MATAR UBA 21

Advertisement

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

     *MATAR UBA*

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

Advertisements

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

 “`NOT EDITED

CHAPTER 21“`

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

NOT EDITED

Advertisements

” To am sorry yanzu me abunyi?”

Iska ya hura Mai zafi kana yace “zan Fara zuwa aikin”

Mamakine ya kama faisal anfi shekara uku Ana bin say ya karb’i aikin Nan Amma Taki kwasam Rana d’aya ya amince tabbas Yana kaunar yarinyar Nan sosai.

“Toh hakan yayi Amma ka Fara Samar da hajiya tukanna kaji me zata ce”

” Okay insha Allah zanyi hakan,sai da safe”

A tare suka katse wayar.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

“Gaskiya nana al’amarin mutummin Nan ya fara bani tsoro yau ki manin sati biyu kenan Yana bacci sannan babu Wanda yazo neman sa”

” Abban Yesmin Nima abin na damina ,ace babu Wanda yazo neman sa,Allah dai ya bashi lafiya”

Ya Asma da “Ameren”

Faisal da Hashim na gani zaune,Hashim ya bugu uban tagumi,Faisal Ne ya dafe kafad’ar sa yace “Take it easy man,komai yayi zafi maganin sa Allah”

Huci yayi Mai zafi kana yace “yazanyi Faisal,wallahi duk duniyar ta daina min dad’i,na tsani yarinyar Nan na tsane ta and now I have to pretend Ina son ta duk bugun numfashina soyayyar Asiya ke karuwa a zuciya ta a yayin da kiyayya da tsanar Safiyya ke karuwa a Raina,wallahi wallahi idan wani Abu ya same ta sai na ga gatan su wallahi sai na say a d’aure ta da ita da uwarta”

“Allah shi kyauta,Amma ya kukayi da mummy ne ta amince da maganar auren kuwa?”

” Bata amince ba” Yana maganar ya d’auki juice dake gaban sa ya tsiyaya a glass cup sai da yayi sipping kana ya d’aura da fad’in “Na rasa yanda zanyi yau da two weeks Kenan,Ina gudun Kar Safiyya ta gane cewar game muke”

“Kar ka damu insha Allah baza ta gane  ba,Kai ma dai Hash baka jin shawara wallahi,tun da ka dawo daga kasar waje ake ta binka ka Fara zuwa company kaki zuwa ka bar bare akai baka san rayuwar Nan tamu ta lalace

ba mutum ba abin yarda bane ba”

“A wannan halin zan Fara aiki? Ta ina zan Fara bazan ma iya concentrating ba”

” Hakane Amma Ina da shawara,Ina ga shine kad’ai mafita da ya rage Mana”

Ajiye glass cup d’in dake hannun sa yayi yace “uhmn Ina sauraron ka”

Magana suke kasa kasa Wanda na kasa ji, (nace idan tayi tsami zanji)

Murmushi Hashim yayi yace “Kai Alhamdulillah nagodewa Allah da ya had’a Ni da aboki irin ka hakan kawaii za a yi”

” Toh yanzu kaga bamu ga ta Zama ba,tashi zakayi  Muje mu nemi mafita”

Tashin su ke da with wayar Hashim ta Fara ringing Ciro wayar yayi daga aljihun sa Yar karamar tsaki ya jaa like, Faisal ke kallon sa irin kallon wa ke Kiran ka? 

Chan ciki yace “yarinyar Nan ta dame ta takurawa Rayuwata”

Cikin kallon rashin fahimta Faisal yace ” Wace yarinya Kenan fa?”

“Badiyya Mana ban San me take nema a guna ba,kwanaki ta daina kirana yanzu kusan sati uku Kenan take damina kullum sai ta Kiran Sam Bata da zuciya wallahi mtsww”

Murmushin gefen Baki Faisal yayi yace ” Haba Kai kuwa sati uku fa kace? Kuma baka damu da kaji Kiran da take maka ba?”

” Ban damu ba,bana son ta ita Kuma ta makale min,Ni ban San meyasa matan yanzu Basu da kunya ba,Wai ace su Rika bin na miji da wanne zanji Dan Allah,da shaid’aniyar Nan Safiya zanji ko da ita?”

” Duk da hakan dai Badiyya Bata chanchanci Haka daga gare ka ba, yarinyar Nan ta nuna maka so iya so sabida laifi kalilan da ta maka sai is d’auki Karan tsana ka d’aura Mata, Allah da kansa kullun cikin sab’a Masa muke kuma yake yafe Mana,kayi hakuri ka saurare ta ko da kuwa baza ku cigaba da soyayya ba”

Huci Hashim yayi yace “Amma Faisal kasan babu macen Dana so a Rayuwata kamar Badiyya,naso ta irin son da ban tab’a yiwa wata ‘ya mace a duniya ba,Amma taci amanata”

” Na sani, na sani Hashim let the bygones be gone please kamanta da duk wannan ya kamata ka saurareta kaji me ke faruwa”

” Toh naji zan kirata Amma ba yanzu ba”

” To ba matsala take your time but jar fa ya wuce yau d’in Nan”

” Naji naji mu tafi ko?”

