Advertisement
🦚WATA TAFIYAR🦚
Story & Written
By
Jiddarh Umar
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*
Advertisements
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAID BOOK
Free Page
08
Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank,
Advertisements
Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.
Ko Katin Waya.
Zaune take kusa Nanne wacce ta aika aka kira ta tun kusan mintuna goma da suka wuce,ta sata a gaba sai wani irin kallo take mata wanda ita sam bata gane na menene ba,ga dai shi kamar kallon ina tausayawa rayuwar ki,kuma kamar kallon zan yi kewar ki,ganin abin bana ƙarewa bane yasa cikin ƴar ƙaramar muryar ta mai haɗe da shagwaba ta ce”Nanne,gani”
Wani irin sanyayyar murmushi ta yi,ganin abin da Asma’u ta yi,wanda a zahirin gaskiya ta jima ba taga ta yi shi ba,to wanda ba ko yaushe yake cikin hankalin shi ba,ina yaga ta yin wani shagwaba.
“Ai na ganki”
“To kice wani abu mana,ko dai dama kin kirani ne dan kawai ki ta kallon fuska ta kina jin daɗi” ta ƙarasa faɗa da dan zolaya.
Dariya ma taba Nanne,dan haka ta ɗan dara”magana zamu yi dake mai muhimmanci Fettel”ta kasara faɗa da muryan maida hankali.
Ganin haka ne yasa ita ma ta natsu “Ina sauraron ki Nanne”
Ajiyar zuciya ta sauke “Fettel ni wacece a wurin ki?
Ɗan shiru ta yi tana duban ta da mamaki, to me yasa kuma take mata wannan tambayar”Ke ɓangare biyu ne na rayuwa ta,na farko ke uwa ce a wuri na, na biyu ke Kaka ce a wuri na”
“Da kyau,to shi kuma Mudansir fa,waye shi a wurin ki?
Ji ta yi jikinta ya fara sanyi game da waɗannan tambayoyi na Nanne” Shi ma matsayi biyu gare shi a rayuwa ta,na farko matsayin Uba, na biyu kuma matsayin Kawu,?
“Alhamdulillah da kika bamu wannan matsayin,ina son ki sani duk abin da kaga ya faru da Bawa to muƙaddari ne daga Allah,kai ma kuma sai ka ƙaddara hakan ne mai ƙyau,kamar dai wannan abin da ya faru tsakanin ki da Mallam tunda daga haɗuwar ku,yin auren ku,da kuma raba auren ku,wannan duk hukunci ne na Allah kuma shi yasan dalilin shi na yin haka kuma ya barma kan shi sanin haka,wannan rashin lafiyar da kike fama da shi,Allah ne ya bata ikon da zata cutar dake bawai kuma dan be son ki ba, A’a sai dan ya jarraba imanin ki,wanda kuma ko wani Bawa na fata yaci tashi jarabawar”dan shiru ta yi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ci gaba”A jiya wanda kika kira da sunan mahaifi ya bada Auren ki ga wani,
Ina mai fata ki bi umarnin shi kamar yanda zaki bi umarnin mahaifin ki, ina mai fatan ba zaki bijire masa ko ki watsa masa ƙasa a ido ba,Fettel ina da yakinin zaki bi umarnin mu,ina rokon ki kar ki kunyata kawun ki “ta ƙarasa faɗa tana haɗa hannayen ta biyu alamun roko.
