Advertisement
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
*MATAR UBA*
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Daga Alkalamin βοΈ
*Milly*
Fadilah Yakub
Advertisements
*(MILHAAT)*
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπποΈ*
*M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
Not Edited
CHAPTER 27
Advertisements
Safiyya na Jin karar motar ta gane ta fita ne tsaki ta jaaa, ta fito fridge ta nufa ta d’auki wannan yoghurt din da Baraka tasa Abu a ciki, tana Bud’ewa ta kafa Kai ta shanye tass ko bismillah batayi ba,wani irin bacci ne taji ya kamata,har ta Fara haurawa Kan stairs taji baza ta iya ba ta dawo kan sofa ta kwanta.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
…….Kiran Hashim sukayi bayan sun gama Shirin,Bai d’auki lokaci Mai tsawo ba ya karaso Kiran Diyya yayi a waya, tsuman tsaye yayi ya sanya kallon su ganin yanda suka had’u suka had’e shikam yayi dace sai yanzu ya Kare musu kyau duk kyawun Badiyya, Asiyah ta ninkata ninkin banin ki.
Iska Diyya ta d’an hura Masa a idon sa yayi saurin Maida kallon sa gareta shi Sam Bai ma San sun karaso inda yake ba, Murmushi yayi Yace “Hello!!”
Murmushin ita ta Maida Masa Tace “Hy”
” Ya Hashim irin wannan kallo haka?”
Asiyah ce ke Masa wannan tambayar.
“Hmm ai ku din me duk Kun tafi da imani na,kunyi matukar kyau sai dai fa gaskiya baza ku fita a Haka ba”
A tare sukace “Meyasa”
Dariya yayi Yace “Kar ku cinye Ni,ni was nake mu tafi ko?”
Ya Bud’e mota zai shiga sai kuma ya tsaya ganin duk zasu shiga baya, kallon su yake yi har Asiyah ta kafar ta d’aya a cikin motar yace “Kuna nufin duk ki biyun a baya zaku zauna Kenan?”
Diyya Tace “Eh Mana”
“iyee sannun ku gani driver d’inku ko?”
“Eh man Kai kace kaji ka Kuma ka gani,dama Kuma ance nan Miji bawan matane”
‘daga gira yayi yace “Harda Ni?”
” Eh man harda Kai”
“Hahaha Aunty,ya Hashim ba bawan matane ba”
“kyaji ki Asiya to mene shi in ba bawan Mata ba?”
“Masoyin Mata dai”
Kama Baki yayi yace “La’ilaaaa”
Diyya Banda dariya babu abinda takeyi, Asiya Kuma said yanzu ta fahimci maganar da tayi don Bata ma San sanda ta furta ba.
Yace “Queen ai gara ki ce min bawan Mata da Masoyin matan nan”
Kunyane ya sa ta shigewa motar ta leko ta window tace “Aunty ki shiga gaba man mu tafi”
Zagayowa tayi ta shige gaba duk da hakan bata daina dariya ba, girgiza Kai kawai yayi Shima ya shige motar ya tsaya kallon ta “To ke Wai dariyar bata ishe ki haka ba?”
“Dasaura”
Hannayen sa ya hard’e wuri guda yace “To idan kin gama sai mu tafi”
“Am sorry am sorry” sai ta Kuma fashewa da dariya.
Waigowa ya kalli Asiyah banda Murmushi babu abinda ta ke yi yace “Kinga abinda Kika jawo min ko?”
Sunkuyar da kanta ta shiga dariya.
” Au kema dariyar kike? Shikenan sun Maida Ni mahaukaci” ganin dariyar tasu Taki karewa ya sa wa mota key suka Bari gidan.
Gidan Abban Yesmin suka nufa,zuwar su yayi dai dai fitowar sa ,Yana ganin su ya yi Murmushi hannu ya mikawa Hashim suka gaisa, yace “Kaga mutanen India yaushe a gari?”
“Jiya just Nan”
“Masha Allah da fatan anyi nasara ko?”
“eh gashi Nan kuwa kana ganinta” ya nuna Masa Asiyah dake gefe.
“Aa’aa Masha y gaskiya naji dad’i,yanzu Asiya kina gani na?”
