MATAR UBA 25

Advertisement

 πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

     *MATAR UBA*

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

Advertisements

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Not Edited

CHAPTER 25

A kasa suka same shi Yana zaune,hannun sa rike take da magazine, yana hango su ya ajiye ya mike,yayi gaba suka Mara Masa baya,cab(Taxi) ya tara Saida suka shiga yace ” Powai’s Hiranandani Hospital”

Advertisements

“Okay sir”

Sun d’auki almost 30mints Kan suka Isa, hakkinsa ya bashi, sannan suka shige asibitin.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

………. Powai’a Hiranandani Hospital had’add’en wuri ne sosai, ma’aikata ko ta ina sanyaye da fararen lab coats a jikin su, wuyan su Kuma a rataye yake da stethoscope, sunyi matukar kyau abinka da farar fata, Kai tsaye ophthalmology center suka nufa, wata Nurse na hango jikin ta sanye yake da farin Riga irin Wanda nurses suke sawa iya gwiwa da farar hular ta irin Wanda nurses kw sawa, fuskan ta d’auke yake da Murmushi nufo su tayi a inda suke zauna Tace “Hashim Shettima right”

“Yeah”

“Alright, come with me”

Tashi suka yi suka bita da jagorancin ta suka shiga office din likitan da already ya San da zuwan su.

Suna shiga suka Tarar Yana ban d’aki Tace “He is in the bathroom room,wait for him”

Kai kawaii ya d’aga Mata.

Bai d’au lokaci ba ya fito,yana goge hannun sa da hand sanitizer,sai da ya zauna ya kalli ida suke,tashi yayi a razane ya ambaci sunnan ta “Di…diyyya?”

Baki a Bud’e take kallon sa kasa magana tayi, tarin da Hashim yayine ta dawo dasu daga tunanin da suka lula.

Karasowa yayi inda suke Yana Murmushi, Mika wa hashim hannu yayi yace “Assalamualaikum Hash”

Kallon hannun sa ya tsaya yi,ganin baida niyar janye hannun sa ya Mika Masa hannu had’e da kawar da kanshi gefe.

Girgiza Kai Ammar yayi Yana mamakin Hali irin na hash Abu kusan shekaru uku Amma haryanzu Bai Manta ba.

Ya Maida kallon sa ga Asiyah da ke zaune ta zuba uban tagumi, yace “Is she the one?”

Ya d’aga Masa Kai riko hannun ta yayi “Stand up” da sauri Hashim ya ture Masa hannu Yana nunashi da d’an ya tsaya “Don’t try it” 

“Excuse me but am just doing my job”

“Most you touch her?”

” Am sorry but I have to”

Mikewa Hashim yayi Nan da idanuwa suka sauya daga fari zuwa jaa.

Badiyya ganin Hashim na kokarin aikata abinda ya aikata a Baya,har ya Kai hannu zai Kai Masa naushi cikin tsawa tace “Hashiiiim” juyowa yayi ya kalleta.

Cikin kuka Tace “Are you Mad? When will you ever change, what sort of non sense is this?,kayi mashi a baya ya kyale ka Amma ka sani yanzu kana cikin kasar sune ba barin ka zasuyi ba”

Ammar yace “Diyya please calm down,take it easy”

Hashim dariya ya shiga yi abun mamaki Kuma idanun sa na zub da hawaye yace “I knew it,I knew it dama Soyayya kuke”

“Hashim please calm down,it has been long and you totally misunderstood us please sit down”

Yana kokarin riko hannun sa, ya buge Masa hannu “Don’t touch me”

“Hashim please calm down, please trust me,I promise you that what you saw that day was a total misunderstanding,I never loved her I liked her as a friend, please am sorry”

Badiyya Banda kuka babu abunda take yi, Asiyah mekewa tayi cikin kuka Tace “Please will someone explain to me,what is going on here?”

Sai a Lokacin suka tuna da basu kad’ai bane a gun,cikin Rawar murya Hashim yace “Baa…bakomai”

“Bakomai kuma taya zaka cemin bakomai bayan gashi Ina duk ki biyun Kuna kuku”

Shiru yayi don Bai San amsar da zai bata ba.

“Aunty Dan Allah ki fada min me ke faruwane,dama kin San Hashim ne?”

