Advertisement
🦚WATA TAFIYAR🦚
Story & Written
By
Jiddarh Umar
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*
Advertisements
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAID BOOK
Free Page
03
Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank,
Advertisements
Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.
Ko Katin Waya.
Zaune yake a bakin ruwa yana shan iska,sanye yake da ƙananan kaya irin na turawa,gaba ɗaya hankalin shi na kan waɗansu turawa dake rawa abikin ruwan daga su sai ɗan kanfai (Pant) hankalin su kwance,kallon su yake a zahiri amma a zahirin gaskiya ba a kansu hankalin shi ya ke ba,domin yayi nisa wurin tunanin ta yanda zai samo ma kanshi mafita a wannan lamarin,duk ta in da yake tunanin lamarin zai zo da sauƙi,amma abin nema yake yafi ƙarfin tunanin shi,
Jin ƙarar wayar shi ne yasa ya dawo haiyacin shi,ya sauke ƙarfaffan ajiyar zuciya,
Ɗaukar dalleliyar wayar shi yayi Samsung S21 Al/Tra,wanda a ƙalla kudin ta zai tasarma dubu dari bakwai,cikin yanayi na kasala irin na wanda ya gaji da tunanin niman mafita ya ƙara wayar a kunnen shi,
“Uncle”
Cikin masifa na ɗayan ɓangaren yace” HARIS ZAMIR,ka fita a ido na fa, wai me yasa kai ba kajin magana ne?
“Uncle!!
” Pls ya isa haka ba na son jin wata magana daga bakin ka,dan haka na baka daga nan zuwa gobe ka baro Malaysia ka dawo Nigeria,duk ma yanda za ayi ayi, haba ace sayin shakara uku kenan har yanzun ana abu ɗaya yaki ci yaki cinyewa,to a gaskiya na gaji,gara ka dawo a san abin yi, dan wannan karon banga abin da zaisa in daga ƙafa ba”yana gama faɗar hakan ya kashe wayar.
Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa,kai shikam Allah ya nuna mashi ƙarshen wannan abin kowa ma ya huta,, tashi yayi daga bakin ruwan yana karkade jikin shi,saboda yashin wurin,a hankali yake ta fiya,har zuwa bakin wata dalleliyar mota, wanda yana isa wani Bature ya buɗe masa kofar motar da sauri, shi kuma ya shiga,wani madaidaicin gida aka buɗe masu Get din suka shiga,gaskiya gidan ya haɗu ba ƙarya,ƙarami ne madaidaici amma yana yin tsarin gidan kadai ya isa ya tafi da imanin mutum,,kamar dai dazu haka ma yanzun yazo ya buɗe mai motar ya fita,kai tsaye cikin gidan ya shiga,dan a zuciyar shi yake raya gara yaje ya fara haɗa kayan shi kafin Uncle ya ƙara kira,dan ya san wannan karon in bai koma Najeriya ba ys tabbatar yana iya biyo shi ya koma da shi.
GIDAN ƊAN NANNE
Sai da ta tabbatar ta daku tukunna sannan ta kyale ta, tana ci gaba da masifa, yayin da Baba Sani ke taya ta”yar banzan yarinya,wacce ake gudar mata wahala amma ita tana rungumar shi,to in ƙara ganin ki da ita,in ba shashaba duk cikin yaran gidan nan wakike gani tare da ita in ba ke,ba gasu Karima, Maimuna,Salma,amma baka ganin kowa kusa da ita sai ke,tunda su sunfi ki wayau,to ba da ni za ayi wannan ba,in ƙara ganin koda kafar ki ne a shiyar bama tare da ita ba saina kusa kashe ki a gidan nan”ranar dai Islamiyar da Hafiza bata jeba kenan.
Tun bayan wucewar Hafiza take zaune a binta,can kamar kuma wacce aka tsikara ta tashi ta shiga haɗa kayanta, sai da ta haɗa iya wanda zata iya ɗauka,sannan ta daura a kai ta fito,dakin Inna Saude ta leka,ganin bata ciki yasa ta nufe kicin dan ta san zuwa wannan lokacin ta na kicin din, ai kuwa anan ta tarar da ita,
“Inna”
Da sauri ta juyo ganin ita ce yasa ta sauke ajiyar zuciya,dan sam ba ta ji zuwan taba,sai Sunnan ta da ta ji an kira gata kuma a tsaye da kullin kaya a kai,
“Na’am Asma’u, ya aka yi ne, ina kuma zaki da wannan kullin kayan?
Dariya ta yi wanda ya ƙara baiyana fararan haƙoran ta, wanda suke jere a bakinta da ɗan wushiryan ta sama da ƙasa” Inna zan koma ne gidan Malam “
Kallon ta Inna Saude ke yi tana salati”Ya Allah daga gareka muke,kuma daga gare ka muke niman taimako,wai ni Allah ka gwada min ƙarshen wannan abin”ƙara kallon Asma’u ta yi, wacce ke tsaye sai wage mata baki take yi.
