SALON SO BOOK 1 PAGE 23-24

Advertisement

 

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

            🌹 SALON SO 🌹

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

    BOOK ONE 📖

Advertisements

Story & written by

Mommyn fareesa

   🅿️23&24

kauda kanta tayi gefe tak’i mgn”yasmeen! imaan ta koya miki rigima yanzun ko? yafad’a suna fita dg cikin company d’in suka hau titi”

     ni bbu wani rigimar data koyamun”mezai hana kasaka suit d’in nan dan Allah”kabarni da ita ahannu”ok dama sbd ita kike fushi?”Eh mana”to bazan karb’a ba”ki y’ar mana tunda bazaki iya rik’e munba”shiru tayi batace komaiba”wayarsa tayi ringing”yana dubawa yaga *stupid girl*(jidda yarinyar dake bala’in sonshi)tsaki yaja yayi rejecting d’in kiran”yarasa yazaiyi da fitinanniyar yarinyar”marar zuciya”ko yayi blocking nata saita canza layi tamasa mgn”shikuma ayanzun bazai yuyuba yacanza layikansa.sbd d’inbun mutane sun sanshi dasu….wani kiran yasake shigowa”kallon yasmeen yyi ya aza mata wayar kan cinyarta yace”.ki d’auka kimata warning karta koma kirana….da mamaki yasmeen ta kallesa tace”.wacece ,kuma amatsayina nawa dazan mata warning akanka???

Advertisements

       tafad’a k’asan ranta tana jin zafin yarinyar 

data kira”harta tsinke beyi mgn ba yanata driving d’in sa”wani kiran yakoma shigowa”yasmeen ta kalli fuskar wayar taga”

*stupid girl*

      sosai yasmeen tayi mamaki”tana ganin rashin zuciyar yarinyar ana k’in kulata tana cusa kanta…..kika bari ta tsinke baki d’aga ba ranki zai b’aci”yafad’a murya akausashe…. d’auka yasmeen tayi cike da jin haushinsa dana yarinyar”jidda tasaki ajiyar zuciya”ahankali tace”. sweetheart!!malama badashi kike mgn ba”na d’auka ne sbd namiki warning akansa”meyasa bakida zuciya?kinkira anshareki amma bazaki fasaba….jidda taja tsaki had’e da cewa”wacece ke ,akanme zaki d’aga mun kira??kibawa me waya wayarsa”d’aukar wayarki danayi hakan kawai zaisaka kisan na isa ne!sanin wacece ni kibari idan kin had’u damai wayar saiki masa wannan tambayar”dg k’arshe kidaina cusa kanki gurinda bakida muhalli….tana fad’in hakan taja tsaki takashe wayar”maimakon ta mayar masa da wayarsa saita cigaba da masa latse latse…..mr Aliyu kuwa beyi zaton yasmeen ta iya masifa hakaba”yanata dariya aransa”afili sai cewa yyi “malama tunda kingama aikin dana sakaki saiki bani wayata….

yafad’a yana k’ok’arin yin parking agefen wani h’ad’add’en restorent”

yasmeen batayi mgn ba ta ajiye masa wayarsa da suit nasa ta fito dg cikin motar”

   

     tana tsaye tana k’arewa gurin kallo yafito yana rufe motar”yasaka suit nasa yana kallonta”

gira ad’age yace”.nasaka sai ashafamun lafiya ko? murmushi tasaki”Allah yaya Aliyu kayi kyau sosai daka saka”

nama lura kai bakason saka kayanmu na asali na hausa fulani”sai kayan turawa”

Kinsaka mun ido kenan?Hmmm!kaga gobe Friday insha Allah”gsky manyan kaya zanfito maka dasu kasaka pls”