Shiru

“Aunty please talk to me”

Ammar da ke ya fahimci maganar da take, hakan Yasa yace “Do you understand English?”

“Yes”

“Okay,Hashim and Diyya are lovers,they love each other alot but unfortunately he got angry at her because of me……..” Nan ya Koro Mata abinda ke tsakanin Diyya da hash, sai da ya gama bata labarin jiki ba Karfi ta koma ta zauna, hawayene masu zafi suke saukowa daga idanun ta,Hashim durkusawa yayi a gaban ta yace “My Queen kukan me kike haka? Dan Allah ki daina bana jin dad’in ganin ki a haka,Diyya past ‘dina ce and you are my present ke nake so Kuma nake Kauna please don’t leave me”

Hannu tasa ta goge fuskar ta gyaran murya tayi Tace “Dr when will my surgery start?”

Kallon agogon dake hannun sa yayi yace “At 10am and the time now is 9:30am, just start up and dress up”

Tashi tayi a dai dai lokacin nurse na ta shigo ya umurce ta da ta kaita d’akin tiyatan,riko hannun ta tayi suka fice da ga office din.

Wani d’aki ya shiga yayi shirya tsaf cikin Kayan da likitoci suke sakawa idan zasu yi tiyata,har ya Bud’e kofan zai fita Hashim yace “How long will it?”

“About two hours” kawaii yace yayi ficewar sa. 

Bin bayan shi sukayi suka zauna a reception,babu Wanda yace wa wani kala, Hashim ear piece Yasa a kunnen sa, waka yayi playing Amma Sam hankalin sa baya Kan wakan, shesshekar kukan Badiyya yake ji Bai San meyasa ba tausayin ta ya ziyarci zuciyar sa,tsaki yayi ya tashi ya bargun,harabar asibitin ya nufa ya nemi wuri ya zauna Bai shigo ba har Saida ya ga time ya d’in fitowar su ya kusa cika ya koma ciki.

Cike da tausayi yake kallon ta tana zaune bata motsaba sai kuka take, Zama yayi a gefenta yace “Diyya please kukan Nan ne mene ne? Dan Allah ki daina Zaki ja wa kanki ciwo fa”

“Hash Tambaya ta kake kukan me nake? Sai kace baka San dalilin kukan nawa ba?”

” Am sorry to say ni ban sani ba”

Yar karamar dariya tayi had’e da kuka tace “As expected dama meyasa zaka sani, tunda yanzu ni ba komai bace a wurin ka,Hashim me na maka da na chan chanci rashin mutunci daga gare ka,yanzu ni diyya, nice kake cewa ni past Dinka ce in my present? Ban tab’a tunanin hakan daga gare ka ba”

“Am so sorry Diyya but ni dagaske nake Asiyah nake so,Kuma auren ta zanyi matsalolin da suka gifta ne yasa ba a d’aura Mana aure ba”

Kan ta Bud’e Baki tayi magana suka hango Dr Ammar nufo su yayi yana Murmushi “How was the surgery?” Hashim ke yi Masa tambaya. ” Yeah Alhamdulillah it was a success”

“Can I  see her now?”

” No just wait for the nurses to dress her ,and she is also sleeping but she’ll soon wake up,she will stay here for three days before we can discharge he”

Hashim duk da Yana Jin  haushin Ammar hakan baisa shi rungumar sa ba Yana Mai masa godiya. Badiyya kuwa ji tayi kamar zuciyar ta zata fita daga kirjinta,saurin fita tayi wuri ta samu ta shiga rera kuka son ranta.

Bin ta sukayi da kallo Ammar mamakine ya kamashi ganin yanda Sam Bai da mu da Badiyya ba kamar Basu ne kamar zasu cinye junan su ba, tsaki yayi yabi bayanta.

Wani irin kallo Hashim ya masa yace “Chan ta matse muku”

Ya juya ya nufi d’akin da yaga an shege da Asiyah,tana kwance hankalinta kwance take bacci Zama yayi ya sata a gaba sai kallon ta yake Kamar za a sace ta.

“Diyya please what happened,why are you crying do want to get I’ll?”

