UBAYD MALEEK 51

Advertisement

 51_*

Sai dare suka samu kansu a dakin afia din ma suka kwana bayan sun kwanta 

Afia ta fuskanci NURUn ta sauke ajiyar zuciya da numfashi ahankali tafara cewa”

NURU mum Dina tasamu matsalar juyewar Rabin Kai dayake Dan tashi wasu lokutan idan tana tuno abinda daya faru na wannan al’amarin.

‘dan shiru tayi tana sake juya al’amarin cikin ranta ta bude Baki tacigaba da cewa”

NURU mum ta rokeni alfarmar na amince na auri Imran sbd nuna sha’awarsa da yayi ga aure Dan samun cikakkiyar nutsuwar Bata kulawa shine ta nuna sha’awarta 

Advertisements

nason auren Hadi a tsakaninmu idan har dad Dina ya amince,

Na zauna nayi nazarin maganarta NURU Nima inason kasancewa tareda ita Dan samun lafiyarta Dan Haka na amince da maganar auren saidai bansaniba ko hakan 

danayi nayi daidai kokuwa?….

Ajiyar zuciya ahankali NURU tasaki tana kallon afian cikin tsananin tausayinta da qaunarta sbd a rayuwa tasamu gata da dukiya da kyakkyawan asali da ilimi 

da komaima na rayuwa Allah yabata Amma ta bangaren mahaifiyarta ta hadu da jarabawa me qarfi wadda gashi dai daga karshe tayi sacrificing rayuwarta kacokan 

akan auren Hadi sbd neman lafiya da kawo sauyi a rayuwar uwarta Wanda hakan yaqarawa NURUn ganin girman afian fiyeda koyaushe sbd tabbas tsakaninta da Allah 

Advertisements

takeso da kaunar mahaifiyarta komai halayenta kuwa.

Cikowa idanuwansu duk su biyun sukai da hawaye NURU tace”

Ina Miki fatan kyakkyawar nasara arayuwa fiyeda kowa afia,

Allah ya dasa Jin Dadi da kwanciyar hankali tareda soyayya me girma acikin wannan auren Kuma Inshallah dad dinku ma bazaiqi hakan ba sbd burinsa dama akanki 

karatunki ne Kuma kin kammala Dan Haka burinsa na gaba akanki bazai wuce aurenki ba.

Ahankali ta furta”

Thank you NURU.

Murmushi tasaki tana dafa hannunta ta girgiza Mata Kai.

Washe gari a washe suka tashi kowa da nasa farin cikin sbd takardunsu dasuka fito Kai tsaye tare data aikinsu 

Murna da farin ciki a ranar ma Saida sukai partynsu cikin Palo wannan karon afia harda rawa Tasha 

Farhat da itama farin cikin ganinsu cikin farin ciki duk ya lullubeta itama tasha rawarta duk da Bata iyaba 

Saiga Imran yakira afia din vcall ta zauna sunayi tana gyara gashinta data sauyawa kala daga baqi zuwa dark brown suka fara fira sama sama wadda yawanci 

idone yake kafe dasu sbd wasu halayenta da kyakkyawar kamilalliyar fuskarta dasuka fara saka Masa Sonta.

Mum dinta yafita yakaiwa wayar suka hau murna mum dinta na cewa”

My baby I love Allah ya albarkaci rayuwarku duka.

Amin ta amsa tareda janyo NURU dake can gefe tana waya da Alama duk wanda take wayar dashi yanada mahimmanci a rayuwarta ta kara Mata wayar tana cewa”

Mum ki gaisa da NURU ki tayata murna itama.

Kallon kallo sukayiwa junansu tareda yin tsit na wasu sakanni kafin NURU ta Dan ago tana kakalo murmushi cikin nutsuwa tace”

Ina wuni?

Ya gida?

Ajiyar zuciya tareda numfashi lailah tasaki kafin ta kalli NURUn cikin nutsuwa tace”

Congrats to you.

Thank you.

Sake kallonta lailah tayi tace”

Kiyi hkr da duk abinda yafaru abaya Ina fatan Zaki yafemun komai ya wuce?

