WATA TAFIYAR 10

Advertisement

 🦚WATA TAFIYAR🦚

       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟

*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*

Advertisements

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“🌍`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAID BOOK

                    

                10

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Advertisements

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

A lokacin da labarin canjin dauren Auren ya riske Nanne,shiru kawai ta yi ba tace komai ba,duk yanda ƴan gulma suka so su ji ko su gani daga Nanne gaba ɗaya ta toshe wannan hanyar,abin da basu sani ba kuwa shi ne tun lokacin da aka saka bikin Asma’u da wannan yaron ita kanta hankalin ta bawai ya kwanta bane da yaron,shi yasa ta dage da addu’o’i ba dare ba rana,sannan tasha yin Istihara amma abin mamaki shi ne ba wannan yaron take gani ba,wani daban take gani,sosai ta dage da addu’a akan lamarin gashi kuma ba a fasa da shi ba,shi yasa kawai ta barma Allah lamarin shi,to sai gashi yanzun ta samu labarin wai an samu canji,hamdala ta yi domin ta tabbatar wannan wani hikima ne na Ubangiji kuma shi yasan dalilin yin haka. 

Baba Mudansir ne ya shigu dakin hankalin shi a tashe ko sallama bai samu damar yi ba”innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun,Nanne waɗannan mutanin sun munafurcemu,sun kuma cutar da yardar mu,Nanne ya zamu yi sun canja auren Asma’u ga wanda muke tunanin mutacce ne”gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake, tsabar kunan da ran shi ke yi,har bai san sanda hawayen takaici ke bin kuncin shi ba. 

Kama hannun shi ta yi,sannan ta zaunar da shi bakin gado,ruwan da ke ajiye bakin gado ta dauka ta tsiyaya mashi a cofi ta mika mashi,”amsa ka sha”

Amsa yayi ya shanye,ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. 

“Ka kwantar da hankalin ka Mudansir,domin na riga nasan abin da ke faruwa,duk abin da ka ga ya faru to da sanin Ubangiji,yaron ya aka ɗaura ma Asma’u aure da shi ba mutacce ba domin na tabbatar duk jahilcin su to ba zasu taba yin haka ba,abin da nake so da kai shi ne kar ka ce komai,kawai kuje kai da su kai ma ƴar ka rakiya har dakin mijinta,mu kuma sai mu dinga binta da addu’a,na tabbatar da duk in da take addu’ar mu zai isa gare ta,har ma da shi mijin nata”dan juyawa bayan ta ta yi “Asma’u in fatan kin fahimce ni? shi sam bai ma lura da ita dake zaune saman gado ba dan hankalin shi a tashe ya shigo. 

Cikin natsuwa tace ” Na fahimta Nanne “

“Yauwa Fettel,sannan abin da nake so dake shi ne ki zama mace mai juriya da duk halin da ta tsince kanta,kar ki zama mai baiyana halin mijin ta,sannan a duk lokacin da kike da wata matsala to ki tuna ki nada dangi masu ƙaunar ki,,kuma  masu son ki,,ki saka hakan a zuciyar ki,a duk lokacin da kike bukatar mu to ki kira mu zamu kasance tare dake duk runtsi duk wuya,ina fatan kar ki manta hakan”

Hawayen idon ta ta share”insha Allahu Nanne “

“Yauwa to tashi ki ƙara kintsawa sai ku tafi,dan kar abar su suna jira,, Mudansir kai kuma sai kaje ka sanar dasu ga ta nan fitowa”

Kai kawai ya iya gyaɗa mata, yana mai matukar tausayi ƴar tsohuwar,ɗan ya tabbatar da daurewa kawai take yi,amma ba komai zai yi kamar yanda take so. 

Ko da ya fito kofar gida anan ya tadda su Ɗan Nanne zazzaune a saman kujeru,ai kuwa suna ganin shi suka kwashe da dariya,Baba Sani ne yace”uban Amarya ina kuma zaka naga kana zuba sauri”ya karasa faɗa cikin salon shaki yanci, suna kara fashewa da dariya. 

Murmushi ya aro ya daura saman fuskan shi”Yaya Sani kenan,sauri nake na faɗa masu su tsaya a tafi da amarya tunda an riga an daura auren”

Baba Auwalu ne yace”to in banda abin ka Mudansir gidan mutaccen zaka kai Shalelen taka”

Shi dai Ɗan Nanne bai ce masu kala ba, 

“Ai in da ƙara ita din ƴar ku ce”yana kaiwa nan ya juya ya wuce,dan ya hango su uncle Ahmad na ƙoƙarin shiga mota,dakatar dasu yayi” Ina kuma zaka je bayan kace tare da Amaryar za a wuce”

Duk juyowa suka yi suna kallon shi domin basuyi tunanin yanda ya dauki fushi ba zai yi saurin saukowa haka ba. 

“Ai na ɗauka ka yi fushi ne”in ji uncle Tahir. 