Daradaran idanun Wanda suka kada suka yi jaa ta ta d’ago ta kalle shi Tace “I don’t what to do Ammar as you can see Hashim is angry with me”

“What do you mean I thought you people are already married”

” No we didn’t actually he broke up with me for about three years now”

” Those that mean since when we are in school?”

“Yeah”Nan ta Koro mishi halin da suke ciki  tun daga ranar da sukayi graduation party har zuwa yanzu.

Yace “What about the girl with you?”

Nan Shima ta fada Masa sanadiyar haduwar su da Kuma matsayin ta a wurin Hashim.

Hakuri ya bata ya bukaci da ta taso ta su shiga office d’insa bata musa ba ta rufa mishi baya.

Ruwan sanyi irin na gora ta Ciro ya mika mata tayi saurin karb’a ta Bud’e Saida ta Sha kusan rabi ta sauke Goran shi ko Ammar kallon ya yake cike da tausayi “You’re hungry right?”

Kai ta d’aga Masa alamun eh, “what will you like to eat?”

“Noodles will be okay”

“Alright”

Telephone ya dauka yayi magana dasu da yaren su na indiyanci,bayan ya gama ya sauke wayar ya ajiye,a hankali yake jaan ta da Hira tun bata kulashi ta har ta Fara bihe mishi,sun cikin hirar a ka shigo da abincin.

Wurin Zama na musamman Wanda akayi don cin abinci a office d’in ajiye Mata akayi,tashi tayi a nitse ta nufi inda abincin yake tana ganin abincin tun Kan ta Fara ci yawunta ya tsinke, ganin irin kallon da Ammar ke mata hakan ya sanya ta nitsu ta fara cin abincin,sai da taci Mai isarta Kan ta tashi daga kan abincin,ta Sanar Masa da zata duba Asiyah, tare suka fita.

Hashim na zaune akan gurer dake gefen gadon da Asiyah ke kwance sai faman gyangyad’i yake, Sallamar da sukayi ne yasa ya Bud’e idanunsa ya d’aura su akan Badiyya,ganin Ammar na biye da ita yayi saurin kauda kansa.

Ammar Kan ta Asiya ya nufa Yana duba idonta da aka rufe da bandaji da jini akai Hashim yace “When will you remove the bandage?”

“After three days” 

“Alright”

” Please can I talk to you for a moment?”

” Are you talking to me?” Hashim ke wannan Tambayar

” Yeah you” sai ya fice Hashim ya bi bayan sa.

Office din Ammar suka nufa bayan sun zauna,ammar ya Fara bashi hakuri kana ya Kara Masa bayani akan abinda ya gani Shirin Hashim yayi Yana kallon sa har ya gama sannan yace “Okay I believe you”

“Thanks does that mean you’re going to marry Diyya right?”

” Nooo I can’t marry her”

” But….but why?”

“cos I don’t love her”

” No hash is a lie, you’re lying you Love her,and you’ll forever love her”

“Hmm no I don’t the only girl in my heart is Asiyah”

” The girl you bring here?”

” Yeah”

” But hash you can marry two wives or more,you can marry them both, after all you’re rich you can take care of them all.”

“You’re right but I don’t have interest of marrying two wives”

“Is okay I won’t force you since you are not interested”

“hmm….  But Ammar……. You can marry her you know”

“hahaha are you kidding me I can’t marry the woman I don’t love and am already married to the woman I love, and we have two children”

“Wow that’s very fast,stay blessed”

Mikewa yayi had’e da Mika Masa hannu yace “Thanks” Hashim ya amsa da “You’re welcome”

Badiyya da tun d’azun ta lab’e tana jin dukkanin abinda suke cewa, tayi saurin barin gun ta koma d’akin da Asiyah take.

Kalaman sa ne suke yawo a zuciyar ta “The only girl in my heart is Asiyah”

Hakan yasa ta fashe da kuka “Aunty kukan me kike?”

Muryar Asiyah ne ya sa ta yin shiru.

“Aunty na san sabida Ya Hashim kike kuka ko?”

“A….a a ba…baa shi bane kawaii dai bana Jin dad’i ne”

“Hmmm haba aunty na zauna dake tsawon watanni nasan Wace ce ke,ke jarumar mace ce, Amma na lura weekness d’in ki Hashim ne, kina matukar son sa fiye da tunanin me tunani,Amma aunty me yasa Baki Sanar dani cewar kunyi soyayya a baya ba?”

