Advertisement
49_*
Shiru yayi Yana kallon padima data lallabo ta tsaya gefensa Jin sunan NURUn daya ambata tana kallonsa da idanuwanta dasukai wasu iri kaman me jiran sammaci ya Dan gyara zama Yana sake murya cikin farin cikin Jin NURUn yace”
NURU me padima zatai Miki??
Shiru tayi sbd jikinta daya fara sanyaya ta bude Baki da qyar tace”
Abal labarin rasuwarta nake samu yanzu duk tsawon lokacin Nan bansan meyake faruwaba Ina matsayin ‘yar uwa Kuma ‘ya acikinku
Advertisements
Dan Allah abal ka sanar Dani komai Kuma idan padima na Nan inason jinta ko yayane..
Wasu hawayen takaicine da sanyin jiki suka gangarowa ammynsu Jin abinda NURU ke fada
Abal kuwa nutsar da murya yayi cikin kwantarwa da NURUn hankali da murya Kai tsaye ta matsayinsa na mahaifinsu su duka yace”
NURU dagani har ammynku da meryam munanan lafiya cikin kwanciyar hankali da nutsuwa sakamakon Miji na gari me adalci da Allah yabaki,
Muna cikin masarautar delah a kebe cikin walwala da wadata tareda ni’imar duniya,
Saidai har gobe da kullum zuciyata takasa samun kwanciyar hankali na uban daya haifi ‘yar da Babu Allah ko miskala zarratin acikin ranta face zuciya irinta kafiran farko da qyashi da hassada tareda taurin Rai yagama cikata,
Padima na nan da ranta saidai banajin tanada sauran qimar da Zaki cigaba da kiranta ‘yar uwarki sbd ta nunawa duniya cewan Babu qauna ta jini a tsakninku har abada
Muda muka haifeta Dole zamu zauna da ita Amma ke Kam ba Dole sbd ta wuce iyakarta….
Tsananin sanyi jikinta yayi da kalaman abal dinsu ta sulale ta zauna bakin kujera ta zauna cikin sanyi da sagewa tace”
Advertisements
Abal meya faru?
Me padima tayi wannan karon?
Kai tsaye yace”
Padima taje gidanki da niyar rusa kyakkyawar rayuwar da Allah yabaki ta hanyar niyarta ta kashe mijinki Wanda tabawa gubar meriz yasha wadda Allah ne kawai yayi da kwanansa agaba da babushi Kuma niyarta shine su maqala Miki wannan sharrin da ita da mahaifin amed dama amed din….
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Innalillahi wainna ilaihirrajiun”
Shine kawai abinda tasamu bakinta yake iya furtawa ahankali idanuwanta na bushewa sbd tsananin firgici da tsoron maganar da abal din yafada cikin rawar murya tace”
Abal abawa padiman wayan Dan Allah…
Shiru yayi Yana shakkar hakan sbd har cikin ransa baya buqatan alaqar NURU da padiman yanzu ya dago ya kalli padiman datai tsamo tsamo da idanuwanta dasuka Gama jemewa ya miqa Mata wayar.
Karba tayi ta Dora akan kunnenta cikin sanyi tace”
NURU
Dakakkiyar ajiyar zuciyar karfin hali NURU tasake cikin kasa gasgatawa tace”
Padima menene abindaya faru???
Numfashi padiman ta sauke cikin muzantuwa da wata irin kunya da wulaqanta saidai Babu yanda zatayi bayan fadan gaskia ta bude Baki ahankali tace”
Dukkanin abinda abal yafada hakane,
Banida ciwon komai nai Miki karya naje gurinki da burina na dabam Wanda yakaini ga sawa maleek garin meriz Wanda zai kawo karshen rayuwarsa saidai hakan be faruba suka gane nice na aikata hakan
Sukaso hukuntani saidai Kuma Basu kaiga yin hakanba amed sukaso kasheni Dan boye tonuwar asirin dayasa na kashesa batareda nasan Yaya zanyiba
Maleek ya zabi da a boye Miki komaine sbd gudun shigarki damuwa….