Wani miyau na fargaba ta haɗiye,,dan ta san yanzun tsayar da Asma’u ba ƙaramin abu bane a yanzun, to ya zata yi,wani dubara ne ya faɗo mata,kallon ta ta yi,cikin duba ta ce “yauwa Asma’u dama akwai wani tsakon da nake son in baki ki kai ma Malam”
Dan waro ido waje ta yi “da gaske Inna”
Itama murmushi dole ta kakaro,domin Allah ya gani tana tsoron haukan Asma’u,sai dai kuma ba yanda za ayi tana ganin ta ta barta ta fita ta koma gidan Malam bancin an raba auren su ko,ita tana tsoron mai zai je ya dawo,sai dai fa duk da haka sai ta gwada ta gani.
“Sosai ma, zo muje ki karɓa”
Da murnar ta kuwa tabi bayan ta, har cikin ɗakin Asma’u suka shiga,kamar gaskiya kuwa ta fara dube buɗe,”Inna a dakina kika ayiye abun”
“Eh A’a kai ina zuwa zauna a nan ki jira ni”har ta juya sai kuma ta dawo ta riƙe hannun ta suka zauna bakin gado,” Asma’u na”
“Na’am Inna”
“Kin ga dare yayi, mai zai hana ki bari gobe sai mu je tare in raka ki gidan Malam din”
Ɓata fuska ta yi,tana fisge hannun ta, cikin magana irin na wanda ya ji haushi ta ce”A’a ni ba zan bari sai gobe ba,Malam na jira na, kawai in zaki ki zo mu tafi tare”
Ajiyar zuciya ta sauke”to ina zuwa,bari in dauko maki,, zauna nan ki jira ni”
Da sauri ta fita,tana fitowa kuwa da sauri ta kullo mata ƙofar ta saka key ta datse ƙofar da shi,tana jin yanda Asma’u ke dukan kofar kamar zata balla shi tana kuma ihu ta zo ta buɗe ta zata koma gidan Malam ne,
Banza ta yi da ita,”da in barki ki tafi gidan nan,ai har gara ki ta haukanki a ɗaki,kuma Allah ya kai mu gobe da kaina zan faɗa ma Yaya Mudansir ya ja masa kunne karya ƙara kawo mata wani abinci a gidan nan tunda bata rasa komai ba anan,kuma haka kawai bancin ansamu yarinya ta dan fara manta shi,shine yanzun ya ke bullo mata ta haka,dan ta lura yanzun da zaran ta ci wani abu na hannun shi, to ranar ta dungan hauka kenan akan sai ta koma gidan shi, haba ita ta gaji da wannan lamarin dole a taka mai birki.
Daren ranar Ahalin gidan Nanne basu yi barci ba,domin irin haukan da ta kwana tana yi,yayin da wasu suka kwana tsine mata Albarka, a kuma wannan lokacin tsohuwa Nanne ke zaune saman Darduma tana nimar mata sauki wurin Ubangiji,ranar dai haka suka wayi gari.
Washegari da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana jirgin su ya sauka a Abuja,yana fitowa daga cikin Airport din kalle kalle yake ta ina zai ga masu kai shi gida,
Ji yayi an rungume shi ta baya, da sauri ya juyo,ganin wanda ya ke tsaye yana mai dariya ne yasa shima yayi dariya ya jawo shi jikin shi suka ƙara rungume juna, “ai nasan sai kai, to sake ni karka karya ni”
“Yaya Haris kana kallon kanka kuwa a madubi, kaga kuwa yanda ka zama”
Dariya yayi”kai ni kan mu je kar ka cika ni da wannan surutun naka”buɗe masu ɗaya daga cikin jerin motocin da aka zo dashi domin daukar su aka yi,suna shiga aka ɗauki hanyar Minna da su, jifa-jifa suke hira da Asim har suka iso cikin garin Minna wanda kai tsaye unguwar Millioniar Cutters,wani tangamemen Get aka buɗe masu suka shiga,ganin su a gida yasa ya sauke nauyayyen ajiyar zuciya yana kuma hamdala a zuciyar shi,bude masu kofofin a kayi suka fito,
Da Uncle Tahir ya fara cin karo a tsaye yana jiran karasowar shi,ɗan ɓata fuska ya yi, ganin yanda sai wani washe baki yake kamar bashi ya gama azal-zalan shi daya dawo gida ba jiya,ya na karasowa ya rungume shi “barka da dawowa ƙasarka ta haihuwa,da fatan ka dawo lafiya”
Shima dan sake fuska ya yi “lafiya Uncle,na same ku lafiya” daganan ciki suka shiga,har bakin kofar shiyan shi ya raka shi”kayi wanka ka ci abinci sai kazo mu yi magana dan suna babban falo kai kaɗai dama ake kira”
Gyaɗa kai kawai ya yi, sannan ya shige cikin.
