Advertisement
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
*MATAR UBA*
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Daga Alkalamin βοΈ
*Milly*
Fadilah Yakub
Advertisements
*(MILHAAT)*
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπποΈ*
*M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
CHAPTER 30
NOT EDITED
Hashim na ganin ta ya yi saurin sakin ta, wayar sa ya zaro cikin dabara ya tura text wa Nana
*ki shigo yanzu*
Advertisements
Baki a Bud’e take kallon ta tace “Asiya kece dama kina raye?”
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
……… Murmushi tayi Tace “Eh nice Mummy”
Baraka ji tayi wani Abu ya tsaya mata a makoshi Rai a ‘bace Tace “Sau nawa nake fada cewar ki dai na Kira na da mummy?” Gyara tsayuwar ta tayi tace Wai tukunna ma uban me ya kawo ki gidana?”
“Na dawo gidan mune”
“gidan ku ke dawa?”
“Ina nufin gidan Mahaifina”
Murmushin keta tayi Tace “Kan na rufe idona na Bud’e ki fice min daga gidana”
“Me ke faruwa a Nan na ganku haka?”
Nana ke musu Wannan tambayar, Baraka kallon ta kawaii tayi ta Maida kallon ta ga Asiyah Tace “Baza ki fice ba?”
Asiyah kawar da kanta tayi kamar ba da ita take ba, hannu takai zata mare ta Hashim yayi saurin rike Mata hannu.
Nuna ta yayi da ‘yar yatsata yace “Don’t you dare try it,idan Kika kuskura Kika sa hannu ki ajikin ta wallahi wallahi sai na sa an Kama ki and I’ll make sure that babu Wanda ya isa ya fiddo ki”
Cike da mamaki take kallon sa Tace “And who the hell do you think you are da zaka Zo har cikin gidana ka nemi Gaya min magana,Kar ka manta kana matsayin d’ane a wuri na tunda auren ‘yata zakayi,Yar da na tsuguna na Haifa for that matter”
Yar karamar dariya yayi yace “eh hakane matsayin d’a nake a wurin ki,tunda Yar ki nake son aure, Amma ba Yar da Kika tsuguna Kika Haifa ba”
Cikin rashin fahimta murya na rawa Tace “Ban gane ba me ka… Kkk…nufi?”
“Ina nufin tunda Masoyiya yata ta dawo Safiyya bata da sauran gurbi a Rayuwata”
Safiyya fashewa tayi da kuka Tace “Dan Allah Hashim Kar ka min haka Dan Allah”
Har cikin ransa baya son ganin kukanta sabida a matsayin kanwa take a wurin sa Amma yayi burus yace “Kiyi hakuri Safiyya ke Kan ki kin San ba ke nake so ba Asiyah nake so”
“Amma kamin alkwari zaka aure ni yanzu kuma kace ka fasa please don’t do this to me”
Baraka tace “Munafuka algunguma Kinga daga zuwan ki kin ‘bata min komai,wallahi Baza ki zauna min a gida ba ki koma chan inda Kika fito ki cigaba da karuwanci ki”
“Babu inda…..”
Nana Ce tayi saurin katse ta Tace “A a Baraka kar kiyi haka duk lalacinta Nan gidan sune”
Baraka Tace “Amma kin San….”
“Kar ki damu zan fad’a miki dalili na,Zo mu shiga daga ciki” hannun ta ta riko ta maida kallon ta ga Asiyah Tace “D’auki kayanki ki shiga kinji?”
Kai kawaii ta d’aga Mata alamun toh.
Suna shiga Nana Tace “Wai dama Asiya bata gidan Nan?”
“Eh bata Nan”
“Toh Amma ina taje haka kin San min kwana biyu ban san me ke faruwa ba”
Nan ta kwashe mata yanda akayi ta zuba mata ruwan barkono a ido,har izuwa yanda baba mai gadi ya kaita asibiti “tun daga Wannan ranar ban sake sata a idona ba sai yau”
“Toh Allah ya kyauta”
” Ameen.”
” Yauwa kina jina? dalilin da yasa nace Kar ki koreta shine tunda har tayi gangancin dawo wa sai kiyi Mata abinda tun a baya bakiyi ba”
“kinyi gaskiya lokaci yayi da zan kashe ta kowa ma ya huta”
“A’a ba kashe ta ya Kamata kiyi ba, wahalar da ita zakiyi ba dare ba Rana da kanta zata tafi ta bar miki gida Kinga yaron Nan d’an gidan Alhaji shettima Yana da karfin da zai tsaya mata so nake ki kwantar da hankalin ki, a tsulale zamuyi maganin shegiya”
“Hakane kawata shiyasa nake sonki,Amma daga Ina kike ne?”