Zubewa qasa tayi duk da NURUn Bata gabanta cikin tsananin damuwa da kanta daya fara juyawa alamar zata birkice tace”
NURU ki yafemun kinji
Kisa maleek ya yafemun kinji
Kisa abal ma ya yafemun kinji
Kisa ammy ma ta yafemun kinji
Bani nakashe amed ba shine ya kasheni na gudu na boye bayan maleek kinji,
NURU kisa mutanen gizah ma kowa ya yafemun kinji
Nima kisa na yafewa padima kinji,
Padima Tama lalata rayuwarta gashi yanzu takoma Kamar Mara hankali nake gani
NURU kinyafemun ko???…….
Shiru NURU tayi dukkanin jikinta na sake yin sanyi sbd daga maganganun padiman tagama gane kanta ya juye wannan rayuwar dame tayi Kama?
Wannan wace irin masiface me mummunan karshe Wanda zaikai bawa ga irin wannan makomar gashi padima da kyanta da cikar zatinta Takoma kayan kwankwani saika kwankwasa kaji sauti.
Cikin sanyin jiki da muryarta data toshe tace”
Na yafe Miki padima Allah ma ya yafe Miki yabaki lafiya idan kinada rabon warkewa.
Karban wayar abal yayi Yana cewa amin dukkaninsu jikinsu a Sanyaye sbd idan abin ya juyo padiman nada tausayi wani lokacin sbd lafiyayyan budurwa takoma saidai zaman gida sbd Babu Wanda zai iya aurenta ahaka saina Allah musamman abubuwan nata sunyi yawa,
Ga rashin budurci,ga mummunan zuciya data kaita ga hakan ga na karshe rashin hankali daya shigo.
Kallon meryam ammy tayi tana cewa”
Rakata daki ki zaunar da ita har abin ya lafa ta ‘dan dawo daidai.
Kallonta Meryam tayi tana kamo hannunta ta jata itakuma tabita tana ‘yan maganganunta qasa qasa batareda kowa yamaji me take fadaba sbd sanin batada zance saina a yafe Mata ba ita takashe amed ba amed ne ya kasheta.
NURU najinsu tayi shiru tana sake Jin al’amarin har cikin ranta dukkanin gabobinta sun saki takasa cewa komai
Abal cikin sanyi shima yace”
Maleek da kansa yasa aka kawomu Nan Dan mu samu sauyin rayuwa tareda boyewa duniya abinda padiman tayi Wanda bazamu taba daina gode Masa akan hakan ba
Ya allah yakara rufa Masa asiri duniya da lahira yayiwa rayuwarki taredashi albarka da zuriar dazaku samu agaba.
Amin ta furta daqyar sbd toshewar da muryarta tayi da mamaki da firgicin dukkanin abin dataji yanzun.
Miqawa ammy wayar abal yayi ammyn najin muryan NURU taji hankalinta ya kwanta sbd Koba komai sunada sauran ‘yaya biyu dasuke fatan su zamo tafarki na gari agaresu Wanda zasuyi alfahari dasu duniya da qiyama.
Meryam ce ta sake sosai tayi magana da NURUn Wanda har lokacin Bata dawo hankalinta duka ba da Haka ta ajiye wayar tanajin sauran bayanin da afia ke koro Mata na NEGES da sauran labarin.
Sai alokacin hawayen tsananin son mijinta Da kaunar iyayenta suka gangaro Mata ta miqe ta nufi dakinta ta turo kofa ta zauna bakin gado tareda fashewa da wani irin kuka Mara sauri sosai tana rufe fuskarta da tafin hannuwanta sbd tabbas idan tace batajin tausayi da kaunar Yar uwarta tayi qarya saidai Kuma bazata iya cigaba da rabartaba Dan kuwa wannan wani al’amarine me girma daya rusa rayuwar farin cikin gidansu dasuka taso dashi Dan kuwa iyayenta har abada bazasu daina Jin damuwa da baqin cikin ganin padima acikin wannan halinba Dan haka tasan farin cikinsu Yi zai ringayi Yana daukewa Dan ‘da duk lalacewarsa acikin Rai yake.