Yar karamar dariya tayi Tace “Eh”
Yatsun sa guda uku ya d’aga yace nawa ne Nan?”
Cikin dariya Tace “Biyar”
Zaro yayi ya kalli hannun sa yace “Asiya biyar Kuma ko dai idon akuya suka sa Mike ne? Amma Kuma ganan idanun ki yanda suke” Yana Mai Kara kallon idanuwanta harda gyara tsayuwar sa.
Maida kallon sa yayi ga Hashim dake ta dariya yace “Hashim gaskiya aikin Nan baiyi ba ace tana ganin uku Tace min biyar,ya kamata mu shirya zuwa wata kasar wannan karon Chaina Zamuje”
Duk su ukun suke dariya shi kuwa magana yake dagaske ya Kuma cewa “look ba maganar wasa nake ba Dole mu kaiki chan”
Hashim yace “Queen ya kamata ki fad’a masa gaskiya ki cire shi daga rud’un da ya shiga ko Kuma mu kaiki Chaina d’in Kinga daga Nan Sai cire Miki kwala kwalan idanun ki su sa Miki irin nasu”
“A a me yayi zafi am sorry Daddy zolayar ka nake Ina gani yanzu”
“umm ummm Asiyah ban yarda ba ina tantama”
“okay tunda baka yarda ba, shaddace a jikin ka lemon green, wanchan motar baka ce,sannan motar da muka Zo da ita Blue ce,Aunty Diyya kuma bakar doguwar Riga Ce a jikin ta, Ya Hashim Kuma bakar Riga da farin jeans da facing cap Fari”
“Ko da naji yanzu Kam na yarda”
Bud’o kofar da akayi ne yasa dukkanin su kallon gun, Nana tana ganin su Tace “Kace Baki mukayi in kitchen sai Jin surutai nake,shine ka bar su a waje, bismillah ki shigo mana”
Diyya dake tun d’azu ta gaji da tsayuwa ta Zama ‘yar kallo a cikin su, tayi saurin bin bayan ta, tana mamakin Hashim sau d’aya fa suka had’u da shi Amma zaka d’auka sun San juna na tsawon shekaru.
Zama sukayi suka sake gaisawa Nana da khamal sunyi matukar farin cikin ganin Asiyah ta samu sauki dama shine first mission ‘dinsu, gyara Zama khamal yayi had’e da gyaran murya.
“Hakika bazan iya misalta Muku irin tsananin farin cikin da nake cikiba, tunda naga Asiya ta samu lafiya, Asiyah tamkar ‘ya take a guna Mahaifin ta babban Abokina be,sanadiyar aikin tsaro da na shiga ne yasa mukayi nesa da juna babu yanda baiyi dani ba Akan na cigaba da Business ‘dina Amma naki,sabida ina matukar son aikin ya hakura ya goya min baya,sabida Zanyi duk abinda naga zan iya yi don inga an d’aure Baraka har sai inda karfina ya Kare”
Nana Tace “Ni kaina ina farin ciki, Asiyah bazan daina neman yafiyar ki ba, sabida na bada babban gudumawa wurin tarwatsa Miki rayuwa, Kama daga Kan mutuwar mahaifiyar ki,Da Mahaifin ki Kai hatta mutuwar kanwarki duk Shirin Baraka ne ko ince Shirin mune”
Cikin Rawar murya Tace “Harda Daddy mummy ce ta kashe shi?”
Kai ta d’aga mata Tace “Eh”
“Amma….Amma….. Anisa…anisa rashin laf…lafiya fa tayi”
“hakane Amma d’aura mata akayi,tana sane shiyasa taki kaita asibiti Kuma ko da ace an kaita ma babu abinda za a iya Mata”
Asiyah dafe kanta tayi tana ambatan ” Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un,Inna wa Inna ilaihirraji’un” hawayene sirara ke saukowa daga idanun ta.
Diyya dake kusa da ita take d’an bubbuga Mata baya a hankali.
Cikin kuka Tace “sama da shekaru goma Amma na kasa manta wannan ranar Yana ‘daga daga cikin iftila’in rayuwa ta sabida babu yanda banyi daku ba a wanchan lokacin ku kaita asibiti ku ka ki”
Nana ita kanta kukan take Tace “Dan Allah Asiyah kiyi hakuri Ni Sam ban so aka kashe Anisah ba,sabida Anisah yarinya ce Mai hankali karama ce Amma tunanin ta na manya.”
