Advertisement
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
*MATAR UBA*
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Daga Alkalamin βοΈ
*Milly*
Fadilah Yakub
Advertisements
*(MILHAAT)*
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπποΈ*
*M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
CHAPTER 31
Not edited
Tashi tayi ta d’auko ta tsiiyaya Masa a cup ta mika Masa da bismillah ya fara sha, Asiyah dake sama tana kallon su abun dariya ya Bata.
Sai da ya shanye ya ajiye cup d’in.
Advertisements
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
……….. A zuciyar sa yace “Yanzu daba don Asiya ba da Shikenan nima na Zama robot sai yanda akayi dani”
“in Kara maka?”
“A a ya ishe ni, Ni Yanzu zan tafi sai munyi waya”
“okay to Muje na raka ka”
“A’a nagode ki yi zaman ki”
Yayi ficewar sa.
Yana fita a gidan ya shiga dialing number Asiyah, duka d’aya ta d’auko, a handsfree yasa wayar kasantuwar Yana driving tana picking yace “Da fatan dai kin canza drink d’in?”
“Wani drink Kenan fa?”
Tana dariya kasa kasa, ” maganar drink d’in da ake Shirin bani Mana”
“A a ban canza ba, Yanzu jira nake na faki idon ta Kan na canza”
Zaro Ido yayi had’e da taka birkii har sai da ya kusa buge wani Mai matching.
Cike da tashin hankali yace “Me kike nufi? Kina so kice min Baki canza ba?”
“Eh Amma yanzu zanje na canza”
“Amma d’azu kince min kin canza”
“A’a baka ji da kyau ba dai,zan dai canza nace maka”
“Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un”
“Ya dai Excellency,irin wannan salati haka?”
Kasa ce mata komai yayi sai sallalami yake “Dan Allah me hakane?”
“Asiyah na Sha fa wallahi na Sha , Shikenan sai yanda akayi dani”
Dariya ta shiga harda kwanciya a kasa ,kasa cewa komai yayi har sai da ta gama Tace “Hello?”
“Ina jinki dariyar me kike?”
“Dariyar ka wallahi dariya ka bani”
“Asiyah ince Miki nasha Kuma ki tssya dariya”
” Eh man ba Dole ba Ashe haka kake da tsoro?”
“Ji man hajiya maganar sihiri fa ake anan kin San fa matar Nan ja’ira ce.”
Yar karamar dariya tayi tace “ina Raye ina numfashi sai in bar a cutar min da kai? Bazaiyu ba,wasa nake maka zuwa nayi na zubar, ka kwantar da hankalin ka”
Jingina kansa yayi a jikin gujerar ya sauke wani ajiyar zuciya yace “zakiyi kisan Kai”
“Ban gane zanyi kisan Kai ba?”
“Saura kad’an da nayi accident na buge wani”
“Wayyo Allah na Kai baka San was bane?”
“Ina zan san wasa kike bayan baki nuna min alamun hakan ba, gaskiya kin cutar dani”
“Dan Allah kayi hakuri ni banyi hakan don na tsorata ka ba”
“Ni gaskiya ban hakura ba”
“please Mana Excellency, kasan fa bana so kana fushi Dani”
“bana fushi dake but sai na rama, Dole na hukunta ki.”
“A’a ni ban yarda ba”
“Gara dai ki bari na rama if not ko Zaki yi bayani a first night”
Sai ji yayi kitt, ta katse call d’in dariya ya shiga yi ya sa wa motarsa key ya wuce gida.
Ita ko dariya ta shiga yi ta kwanta a katifan ta, tana Kara jin soyayayya da kaunar say na Kara narkuwa a zuciyar ta.
A parlor ya tarar da Momy na zaune cikin Ladabi ya gaida ta har ya Mike Tace “Son zauna ina da magana da Kai”
Sai da yaji wani rass don idan yaji Tace hakan yasan babbar maganace.
Dukkanin nitsuwar say ya tattara, gyaran murya tayi tace “Na lura a cikin kwanakin Nan ba ka cikin nitsuwar ka wai me ke faruwane?”
“Mum wallahi maganar Asiyah ce take damina”
“Toh wani abun ne Kuma ya Faru?”
“A’a haryanzu dai Wannan maganar nata da Mummyn ta ne”
“A gaskiya bana jin dadin yanda ka Zama jibi fa,yanda ka wani kwanjame haba,in fa abun Nan bazaiyu ba ka rabu da yarinyar Nan”
A firgece ya d’ago kansa ya kalleta cikin Rawar murya yace “Dan…..d..Dan Allah Mom Kar kice haka wallahi idan na rasa Asiyah komai zai iya samina, zan iya rasa ta” riko hannayen ta yayi ya had’a da nashi ya d’aura da fad’in “Rasa Asiyah tamkar rasa Raina ne Mom” ya karasa maganar hawaye na gangarowa da ga idanun sa har kuncin sa.
Kallon mamaki take masa (tun Yana yaro rabona da ganin hawaye a idanun sa ba,a Lokacin da mahaifin sa ya rasu baiyi kuka ba duk da shakuwar dake tsakanin su sai dai ta shiga tashin hankali matuka).
