Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
Advertisements
*23*
Likitocine suka rufu akanta dan gano meke damunta,
Awanni biyu suka kwashe kamun bincikensu yazama ready,
Kamun lokacin Hammad mummy ya kira a waya ya sanar da ita suna asibiti zahra ba lafiya.
Daddy na gida lokacin daya yo wayar dan haka ษunguma sukayi zuwa asibitin dan hankalinsu ya tashi.
Sun iso ba jimawa,likita ya buฦaci ganinsu,bayan sun zaunane,likitan ya zare glass ษin idonshi sannan yaja dogon numfashi yace.
Advertisements
“munyi bincike zahra na fama ne da ciwon hawan jini,sannan zuciyarta ta kumbura,single mistake ze iya janyowa ta rasa rayuwarta,dole ne akaucewa duk wani abu daze ษata mata rai,ayi mata kuma abinda takeso,insha Allahu zuwa nan gaba zaa iya nasarar warkewarta gaba ษaya”
Hammad hannu yasa ya dafe kansa,hawaye na bin idanunsa,yaushe ne zahra zata tsira daga baฦin cikinsa?yaushe ne zahra zata mori rayuwarta kamar kowa?wannan sune tambayoyin dake yawo a kansa.
Magunguna likitan yabasu,jiki asanyaye suka fito daga office ษin daga mummy har daddy kallon tuhuma sukewa hammad ษin.
Hakanne yasa ya kasa zama cikinsu ya koma can gefe ya takure,yana adduar Allah yaba zahransa lafiya.
Baa basu damar ganinta ba se bayan kwana biyu.har rige rige suke gurin shiga ษakin da take,hammad daga bakin ฦofa ya tsaya yana kallonta,sosai tausayinta ke nuฦurฦusar zuciyarsa,ta rame lokaci guda tayi fari sekace wacce ta shekara tana ciwon.
Har lokacin bacci take, sede bana daษi bane,dan oxygen ne a bakinta.ga sauran naurori da suka kewayeta.
Hammad sosai lamarim ya firgitasa kuka sosai yakeyi da ฦyar daddy ya rarrasheshi.
Wata guda Zahra ta kwashe a asibitin sannan ta samu sauฦi,koda aka sallameta fafur tace ita gun mummy zata koma,dole hakan akayi dan gudun ษacin ranta.
A iya zamanta a asibitin magana bata taษa haษata da hammad ba,dan ko ganinsa batason yi,yana shigowa take lumshe idonta,
Duk abinda ke faruwa iyayensu na lura dasu sede basu sa kansu aciki ba tunda basu sako su ba.
Hammad ji yake kamar zeyi hauka gudun gidansa da zahra tayi daurewa kawai yakeyi,kallo ษaya zakai masa ka ษauka ya shekara yana ciwo sabida tsabar ramar da yayi.
ฦaki guda mummy ta ware mata,sannan taci gaba da kulawa da ita.
Hammad rashin zahra kusa dashi ba ฦaramar illatashi hakan yayi ba,shiyasa kullum yana gidansu shima ko ze samu sauฦi,gashi fafur taฦi bari su haษu.
Bayan wata biyu da dawowarta gidan,tasamu mummy a ษakinta,bayan sun gaisa tace”mummy inaso ne inci gaba da karatuna tunda nasamu sauฦi”ta faษi a shagwaษe.
Shuru mummy tayi tana nazarin ta,zuwa can ta ce,”to ay kinga bamu da iko akan hakan,kije ku yi maganar da mijinki,abinda ya yanke se ki sanar damu mu kuma mu aywatar”mummy ta faษi fuskarta cike da walwala.
Ran Zahra in yayi dubu ya ษaci,ita fa bason ganinshi take ba,bare har suyi magana,miฦewa tayi bakinta a gaba alamar jin haushi ta fice daga ษakin zuwa nata.
Girgiza kai mummy tayi sannan tace aranta”kwayi kwa gama shashancin naku ku koma gidanku”.
Zahra kwanciya tayi tana nazarin ta inda zata ษullowa lamarin,dan da gaske karatunta takeso taci gaba dayi,ganin bata samu mafita bane yasa ta miฦe jiki ba ฦwari ta nufi ษakin Hammad ษin.
Tura ฦofar tayi ta shiga bakinta ษauke da sallama,baya cikin ษakin,jiyo sautin ruwa tayi a toilet,hakan ne yasa ta fahimci wanka yake.
ฦakin ta shiga ฦarewa kallo,sosai yayi datti,ga kayan da yake cirewa duk a ฦasa baa kwasheba,inba hancinta ne ba ษakin har ษan wari wari taji yakeyi.
fitowa yayi ษaure da tawul aฦugunsa,yana riฦe da wani ฦarami a hannunsa yana goge ruwan kanshi,sam be kula da ita dake zaune a gefen kujera ba,kamshinta yaji ya daki hancinshi. ษauka yayi gizon da take masa kullum ne zama yayi gefen gadon ya dafe kanshi hawaye na bin idanunsa yace”haba zahra ta,nace miki na tuba,kiyafemin,nasha wahala sosai arayuwata arashinki,koda na sameki bansan ke bace ฦดarfillon danake nema,na rayu cikin so da kaunarki tun bayan faruwar lamarin nan,zahra ki daure kisoni koda rabin wanda nike miki ne”ya ฦarasa maganar hawaye na bin idonsa.
Sosai zahra maganganunsa suka shigeta,sede batajin akwai yafiya tsakaninta dashi.
Gyaran murya tayi,a firgice yakai dubansa gareta,mamakine ya cikashi ta yadda ta shigo ษakin besani ba.
Jikinshi har rawa yakeyi yataso yazo gareta,tsugunawa yayi ya kama ฦafafunta,ya ษora kanshi akan cinyarta,ya fashe mata da kuka kamar wani ฦaramin yaro,yana faษin”ki gafarceni zahra,sharri shaiษanne yasa na aykata hakan kiyi hakuri zahra kibani damar gyara kuskurena don Allah kimin afuwa zahra na gaza jure raahinki kusa dani”kukan dayaci ฦarfinshi ne yasa yayi shuru.
Zahra lumshe ido tayi hawaye na biyo idonta,sosai take ฦaunar Hammad so ba na wasa ba,haka zalika sosai take ฦin soja me ulcer ฦi bana wasa ba,yazatayi da wannan rayiwa tsakanin so da ฦiyayya.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings