UBAYD MALEEK 44

Advertisement

 ****************

Shiru Imran yayi Jin sunan NURU data ambata Yana nazarin abin cikin ransa sbd baya fatan samun wani kebantaccen lokaci dagashi se NURU Dan bazai iya riqe 

zuciyarsa ba,bazai iya danne kansa daga Mata tambyarda yaketa son Jim amsarta daga gareta Dan Dan kuwa zuciyarsa takasa amincewa ta yarda ba auren tilas 

neba akaiwa NURU Dan batada gata,

Yanason ji daga bakinta cewar ta aminnce da auren kokuwa haryanzu tana sonsa Dan a shirye yake daya qararda duk abinda shida mahaifinsa suka mallaka Dan ya 

Advertisements

kwatar Mata yancinta a warware aure abarta da Wanda ta zaba Dan Haka wannan alqawarinane duk suka hadu harsuka samu damar magana yanada burin sanin raayinta 

akansa da aurenta Duk da Haka baiso haduwarsu tazo ta wannan hanyarba Dan shi me kishine bazaizo NURUn taje irin wurin Nan ba duk da aikintane Amma baida 

niyar barinta Koda shine ya aureta ta ringa shiga irin wainann cases din.

Numfashi ya sauke tareda boyayyar ajiyar zuciya ahankali kafin ya bude Baki yace”

Ba damuwa zan bincika tafiyar inshallah zanyi kokari ko cikin Daren nan ne na taso ko gobe tunda safe kifada Mata.

Aje wayar yayi Yana sauke ajiyar zuciya da numfashi atare Yana rufe idanuwansa da Basu Gama dawowa daidaiba tun ciwon dayayi ya warke 

Ya miqe tsaye Yana jefar da wayarsa kan kujera sbd wasu feelings dinsa da afia ke Shirin tado Masa kokuma Tama tado Masa shi akan soyayyar NURU data fara 

Advertisements

koyawa kansa dangana.

Afia kuwa tana aje wayar taji hankalinta ya Dan kwanta sbd tanada tabbacin mum dinta zata samu damar fara wata kyakkyawar rayuwar koba a gidan dad dinta ba 

tana Mata fatan samun rayuwa kwanciyar hankali da nutsuwa tareda sauyawa Dan kuwa wannan al’amarin daya faru babban darasine gareta.

Tana buqatan mgnar da NURU gashi ba waya hannun NURUn sai kawai ta fito da kanta zata nufi gurin NURUn tasamu tsaro a bakin sashinta tareda umarnin ba fita 

koina sai gobe.

Da mamaki ta kalli Wanda yake shugaban tsaron tace”

Daga Ina umarnin yafito?

Sauke Kai yayi cikin nutsuwa yace”

Daga gurin MALEEK.

Siririn numfashi ta sauke tareda hakura ta juya Takoma batareda tace komaiba sbd daga yanxu umarnin dad dinta abune me girma a rayuwarta da bazata iya 

tsallakewaba badan alfarwar da yayiwa mum dinta kawai ba hadda tabbatarwa datai shine komai nata samun mahaifi kamarsa sai antona.

Dawowa tayi ta nufi bedroom dinta Kai tsaye ta tube sai alokacin tasamu damar qwarin watsawa jikinta ruwa tanajin al’amarin ya warware Mata Inshallah.

Acikin Daren ranar Mr Omar yayi qwalailar bincikensa tareda yonasi wani jami’in tsaron maleek suka gano jaridar data fara wallafa labarin 

Suka zurfafa binciken daya nuna Kai tsaye jaridar ta fitarda labarin ne tun qarfe shida na safiyar ranar alhalin ba’a Kuma maganar kisan Bata bayyanaba sai 

qarfe takwas na safe ma su maleek suka Isa gurin Kuma Basu Kira hukuma ba sai qarfe Tara hakan ke nuni da labarin yasamu masu jaridar ne kamar ma tun cikin 

Daren da abin yafaru kenan kafin afkuwar abin ma.

Da wannan aka Isa gidan jaridar Kai tsaye aka kama shugaban companyn zuwa headquarters Kai tsaye Maleek yabada umarnin rashin sassauci ga binciken mutumin 

Wanda dam jira suke su Kuma jamian tsaron suka hau gana Masa azabar data sakashi saurin bada bayani Nan take cewar wani ne acikin Daren yakawo Masa 

information din saidai baiga fuskarsa sosaiba.

Kallonsa commissioner din yayi Yana jinjina Kai yace”

Me kagani Wanda zaka iya tunawa game dashi Wanda zai taimaka Mana nemosa da kanmu?