Murmushi irin nasu na manya tayi ta sa hannu ta share masa hawaye had’e da fad’in “Son kuka?”
D’ago idanun sa yayi da suka Riga suka Kad’e sukayi jaa, kallon ta yayi Murmushin gefen baki yace “Hmm Mom da ace zan iya fasa Miki kirjina ki gani na tabbata Zaki ga sunan Asiya ne a rubuce a ciki”
Huci tayi mai zafi ta Tsaya kallon sa ta sun d’auki kusan dakika goma ba Wanda yace komai.
Hannu tasa ta shafa kansa tace “Son in dai kana kaunar yarinyar Nan har haka nima ina kaunarta sabida ina son abinda kake so, zan tsaya maka wurin ganin ka auri Asiyah Amma da Sharad’i”
Murya na rawa yace “iiii….innaa… Jinkiii koma.. koma mene ne Ni zanyi in dai zan Samu Asiyah”
Hannun ta ta zare acikin Nasa ta Kuma sauke hannun ta dake kansa.
Ganin tayi Shiru yace “Mummy kinyi Shiru,ina jinki”
Cike da nuna muhimmancin maganar ta gyara Zama ta d’aura kafa d’aya akan d’aya tace “Ina so kaje gidan Nana ku dai daita tsakanin ku da Yesmin,idan kayi hakan zaka auri Asiyah”
Zaro Ido yayi a razane ya Mike yace “Yesmin!!!!
Itama mikewar tayi tace “Eh Yesmin ko ban Isa da kai bane?”
Cikin Rawar murya yace “Amma….Amma mom kin fasa san akwai maganar aurena da diyya, ya Kuma Zaki ce na auri Yesmin?”
Cike da gadara tace “Eh ina sane”
“To Amma Mata uku Kenan zan aura?”
‘daga kafad’a tayi Tace “Oho wannan matsalar takace ba nawa ba all I Know shine zaka auri Yesmin and that’s final”
Ta juya zata tafi yayi saurin so gabanta, durkusawa yayi ya had’a hannu wuri gudu Yana kuka Kamar yaro harda majina yace “Dan Allah Mom karki min haka wallahi ko karai bana jin soyayyar Yesmin.”
Har cikin ranta take jin tausin d’an nata but Babu yanda zatayi ta Riga tayi was kawarta Nana alkawari, ta dad’e tana neman hanyar da zata bullo wa al’amarin amma ya nace shi Diyya yake so yanzu Kuma ya koma Kan wata Asiya.
Kukan da yake ne ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula, a tsawace tace “Hashim!!!
A razane ya Mike Yana kallon ta,nuna shi tayi da d’an yatsa tace “Kul ka kiyaye ni zan sab’a ma kana jina ko? Kayi yanda nace ko ranka idan yayi dubu sai ya ‘baci” tana kaina ta wuce haura d’akin ta.
Ba ta Kai ga haurawa sama ba taji wani irin kara, a razane ta juyo ta hango Hashim na yashe a kasa baya motsi, da gudu ta nufi inda yake tana Kiran sunan sa Amma ba amsa.
Da gudu ta fita ta Kira Mai gadi, da taimakonsa tasa shi a mota suka zarce asibiti.
“Hmm Nana kenan,ke wallahi dadina dake kauyanci sai kace ba girman cikin garin gombe ba?”
“Baraka Kenan, ke dai baza ki fahimta ba Shifa Rayuwar Nan bata da tabbas isan yau kaine gobe ba kai bane ba,ya kamata ki rage wasu abubuwan ko ince ki daina su gaba ki d’aya”
Shewa tayi harda tafi Tace “Allah mutuniyar kice min wa’azi ki ka koma”
“Be serious Mana Baraka is high time ki daina Kar ki Zo kina da na sani daga baya”
“Nifa yanzu Sam na kasa gane me ke damunki infact ma ni ban yards dake ba totally, Anya dawowan Nan da Kika yi ba da biyu ba kuwa?”
Kirjin Nana ne ya buga dum ba ita kad’ai ba hatta khamal dake kallon su a karamin cameran da ta makala ya tsorata.
Muryar shi taji a ear pod d’in dake kunnen ta Yana fad’in “Calm down calm down Kar ki bari ta fahimci komai?”
Jin muryar mijin nata ya sanya ta yi saurin gyara Zama tace “What exactly do you mean Baraka?”
“What I mean is that I can feel it”
“Feel what”
” I don’t know but I have a weird feelings that you are trying to back stab me”
Murya na rawa Tace “Back stab you? Yanzu Baraka kina ganin Ni zan cutar dake ne?”
‘daga kafad’a tayi Tace “Who knows?” Hannu tasa ta d’auki wayar ta dake ajiye a gefen ta ta shiga latsawa, kana ta ‘dago Kai tace “Yanzu dai kina so kice min kin daina harkar bariki Kennan ko?” Ta cigaba da danna wayarta Kamar ba ita tayi maganar ba.