Ɗan murmushi ya yi” Eh na yi fushi kam a dazu,amma yanzun kuma na sauko,dan haka ku tsaya kawai sai mu kai ta gidan ta tare”

Sosai suka yi farin ciki da wannan abin,dan haka hira suka shiga janshi da shi har zuwa sanda Inna Saude da wasu matan dangin Baban ta su biyu suka rukota har baƙin wani Dalleliyar mota wanda suka zo da shi,sauran matan na ƙoƙarin shiga bayan sun sakata ne,wata  mata wacce ke sanye da Leshi ruwan madara wanda kallon ɗaya zaka mai kasan ba da ƙaramin kuɗi aka siye shi ba,sannan fuskan ta a rufe yake ruf da mayafin ya,ta yanda duk kallon mutum bai isa ya shaida kamannin ta ba,ita ta dakatar da su”bayin Allah ku shiga ɗayan motan can dan kar amarya ta matsu,kasancewar sun ga yanayin ta yasa suka dauka ko tana cikin dangin Angon ne,dan haka juyawa suka yi suka shiga ɗayan motar yayin da ita kuma matar ta shiga motar da Asma’u take wanda ya zamana daga ita sai Asma’u a bayan motar, sai direba a gaba shida Baba Mudasiru. 

 A hankali motacin ke tashi suna barin layin unguwar suna hawa titi da kyau,dan unguwar M Y Wushishi za a kai ta,wai nanne gidan mijinta yake. 

Ganin sun hau titi sosai ne yasa matar  wacce bansan sunan taba,ban maga fuskanta ba,ta rike mata hannu da ɗan ƙarfi amma ba yanda za ta ji zafi ba,ganin ta juyo tana kallon ta ne yasa cikin ƙasa da murya irin ta masu raɗa ta shiga faɗa mata wasu maganganun wanda ƙwaƙwalwar ta ta kasa ɗauka,ta kuma kasa fahimtar in da ta dosa,dan ce mata ta yi “Asma’u ɗan Allah ki zama mai wayau mai kuma lura,mijin ki na cikin wani hali yana kuma buƙatar taimakon ki,idan kin shiga gidan a matsayin matar shi,to zasu kawo miki wasu takardu  ki saka masu hannu,dan Allah ina rokon ki koda wasa kar ki yarda kisa, haka kuma duk wuya duk rintsi kar kisa hannu a takardun nan,domin a lokacin da ki ka rattaba hannu akan su, to a lokacin za ku bar duniya ke da mijin ki,dan Allah ki yi amfani da ilimin ki,ki nuna masu ke ba mahaukaciya bane kamar yadda suka dauka,ki shayar dasu mamaki,sannan daga karshe, duk wani hanyan da za ki bi ki bi domin ganin kin gudu da Zabihullah daga cikin gidan nan ko ta halin yaya ki samu ku gudu,kuma kasar zaku bari baki daya ba wai garin ba,domin duk in da kike tunanin ɓoyewa ina mai tabbatar miki sai sun riga ki zuwa”wani irin zobe mai azababben kyau ta ciri a hannun ta ta kamo yatsar Asma’u ta saka mata”wannan zoben na tabbatar da zai taimaka maki ta wani hanyar idan kika sai da shi,amma a lokacin da kuke bukatar barin katsar domin na tabbatar da kudin wannan zoben zai isheku rabin rayuwa,kuje wata ƙasa mai nisan gaske ki nima ma mijinki lafiya har zuwa lokacin da zai dawo haiyacinshi,ki kula sosai Asma’u domin a yanzun haka zayuwarku na cikin hatsari,ni ba lallai bane ki kara ganina domin yanzun haka nima na suke su kashe ni,idan kuma har muna da rabon haɗuwa,to ina mai rokon Allah daya hadamu cikin kyakkyawan yanayi,”a dai-dai nan akayi parking motocin cikin dankareren gidan wanda tsabar rudewa da tashin hankali da kalaman matar duka jefa ta a ciki yasa bata masan da isowar su ba,haka kuma tana kallon sanda matar ta yi saurin bude kofar motar ta fita, tabi ta bayan fulawoyin ta bar cikin gidan da sauri, ita ba wawuya ɓace kamar yanda mutane da yawa suke ɗaukar ta mara wayau,duk da ta san tana da matsala amma ba wai sun cire mata hankalin ta gaba ɗaya bane, sai dai ace sun taɓa mata wani sashi na tunanin ta,kamar ace cikin kashi ɗari to sun taɓa kashi ishirin,lallai tana cikin tashin hankali da tsaka mai wuya, amma kuma anya maganar matar nan gaskiya ne kuma, to koma dai menene ta tabbatar da zata gani da idon ta,in ma da gaske take ko akasin haka, amma kuma yanayin matar bai yi mata kama da makaryaciya ba,to yanzun ya zata yi idan maganar matar ya kasance gaskiya,to fa ta tabbatar da ta shiga uku, Allah dai yasa ba kaha bane, wannan ne kaɗai  fatanta.

Buɗe mata ƙofar da Baba Mudasiru yayi ne ya dawo da ita hankalin ta”fito da Bismillah Asma’u “….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like