Unguwan Daji,Gidan Ɗan Nanne
Ba ita ta buɗe ta ba sai da takwas na safe,saboda zuwa lokacin yawanci mutanin gidan sun ragu,tana buɗewa ta da sallama ta shiga ɗakin,zaune ta same ta kamar ko wani lokaci da sandanta a hannu,sai dai wannan karon yanda kasan mahaukaciya sabon kamu,dan yanda ta bar baza suman kanta ya sauko mata har gadon baya,ga idonta da yayi zuru zuru sai zare su take yi,alamun dai yau akwai rigima ke nan. A hankali ta ƙira sunan ta”Asma’u “banza ta yi da ita,ƙara kiran sunan ta ta yi nan ma shiru ta mata sai uban harara data maka mata,” Taso muke Nanne na kiran ki”
Jin ance Nanne na kiran ta yasa ta ja wani uban tsaki ta murguda mata baki,,sannan ta tashi ta fita abin da,
ɗakin ta fita bako ɗankwali akanta yasa da sauri tabi bayan ta,”Asma’u zo kisa ɗanƙwalli, tsaya in kawo maki”amma ina kamar ba da Ita ake magana ba, dan ma tuni ta shige shiyan Nanne, wacce ke zaune kawai sai ganin mutun ta yi tsaye a kanta”na shiga uku, ke me haka, kin tsayamin aka”
Hararan Nanne ta yi, ganin haka yasa ta gane yau ƴan iskan na kusa ke nan, “to Allah ya kyauta,ni ma wuri ki zauna” Sai da ta ja mata tsaki sannan ta zauna,kallon-kallo suka shiga yima juna tsakanin ta da Nanne,
Can dai da abin ya ishe ta,ta kalli Asma’u taga sai faman hararan ta take tana murguda mata baki”Allah ya tsine maku Albarka,ƴan shegu marasa kunyan fitsararru,ni dai ba haka jikana take ba, kuma in Allah ya yarda ba abin da za ku yi da ita,jikata tafi karfin shaidanu irin ku,”
Tsaki mai ƙarfi ta ja tana ƙara murguda ma Nanne baƙi,
Allah sarki tsohuwa, sai kawai ta fashe da kuka”debabbun Albarka,kukan ko a cikin jinsin Aljannu daga ganin ku ƴan Ta’adda ne “
Shigowar Salma da Karima ne ya katse mata surutan da take yi, sai dai ba ta bar kuka ba da facen majina,
“A’a Nanne lafiya,waya taɓa ki” Cewar Salma.
Ita dai Karima kallon abin da Asma’u take yi kawai ta ke.
Cikin kuka ta ce “ni da waɗannan yan Ta’adda ne”
Gaba ɗayansu kallon ta suka yi,Karima ce ta ce”ina suke”ƙara fashewa ta yi da kuka tana muna masu Asma’u dake zaune ta daura ƙafa ɗaya kan ɗaya,
Gaba ɗayan su, lokaci ɗaya suka kwashe da dariya har da tafa hannu,suna nuna Nenne su nuna Asma’u,ita dai sai tsaki take tana yamutse fuska,
Tsawan da Baba Mudansir ya masu shi ya dakatar da su, dan shigowar shi kenan.
Millioniar Cutters
Zaune suke a wani ƙayataccen falo,su uku ne shine cikon na huɗun su,Uncle Nasir,,Uncle Tahir,Uncle Ahmad, sai shi,gaba ɗayansu zaune suke saman tebur dake ɗauke da kujeru, magana suke yi,,
Uncle Nasir ne ye”a gaskiya lokaci ya yi da ya kamata ace mun kawo karshen wannan abun,dan shekara uku ba wasa ba ne “
“Maganar ka gaskiya ne,ni kaina matse nake da wannan lamari” Cewar Uncle Tahir.
“A gani na Aure kawai ya kamata mu yi ma shi,kaga ta hakanne za musamu cikar burin mu na shekara da shekaru” In ji Uncle Ahmad.
Gabaɗaya hada baki suka yi wurin kiran kalmar Aure,har dashi uban gaiya.
Cikin ɓata fuska yace”Uncle Aure fa, ta ya ya, a hakan”
Basu amsa yayi”saboda ta hanyar matar kadai zamu iya samun abin da muke so”
Gaba ɗayansu shiru suka yi suna nazarin maganar shi, Uncle Tahir ne yace”wacce irin mace ya kamata ya Aura,”kallon Haris ya yi “ko kana da wacce kake so ne?
Girgiza kai ya yi” Babu sai dai ko zan bincika”
“To in ma kai zaka bincika ko mu zamu bincika ma, ya kasance ko ma wacece,dole zai kasance wacce ba ta yi zurfi a karatun Boko ba,ba ta da wayau sosai, ba ta da cikken hankali,,ina fata kun gane,kuma ba na son a ɓata lokaci”cewar Uncle Ahmad.
” Ta yaya zamu samu irin wannan yarinyar,kasan yaran yanzun da shegen wayau”Uncle Nasir ya fada
“Ai shi yasa nace mara hankali”
Haris ne ya katse su”shi kanan zan samo irin matar da kuke so in aura,zan nemo irin ta a duk in da ita”yana kaiwa nan ya tashi ya fita.
To fa akwai magana kenan a ƙasa……
GIPHY App Key not set. Please check settings