Murmushi NURU tasaki tana girgiza Kai a natse tace”

Yariga yawuce na Dade da yafe Miki sbd girma da darajarda afia take dashi a zuciyata.

Nagode sosai” lailan tafada tana sake murmushin daya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta Dora da cewa”

Ina gaida farhat.

Jawo farhat NURUn tayi tana cewa”

Sweetie zo ga mum dinki ki gaisheta.

Zama farhat tayi tana karban wayan fuskarta daukeda farin ciki sbd yanzu tafara sakewa da mum din tasu sbd ta sauya sosai yanzu har cikin ranta takeson 

yayan nata ita Kuma farhat dama tsorone yasata take shakkar kusantar lailan.

Har Imran suka gaisa dashi kafin NURU ta miqe Takoma ga tata wayar datakeyi da Bata oga kwata kwatan Wanda duk wayar datayi da lailah da gaisawa datai da 

Imran duk yanaji Kuma shima hakan yasashi farin ciki ganin atlast dai afia tasamu soyayyar mahaifiyarta dataketa kwadayi tun tasowarta.

Da daddare sbd gajiya tunda suka kwanta Basu farka ba sai qarfe takwas na safe suka miqe cikin sauri sukai sallah kowa yafara Shirin fita aiki musamman afia 

datafi NURU buqatan fita da wuri sbd yanayin aikin nasu ba daya ba.

Cikin ikon Allah kowaccensu tafara aikinta cikin aminci da kwanciyar hankali har sun Dan fara sabawa cikin kwanaki kadan.

Yau NURU ce tajasu suka fita tare suka biya ta ajiye afia asibiti kafin ta wuce gurin aikinta tana sake trying numbern MALEEK dabata shiga tun safe rabonta 

dashi tun jiya cikin Daren dasukai vcall.

Tunanin rashin samunsa yasakar Mata ciwon Kai da damuwa qarshe Bata Bari yamma tayi sosaiba ta tattara ta baro office din harta Kama hanyar zuwa gida ta 

fasa ta nufi asibiti gurin afia sbd tayita kiranta tafada Mata zata wuce gida idan tagama takira zata Aiko Edward yazo ya dauketa Amma afian Kuma Bata dauki 

wayarba shiyasa Mata biyawa asibitin Dole tana sakin Dan qaramin tsaki sbd kanta dake tsananin sarawa

Tana yin parking cikin asibitin saidata dakata cikin motar ta sauke ajiyar zuciya da numfashi sbd yanzu Kam kaman hadda jiri tana gani Haka ta daure ta fito 

sanyeda shades sbd Rana ta nufi ciki.

Direct hanyar office din dazata samu afia wato office din Dr Damien ta nufa saidai kafin ta qarasa tana daf da Isa ta dakata sbd wani jiri daya dibeta tayi 

gefe zata Fadi afia data hangota zuwa ta taso tana kawowa ta tareta cikeda mamaki da ‘yar damuwa tana kallonta tace”

Lafiyanki kuwa???

Gyara tsayuwa NURUn ke kokarin Yi tana Dan dafe goshinta ahankali tace”

Bansaniba kawai ciwon Kaine yake damuna yanzu Kuma Kamar karna baro office jiri yafara kamani Ina ganin stress ne da rashin bacci.

Kallonta afia keyi da kyau kafin ta gangaro da idanuwanta zuwa kirjin NURUn ta kalla tasake maida idanuwanta kan fatar hannuwan NURUn saitaga kaman Bata 

gani sosai ta kalli NURUn tana cewa”

Bana tunanin stress ne kadai muje nadubaki mugani sbd jiri matsala ne zai iya jefar dakai inda zaka halaka kanka.

Suna Shiga office din Dr Damien ta zaunar da NURUn tana juyawa ta dauko ruwa takawo Mata ta Bata Tasha ta durqusa gabanta tana cewa”

Muji pulse dinki.

Bata hannunta tayi ta riqe tana Jin pulse din NURUn tayi shiru zuciyarta na bugawa 

Duk Bata yarda ba ta juya da ita kan gadon scanning din dake office din Dr Damien din NURU ta kwanta tana gyara Mata kafafunta.