Da sauri ta ɗaura hannayen ta itama saman na Nanne,yayin da wasu irin hawaye ke zubo mata wani na bin wani tsabar yanda maganar ta dake zuciyar ta a lokaci guda,da kuma irin maganganun da Nanne ta fada” Ɗan Allah Nanne ki sauke hannun ki,ni ba sai kin roƙe ni ba,halan baki san irin darajan da kuke dashi bane a wuri na Nanne? Da kin sani da baki tsaya ɓata bakin kiba wurin roƙo na sai dai kawai ku ban umarni,kuma wallahi zan yi” ta faɗa tana sauke wani nishin kuka mai haɗe da shassheka”Ku ne rayuwa ta, ku ne duniya ta,ba ni da wasu bayan ku,domin da ku na fara tozali a lokacin da ido na suka fara ganin mutane,haka kuma daku na fara cin karo a lokacin da na fara tafiya,ta yaya za a yi na iya bijire ma maganar ku,Nanne na amince zan aure shi,koma wanene shi,tunda har kuka amince da shi nasan ba zai cutar da ni ba,domin nasan ba za ku Bani wanda zai cutar dani ba ko kaɗan,na yarda daku kuma nayi imani da zaɓin ku”tana kai nan ta fashe da kuka yayin da ta kifa kanta a cinyar Nanne,sosai ta yi kuka yayin da Nanna ke ci gaba da mata nasiha akan yarda da Ƙaddara, sai da ta tabbatar da ta samu natsuwa sannan ta ɗaga ta”zuwa bayan sallar La’asar zai zo sai ku gaisa,dan Allah kar ki nuna mai komai kin ji ko?
Kai kawai ta gyaɗa mata,sannan ta yi mata sallama ta koma shiyan su,wanda da kyar ta kai kanta, tana shiga daki kan gado ta ƙara faɗawa tana kara fashewa da kuka,wannan wani irin rayuwa ne haka,ita dai abu ɗaya ne ta sani shine su Nanne ba zasu taɓa yin abin da zai cutar da ita ba,amma shi wani irin mutum ne da har zai iya cewa zai aure ta a haka, to kodai besan irin laluran dake tare da ita ba ne,a bayyane ta ce”Allah kasa hakan ya zama Alhairi ga rayuwata dama Ahlina gaba ɗaya”
Sai misalin karfe huɗu da rabi Habu ya kawo shi har ƙofar gidan,sannan ya shigar da shi falon baƙi,dan sun riga sun yi waya da Baba Mudansir,shi ne ma yace in sunzo ya sauke shi falon baƙi sai ya shiga ya kira Asma’u.
Tun daga shigowar motar su cikin unguwar har izuwa parking din su kofar gidan Ɗan Nanne ba karamin mamaki mutane suke ba,dan abin bai kara daure masu kai ba har sai da suka ga wanda ya fito cikin motar ya shiga cikin gidan Ɗan Nanne,domin Haris Allah ya mishi baiwar iya ɗaukan wanka,wanda a duk inda ya shiga dole a juyo a dube shi,amma in ɗayan ba ya nan, dan masu iya magana suka ce,ko Baba ma da Baban shi, kasancewar bayan sallar La’asar ne yawancin matasa duk sun dawo aiki,sai zaman canba da aka ɗaura, yasa duk in da suka gifta sai an bi su da kallo.
Tunda ya shigo unguwar yake ƙara masu kallo,kai shi kam su uncle sun cuce shi,yanzun a irin wannan unguwar zai dauki mata,kuma wai mahaukaciya,ko da yake idan ya tuna wasu abubuwa yakan ji sauki a ran shi game da hakan,har ma wani bi ya tsinci kan shi cikin farin ciki,ajiyar zuciya ya sauke ganin sun tsaya a wani Kangwon gida in ji shi wai gidan Ɗan Nanne ne Kangwon gida,jagora Habu ya mai har cikin falon gidan wanda ba laifi,amma a wurin shi wannan falon ko me ba Fulawoyin gidan shi ruwa ya tabbatar falon gidan shi yafi wannan,shi wallahi da badun yasan abin da zai samu akan wannan auren ba da ko motar shi yarinyar ta taɓa to sai an wanke ta,da kyar da Kyankyami ya samu ya ɗan dosana a kujera kasancewar ya ji alamun za a shigo,
Da sallama ta shigo falon,sai data jira ya bata amsa sannan ta ƙarasa shiga,ɗan nisa da shi ta zauna kanta a ƙasa,
“Ina wuni” ta faɗa cikin sanyin murya.