Allah yakaimu goben”Ameen yah Allah”tafad’a suna shiga ciki”

mutane kowa na zaune yana cin abincin sa akan tables dake gurin”

wani table ne dake can k’arshe bbu kowa”acan yanufa”yasmeen nabinsa abaya”

suna zama wani ma’aikaci ya iso gurinsu”yana kallon mr Aliyu”yyi saurin cewa MAI NASSARA we are happy to see you  welcome both!!

yatsina fuska mr Aliyu yyi kafin yace”.bana buk’atar ganin kowa anan”zan muku dable na kud’in ku”

sosai yasmeen ke mamakinsa”yaya Aliyu! shiiiiiiiittt! yafad’a yana galla mata harara”

da sauri ma’aikacin yabar  gurin yana murna”acikin 5 minit gurin yyi tsit”

Aka kamusu abincin da mr Aliyu yyi order yabiya”itadai yasmeen kanta ak’asa tana latsar waya”fatanta sugama taje tayi sallar azahar”

abincinsa yafaraci hankali kwance bebi takan yasmeen ba”

ganin tak’i kallon abincin yasakashi cewa”wai kina jira nace kici ne ko kuwa?”kinsan dai bazan yi asaraba”nifa na k’oshi dan Allah”kuma kaikace rakoka kawai zanyi”

be dameniba da k’oshinki  gara kawai kici”ko kuwa nabada shi na cire kud’in abincin a salary naki”

Nawane kud’in abincin?”5k ne duk plate d’aya”zaro ido yasmeen tayi”sbd ita azatonta duk tsadarsa be wuce 2k”

Itadai harga Allah tanaso albashinta tadinga tarawa a account nata ta siya musu gida ko me d’aki d’aya ne.

Ai bazata yarda acire wani abuba”badan tasoba taja plate d’in dake shak’e da abinci da miya da uban naman kaji”tasan cewa abincin yafi k’arfin ta”zatadai daure taci kawai”

Duk abinda takeyi yana kallon ta ta wutsiyar ido”da yadda take cin abincin ta da alama yamata dad’i”

Afili yace”.anaso ana kaiwa kasuwa”shiru tayi sbd tasan da ita yake”

sunfi 20 minit suna cin abincin”kafin mr Aliyu yarigata gamawa”

kina jiran sai nace kiyi sauri ne?”batace komaiba tacigaba da cin abincin ta”

hakan yyi daidai da wani guy yashigo gurin”idanuwansa suka hasko masa yasmeen”

Atake yanufi gurin table d’in su”hii baby! yafad’a yana k’ok’arin zama gefenta”saima asannan yalura da mr Aliyu”

D’ago kansa mr Aliyu yyi, yayiwa guy d’in kallon second 5 yad’auke kansa”yafara d’aukar keys nasa da wayoyinsa”fuskarsa ahad’e”yamik’e tsaye”

baby bakya mgn ne?”kafin yasmeen tayi mgn”mr Aliyu yace”.K!tashi muje”yafad’a cikin izzah yana hura hanci”

Pls yayanmu kabani 3 minit nayi mgn da baby”wani banzan kallo mr Aliyu yajefesa dashi yana matsowa gab da yasmeen yafinciki hannun ta”

Sosai guy d’in yasha jinin jikinsa”sbd ayanzun yagane mr Aliyu MAI NASSARA CEO na company d’in MAI NASSARA INTERPRISES!!

bece komai ba yabisu da kallo har suka fita dg wajen”

suna fitowa yasmeen tafara k’ok’arin k’wace hannunta”cikin jin haushi tace”. dan Allah kadena tab’ani yaya Aliyu”kasan bbu kyau… 

tsaki yaja, yakama masifa”bazan dena tab’aki d’in ba”ai sokike atab’akin sbd kina mun musu ko?dakuwa kinyi saina tab’aki”yana fad’in hakan yabud’e motar yaturata ciki”yazagayo yashiga”

mamaki takeyi aranta ina ruwansa da guy d’in nan na d’azun?”