“Nazo wucewa ne nace bari na tsaya mu gaisa”
“Ina zakije Haka?”
“umm…umm hajiya tace ba lafiya”
“Ayya zazzabi ko?”
“Eh kin San Kuma jikin tsufa” mikewa tayi Tace “To ni zan wuce idan na samu sarari zan Zo mu Sha hira”
“To Shikenan sai na ganki.”
Tare suka fita Baraka wani irin mugun kallo tayi wa Hashim da Asiyah ta buga uban tsaki ta Maida kallon ta ga Nana “Muje nayi dropping ‘dinki”
“A’a Kar ki damu da mota ta na taho?”
“Tana Ina,ban ganta ba?”
“A waje na barta”
“Alright take care.” Ta shige motar ta, ta fice.
Wurin su Hashim Nana ta nufa tace “Kai Kuma ka yi maza ka bar gidan Nan Kuma Kar ka Kuma zuwa gidan Nan”
Cikin muryar kuka Safiyya Tace “Sabida me zakice Kar ya Kuma zuwa ni Kuma ya zanyi?”
“Banda ke Safiyya me zakiyi da na mijin da baya son ki?”
Zama tayi a kasa ta fashe da kuka, cikin sauri Asiyah ta nufe ta rike ta tayi, Safiyya da dukkanin karfinta ta ture ta.
Da gudu Hashim yayi kanta d’agota yayi ya rungume ta a tsawace yace “Baki da hankali ne?”
“Eh bani da shi”
“Hmm ba laifin ki bane,Queen tunda kema kin San yarinyar Nan Bata da hankali ki daina shiiga harkarta”
“To Shikenan King”
Peck ya mata a goshi yace “please ki shige ciki kinji?”
Murmushi tayi Tace “Toh Shikenan take care”
“You too” ya shafa fuskar ta ya tafi.
Yana tafiya Asiya ta d’auki jakar ta ta shige, Nana Ce ta riko Safiyya ta kaita har d’akinta sai da ta rarrashe ta takwantar da hankalin ta kana ta yi tafiyar ta.
A gidan ta ta tarar da Hashim, “yauwa Hashim kamar kasan ina son magana da kai,banji dad’in abunda kayi wa Safiyya ba, yarinyar Nan fa Bata da matsala ko kad’an kawaii ta had’u da sharrin uwane”
“Na sani Amma bazan iya jure ganin ana wulakanta Asiya ba”
“Amma….”
“Nana kyaleshi bazai fahimce ki ba, after all bashi ne matsalar mu ban yanzu,Baraka ta tonawa kanta a Siri tana bawa Yar ta magani Wanda yake juya Mata hankali,sannan d’azu nayi recording ta ambaci barkonon da tasa mata a Ido yanzu evidence d’aya ya rage Mana ta ambaci kisan da tayi” khamal ke Wannan maganar.
“Hakane wannan ai abu mai saukine zata fad’a Amma ni yanzu damuwa Safiyya ta samu lafiya idan mukayi kuskuren wani abu ya Sami Baraka ba tare da Safiyya ta ga Wannan tulun ba to fa har abada Rayuwar ta a haka Zata Kare in ba wani ikon Allah ba”
Iska ya hura Mai zafi kana yace “Kuma a haka kuke so Asiya tayi rayuwa a Wannan gidan?”
Murmushi Nana tayi Tace “Nasan halin da kake ciki, but Asiya is a smart girl tun tana yarinya take tare da Baraka, she knows how to handle her,yanzu Kaine dai ya Kamata ka kula da kanka”
Cikin rashin fahimta yace “Bangane na kula da kaina?”
“Abin nufi nasan Baraka baza ta barka haka ba musamman da ka nuna baka son Safiyya babu abinda baza tayi ba don ganin Safiyya ta mallake ka”
Khamal yace “Hakane Hashim ka dage da azkar don gaskiya matar Nan Bata da imani”
“Toh insha zan kiyaye” Sallama ya musu yayi ficewar sa.
Asiyah na shiga d’akin ta Murmushi tayi a bayyane Tace “Oh kamar ba a yi ba,Ya Allah gani gare ka ka tsareni daga sharrin matar Nan”
Gyallen da yafa ta cire ta ajiye a Kan gado Bata ji shigowar mutum ba sai saukar Marin da taji a fuskar ta.
Cikin ‘bacin Rai Tace “Safiyya ni? Ni kika mara?”