Tunda ta shigo yake kare mata kallo,shi wallahi da badun lamarin iskokan yarinyar ba,da kuma planning din su a kanta,wannan in ta samu wanka ba ƙaramar mace za a yi ba,dan yarinyar ta ko’ina a cike take,daga sama har ƙasa,kalan Skin ɗinta kuwa shi ake kira one in town,kalan ruwan zuma farar saƙa,wanda zaka ganshi irin tar dinnan,haka kalar fatanta yake,ga sanyi murya kamar ita ta zaɓar ma kanta,idan kuma yayi la’akari da yanayin fuskanta tu bama sai an faɗa ba tana da suna mai tsayi,dan goshinta zagaye yake da suna har zuwa gefen kunne ta,duk kwance yake da suma wanda ya kwanta mata luf a fuska kamar dai irin na jinjirai,gaba ɗaya ni ma yake ya shagalta da kallon suran yarinyar wacce ya tabbatar da,irin su ake cewa ta leko ta koma,shi ne abin dake shirin faruwa tsakanin shi da ita,jin tana ƙara gaishe shi ne yasa da sauri ya dai-dai ta natsuwar shi”lafiya ya kike”
“Alhamdulillah” ta amsa
Dan shiru wurin ya kara ɗauka na wasu yan daki kai,da kyar ya iya amayo waɗansu kalamai,wanda shi kan shi ba ƙaramin jinjina ma kan shi yayi ba.
Shima cikin wani irin salo da ƙwarewa na irin wayayyu maza ya ce “Baby ya jikin ki”
Ta gefen ido ta kalle shi,sabon salo wai Baby,amma fa gay din gaskiya ya haɗu, dan shima fare ne amma ba kar ba, sai dai yafi ta hasken fata, dan in zata tsaya a kusa dashi ana iya kiran ta da baka a kan shi “da sauƙi”
“Baby idan kina buƙatar wani abu ki faɗa min kin ji,kin ga bikin mu sauran wata ɗaya,idan har akwai wani abin da kika shirya sai ki sanar da ni,yanzun zan baki number waya na”
A hankali tace “ba abinda zan yi,kuma ba nada waya”
“Ok ba damuwa” daya daga cikin wayoyin hannu shi ya cire sim din ya ajiye mata a gaban Table din da yake gaban shi,hade da wani kwali, da leda”ga wannan wayar ki fara maneji da ita,sai wannan magani ne in ji uncle dina wai hayaƙi zaki dinga yi da shi safe da yamma “
“Na gode Allah ya saka da Alhairi”
“Amin Baby, to zan koma amma sai Next week zan dawo”
“To Allah ya kaimu”daganan fita yayi ya wuce, yana mai sauke ajiye zuciya.
Ɗauka wayan da kayan ta yi ta fita a falon,dai dai babban bishiyar tsakar gidan Ɗan Nanne ta tadda iyayen su mata zaune suna shan iska, wanda a zahiri zaman jiran shigowar Asma’u suke yi,dan tuni suka samu labarin zuwan wanda zai Aure ta,har ta da irin motar da yazo da kalan kayan da ke jikin shi duk sun samu labari, dan haka tana isowa kusa da su ta ce “sannun ku Mama”
“Yauwa su Asma’u an dawo kenan daga wurin hiran”
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Maman Hafiza,matar Baba Sani ne ta ce “to kawo ledar muga me ke ciki”
Ba tare da tunanin komai ba ta tasa hannu ta cire dan karamin kwalin da hayakin ke ciki,, sannan ta mika masu lidan.
Da sauri Inna Larai ta ce”A’a to ya kuma kika cire wannan, kodai shi na musamman ne”
“Inna wannan magani ne a ciki, hayaki ne yaban wai inji kawun shi”
Tana kaiwa nan ta juya ta shige shiyan su,da Inna Saude ta ci karo.
Cikin murmushi ta ce”ba dai har sirikin nawa ya wuce ba?