Cikin muryar kuka Tace “Sabida baida amfani, ke yake so yanzu ba ni ba like he said am his past and you’re his present,so it’s not a big deal”

” No ba haka bane Hashim Yana sonki, har kuka yayi d’azu bayan haka maganganun sa sun nuna cewar haryanzu Yana Jin haushin Dr Ammar in da ace baya sonki da zuwan yanzu da ya manta da ke Amma Bai Manta dake ba”

“Hmm Asiyah Kennan ya jikin naki hope ba Kya Jin komai?”

“Bana Jin komai,meyasa Kika canza zancen?”

” Sabida bana bukatar hakan,Kinga da ace muna da Kayan aiki ni zan Miki aikin a nija Amma Sabida rashin Kayan aiki masu Karfi shiyasa na Bari aka kawo ki Nan”

“Amma aunty kina ganin zan sake gani?”

“Eh da yardan Allah, Ammar na da kokari sosai Abokina ne,Kuma ta tabbatar Mana da cewar aikin nakin is a success,Nan da kwana uku za a cire Miki bandejin”

Murmushi tayi Tace ” Nagode sosai aunty ba don ke ba da ban San halin da nake ciki ba yanzu”

” Shhhsh,  karki Ce haka,Allah baya barin wani don wani ki daina fad’in haka kinji”

“Insha Allah bazan sake ba”

“Asiyah kin San mene ne burukana a yanzu?”

“A’a sai kin fada”

“A baya baban burina shine na Zama likitan Ido,sannan na Aurin na mijin da yake Sona nake son sa,Allah ya cika min burina na farko Amma na biyun Sam ya fita a Raina,tun sanda na had’u dake nake burin naga kin samu lafiya dake nake kwana nake tashi sai yau Allah ya cika min wannan burin nawa abinda ya rage shine a Kama wannan Mara imanin Baraka da yarta”

“Ni kaina na kosa na samu lafiya sanida na dauki fansar mahaifana da kanwata da ta kashe”

” Insha Allah ni zan cika Miki wannan burin naki” Hashim ke wannar maganar zagayawa yayi ya rike hannun ta “Banji kin ambaci maganar auren mu ba ko dai kin fasa be?”

Murmushi kawaii tayi batace Masa komai ba ita a ganin ta cin fuska ne yake yiwa Diyya hakan yasa ta zare hannun ta a nashi a hankali.

Babu Wanda ya sake cewa komai sun d’auki tsawon mintuna ashirin Kan yace “Ni zan koma masauki,akwai wani abunda kuke so ne na kawo muku?” Yana maganar idonsa akan Diyya.

Kawar da kanta tayi yace “Diyya magana nake kinyi shiru, babu abunda kuke bukata?”

Murya na rawa Tace “Wanka”

Zaro Ido yayi ya kalle yace “Wanka zan kawo Miki?”

“Ina nufin Wanka nake son yi”

“Oh okay,but idan muka tafi wa zai kular min da my queen?”

Asiyah tayi saurin fad’in “Kar ka damu akwai nurse ai zata kula dani,yanzun ma nace Mata yunwa nake ji zata kawo min abinci,Amma asibitin Nan yayi daga cewa ina jin yunwa sai a ce za a kawo min”

Dariya Hashim yayi yace ” Malama kud’in mu zaki ci duk Yana cikin hospital bills so ba kyauta zasu Baki ba”

” Oh to sai yanzu na fahimta”

Shafa kanta yayi yace “You look more beautiful when you smile queen”

Ya Maida kallon sa ga Diyya yace

“Muje ko?” 

Kai kawaii ta d’aga masa, ta fice, ganin ta fita ya manna wa Asiyah kiss an goshi yace “Sai mun dawo”

“Take care.”

Tarar da ita yayi tana tsaye a katafaren gate na asibitin sai da ya tare taxi yace “Muje ko?”

Ko kallon sa batayi ba ta shige motar, d’aga kafad’a yayi “Kinyi a banza” Yan aiyana hakana a ransa.