Tana Dora Mata abin scanning din take cikin jikin NURUn ya bayyana baro baro ta ajiye abin tana kallon NURU da cikakken mamaki da tsoro harma da shakku da 

firgici duka 

Bakinta na rawa Kai tsaye ta fuxgo kalmar cikin tsananin mamaki tace”

NURU you are 7weeks pregnant.

Da sauri NURU ta kalleta tana saukowa daga gadon tana goge jikinta da tissue ta Dora hannunta kan cikinta cikin son tabbatarwa tace”

Pregnant???

Ni¿

Wani irin Murmushin farin cikin da Bata taba tsammanin yiba ta sake dafe cikin tana dagowa ta kalli afia datai mutuwar tsaye tana kallonta cikin mugun 

mamakin da batasan lokacinda bakinta ya furta”

Dad ne???

Sai alokacin kunyar afia din takama NURU ta Dan takaita farin cikinta tana kallonta ta daga Mata Kai ahankali tana cewa”

Yes wannan qaninki ne afia.

Wani yawun sabon mamaki afia ta hadiye tana sake dulmiya cikin tunani da tsananin mamaki alokaci daya Kuma hadda kunya tana kamata 

Daga ita har NURUn sai suka samu kansu da kunyar juna afian tayi saurin juyawa tana zaro takardar scanning din da batama Gama dubawa ta miqawa NURUn ba 

shiri bakinta na furta”

Congratulations.

Kallonta NURU tayi ahankali tace”

Thank you tana sakin murmushi.

Bakin afia mutuwa yayi murus da mamakin al’amarin dakuma kunyar dad dinta Haka ta raka NURUn har mota Dan Dole itace taja motar tabar gurin aikin ranar 

saidai Kuma gobe suka nufo gida tana satar kallon NURU wadda farin cikine fal cikin ranta Allah zai Bata ‘da ko ‘yar kanta.

Suna shigowa gidan tun daga motocin maleek dake harabar gidan taga alamun an sauya musu parking wanda hakan ke nuni da yadawo kenan 

Cikeda murna ta fito motar tana mantawa da komai ta nufi hanyar office dinsa na cikin gidan dayake aikin office aciki sbd hango Mr Omar agurin tasan Yana 

can Dan Haka ta nufi gurin cikin tsananin farin ciki da murna.

Tsaye suke daga bakin kofa tareda baqinsu ‘yan China dasukazo wani aiki harsun Gama magana sun fito kenan zasu wuce ya hangota tana tahowa 

Sanin sabon daya koya Mata da yanayin yanda take tahowar ya tabbatarda abinda zai faru ya hadiye wani ‘dan yawu ya waiwaya ya kalli Mr Omar Wanda take 

yagane kallon ya matso Yana washewa bakin Baki Yana nuna musu hanya da cewa”

chairman Zhou let me see off please?

Gyada Kai sukai suna sake bawa maleek hannu suka tareda Mr Omar zuwa gurin motocinsu da securities ke zagaye suna jiran fitowarsu.

Da gudu ta qarasa qarasowa ta fada jikinsa tana Dora bakinta kan nasa ta bashi wani lafiyayyan kiss daya sanyashi dagota ya kalli fuskarta kafin yasake 

maida fuskarsa yayi kissing din lips dinta Yana fidda wani lafiyayyan murmushin dayasa afia kusan suman tsaye sbd Bata taba ganinsa akan fuskar dad dintaba 

Ita gabaki daya daburcewa tayi ganin abinda idanuwanta suka ganar Mata wato dai ba yanzu bane al’amarin ke faruwa sbd komai data gani ya nuna dad dinta ya 

dade da tsunduma wata sabuwar daddadar rayuwa hakama NURUn.

Wayyo Allahna” tace tana juyawa da sauri zata bar gurin sbd ita duk kunyar komaiba ya rufeta Jin take Kamar ta nutse a qasa 

Tana juyowa saura kadan suyi Karo da Mr Omar da shima yake tsaye agurin Yana jiran sugama soyewar ya qarasa.