Itama murmushi ta maida mata,dan a zahiri tana iya ganin irin son da matar ke mata”ya wuce Inna, gama maganin da ya kawo min “ta mika mata kwalin maganin.
Baƙin bishiya kuwa,buɗe ledan suka yi,waya ne a ciki, sai kayan maku lashe,nan inna Larai ta kwashe ta raba masu da ya’yan su” Kowa yaci, dan dole mu rage zafi, dan wannan abin da aka mana ba ƙaramin cin fuska ba ne “
“Humm ku dai ku kwantar da hankalin ku,wai ku a tunanin ku wannan auren yuwa zai yi ne?
Gaba ɗaya juyowa suka yi suka kallon inna Balki, matar Baba Mudansir, ” Me kike nufi Balki”
A ƙofar gida kuwa, tun bayan Wucewar Haris unguwa ya ɗauka ai Haris Zamir shi zai Aure Asma’u harma ansa biki nan da wata daya,wani ɗan saurayi da ke zaune a gefe ne yace”wai nikam waye Haris Zamir dinnan ne?
Wani ne mai suna Mu’azu ya ce “kai kana garin nan amma bakasan Zamir family ba”
Na suka dasu ne ya ce “to ai Mu’azu ba abin mamaki bane idan ka yi la’akari da yanayin family ɗin”
Wanda ya fara tambayar ne yace”ni dalla ku faɗa min abu,naga sai wani kwana kwana kuke min”
Mai suna Mu’azu ne ya ce “su ba wasu sanannun masu kudi ba ne kamar sauran shahararrun masu kuɗi,idan kaji ana kiran musulmin kuɗi to ya ƙare a Zamir family,domin su tun azaliyan su sun gaji dukiya wurin kakannin su,Allah ya musu dukiya wanda su karan kansu basu isa su ƙarar da shiba,sai dai kuma su basa buƙatar wani daukaka ko nuna su shahararrune ta fanni komai,shi yasa ba kowa ya san su ba,kuma ba ƙaramin taimako suke yi ba,sai dai komai nasu sukan gudanar da komai ne kan tsari,”
“Aiya gaskiya sun burge ni,hala wannan ne kaɗai ɗan su?
” A’a ba shi kaɗai ba ne,dan yana da ƙani mai suna Zabihullah Zamir,wanda shi ne asalin wanda ya gado hannun Arzikin iyayen su,in kanajin ana fadin yaro da kudi abokin tafiyar manya, to shi ne,domin sam bai damu da tarin dukiyar da Allah ya azurta family su dashi ba,dan shi mutum ne mai harkoki da yawa,kuɗi gare she na tsiya,domin dukiyar da Zabihullah Zamir ke da shi duk kudin family su to bayan shi sake,domin shi bai ma cika gudanar da harkokin shi cikin ƙasar nan ba,a takaice yakan ɗauki shekaru bai ko leko Nijeriya ba”
“To yanzun yana ina?
Gaba dayan su shiru suka yi,Mu’azu ne ya fara leke leke, saida ya tabbatar da ba wanda za iya jin abinda zai faɗa sai su, sannan cikin ƙasa da murya ya ce “wasu sun ce wai shekara uku data wuce ya mutu a haɗarin mota, yayinda wasu ke cewa Kasheshi aka yi,wasu kuma na ganin har yanzun yana raye, to dai ba wanda ya san gaskiyar magana har yanzun”
Bude baki suka yi gaba ɗaya suna mai kallon mamaki”to matar shi fa da yaran shi “
“Kai dai ka iya tambayar banza, nace maka ƙanin Haris ne,yaro ne ƙarami, kwata kwata bai wuce shekara shirin da shida, a lokacin da abun ya faru ba, na dai samu labarin zai auri wata yar uncle ɗinsu, to bansan yanda abin yake ba kawai sai labarin mutuwar shi da muka samu”
Ajiyar zuciya dukkan su suka sauke, jin an kira sallah Magrib.
GIPHY App Key not set. Please check settings