UBAYD MALEEK 40

Advertisement

 

***************

Tun ranarda jekadi tadawo labarin dawowarta ya Isa ga neges suka tsaya jiran Jin wani labarin dazai fito daga gareta Amma shiru ba wani zancen komai karshema daya bugi cikin Anneti saiya samu labarin maleek na Nan kalau daganan suka lalibi padima  sai sukaji shiru babuta Babu labarinta amed yayi neman wayarta harya gaji Bata zuwa Nan abin ya daure musu Kai, Nan yakoob mahaifin amed neges yasakashi tsananta bincike akan al’amarin sbd ‘batan padima Kai tsaye na nufi da akwai matsala babba sbd ko yayane dai tasan sirrinsu Kuma idan har ta tabbata ‘bata tayi to maleek ya ankaro da akwai masu Masa zagon qasa kenan.

Kwana biyu yakoob na tsananta mugun nmbincikensa acikin gizah batareda sanin kowaba ko ankarewar kowa akan sha’anin bincikensa ya tabbatar Masa da cewan tabbas padima ta dawo gizah saidai Babu Wanda yaganta Kuma alamu da binciken da yayi a airport sun tabbatarda tareda jekadi ta iso gizah Kuma motar cikin masarauta ce ta dauko su take ya fada laluben drivern daya daukosu cikin direbobin masarauta suka cabkesa tareda boyesa wani mugun wuri cikin masarautar suka fara gana Masa muguwar azaba harsaida yafada musu cewar tabbas ya dauko jekadi da padima yafadi inda ya ajiyesu.

Advertisements

Gyara tsayuwa yakoob yayi tareda sauke Kai qasa Yana gurfanawa cikin tsananin girmamawa da sassauta harshe yace”

Allah ya taimaki neges tabbas tunaninka gaskia ne wannan yarinya tadawo cikin gizah tareda jekadin maleek saidai haryau Babu Wanda yaganta ko yasan inda take Wanda hakan ke nuni da MALEEK yasamu masaniyar akwai abinda yake faruwa Dan Haka yarinyar yanzu rayuwarta nada gargada akan sirrin Nan duk da batasan komai gameda aikin datayi ba saidai bama buqatar bawa kuskure kofa a dukkanin aikinka neges.

Wani numfashi neges AL’MANSOOR yasaki Yana gyara zaman mulkinsa kan wata doguwar kujerar hutawarsa dake cikin palon shaqatawarsa na kuryar sassanshi ya Dan waiwayo ya kalli amintaccen nasa yakoob yace”

Kartayi mutuwar banza ayi amfani da ita tunda ita tasaka kanta aciki,

Maleek Yana tsallake komai to Bari muga ta Yaya zai tsallake wannan,

Aci amfanin yarinyar na karshe

Tsohuwar matar maleek din takira da tata matsalar nabata damar zuwa dukkaninsu zasuyi Mana amfani Dan haka kasan abin daya kamata kayi.

Angama me delah da gizah.

Advertisements

Juyawa yayi ya fice daga Palon yabi ta wata hanyar dazata fiddashi sashen batareda kowa tagansaba ya fice.

Washe garin ranar lailah ta sauka a gizah Wanda yasa kowa cikin mamaki sbd sanin Bata taba zuwaba sai tareda maleek shima Saida babban dalili bare yanxu dasukejin kishi kishin rabuwarta da maleek sai zuwan nata yasaka kowa cikin mamaki musamman Anneti saidai Bata nuna Mata komaiba.

Matsalar farko data fara fuskanta shine sassanta shine akaiwa sabon gyara da tsari yazama na NURU saidai tun kafin zancen ya habbaka yazama wani al’amarin daban Anneti tasaka aka gyara Mata wani sassan daban Wanda beyi girman na NURUn ba ko kadan aka Aiko Mata da bayi biyu masu Mata hidima Wanda hakan yayi mummunan baqanta Mata wato har anan dinma saita fuskanci wulaqanci irin wannan?

Hmm zatayi lokacin kowa daga baya har Annetin sbd bazata dauka wulaqanci irin wannan ba.

Wanka tayi sai alokacin tasamu damar Dan cin wani abinci Takoma daki ta kwanta Dan hutu take tsananin buqatar yi ayanxun ko kyawun fuskarta ya dawo daidai na rashin hutu da bacci da nutsuwar dabata samuba tun shekaran jiyan sbd fitinar dake gabanta Dan haka zata huta sosai kafin tafara fitowa aganta asan haryanxu tana Nan a LAILAH MALEEK dinta kyakkyawar mace me lokaci.

Ta bangaren jekadi kuwa ganin yadda  jikin padima yarikice yasata kebe kanta cikin dakinta ta nemi numbern Mr Omar tayi Masa bayanin dukkanin komai ta Dora cewa lailah na gizah ta iso.

Shiru Mr Omar yayi tareda sauke Dan numfashi sbd baiso katse hutu da Jin dadin maleek ba Dan kuwa hutun gaske maleek din keyi a kwanakin Dan ko ayyukansu tuni suka taru suna Nan Yana Dan kokari Yana rage masu rayuwar sbd maleek din yasamu hutawa dakyau Amma Kuma wannan zancen Dole ya sanar Masa dashi.

Sake sauke numfashi yayi yace”

Zan sanar Masa duk abinda yace zakiji Amma dai kafin Nan inaga ki Dan Bata maganin meriz din kadan tasamu karfin Koda kyakkyawan numfashi ne sbd na tabbatarda maleek bazaiso ta rasa ranta ba dama amfanin riqeta din asan asalin su waye suke aikin Amma dai zan sanar Masa yanxu Inshallah.

Kashe wayar yayi tareda sake fitarda numfashi me zafi Yana tunanin Dole ya isarwada maleek wannan sakon batareda Bata lokaciba duk da ba Haka yasoba 

Yaso ubangidansa yasake samun hutu wadatacce Dan kuwa tsawon shekaru Basu samu irin wannan hutawarba sbd kullum cikin aiki da bincike suke matuqar ba ciwoba maleek baya sati biyu a jere zaune baiyi tafiya sai kwanakin Nan dayaga alamar kila har fiyeda watama zasuyi suna hutawa yanxu ga wani aikin.

Ajiyar zuciya ya sauke akaro na biyu kafin ya daga wayarsa ya Nemo numbern MALEEK ya saka Kira Yana nutsuwa tareda daidaita murya

Saidata kusa yankewa kafin maleek din ya daga cikin kamewa yace”

Yes Mr Omar.

Barka da hutawa MALEEK,

Dama saqone daga gizah, jekadi takira jikin yarinyar Nan yakasa daukan meriz tana cikin mawuyacin halinda kowane lokaci zata iya rasa ranta shine jekadi ke neman qarin umarnin taci gaba da aikinta kokuwa ta dakata daga Bata din?

Shiru yayi na wasu seconds daidai fitowar NURU daga wanka fatar jikinta na daukan ido ya zubawa fuskarta fararen idanuwansa batareda ta ankareba yaji tunaninsa na sauyawa akan padiman ya sauke boyayyan numfashi ahankali tareda Miqewa tsaye ya fice daga dakin ya nufi Palo Kai tsaye yace”

CONTINUE HERE>>>>>>

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like