“Abinda na kasa ganewa anan shine mummy nason Daddy sosai sabida yanda take nunawa tana kishin sa,Amma ace ta kashe shi,Taya ma hakan ta Faru bayan a accident yayi?”
“hakane accident ne Amma Baraka ce sila, Soyayyar da take Masa duk ba gaskiya bace son abin duniya ne kawai irin na Baraka,sannan tana kishin mahaifiyar ki, Sadeeq mutum ne Mai son mutane,gashi da kyauta, hakan yasa take kishi sosai, Baraka irin mutanen Nan ne masu mugun hassada a Lokacin muna jami’a kawayen mu mu had’u ne bamu rabuwa, Ni da mahaifiyar ki sai Baraka da Kuma Amina,aminace ta Fara aure a cikin mu tun muna ss2 Alhaji Ahmad shettima ne ya aureta a Lokacin target d’inta Kenan Amma Amina mutum ce Mai ibada hakan yasa Bata ci nasara akanta ba, Fatima Kuma bawai bata ibada bane a’a kawai ta yarda da wacce bai kamata ta yarda da ita bane, tun Kan ayi auren Sadeeq da Fatima taso raba su Amma abin yaci tura ta dad’e tana shirin raba su day asiri Amma hakan baiyi ba shine ta samu damar kashe ta da poison daga Nan ta samu ta aure shi”
Hashim cike da mamaki yace “Kina nufin Mahaifiya ta kawar kice?”
Cikin rashin fahimta tace “Mahaifiyar ka Kuma?”
“Eh suna na Hashim Ahmad shettima”
“Ah ikon Allah,lallai Hashim ka girma rabona da Kai tun kan ka tafi kasar waje karatu”
“Hakane nayi mamakin yanda akayi ban gane ki ba,duk da ina Miki kallon sani”
Yar karamar dariya tayi irin tasu ta manya tace “Ai dole an kwana biyu ai”
“Hakane ina Yesmin?”
Kan ta bashi amsa suka jiyo muryar ta Tace “Gani Nan,mummy Baki mukayi?”
Zama tayi akan kujera Mai d’aukan mutum d’aya.
“Eh yayan ki ne Hashim”
“Oh Allah sarki kullum ina jin labarin ka Amma ban Sanka ba”
Murmushi yayi Yace “Gashi yau ki. Ganni”
“Hakane shekaran jiya ma a gidan Mummy Amina na wuni,har…..”
“Yesmin Dan Allah surutun ya Isa haka”
Ya Maida kallon ga Nana yace “Amma Nana kin tafka babban kuskure,kiyi ta istigfari”
“Ina Kai Abban Yesmin,ba dare ba Rana” ta karasa maganar tana share hawayen da suka zubo mata.
“Yanzu kuka ba naki bane idan na zakiyi kiyi shi akan Sallaya” ya Maida kallon sa ga Hashim “Masha Allah abun duk na gida ne,to yanzu mafita d’aya ya rage Mana mu kama Baraka red handed shine kad’ai inda zamu samu a kamata”
Asiyah Tace “But she is so clever Taya za a yi mu samu evidence?”
Murmushin gefen baki Nana tayi tace “simple Amma fa akwai risk,dole zan koma na bata hakuri mu cigaba da kawance,ke Kuma Asiyah zaki koma gidan ku”
Khamal,Diyya, Hashim,da Asiyah a tare suka ce ” whaaaat?” har Saida Yesmin ta d’an tsorata sabida duk ta Maida hankalin ta Akan wayarta tana chatting.
Hashim murya na rawa yace “No baziyu ba gaskiya Asiyah baza ta koma gidan Nan ba,kin manta yanda take Mal treating d’in ta ne? Itace fa sanadiyar makancewar ta Allah ya kawo Mana da sauki da ita da gani har abada, gaskiya a canza wani shawara”
Khamal yace “Babu wani mafita Hashim, don tun Kan ku dawo muke ta shiri da ita this is the only way,in dai muna so mu kamata da laifin shine kad’ai abunda zamuyi,zamuyi amfani da Asiyah ne wurin tona Mata asiri human rights zasu shiga zancen, sannan Nana zata koma Mata ne sabida tasa ta fad’in ita ta kashe su da bakin ta Ni kaina bana so Nana ta rab’e ta sabida annoba ce, zamuyi hakan ne sabida mu kwato wa asiyah hakkin ta”
Hashim Kam jinsu kawaii yake yi don shi Sam hankalin sa bai kwanta hakan ba.