Sai yamma lis tasamu damar fitowa bayan ta sauya wanka da Kaya idanuwanta da fuskarta a ‘dan kumbure
A shirye ta fito Dan zuwa gurin Anneti farhat da afia ma dake sashen har lokacin sbd takasa tafiya tabar NURUn cikin wannan halin suka miqe tareda jekadi da Akira suka nufi sashen Annetin wadda itama tana Dan daurewane sbd ita qaddara ba’a canzata Amma tana cikin hali na damuwa da baqin cikin wannan al’amari daya faru na NEGES Wanda a safiyar ranar ya tattara yakoma delah gabaki daya da zama sbd shirye shiryen Nadi da aketayi Wanda ake qara la’antarsa akan wasu abubuwan da dama
Anneti kuwa maleek ya hanata zuwa koina yace tayi zamanta a gizah sbd dama auren kawai sukedashi a tsakaninsu babu wani kebewa irinta ma’aurata dasukeyi sbd tsufa da manyanci daya Kama.
Ganinsu yasanyaya ranta musamman NURU wadda tagama samun tabbaci daga gurin jekadi cewar tazama cikakkiyar macen UBAYD MALEEK wadda a fili ya nuna hakan Kuma ko agurin kwanciya da ita ya nuna hakan sbd alamu dasuka nuna ba so daya ya sadu da itaba acikin daren wannan shine cikakkiyar alamar tasace ta har abada tasamu guri me girma a zuciyarsa da rayuwarsa da yardar Allah.
Kayan marmari aka kakkawo aka jere musu Anneti tasa aka kawowa NURU nata hadin wani sirrin daban suna ‘yar Hira sama sama jekadi na miqo Mata tana Sha a Dan kunyace harsuka Gama sukai sallar magriba Basu barota ba sai bayan ishai
Suna fitowa afia ta kalli NURU cikin sakewa tace”
Meye sirrin wanna maganin da Anneti ke Baki?
Kodai na……
Kallonta da NURU tayi yasata dakatawa da zancen tana ‘yar dariya.
Murmushi NURU tayi tana tafiya a natse tana cewa”
Idan nafada Miki sirrin bazaki iya bacci ba nikuma inason ki ringa samun bacci yanzu sbd ki koma AFIA UBAYD MALEEK dinki ta asali duk wannan ‘yar ramar ta fice.
Murmushi afia tayi tana cewa”
Thank you Ms NURU YONAS.
Suna Isa ko zama basuyiba saqon mr Omar ya samesu na cewa gobe zasu koma Inshallah Dan Haka su shirya.
Wanka kawai tayi tayi Shirin bacci ta haye gado ta kwanta da wuri sbd ciwo ciwon Kai datake ji.
Washe gari da safen kayanta ta hada acikin qaramar akwati saina farhat data saka Akira ta hada Mata ta shirya tsaf ta nufi sashen Anneti tareda jekadi dake gefenta tana sake nanata Mata wasu maganganun akan zama na aure.
Koda suka Isa ga mamakinta kusan kayayyaki ta tarar jere a tray Ana jiranta Kai tsaye Anneti ta nuna Mata kujera tana cewa”
Zauna jekadi ki nuna Mata komai yanda yake ta shanye shekara daya zasuyi ajikinta suna aikinsu.
Miqewa tayi ta shige sbd ganin yanda NURUn kejin kunyar Sha din
Tana shigewa jekadi ta zage tana zuzzuba matasu tana Bata tana shanyewa a wahalce sbd sunyi Mata qarfi sosai a Baki daqyar ta shanye kusan duka sauran daya rage ganin tana neman yin amai yasa Dole jekadi ta qyaleta.
Koda Anneti ta fito daukeda kyautar Dan qaramin akwatin turarukansu na asalin hadin Ethiopia masu wani irin kamshi kamar na turarukan oud ko itacen turaren wuta qamshinsu dai me sanyi da Sanya nutsuwa ta miqawa NURUn tana cewa”
NURU Allah yayiwa aure albarka.