Murmushi kawaii Faisal yayi yabi bayan Hashim.

Kwance take ajikin Sa suna kallon American film Mai suna RUSH HOUR, wayar Abban Yesmin ke ringing tun d’azu ankira yafi sau uku,ganin sabon number shiysa bai d’aga ba,Nana ganin Kiran yayi yawa Tace “Ya kamata ka d’aga Kiran Nan Naga Mai Kiran a matse yake”

Yar karamar tsaki yayi yace Miko min please” tashi tayi Mika Masa kana ta koma ta kwanta a jikin sa, kwanciyar ta yayi dai dai da shigowar wata Kiran, duka biyu ya d’aga da “assalamualaikum”

Daga d’ayan ‘bangaren aka amsa da ” wassalam am sorry to disturb you sir”

“Is ok who am I talking to?”

Ya amsa da “Dr Hassan from Doma hospital”

” Oh am so sorry,how may I help you?”

“Good news sir, the person you brought to our hospital just woke up”

Abban Yesmin min baisan sanda ya ture ta ya zauna ba yace “Are serious? When did he woke up?”

“About an hour ago”

” Okay okay am on my way now”

Sai da ya katse wayar yaga ya ture ta har kasa ita kuwa sai tura Baki take Taki tashi Yana ganin halin say take ciki da sauri ya nufe ta Yana fad’in “am sorry baby” had’e da d’aga ta ya d’aura ta akan dugawar sofar da suke zaune akai, bata ce Masa komai ba a Karo na biyu ya kuma fad’in “sorry baby Baki ciwo bako?”

Kai kawaii ta d’aga Masa kana Tace “Wai me aka ce maka ne Haka? Duk ka fita hayyacin ka” tana maganar cikin shagwab’a, Murmushi yayi yace “wallahii daga asibiti ne Wai mutummin Nan ya farfad’o Murmushi tayi da Yar karamar Dariya Tace “Dan Allah dagaske?yaushe?”

” ‘dazun Nan,yanzu tashi ki shirya Muje mu gano shi”

Ta amsa da ” to”

Tare suka haura sama suka shirya sannan suka sauko tare,yau shi da kansa ya bud’e mata motar ta shiga sannan ya zaga ya Danna was motar key Kai tsaye asibiti suka nufa.

Kai tsaye d’akin da baba Mai gadi ya nufa sukayi, hanne sharrar baccin ta take Bata ma San sun shigo ba,dundu Nana ta Kai Mata had’e da fad’in “shasha ke Baki san ba a gida kike ba dubi yanda Kika wangale Baki duk yawun bacci”

Murmushi Abban Yesmin yayi yace ” ke dai da ‘yar d’akin ki ba a raba ki da drama”

Maida kallon sa yayi ga baba Mai gadi da tunda suka shigo yake kallon su Abban Yesmin ya karasa kusa da shi yace “Sannu baba”

“Yauwa sannu”

“Ya jikin naka?”

” Da sauki Alhamdulillahi”

“To Masha Allah”

Maida kallon sa yayi ga  Nana yace “Bari na je office d’in Dr su that yasan mun Zo ko?”

” Ta amsa da to”

Yana fita ta Kara kusa da Shi,Tace ” sannu baba “Ya jiki”

Ya amsa da “sauki”

Kare Masa kallo tayi dakyau a zuciyar ta Tace “wannan kamaar Mai gadin Baraka”

Sai ji tayi yace ” Hajiya Ashe kece? Dan Allah kinji labarin Asiyah?”

Kallon sa take cikin rashin fahimta ” Asiya kuma ta ‘bata ne?”

Nan ya kwashe Mata duk abinda ta Faru, girgiza Kai tayi Tace “Ni kaina na manta ranar da naje gidan Baraka ban San duk wannan ba,Amma Kar ka damu insha Allah zan Nemo ta” tashi tayi ta bi bayan mijin nata.