Tashi Diyya tayi daga inda take zaune ce to matso kusa da shi, cikin murya Mai sanyi ta ambaci sunan sa “King”
‘dago kansa yayi ya kalle ta “please ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai sameta”
Girgiza Kai yayi yace “Take a look at her” yana nuna mata inda Asiyah ke zaune ya ‘daura da fad’in “hankalin ta a tashe yake Kuma kice ta koma,gaskiya bazaiyu ba, Asiya Nan Jin su Murmushi tayi ta taso itama ta zauna a gefen sa sai suka sa shi a tsakiya Tace “Ya Hashim Please Kar ka damu komai zai yi dai dai kaji”
“Look bazan ba fahimce ku ba kawai Ni baza kije ba”
“please…..”
Riko hannun ta yayi yace ” I don’t wanna loose you queen, Baki San halin da na shiga ba a rashin ki har na kusa zaucewa,idan wani abu ya same ki bazan iya jurewa ba ya kamata ki fahimce Ni”
“Wanann wani irinn Soyayya Hashim yake yi wa asiya? Nasan baya min irin wannan Soyayyar,ko dai tausayin ta yake Jine? Amma da me ta fini?” Diyya ke jero wa kanta wa’annan tambayoyin Wanda duk ba mai Bata amsoshin su.
Maganar su ce ta dawo da ita daga tunanin da ta shiga “Ya Hashim I will be careful I promise you,and insha Allah babu abinda zai sameni tunda a baya ban mutu ba yanzun ma hakane”
“Amma ai taso kashe ki,ta kashe Dad da mom sannan ta kashe Anisah ke kad’ai ce kika rage tana samun dama zata hallakaki tunda ta iya sa Miki barkono a Ido ba gargada zata iya sa Miki poison a abinci,so ni ban yarda ba”
Yana Kai Nan ya tashi ya fita,bin bayanshi tayi tana Kiran sunan shi Amma Bai kulata ba,cikin mitary say ya shiga har yasa key tayi saurin kwace wa.
“Haba king” kallon ta yayi don baiyi tunanin zata kirashi da wannan sunan ba ta d’aura da fad’in “Nasan baka so a cutar dani ina alfahari da hakan but me kake ganin zamuyi in ba wannan ba ko kana da wani shawarane?”
Girgiza Mata Kai yayi alamun a’a.
“Good to kayi hakuri muyi hakan kaji yanzu kan tashi mu koma ciki kaji king?”
Murmushi yayi Yace “Shikenan na amince Amma da sharad’i”
“Uhmnn ina jin ka mene ne sharad’in?”
Fuskar sa ya nuna Yana Murmushi har saida dimple ‘din fuskar sa ya nuna zaro Ido tayi Tace “me hakan yake nufi?”
“Me kuwa peg Zaki bani”
Zaro Ido tayi Tace “Peg Dan Allah ka rufa min asiri”
“Asirin ki a rufe maza ina jira” ya rufe idanun sa, sai Karan Bud’e kofar yaji yayi saurin riko Hannunta “Ina Kuma zakije?”
“Ka manta Ana jiran mune?”
“Ban manta ba ki bani peg ‘dina kawaii”
“Na maka alkwarin ka bini bashi”
“bashi zuwa yaushe Kenan?”
Cike da kunya Tace “Our first night.”
Har cikin ransa ya ji dad’in maganar sai Kuma ya ‘bata fuska yace “Ni ban yarda ba wayo Zaki min”
“Allah da gaske nake”
“Tunda kince Allah na amince”
“To tashi Muje”
Sakin hannun ta yayi suka fita,suna zuwa parlor shirun kamar ba kowa,kowa da abinda yake ayyanawa a ransa.