Amin jekadi tace tana karbanwa NURUn wadda take godiya cikin girmamawa da ladabi kafin sukai bankwana suka fito.
Qarfe goma Sha daya suka fito zuwa airport har lokacin Babu Wanda yaga MALEEK acikinsu har suka Isa airport suka shiga jirgi jirginsu ya daga Saida suka Isa Paris suka sauka tukuna suka San bataredashi suka dawo ba shi sai bayan nadin sarauta zai dawo.
Ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke lokacinda suka fito daga cikin motar data ajesu daidai kofar shiga palon gidan
NURU ta lumshe ido tareda karanto adduar samun zaman lafiya da ingantacciyar rayuwa a gidan auren nata tayi bismallah ta jefa kafarta ciki da sallama tana kallonsu mum Sarah dasuka jera suna Mata sannu da zuwa cikin farin ciki da murnar dawowarsu.
Afia ma kusan adduar samun nasarar rayuwa da qarfin gwiwan cigaba da rayuwa kaman da tashigo tana murmushi wa su mum Sarah dasune kusan suke taredasu tun suna yaransu haryanzu Dan Haka yanzu ta yarda da cewa basai Wanda ya haifeka yake iya zama uwa agarekaba hakama basai jininka ne kawai zai amsa sunan ‘dan uwa agareka.
Da wannan kowaccensu ta nufi dakinta sukai wanka da salloli suka fito cin abinci,
Sanyeda wasu riga da wando marasa nauyi ta fito gashinta a daure kyakkyawar fuskarta tayi fayau ta nufo dining din afia tabita da kallon burgewa sbd ita akoda yaushe tana yiwa NURU kallon kyakkyawar halitta me sanyin kyau da shiga zuciya saidai takasa ganewa ko ta yadda dad dinta da NURUn zasu iya rayuwar aure a tsakaninsu.
Ganin kallon da afia ke Mata yasata sakin murmushi Tana zama kan dining tace”
Thank you.
‘yar dariya afia tayi tana cewa”
Kinma riga kinsan Ina yabawane kenan.
Wani murmushin takuma saki tana cewa”
Nariga nasan ko kallonki me yake nufi ai.
Suna Gama cin abincin kowaccensu ta nufi daki sbd gajiya da baccin dasuke buqata musamman gobe kowaccensu tayi niyar fara fita makaranta sbd satin zasu fara exams dinsu na karshe Inshallah kafin sukama ayyukansu na Gina career dinsu.
Rashin waya a hannunta yasa washe gari kafin su Isa makaranta tasa aka tsaya wani qaton shagon waya ta siya waya tasaka layinta suka wuce tana gani sakon baquwar number na shigowa wayarta batareda ta duba ba ta saka wayar jaka ta shige class.
Sai yamma suka dawo wanka tafara yi kafin ta Dan kwanta tayi hutun AWA daya da rabi kafin lokacin sallar magriba yayi ta tashi tayo alwala tazo tayi sallar ta Dan dauko takardunta zatai karatu sai alokacin ta duba wayarta ta bude sakon daya shigo dazun taga ansaka”
_Inidemìní āderíki kwēn of GIZAH_
(Gud morning Queen of gizah)
Wani irin Murmushi ne ya sauka kan kyakkyawar fuskarta har tana Dan dafe goshinta sbd wani yanayi data tsinci kanta bayan karanta sakon tasake kallon numbern ta Dan sunkuyar dakai tana murmushin sbd sanin tabbas MALEEK ne yayo sakon ta daga wayar ahankali tanason yimasa reply Amma takasa sanin me zata rubuta saita ajiye wayar tareda daukan takardunta tana karatu Wanda fiyeda Rabin hankalinta baya Kai Yana kan tunaninsa.
Kwana shida sukai da dawowa suna zuwa school aka fara exams Dan Haka kansu yadauki zafi Sosai musamman afia dasuke likitoci gabaki daya basuda lokacin kansu bare na gida shiyasa farhat ta daga musu kafa Dan itama nata karatun Yana daukan zafi yanzu sbd tashiga secondary yanzu.