“An mare ki, kad’an ma Kika gani in dai akan Hashim d’ina ne,me yasa baki mutu bane”
Murmushi Asiyah tayi ta shiga tafi hannun ta dukka biyu ta d’aura a Kunkumin ta Tace “Yau naga karfin Hali,Hashim d’ina you mean my king ne naki?”
Hannu ta sake kaiwa zata mare ta riko hannun ta tayi ta wanka mata maruka lafiyayyu guda biyu Tace “yanzu da da ba d’aya bane A baya na barki, Amma a yanzu Baki Isa ba,Yau Kuma zan nuna miki banbanci da ke tsakani na dake.”
Sa mata kafa tayi ta Fad’i ta shiga Kai mata duka ta ko ina, Safiyya ihu take tana neman d’auki Amma bata daina zagin Asiyah ba ,Asiya kuwa yanda kasan ta samu jaka Saida ta ake ta son ranta ta sake ta,ta Kuma hankad’ata waje, ta nuna ta da yar yatsa “idan Kika Kuma shigo min d’aki ba tare da izini na ba sai na karya ki”
Cikin muryar kuka Tace “Allah ya Isa muguwa azzaluma ban yafe ba”
Ganin Asiya tayi kanta da gudu ta tashi ta wuce d’akinta.
Dariya ma abin ya bawa Asiyah, ta ja kofarta ta rufe a bayyane Tace “Yau Kam nasan za a min welcome yanda na daka mata ‘ya Nima hakan za a min,ko da yake duka ya zame min man shafawa duk da na kwana biyu” tana kallon fatar jikinta.
Karar wayarta ne ya sanya ta d’auko purse d’inta ta d’auko wayar gamin Hashim ne tayi Murmushi Tace “King”
“Umm queen ni gaskiya a canza min sunan Nan bana so”
“Laa to me yasa?”
” Haka kawaii bana so”
“But da sunan Aunty take Kiran ka dashi”
“Eh na sani ke daban ita ma daban Wannan sunan da take kirana dashi ne,saboda haka a canza min”
“To yanzu fad’a min wani suna kake so na Rika Kiran ka dashi?”
“koma wanne Wanda ta dace dani”
“Toh idan na Kira ka Excellency yayi?”
” Idan ya Miki Nima yamin”
“To Nima a canza min queen din nan tunda sunan da kake kiranta dashine.”
Cikin murya Mai sanyi kamar rad’a yace “First Lady”
Murmushi tayi Tace “I like it”
“Like ma ba love ba?”
“Sorry to I love it”
” Ban yarda ba cire to d’in”
Yar karamar dariya tayi Tace “I love it”
“Yauwa yar Budurwata I love you”
” I love you too Dan Saurayina.”
Hirar su suka Sha sosai har aka Fara kiraye kirayen sallar azahar,yace mata zashi masallaci sannan zai bawa Nana CC camera ta kawo mata,Sabida gudun matsala.
Asiyah na idar da sallah ta kwanta, baccin ta take hankalin ta kwance ba ta tashi ba har Saida aka Kira sallar la’asar ban d’aki ta fad’a ta watsa ruwa had’e da d’auro alwala tayi sallah,cikin ta ne ke kugi wani irin yunwa take ji,da sauri ta tashi tayi hanyar kitchen, indomie ta d’aura don shine abinda zaifi Mata saukin girkawa agurguje ta daka Kayan Miya ta had’a indomie, tana saukewa ta juye a plate ta Fara ci Kennan Yar aiki ta shigo kallon ta tayi Tace “Wane Ne ke?”
“Yar masu gida” kawaii Tace Mata tab’e baki tayi,tayi ficewar ta,Saida ta cika cikinta ta d’auko lemu mai sanyi ta kora kana ta fita, a parlor ta tarar da Safiyya da Baraka,cikin girmawa ta gaishe ta tsaki tayi had’e da kawar da kanta.
Tab’e Baki Asiya tayi a zuciyar tace “ke Kika sani”
Daki ta koma ta d’auko wayarta fita tayi ta zauna a garden na gidan.
Chatting d’inta take hankalin ta kwance da farin cikin ranta,tana cikin chat din ne Diyya ta Kira ta, ta Kara mata karfin gwiwa akan ta dage da azkar tayi mata godiya sosai.
Bata koma cikin gidan ba har Saida taji ana Kiran sallar Maghriba, Asiya mamaki ne ya Kamata tana ta jiran a dake ta ko Kuma a balbale ta da masifa Amma shiru kake ji,har garin Allah ya waye Basu kulata ba ita ma Bata kula su ba.