Wahalallen numfashi ya sauke Yana hadiye yawunsa dasuka gama gauraya da jinin dukan da akai Masa yace”

Idanuwansa zuwa saman hancinsa sbd Yana sanyeda baqin nose mask.

Ajiyar zuciya commissioner ya sauke tareda Mr Omar Wanda dama Allah Allah yake su samu bayani me kyau dazai bada hujja me ma’ana ya kalli commissioner Yana 

cewa”

Zansaka aturo Mana Wanda zai Mana  sketch yanzun Nan kafin safe nakeson agama inshallah.

Juyawa yayi ya fice commissioner yasa aka maida managern aka rufe Kafin a me sketch din yazo.

Daganan Kai tsaye Maleek Mr Omar yakira ya sanar Masa komai 

Shiru MALEEK yayi na ‘yan mintuna kafin ya Dan motsa tareda bude Baki yace”

Kaje da kanka gurin tareda wani me sketch din gurinta itama ayo na idanuwan Wanda yakai Mata meriz sai ahada agani Dan nasan mutum dayane sbd tabbatarwa.

Bayan Mr Omar ya tabbatarda anfara zana fuskar Wanda managern gidan jaridar yagani tukuna cikin tsakiyar Daren ya wuce delah Ana fitowa sallar asuba Yana 

sauka ya wuce Dan aiwatarda dayan aikin.

Qarfe takwas na safe afia ta Isa sashen NURU Kai tsaye bedroom dinta ta nufa har lokacin NURUn na bacci ta tashi ba saidai kasa hakurinda afia tayi yasa ta 

tada ita ahankali tana Kiran sunanta.

Bude ido NURUn tayi ahankali tana kallon afia dake tsaye tana kallonta cikin kulawa tace”

Sorry na tasheki 

Ina tsananin buqatan taimakonki ne Dan Allah.

Da mamaki NURUn ta tashi zaune tana tattare gashinta ta dauki band gefen gadon ta daure gashin tana yaye bargonta tace”

Lafiya dai Ina ko??

Ajiyar zuciya afia ta sauke tareda juyawa ta nufi sofa ta zauna tana kallon NURUn tace”

Ki kimtsa tukuna sai muyi mgnar.

Zuro qafafunta qasa tayi tareda miqewa tsaye sanye cikin kayan bacci riga da wando masu santsi farare tas sun lafe jikinta ta nufi toilet tashige tana 

waiwayen afia akan tunanin ko wani abun yakuma faruwane.

Brush kawai tayi takasa wanka sbd hankalinta yafara tashi akan tunani da wasi wasin lafiya.

Tana fitowa Palo ta fito inda afia din Takoma ta zauna tana Dan kallon tv sama sama Amma hankalinta nakan yanda NURU zata karbi zancen saidai tasan yanada 

wuya takasa Mata wannan alfarman tunda aikintane.

Zama NURU tayi kusada afia din tana kallonta dukkanin hankalinta akanta tace”

Gani menene??

Numfashi afia tasake sauke akaro na biyu tana kallon NURUn cikin nutsuwa da nuna damuwarta da mahimmancin da maganar take dashi agurinta tace”

Maganar mum dinace yau nazo neman alfarma dama taimako agurinki,

Kinsan yanda nakeson mahaifiyata dakuma yanda nasamu wannan sassaucin yazo gareta, Dan Allah ko Zaki min alfarmar cika sauran formalities na karbota a 

matsayinki na lawyer duk da nasan Baki Gama zama cikakkiyar lawyer din ba Amma dai kinada damar zuwa.

Akaro na farko yau Ina roqonki wata alfarma Ina fatan Kuma Zakiyi sbd Ni Dan nasan abinda mum tayi Miki Bata cancanci ki taimaka din ba Amma Kuma Ina 

roqonki kiyi sbd Ni da farhat.

Tsit NURU tayi tana dauke wuta sbd Bata taba tunanin wannan maganar ba bama ta taba kawo tunanin shiga cikin wannan al’amarin ba gaba daya 

Musamman na mum din afian Wanda shigarta kamarba bazai yiyuba sbd ba ita ke ikon kanta ba hakama ita tayaya zata iya zuwa Kai tsaye wannan aikin?¿

Kasa cewa komai tayi ta dago ta kalli afia batamasan me zata ce Mata ba Dan neman alfarma agurinta da afia tayi kamar abune da bazata iya cewa aa ba hakama 

Kuma tanajin shakkar amincewar sbd batamasan ta Yaya zata sanar da Wanda yake ikonta zancen.

Ganin Shirun NURUn yasa afia shiga damuwa takira sunan NURUn tana cewa”

Bazaki iyaba right???