A hanyar ta ta zuwa office d’in suka had’u dashi Nan ta kwashe komai ta fad’a Masa yace “Innalillahi was Inna ilaihirraji’un, gaskiya Baraka Bata da imani tabbasa Naga farar paper Amma ban bud’e ba,na Adana Masa shi har sai ya farfad’o Kuma ma paper na Nan acikin mota ta”

Tace “Bara  naje na d’auko”

” A’a Bari zan d’auko da kaina,ki je ki zauna tare dashi sannan Ki tabbata yaci abinci musmman fruits d’in Nan”

Ta amsa da to,Yana tafiya Yana jinjina halin Baraka sannan ya d’auki alwashin d’aukawa Asiya fansa ko ba komai sunyi zaman mutunci da Sadeeq (mahifin Asiyah) Kan ya rasu,cikin wannan tunanin ya je ya d’auko paper ya dawo ya tarar da dasu Yana cin ayaba kamar Wanda ya shekara baici abinci ba.

Tambayoyi ya shiga yi Masa akan Baraka Yana bashi amsa baba Mai gadi yace “Nan wani asibiti ne?”

Nana Tace “Doma hospital”

Baba Mai gadi ajiye lemon da ke hannun sa yayi yana kokarin tashi har ya mike yaji kafarsa ta Masa nauyi Bai San sanda ya koma da baya ba, Abban Yesmin dake kusa dashi yayi saurin taro shi Yana fad’in “Baba lafiya kuwa? Inna Kuma zaka?”

“Asiyah, Asiyah na asibitin Nan,Nan na kawo ta”

Nana da Abban Yesmin kallon juna sukayi,Abban Yesmin yace “in ko hakane Banga ta Zama ba bara naje Na duba, record yaje ya bada sunan ta nurse dake aiki a gun Tace “Asiyah Sadeeq yarinya Mai ciwon idon na ko?”

” Eh…eh ita”

” Ai ko an Kore ta sabida Basu da kud’in biyan aiki”

Dafe Kai yayi yace “Amma kin San inda take Ne yanzu?”

“A’a ban sani ba”

Ta cigaba da harkan gaban ta,komawa yayi ya fad’a musu yanda ake ciki,hanne ban da aikin kallon su ba abinda take you.

Baba Mai gadi yace “An Koreta Kuma? Amma zan so ganin Dr Badiyya maybe tasan inda take”

” Wace ce ita d’in?”

” Itace take kula da ita,likitar Ido ce”

Abban Yesmin yace ” Na gane,bara na je Na duba”

Yana zuwa office d’in ta ya samu a rufe tambayar nurse da ke kokarin wucewa ta gefen sa yayi saurin ce mata “Dan Allah baiwar Allah, Dr Badiyya bata fito bane?”

“Ta fito da safe Amma ta tashi”

” Okay Amma yaushe zata dawo?”

” Inaga sai Kuma da safe”

” Okay nagode”

“Baba Dr Badiyya bata Nan Amma gobe zata shigo”

” Toh Shikenan Allah ya Kai mu goben”

Duk suka amsa da ameen.

Sai da suka Kai har bayan sallar Isha suka koma gida sannan Nana ta Hawa hanne kunne da ta kula da shi yanda ya kamata.

Hashim tunda suka fita Basu dawo ba har sai da sukayi sallar Isha ko wanne ya koma gidan su,Yana shiga bayan yayi Sallama da hajiyar say ya shige d’akin sa,ban d’aki ya fad’a ya watsa ruwa bayan ya watsa ruwa ya zurma jallabiyarsa ta bacci ya kwanta,kwasam ya tuno tun safe Tau basuyi ways da Safiyya ba,d’auko wayar sa yayi yaga missed calls ‘din Safiyya har uku, Badiyya missed call ya Kai goma,tsaki ya jaa yace “jarababbu”

Kiran Safiyya yayi magana take kamar baza tayi ba,irin an b’ata Mata Rai din Nan,hakuri ya shiga bata had’e da kiranta ta dad’ad’an suna kana ta huce ta saki ranta,sun dad’e suna waya sun d’auki kusan mintuna talatij yace Mata bacci yake ji Nan ma da kyar ya rarrashe ta ya kashe wayar,Yana kashe wayar yayi dialing number Badiyya,har ta Fara bacci Asiya yace ta tada ita cikin sanyin murya take Kiran sunan ta had’e da tab’a ta,” Aunty,aunty” ta amsa da “na am”  cikin  muryar bacci da alamu taka Jin dad’in baccin nata,har wayar ta katse ya Kuma Kira a Karo na biyu, d’an Kara bugata Asiya tayi Badiyya ha don taso ba ta nufi inda tayi plugging wayar ta achaji ganin Wanda ke Kirane yasa tayi sauri picking call d’in, murya Na rawa Tace “Ass..ssalmmu alaikum”

Ya amsa da “wassalam Dr Badiyya ya kike?”

” Ta amsa da lafiya Lau ya gida” 

” Lafiya lau, lafiya kuwa Naga kike ta kirana?”

Yar karamar huci tayi Tace “Gaskiya ba lafiya ba”

“Uhmn Ina sauraron ki me ya Faru?”