Asiyah na kwance a d’aki taji tana bukatar Shan Abu Mai sanyi, a hankali take saukowa daga Kan stairs maganar da taji sukeyi ni Yasa tayi saurin komawa baya don tabbatar da abinda taji “Mummy na fad’a Miki ni fa bazan sa mishi komai yasha ba,nafi so ya Soni tsakani da Allah bada asiri ba”
“Banda ke Safiyya kina ganin idan Wannan yarinyar tana raye ina zai kulaki? Ita ma asirin ta Masa Amma ke zan had’a Miki Mai karfi Wanda bazai guje ki ba”
“But Mummy asiri fa na karyewa”
“Haba Safiyya, kina da ni ai baki da wata matsala bazan Bari hakan ya Faru ba”
“To mummy na amince”
” Yauwa Daughter ga Wannan shi Zaki sa Masa a abinsha”
Karb’a tayi Tace “To Amma taya za’a yi Sha bayan kin san ba zuwa gidan Nan zaiyi wurina ba”
“Kiranshi zakiyi yazo idan ta Kama har kuka ki Masa”
Fridge d’in dake parlor ta nufa ta d’auko baban gorar Exotic ta karb’i maganinn ta juye duka a ciki Tace “Kan yazo ya jika sosai maza jeki ki kirashi ni yanzu zan fita zan ajiye Miki shi a marfin fridge d’in”
” To mummy sai kin dawo” saukowa Asiyah ta nufi hanyar kitchen kamar bata ga kowa Baraka a zuciyar ta tace “yarinyar Nan ta koyo rashin kunya” a bayyane kuma Tace “Asiyah Zo Nan”
Ba musu tazo,durkusawa tayi Tace “Ke Baki San yanda ake gaisuwa bane?”
“Yi hakuri mummy ban lura da ku bane”
” Mtsww matsalar kice Wannan tunda Allah yayi kin dawo sai ki d’aura daga inda Kika tsaya” ” ban fahimta ba Mummy”
“Ina nufin aikin gidan Mana,sai ki shige d’aki ki kulle Kanki kamar wata uwar mace”
” Insha Allah zan Fara”
“Da kin taimakawa kanki, tashi ki bani wuri”
Tashi tayi ta koma d’akinta ,tana shiga ta Kira layin sa Yana picking ta fad’a Masa plan d’in da ake shiryawa, Yar karamar dariya yayi yace “Kar ki damu ba zuwa zanyi ba”
“A a kazo please”
“Meyasa Asiyah so kike ta mallake ni?”
“A’a kasan bazan so hakan ba kawaii dai kazo I’ll handle it bazan bari kasha ba nasan zata Kira ka.”
” Eh ga kiranta ma Nan ya shigo”
“Good sai kazo” ta katse wayar.
Tana jin karar motar Baraka na barin gidan ta leko ta Duba ba kowa a parlor cikin sauri ta nufi fridge ta d’auke exotic d’in ta d’auko wani ta ajiye a madadinsa tayi saurin komawa d’akinta ta juye a toilet.
Safiyya tayi mamakin yanda akayi ya amince zaizo cikin sauki, ba tayi Tunanin komai ba itae duk a wautanta tausayin ta yaji.
Bai d’au lokaci ba ya karaso gidan Asiyah ya Fara kira jiran ta yayi a waje Saida suka d’auki tsawon Mintuna talatin Kan ta fito ta koma cikin gida, tana shiga ta Kira Safiyya ya Sanar da ita ya shigo, fitowa sukayi suka zauna a parlor yace Yana “Yau anan zamu zauna?”
Murmushi tayi tace “Eh ai yanzu ka Zama na gida”
Tab’e baki yayi yace “Okay,gani kince kina son ganina?”
“eh dama…..dama….”
“Dama me? Kiyi magana please Ina da abubuwan yi a gabana na baro Nazo Nan,idan baki da abin fad’a zan tafi”
“Sorry dama so nake na baka hakuri akan abunda nayi maka nayi wasa da emotions d’inka bayan Kuma nasan bani kake so ba”
“Bakomai ya wuce a gaskiya naji dad’i da Kika gane gaskiya”
Murmushi tayi Tace “thanks for understanding, barina kawo maka abinsha ko?”
“Okay dama ishi nake ji”
” Me zaka Sha to?”
“As usual kin San favorite d’ina ai”
” Hakane”
Tashi tayi ta d’auko ta tsiiyaya Masa a cup ta mika Masa da bismillah ya fara sha, Asiyah dake sama tana kallon su abun dariya ya Bata.
Sai da ya shanye ya ajiye cup d’in.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
PLEASE SHARE AND COMMENTS
MILHAT CE
YAR TERAWA ποΈ
GIPHY App Key not set. Please check settings