musamman NURU data qaraso daqyar da saurinta tayi kan farhat din ta kamota zata duba Lailah ta tareta da hannunta tareda turata baya cikin bacin Rai takalli su mum Sarah tace”
Tashin farko Wanda yayi wannan aikin da Wanda za’a kaiwa nakeson ji.
Tsit sukayi Wanda yasa ranta sake baci ta juyo ta kalli NURU dake kallonta wannan karon cikin qarewar hakurinta.
Tace”
Me kikeyi a dakin dakika fito?
Nace kibar dakin afia shine Kika koma na farhat kina tunanin cutar datasa na koroki daga dakin afia banawa farhat guduntane?
Sarah so nawa zanfada miki dokikina da tsarina acikin gidan Nan?
Kije dakin farhat Dana afia duk wani trash na yarinyar Nan akwasosu yanzu yanzun nan akaisu guestroom.
Dauke wuta dukkaninsu sukayi kowa yakasa motsi afia dataga abin na neman yawa ta matso gurin mum din tace”
Mum Dan Allah ki kyaleta tunda kin hanata zama dakina kince adaina Mata komai ko Bata komai
Mum harfa Edward kin hasa ya dauketa da mota yafita da ita
Mum Dan Allah kadaki kaita guestroom this is too disrespectful Koba komai Matar dad ce……wani lafiyayyan Mari ta saukewa afia dayasa dawowa cikakken hayyacinta na sanin mum dinsu tabbas tasamu matsala kila.
Cikin tsawar lailan tace”
Ki fito da kayanta yanzu Nan nace….
Gyaran murya mr Omar yayi daga bayansu dukkaninsu suka juyo kowa na dauke wutar Shiga firgici musamman afia data juyo gabaki daya gabanta da mugun harbawa
Su mum Sarah kuwa kowa rawar jiki ya dauka suna sauke kawunansu.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_๐๐๐
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
ฦaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐๐
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐๐
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐๐
0903 234 5899
GIPHY App Key not set. Please check settings