Zubawa afian ido NURU tayi tana sake shiga tunanin rasa abin cewa ta girgiza Kai ahankali ta bude Baki tace”

Afia Babu alfarmar dazaki roqa gurina nakasa Miki matuqar Bata sabawa ubangiji bace saidai ta Yaya za’a sanarwa dadynki Kuma Kinga…..

Katseta afia tayi da cewa”

Dad dakansa jiya gabanki yabada damar komai gameda case din mum din wannan maganar ta sirrice yanzu idan nace zamu dauko lawyer daga waje then komai zai iya 

sauyawa 

So please NURU ki amince dan Allah dad Bai taba dakatar damuba ko hanamu harkan data shafi karatu bare yanzu aiki Dan Allah ki yarda Ina roqonki.

Dagowa NURU tayi takalli afian tareda Dan sauke ajiyar zuciya tace”

Na amince Amma sai dad dinki ya amince Zan nema izininsa.

Shiru afia tayi tana kallon NURUn tana nazarin abin data fada din saidai tunda ta amince batada zabin daya wuce itama amincewa da bayanin tace”

Thank you.

Miqewa tayi zata fice ta dakata da cewa”

 Anjima Imran zai iso inshallah saikuyi mgna.

Ficewa tayi tabar NURUn zaune mamaki na kasheta Jin da Imran zasu tafi kenan.

Faduwa gabanta yayi sbd tunani biyu dasuka shigeta take,

Na farko ta Yaya zata fadawa MALEEK maganar zuwan harda qarin Imran ne abokin aikin,

Ma biyu tayaya zata iya fita daga ita sai Imran bazata iyaba sbd tasan Imran din sai yayi kokarin tado Mata da maganarsu data wuce wadda hakan baya cikin 

abindata shirya dawowa dashi.

Bangare daya afia nason daureta da jijiyoyin jikinta.

Daqyar ta iya tashi daga Inda afian ta barta ta nufi bedroom tafada toilet jekadi dake jinsu batace komaiba ta juya ta fice daga sashen Kai tsaye ta nemi 

numbern Mr Omar ta fada Masa komai yace idan yadawo zai sanarda maleek.

Qarfe goma Sha biyu na ranar Mr Omar ya sauka a airport na gizah na dawowarsa Dan yagamo abinda yaje Yi Kuma adaidai lokacin Imran jalal ya sauka a airport 

din cikin sa’a suka hadu dukkaninsu motar masarauta tazo daukansu shi Mr Omar drivern maleek yazo daukansu shikuma Imran drivern Anneti afia tasaka yazo 

daukansa.

Kallon kallone yashiga tsakaninsu Mr Omar ya saki wani murmushi Yana miqawa Imran din hannu yana kallonsa yace”

Barka da zuwa Barr Imran jalal and all the best.

Miqa Masa hannu Imran yayi Yana cewa”

Thank you Mr Omar.

Murmushi Mr Omar yasake sakewa Yana Dan kallon gefen Imran din yace”

Kai kadai kazo??

I mean nasan kasan kana buqatan wani lawyern ga aikin.¿

Sai alokacin Imran yasaki murmushi Yana kallon Mr Omar din yace”

Aikina ne Kuma nasan da hakan shiyasa lawyern da nake buqatan muyi aikin tare tana Nan Dama 

Fata dai kawai idan zaka iya jimirin ganin hakan.

Wani irin Murmushi me Fadi Mr Omar yasake Yana sake cewa”

Good luck with that too.”ya juya ya wuce Yana sake sakin murmushi yashige mota aka jashi sukabar Imran din a tsaye Yana bin motar da kallo kafin ya sauke 

numfashi me zafi yashiga tasa motar da akazo daukansa  suka wuce Suma Yana Jin tamkar zuciyarsa nason karbuwa da qiyayyar Mr Omar sbd koyaushe shine yake 

shiga hancinsa da kudundune Amma sbd qiyayya bata cikin abindayake Bari Yana shigarsa yasa yake yaqar hakan Yana dannewa sbd ya dauki qiyayya wani aikin 

wahala da kake dorawa kanka yazo Kuma ya ringa wahalar dakai ka rasa focus da sukunin rayuwa karshe ka wargaza kanka agurin qiyayyar wani.

Kai tsaye dukkaninsu masarauta suka nufo cikin sa’a kusan atare motocinsu suka iso Mr Omar ya wuce Kai tsaye sashen maleek daukeda sketch din dayazo dashi 

daga delah shikuma Imran afia ce da kanta ta bada umarnin kaisa sashen baqi na musamman kafin ya huta suyi mgn.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like