Kallon kallo sukai itada Mr Omar dake sakin murmushin Haka yakeson ganin megidansa ya sake kallon gefen su maleek din ya juyo ya kalleta da ido yayi Mata 

alamar tasake waiwayawa tagani

Ta juya ahankali daidai lokacin NURU ta Dan daga duga duganta takai bakinta kan kunnensa daya rankwafo yana riqeda qugunta cikin rada tace Masa”

_Nenyì Irìguzí_ (Am pregnant).

Wani irin Abu yashigesa ya dagota ahankali yana kallon cikin idanuwanta da ido yake tambayar” da gaske??

Kai ta gyada tana zagayo da hannuwanta qugunsa tana cewa”

And I missed you yau duka bani muryanka ba.

Dago fuskarta yayi ya hade bakinsu yabata wani irin lafiyayyan kiss daya sata kallonsa a kasale tace”

Are you this happy??

Kamar yaro haka ya daga Mata Kai Yana kamo hannunta suka nufo ciki 

Afia da Mr Omar sukai saurin barin gurin har suna ture juna tayi saurin fadawa Palo ta nufi dakinta da gudu tana cewa”

Heyyyy

NURU kin wuce tunanina

Dad kuma bazan iya cewa komaiba sbd yau Naga asalin MALEEK da bakowa zai taba samun damar ganiba sai su Mr Omar ‘yan kullum da kullum din MALEEK.

Suna shigowa dakinsa suka wuce Kai tsaye acan aka qarasa sauran murnar da farin cikin cikin Wanda yasata mamakinsa Dan Bata dauka yanada sauran son haihuwa 

har hakaba.

Sai dare gurin cin abinci Afia tasamu ganinsu lokacin ba kunya NURU tayi wanka tana sanye da wata lalatacciyar riga Mara tsayi Sosai gashinta daure tsakiyar 

Kai kaman baby shikuwa akai akai idanuwansa na kanta 

Duk sai taji abin wani iri saidai Kuma farin cikin data gani taredasu din ya tabbatar Mata da ba qaramin so sukewa juna ba

Ta ajiye spoon dinta ahankali ta dago ta kallesu cikin farin ciki tana murmushi tace”

Congratulations dad you are having  another child Allah yakawo manashi lafiya.

Murmushi yasake Ya kalli afian yace”

Thank you princess Afia.

Da ihu farhat tayi kan NURUn tana cewa”

My aunt zata haifamuna baby me kyau kamanta.

Murmushi NURU tasake tana kissing kumatun farhat din.

Tun daga dining din Babu Wanda yakuma ganin NURU sai washe gari da safe dasuka fito cin abinci sai alokacin afia tabada shawaran NURUn tafara ganin likita 

musamman akan jirin aikuwa ba Bata lokaci Mr Omar dakejin kaman ya taka kan jariri yakira Dr Damien yazo har gida ya duba NURUn daganan yafara zuwa dubata 

akai akai.

Lokacinda su abal dinta suka samu labarin cikin hadda sadaka ammynta tayi meryam kuwa tuni tafara takura tanason zuwa gurin NURUn saigashi kuwa maleek da 

kansa yasa jekadi taje har Delah ta daukota dama Kuma itama jekadin tana Shirin zuwa ne harsai NURUn ta haihu.

Zuwan jekadi da meryam da sati biyu maleek ya dauketa suka tafi _Maldives_ inda sukai zamansu acan suna hutawa Saida cikin yashiga wata na budu kafin suka 

dawo lokacin anfara maganar auren afia Imran Wanda tun kafin suyi tafiya dad din Imran din ya nemesa yayi magana da afia tace da amincewarta take yace ya 

Basu aka tsaida Rana.

Imran yadawo Paris gabaki daya da lailah sbd gidansa a Nan Paris yake bazai zauna gidan mahaifin matarsa ba ba girma bane Dan Haka murna kan murna agurinsu 

NURUn da afian sbd bazasuyi nesa da juna ba take aka hau Shirin biki gadan gadan musamman uwar amarya lailah da ba laifi yanzu ta warke harta fara komawa 

ayyukanta zata fara daga farko Dan ma a qarqashin kamfanin dad din Imran din take aiki.