Bayan sun Isa hotel din da suka sauka, ta shige d’akin su Shima ya shige nasa, Diyya Kai da gwiwa ta had’a Banda kuka babu abinda take yi sai kuka ta dad’e a Haka na ta tashi ta shiga ban d’aki ta d’auro alwala dake tayi sallar azahar a asibiti, sallar la’asar kawaii tayi akan sallayar baccin wahala yayi awun gaba da ita, ganin bata fito ba hakan yasa ya nufo d’akin su ya dad’e Yana kwankwasa kofan Amma shiru hakan ya sa ya tura kofan ya shiga.

Ganin ta dukun kune sai sharar baccin ta take yace “lallai ma wato Nan baccin ta ma take hankali kwance ni Kuma na tsaya Zaman jiranta” hannu yasa zai tada ta sai kuma ya fasa “maybe baccin take bukata zan tafi kawaii idan ta tashi ta same ni a chan, ficewar sa yayi ya ja kofar.

Hiran su suke Sha sosai da Masoyiyar sa,tun farkon Soyayyar su basu tab’a Hira sama da mintuna talatin ba hakan yasa yake Jin wani irin farin ciki na musamman.

Diyya na tashi daga bacci ta sa hanni ta d’auki wayarta karfe Bakwai saura, tsaki tayi Tace “Me yake yi haka tun dazu Bai min magana ba”

Message ta gani a fuskar wayarta “Na shigo na samu kina bacci shiyasa ban tashe ki ba, idan kin tashi ni na wuce asibiti sai kin zo”

Tsaki kawaii tayi ta shiga bathroom ta watsa ruwa sannan ta shirya ta d’auki Kaya set biyu wa Asiyah tasan Dole zata bukaci wanka.

Taxi ta hau ta wuce asibiti, tana shiga d’akin ta tarar dasu sai dariya suke sai taji ba Dad’i da sallama ta shiga Asiyah ce kad’ai ta amsa Mata sallamar  “Aunty kin tashi? D’axu nake tambayar Ya Hashim inda ya baro min ke yace min Kanki na ciwo kina bacci da fatan kinji sauki ko?”

Kallon shi tayi taga ya kauda Kai “To meyasa ya mata karya?” A ranta ta aiyana hakan a bayyane kuwa tace “Alhamdulillah da sauki stress ne kawaii dama”

“Allah sarki Allah ya sa kaffarane”

“Ameen”

“Ya kamata ki watsa ruwa  tun safe rabon ki da wanka, gashi Kuma nasan bakiyi sallah ba”

Murmushi tayi Tace “Zanyi”

Da taimakon ta suka shiga ban d’aki tayi wanka,duk a ban d’akin tasa kaya sannan suka fito tare.

Zaunar da ita tayi a bakin gado tana shafa mata Mai suna Hira sama sama.

Hashim mamakin diyya yake meyaay take taimakata bayan yasan halin Diyya da muguwar kishi duk da tasan cewar Yana son Asiyah hakan bai Hana ta daina kula da ita ba, Allah ya sa ba da wata manufa take ba..

Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a  yaune za a bud’ewa Asiyah Dr Ammar ne a kanta Saida ya Mata wasu allurai yace Nan da awa d’aya zai Bud’e Amma Kan ya fita yace da ita wane ne take son fara gani idan aka Bud’e Mata ido, ga mamakin su ta ambaci sunan Badiyya, duk sun d’auka Hashim zata ce har ita kanta Diyya tayi mamakin Jin hakan Tace “Amma Asiyah me yasa kikace ni kike son fara gani?”

“Aunty you’re like an angel to me, I just want to see you”

Murmushi kawaii tayi,yayin da Hashim yake mamakin irin shakuwar dake tsakanin Asiyah da Diyya, Ammar fita yayi  awa d’aya na cika ya shigo da nurses guda biyu a biye dashi.

Ba Asiyah kad’ai ba hatta Diyya da Hashim Saida sukaji kirjin su ya soma bugawa.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

Please share and comment

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MATAR UBA 19

Advertisement πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦         *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️             …

MATAR UBA 37

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*  …

MATAR UBA 14

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦              *MATAR UBA* CHAPTER 14“` “A a nagode” ta juya tayi…

MATAR UBA 12

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*   Love. “`NOT EDITED CHAPTER 12 PREVIOUSLY“`  Shafe kansa yayi,…

MATAR UBA 23

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*  …

MATAR UBA 3

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦        _(A True Life Story_ )…