Dg yanzun Idan ina tare dake karki koma kula wani d’an iska!kinajina?”dolene kiyi obey d’in rules& regulations d’ina”

Idan bakya tare dani zaki iya kula ko waye”

shiru tayi batace komaiba”suna isowa company d’in”ko gama parking be yiba ta fito dg motar”

masjeed ya wuce yyi sallah”itama yasmeen a office nashi tayi sallar”

yana shigowa bbu ko sallama yazauna kan kujera yanata harare harare”

yaya Aliyu!banza yamata beko kalletaba”yaya Aliyu!!takoma kiran sunansa akaro na biyu”

menene wai?koso kike namayar dake agun d’an iskan dakike fushi akansa anrabaku?”

nidai dan Allah ba wannan ba kayi hak’uri zanje gida”tunfa jiya rabona da gida”

Saiki bari time d’in tashi yyi”kamun alfarma tunda ayanzun ba aiki nakeba”

banza yamata”hakan yasa bata koma cewa komai ba”saima ta d’auki wayarta takira imaan suka fara fira….gaba d’aya mr Aliyu na sauraron firarsu”da yadda yasmeen ke shewa suna fira da imaan”

mamaki yakeyi wai yaushe yasmeen tayi irin wannan shak’uwar da imaan”

Kud’in wayarta suka k’are”atake imaan ta biyo kiran”

gaba d’aya mr Aliyu yagaji da surutunta”yana k’okarin mgn akayi knocking d’in k’ofar”

yasmeen takashe wayar”taje ta bud’e”salim ne tsaye yana kallon ta yace”.wani saurayi nason ganinki yana a first floor”

gsky badai niba”cewar yasmeen cikin mamaki”gsky kece sbd yafasilta kamanninki”

Da sauri mr Aliyu dake sauraron su yakunna TV me had’e da wearing d’in CTV camera” yashiga tun a first floor”atake fuskar guy d’in d’azun tabayyana”

yana huci ya kashe TV d’in”yasmeen na k’ok’ari shigowa tajishi yana waya da securities d’in compony d’in”sukama mutumin dake a first floor”har yana fasilta kamanninsa”

Da sauri ta k’araso ciki”tana k’okarin masa mgn taga yakoma saka wani kira”

Yaya Aliyu akanme zaka saka akamashi??”tafad’a tana kallonsa”

Hellow !kana jina?maza ayanzun karubuta takardar korawa salim”

yana fad’in hakan yakashe wayar yana huci ya mik’e tsaye”

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un!!haba yaya Aliyu!meyayi zafi haka?dan Allah kayi hak’uri kamayar da salim aikinsa”

baza’a mayar dashi d’in ba”shida aiki anan har abada”

Shikuwa zan nuna masa ba’a ja dani”wato biyomu yyi abaya ad’azun ko?”

yaya Aliyu karka saka sukamashi….ke dallah yimun shiru”

Kuka tafashe dashi tana cewa taya zaka saka akamashi sbd laifina”nizaka hukunta basuba”dan Allah kamayar da salim aikinsa…..banza yamata yana gyara tsayuwarsa”yak’ara wayarsa akunnansa”

Kun kamashi?”good”yafad’a yana kashe wayar”

yasmeen batace komaiba ta d’auki hand bag nata tana kuka tanufi k’ofar fita”

K!ina zakije?”wlh yaya Aliyu nagama yimaka aiki muddin baka mayar da salim ba”ka tausaya masa da aikin nan yadogara”wanda kasaka akama bedameniba”kanada hujjar yataka maka doka”

Tana fad’in hakan ta murd’a k’ofar da sauri ta fita……✍️

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAU DA GOBE 17&18

Advertisement  🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾   🌹YAU DA GOBE 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & writing by mmn fareesa 🅿️17&18 ……Wani irin mummun…

SALONSO 35-36

Advertisement  🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾             🌹 SALON SO 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾     BOOK ONE 📖…