Daga NURUn har afia gabaki daya kashe wayoyinsu sukai suka ajiye Saida suka kammala Kuma har lokacin maleek be dawoba sbd abubuwan dayakeson saisun daidaita a gizah kafin yabarota shiyasa shima ayyaukansa na Nan Paris suka taru ga hutu dayake buqata na duk wainnan gwagwarmayar da akai Yana buqatan samun nutsuwa.
NURU ce tafara gamawa da kwana biyu kafin afia Nan hankalinsu ya kwanta suka hau Taya juna murna tareda farin ciki har wani Dan party suka hada acikin gida na tsananisu su uku da farhat saisu mum Sarah da ‘yan aikin gidan NURU da kanta tayi musu katoton cake suka yayyaknka abinsu aka bawa kowa sunata farin ciki dayake ciki Palo ne sukai abinsu Babu me wasu kayan nauyi ajikinsu
Ita afia jeans ne three quarter da blue da purple riga Mara dogon hannu
Itama NURUn pencil jeans ne dogo dayafi na afia tsayi ajikinta Ash daya kwanta jikin dogayen sirarun cinyoyinta da fadin hips dinta sai farar riga me hannun shimi ta nufi kitchen ta wanko hannunta daya Dan baci da cake ta fito duba massages dinta saiga Kiran abal dinta ta daga cikin farin ciki suna tayata murna da Dan mamaki tace”
Abal waye yafada muku?
Murmushi abal dinta yayi kawai ya bawa amminta ta tayata murna itama tareda Sanya Mata albarka aka bawa meryam Nan tahau ihun tayata murna tabawa afia itama sukai Mata adduoi da Taya murna ta karba wayan kenan ta Dora a kunnenta taji qamshinsa daf da ita sosai Yana Shiga hancinta tayi saurin juyowa ahankali tana sauke wayar daga kunnenta
Sukai ido biyu dashi Yana tsaye daf da ita a bayanta fararen idanuwansa nakanta Yana Mata kallon daya sata juyawa ta kalli gefen Afia ahankali wadda itama gabaki daya Bata lura da shigowar dad din nata ba
Ahankali ya bude bakinsa daya motsa kadan ba sauti yace”
Congrats lewa.
Wani irin Murmushin farin cikine me tsanani ya lullubeta ta matso ahankali ta matsu dashi sosai ta lakaci tsakiyan cake din dake gefenta kadan da babban yatsanta takai bakinsa ya bude bakin ahankali ta zura Masa yatsan ya kame ya kasa hannun da harshensa ta lumshe ido ta bude tana zare yatsan sbd Jin yanda yake tsotsa ya Kai hannu ahankali zai kamota
Farhat data lura dashi alokacin cikin tsallen murna tace”
Yeeeehhh daddy yadawo.
Matsawa baya NURU tayi ahankali tana dauke idonta daga kallon dayake Mata ta juyar da Kai tana boye kyakkyawan murmushin dake kan fuskarta
Afia ta juyo da sauri cikin farin ciki tana cewa”
Barka da dawowa dad.
Thank you and congratulations to you Dr AFIA UBAYD MALEEK.
Wani qayataccen murmushin farin ciki tasaki sbd ganin alfari da ita a fuskar dad din nata ta matso ta ‘dan rungumesa tana cewa”
Thank you dad.
Dafa kanta yayi Yana cewa”
Ina Miki fatan nasara da albarkatacciyar rayuwa agaba.
Amin ya furta tana kallon NURU dake tsaye gefe tare dasu mum Sarah ta miqa Mata hannu tana cewa”
Dad ka Taya NURU murna itama.
Kallon NURUn yayi Yana dauke Kai ahankali yace”
Allah yayi Mata albarka yabata sa’ar rayuwa.
Amin afia da farhat sukace suna kallon NURUn data ki dagowa ta kallesa sbd Jin idanuwansa dake yawo ajikinta wainda tun anan tanajin kaifi da Dafin son dasuke dauke dashi.
GIPHY App Key not set. Please check settings