Hakuri ya Basu sannan yace ya amince,anan ne ya ke fad’a musu abinda ke tsakinin su da Safiyya, Asiyah Tace “Allah sarki Kanwata bata chanchanci hakan ba, hakan zai karya mata zuciya”
Nana tayi saurin fad’in “Babu abinda zai sameta, sabida ba a cikin hayyacin ta take ba, ita ma asiri aka Mata,sannan Safiyya bata son Hashim ko kad’an tun Lokacin da ta San labarin Hashim babu yanda bata yi ba Akan ta shige Masa ba Amma taki,Amma Ni a Lokacin ban San Kai bane don Taki fad’a min a fad’in ta sai komai ya kankama zata Sanar dani”
Diyya cike da mamaki Tace “Asiri Kuma Baraka ce ta mata,Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un wannan wace irin uwace haka?”
“Baraka Kennan tafi sonka kanta fiye da kowa in dai zata samu biyan bukata bata da matsala”
“Toh Allah ya kyauta”
Duk suka amasa da ” ameen”
Nana Tace “Tunda kin amince da plan d’in ya kamata ki koma gidan cikin gaggawa sannan akwai wani tulu a karkashin gadon ki, sannan akwai a d’akin Safiyya idan, sannan akwai a d’akin Baraka,sanin Kanki ne baraka bata Bari kowa ga shiga mata d’aki, daga Ni sai Safiyya, idan kika samu damar fasa na d’akin Safiyya,abun zai Zo Mana da sauki, Don malam yace ko da ganin tulun Safiyya tayi sihirin zai lalace, da fatan kin fahimta?”
“eh na fahimta”
Khalmal yace “Yanzu yaushe Zaki koma?”
“Gobe nake son komawa”
Nana tace “Ki bari sai jibi,don yau d’in Nan zanje gidan ta, in ya kwana biyu sai ki koma”
Ta amsa da “To Shikenan”
Khamal yace “Yauwa na manta ban Sanar daku ba,akwai camera da zan bawa Nana duk sanda zata je gidan sai ta makala zai Mana video na komai,Ni Kuma Ina nan ina recording a laptop d’ina.”
A haka suka Gama shirya yanda zasu Kama Baraka.
Baraka ba ta dawo ba har Saida ta gama sheke ayan ta da wani Alhaji kana ta dawo gida, a Lokacin karfe Bakwai da rabi haryanzu Safiyya bata sa inda take ba baccinnta take , Murmushi tayi Tace “Yar iska Ni zaki rainawa wayo tukanna ma” hannu tasa akan Safiyya ta Fara shawa a hankali tana lashe baki kamar wata sabuwar mayya hannu tasa a sugar ta tana wasa da dukiyar fulanin ta.
(Ni kaina da nake d’auko muku rahota abun yayi matukar bani mamaki,me hakan yake nufi,meyasa take shafata haka? Koma dai menene zakuji muje zuwa)
Door bell taji wani irin tsaki tayi cikin zafin nama ta nufi kofar tana Bud’e wa ta Fara masifa “Kai Bala bance maka Kar ka kuskura ka dame Ni ba me ya…..” Ganin wacce take tsaye ta tsaya baki a Bud’e Tace “Kece?”
Murmushi Nana tayi Tace Eh nice”
Hashim tunda suka bar gidan Abban Yesmin, ya zarce dasu inda ake sayar da wayo yi, yace su zab’i son ransu ganin sun tsaya Rawar Ido ya d’auka musu iPhone 13, sannnan ya mikawa Asiyah karmar waya Shima sabuwa a kwali,ta kalli Tace “Wannan fa?”
“Dole ki rike karamar waya kin San bazaiyu ki rike babbar waya a Wannan gidan naku ba” ya karasa maganar rai a d’an ‘bace dariya kawai tayi suka Masa godiya.
Diyya Kam tun da suka baro gidan ta kasa sakin jikinta, hashin ya kura da ita ya gano kishine ke cinta “To meyasa baza tayi koyi da Asiyah ba ita Sam bata damu ba Kuma yasan Asiyah na son shi” a ransa yake ayyana hakan ,cikin wannan tunanin suka Isa gidan su Diyya.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Please vote and Comment
Milhart ce
Yar terawa
GIPHY App Key not set. Please check settings