Maida kallon ta tayi ga Asiya sai tayi saurin shiga ban d’aki ta rufe kofar ta ciki,Jin tayi shiru yace “Hello kina jina kuwa?”

“Eh Ina Jin ka” murya kasa kasa.

“Ya Kuma kikayi shiru?”

“Am sorry bani kad’ai bace na d’an keb’e ne”

“Okay ba matsala to ya akayi?”

” Hashim haryanzu kana fushi Dani ko?”

” Look Badiyya wannan dalilin ne yasa bana d’aga Kiran ki na fad’a Miki bana so kina tinkarata da wannar maganar idan Baki da abin fad’i Ni zan kashe wayata”

” Am sorry dama taimako nake nema a gun ka”

“Taimako ta me Kennan fa?”

Murmushin takaici tayi sabida yanayin yanda yake amsa Mata maganar cikin fushi,tsawa da Kuma takama.

Tace “akwai wata yarinya asibitin mu,idon tane ya samu matsala Ana bukatar kud’i Mai yawa,kuma marainiyace aikin ma baza a iya yi Mata a kasar Nan ba sai India shine nake so Dan Allah inda Hali ko zaka taimaka mata,yau kimanin sati uku Kenan nake neman ka tun ciwon baiyi chronic ba Amma baka saurareni ba”

A zuciyar sa yace “Allah sarki” Amma a fili yace “Sorry for that yanzu kud’in ya Kai nawa ne?”

” Da dai Rabin million ne Amma yanzu zai Kai d’aya harda rabi”

” Karki damu zan taimaka Mata,a wane asibiti kike aiki?”

” Doma hospital ne”

” Okay tana asibitin ne?”

” A a yanzun muna gidan mu,sabida gudun Kar a wulakanta ta a asibin”

“Kin kyauta,yanzu abinda za’a yi mu had’u gobe da karfe goma a asibin”

” Toh insha Allah nagode sosai Allah ya saka”

” Kar ki damu,sai da safe”

Ta amsa da “Allah ya tashe mu lafiya”

Ya katse wayar,Yana Jin wani irin yanayi a kanta Wanda shi kansa Bai San mene Ne ba.

Badiyya kuwa ji take so da kaunar sa Na karuwa a cikin zuciyar ta had’e da murna Asiyah zata samu sauki,tana komawa d’akin da niyar fad’a Mata Albishir ta tarar har tayi bacci,shafa kanta tayi sannan ta gyara mata bargon da ta rufe jikin ta dashi.

WASHE GARI

Tun karfe takwas Badiyya ta shirya sannan ta shirya Asiya, Asiya Tace “Aunty Ina zamuje ne”

Murmushi tayi tayin da take Kama Mata gashin kanta da ribbon “Asiyah kin  kusa samun sauki insha Allah”

“Bangen ba aunty? Baba Mai gadi ya dawo ne?”

” A’ a, Amma akwai Wanda mukayj magana dashi yayi alkawarin yau d’in Nan zai biya Miki kud’in aikin Nan”

Asiyah Baki har wuya ” Dan Allah aunty dagaske kike?”

” Eh Asiyah dagake nake”

” Alhamdulillah Allah nagode maka ,aunty nagode sosai ban San me zance Miki ba sai dai ince Allah ya biya Miki bukatun ki na Alhairi”

” Ameen ameen Asiyah,to tashi mu tafi” ta gyara mata hijab d’in jikinta tasa Mata bakar eyeglass tayi kyau matuka,kamar ba makauniya ba.

Karfe Tara chip suka Isa asibitin a office d’inta ta ajiye ta kana ta fita don duba patient d’inta masu matsala irin na asiyah, bayan ta gama ta koma office, zaman ta ke da wuya ta ga Kiran hashim, cikin sauri tayi picking Bai jira tace komai ba yace “Kina Ina? Na shigo asibitin ku?”

Tace “Ina office d’ina gani nan zuwa”

” No ki fad’a min inda kike kawaii am coming” 

Nan ta Masa kwatance,ya katse wayar.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

Kuyi hakuri da rashin post d’ina bawai bana son typing din bane Ni kaina na kosa Naga na gama Amma Kun San harkar makaranta sai a hankali musamman ‘bangaren da nake karanta duk Wanda yasan pharmacy yasan karatun ba sauki

 Sannan da rashin comments dinku Yana Kara kashe min jiki

Please kuyi comments sannan kuyi sharing

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MATAR UBA 33

Advertisement   πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*…

MATAR UBA 30

Advertisement πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*  …

MATAR UBA 3

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦        _(A True Life Story_ )…

MATAR UBA 10

Advertisement   πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦        _(A True Life Story_…

MATAR UBA 28

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*  …

MATAR UBA 4

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦        _( CHAPTER 4 πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ ……..…