Sosai akai shagali a gizah na auren afia din Wanda hatta iyayen NURU sun halarto tareda kaleeb sosai tayi farin cikin ganin iyayenta Suma sunyi farin cikin 

ganinta musamman cikinta daya fara tsufa a gizah kowa yasan MALEEK na gaf da samun magaji kila suke fata.

Padima dai ba laifi tananan sama sama wani lokacin kalau wani lokacin Kuma abin ya Dan juye ahaka aka gama bikin suka tattara suka dawo Paris afia ta tare a 

babban gidan mijinta Wanda mum dinta take sashe guda na musamman da Imran din ya ware Mata.

Ranarda afia tacika wata hudu cif da aure ranar nakuda ta tasowa NURU 

Maleek ya tattara mulkin da sarautar ya ajiye suka dunguma zuwa asibiti sbd ganin gidan zata wahala bazai iya jure ganin hakan ba 

Saigashi cikin ikon Allah suna Isa ta haifi qatoton jaririnta me Kama da farhat sak.

Koda maleek ya karbi Dan wata hamdala yasaki Yana godewa ubangiji yayi Masa huduba da sunan Mr Omar tareda yiwa Mr Omar wata gagarumar kyautar datasaka Mr 

Omar din rungumesa Yana hawayen godiya duk dai yatara tarin dukiya me yawa a qarqashin maleek din Amma sai bazai iya dainawa maleek din aiki ba sbd sunzama 

kaman jini.

Acikin motarsu ta dawowa gida duk yabita ya lashe da kisses itada baby Omar Wanda hotonsa tuni yafara yaduwa a duniya Matar UBAYD MALEEK me gizah ta haifar 

Masa baby boy.

Daqyar ya suka iya raba gurin kwanciya sbd jekadi data Dan sako NURUn agaba har aka samu sukai 50days daga Nan delah suka tafi tayi sati biyu gurin iyayenta 

daganan suka dawo gizah tayi kwana biyar kafin tadawo Paris su afia sukazo aka wuni gidan suna Yan kus kus dinsu na kayan datazo dasu suka raba 

Washe garin ranar maleek ya dauketa suka tafiyarsu _Santorini_ sbd wata sabuwar duniyar da NURUn ta jefasa a Daren jiyan inda sukai wata daya kafin suka 

dawo 

Saidai Koda ta dawo da sabon ciki ajikinta wanda yazo Mata da Dan laulayi da son jiki Haka shima duk ya shirirce gurin tattalinta da jinya sbd koyaushe tana 

lafe ajikinsa karshe dai Mr Omar Dole ya rungumi wasu ayyukan da kansa yakeyi a office.

##MAMUH#

*ALHAMDULILLAH YA ALLAH*

*MUNZO QARSHEN WANNAN LABARIN ME SUNA UBAYD MALEEK WANDA NAKE FATAN KURA KUREN CIKI DA ABUBUWAN DANAYI BA DAIDAIBA ACIKI ALLAH YA YAFEMABA GABAKI DAYA 

HAKAMA KURAKURAI IRIN NA MANTUWA DA TYPING ERROR DUK INA FATAN ZAKUMIN UZURI HAKAMA WAINDA ZASUGA BAI KAI MUSU INDA SUKESO BA SUYI HAKURI AMMA DAI KYAN L

LABARI AGAMASHI ANA MARMARINSA BASAI MUNKAI INDA ZAKUJI YA GUNDUREKU BA NIMA BASAI NAKAI INDA RUBUTASABA ZAI GUNDURENI DAN HAKA INA FATAN NUSHANDIN YAYI 

DAIDAI YANDA ZA’A DADE ANA TUNAWA*

*NAGODE SOSAI SOSAI DA KAUNA DA KUKA NUNAWA LABARIN KUMA INSHALLAH INA MANA FATAN HADEWA A GABA DA LABARIN DAZAIFI UBAYD DA NURU DADI* 😜😜

*NAGODE*

*_MAMUHGEE_* 💋

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like