“Eh inshallah na bari kema ina so ki bari,sabida mun Zama d’aya so nake mu gudu tare mu tsira tare”
“Hmm Nana Kennan nifa na Riga nayi nisa bana jin Kira, ya kamata ace zuwa yanzu kin San ko ni Wace Ce , bani da tausayi bani da imani,zan iya ‘batar da mutum don biyan bukatana”
Ajiye wayar ta tayi tace “Kin t’aba tunanin zan iya kashe kawata? Kin San dai duk kusancina dake baki Kai yanda muke dake ba, na kashe ta ne sabida ina kishin nasarar da take Samu a rayuwarta, rayuwarta na tafiya dai dai yanda ya kamata yanda Kika San itace ta ke tsara tsarin Rayuwar ta”
“Fine Ashe kin San rayuwarta Normal yake tafiya, to shine banbanci mumuni da Mugu”
Dariya tayi tace “Na Sani wallahi ni muguwace tunda Sadeeq ma nice na kashe shi”
Zaro Ido tayi tace “ban gane ba Sadeeq accident yayi ko ba haka ba?”
“partially” sai ta kwashe da dariya, cikin tsoro tace “Baraka tell me what I don’t know, kina nufin ke Kika kashe shi?”
“Eh mana, wasu kud’ad’e na bukata a gunsa ya hanani,Babu yanda banyi dashi ba nayi fushi, fad’a m, Shagwab’a duk yaki shiyasa na cire birkin motar tasa,mtsss Sadeeq Wawane wallahi akan 10mil ya Rasa ransa”
“Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un, Baraka Akan 10mil Baraka kinfi karfin 10mil ko a Lokacin Yana raye a Rana d’aya kina iya samun 5mil Amma Kika kashe shi?”
“Ke Dallah malama na kashe shi Kuma na kashe banza, nan ma ba fad’a Miki yanda akayi Anisah ta mutu ba,da Kuma me zakice?”
“Sanar dani”
“Hmm bayan mun fita dake mun ma Isa wurin party na tuna na bar karamar wayata a gida Kuma akwai call d’in da nake jira sai na fita na dawo gida ina dawo wa na tarar da parlour a hargitse har bed doom dina, hakan yasa na gane kud’i take nema, idan Asiyah na kusa bana iya cutar da Anisah, kin tuna maganin da Boka ya bani yace nasa mata a abinci tana mutuwa zan Samu ciki na haihu?”
“Eh eh eh na tuna”
” Gooood to shi na d’auka na same ta a kwance a d’aki na bata Tasha ganin zata iya fad’a wa Asiyah na bata Abu Tasha na yanke shawarar karasata kawai”
“Ban fahimce ki ba, karasata ta yaya?”
“Uhmnn pillow na danne shigiya na kashe ta dashi, cikin ruwan sanyi ta mutu, Allah sarki sai sunan Asiya take Kira ta kawo mata a gaji Amma Asiyah tayi Mata nisa, daba don hakan ba da ban haidi Safiyya ba, Baki ga kamannin ta sak na Anisah ba?”
“Eh sosai ma ai jini d’ayane”
“mtsww matsalar suce wannan Kinga Safiyya ma Kamar Yar tsana take a wurina ina rage zafi da ita duk sanda sha’awata ta tashi na sauke su a kanta, bazan boye miki ba na tsani ganin ta sabida kamar da take da Anisah,yanzu tana auran Hashim Shikenan zan San yanda zan raba shi da numfashin sa na kwace dukiyar sa, daga Nan barin kasar zanyi na Fara sabuwar rayuwa”
Jinjina kai Nana tayi tace “A gaskiya kinyi nisa sosai Ashe akwai abubuwan da ban sani ba har haka?”
“Barakace fa ko kin manta da wa kike magana ne?”
“a a ban manta ba”
“Yanzu mayyar Nan nake so na ga bayanta da nayi niyar kashe ta a Daren yau,but sai naga Hashim sun dai daita tsakanin su da Safiyya Kinga Kennan burina ta kusa cika ita Kuma Asiya sai na lalata rayuwarta, Kawata kin San mene ne?”
“A a sai kin fad’a”
“Wallahi kwanakin Nan hankalina ya koma Kan Asiyah, Kinga yanda nonuwan ta suka ciko kuwa wallahi inaa mararin su, so nake Nasha su”
“Asiyar da Kika tsana?”
“Eh ita,ita sha’awa ina ruwanta da tsana?”
“Hakane Babu Kam”
Wayar Baraka ne ta Fara ringing Murmushi tayi ta d’aga tana picking
Tace “Alhaji na har ka shigo?”
Banji me akace ba naji Tace “Toh gani Nan zuwa”
Katse wayar tayi Tace “To malama Ni fita zanyi”
“To nima gida…..” Hango Asiya tayi a saman stairs tana kuka hakan ne yanuna Mata cewar taji hiran nasu.
Hannun Baraka tayi da sauri ganin tana kokarin kallon abinda take kalli. Tace “Muje ko?”
Ba ta jira amsarta ba taja ta suka fita.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Please Vote and comment
GIPHY App Key not set. Please check settings