SALON SO BOOK 1 PAGE 25-26

Advertisement

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

            ๐ŸŒน SALON SO ๐ŸŒน

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

    BOOK ONE ๐Ÿ“–

Story & written by

Advertisements

Mommyn fareesa

   ๐Ÿ…ฟ๏ธ 25&26

yasmeen na fitowa ta wuce floors d’in”alast floor tahad’u da khaleel zai shigo”d’auke kanta tayi sbd batason yaji wani abu abakinta”tana k’okarin danna bottom d’in k’ofar taji muryar salim

abayanta”yasmeen dan Allah kitaimakeni kibawa both hak’uri”wlh da aikin nan na dogara”this month matata ke haihuwa”yafad’a yana matsowa yakama hannun khaleel daya tsaya yanason jin meke faruwa?dan Allah kasaka baki kaida ita amayar dani bakin aikina…juyowa yasmeen tayi tana goge hawayenta tace”.salim bbu abinda zan iya yimaka”kaje da kanka k’ila yasaurareka”tana fad’in hakan ta dannan bottom d’in, k’ofar ta bud’e tayi saurin shiga yarufe……

Khaleel yadubesa kafin yace”.meke faruwa ne??atake salim yasanar masa komai”

Ajiyar zuciya khalell yasaki yace”.kaga gsky kaima baka kyautaba anan”daya turo kamata mgn da saikak’i zuwa ,gashi kajawa kanka”yanzun kaje gida zuwa gobe insha Allah zan saka amaka mgn”

Advertisements

Amma ayanzun gsky yana cikin fushi bazai saurarekaba”cewar khaleel azuciyarsa yana yiwa abokinsa wani zato akan yasmeen”

Jikin salim asanyaye shima yawuce yadanna bottom d’in k’ofar yafice”

Khaleel yawuce office d’in mr Aliyu”

       yana tsaye sai huci yakeyi”kallo d’aya zaka masa kasan ransa ab’ace yake”

       kaddai kace mun yarinyar nan ce ta turoka?”cikin b’oye yasan komai yace”.wace yarinya kenan?”

       tab’e baki mr yyi yace”.yasmeeen manah”wani abu yafaru ne?”yaka mata dan Allah kadinga hak’uri da yarinyar nan”kanacin zalinta da yawa wlh”wani banzan kallo mr Aliyu yayiwa khaleel kafin yace”.karka gayan maganar banza”ko yanzun ba itace sanadiyyar b’acin rainaba”ta isa tabani umarni ne”har tana cewa” idan ban maido salim ba tagama aiki anan”kar Allah yasa tayi aikin”sosai khaleel yafara fahimtar wani abu agun abokinsa”yana b’oye dariyarsa”yace”.tayi daidai akqn me zaka kori salim?sanar masa yadda akayi mr Aliyu yyi”yad’ora da cewa”shi wancan d’an iskan zuwa gobe idan yagama jigatuwa zanje namasa warning akanta”kafin asakesa”kaga gobe idan yaga wata mace sai yasake k’ok’arin binta da hujja”.

        salim kuwa da matarsa amma sbd Allah yayisa dashegen son mata”yana tsayamun a building suna fira ,sannan aka aikosa”dalilin dana koresa kenan….

Be kyautaba gsky”amma kayi hak’uri kamaido yasmeen”sbd kaga da bakinka kasanarmun ana k’aruwa da basirarta a company d’in nan”

       Inban mantaba jiya achat kasanarmun abinda aymaan yaso aikata mata….. k’arar turo k’ofar yasaka khaleel yin shiru”imaan ta shigo da sallama”suka had’a ido da khaleel”

murmushi yasakar mata”itama tana murmushin tace”.yaya khaleel ina wuni??”lafiya qlau imaan ya skul? alhmdllh”tafad’a tana matsowa saitin Inda mr Aliyu ke zaune”

Cike da shagwab’a ta dafa bayansa tana cewa”yaya Aliyu lfy na kira anty yasmeen tak’i d’agawa”dama d’azun muna mgn naji tace”.ina zuwa takashe wayar”to nasake kira kusan sau 20 ba’a d’aga ba”tana ina yanzun??”

Imaan meyesa surutunki yayi yawane?”aiki nakeyi kinzo kindameni”ina ruwana da Inda taje ko take??”tunda kinkira bata d’agaba”takuma gani ,ke mai zai hana kirabu da ita”tunda bata buk’atar hudd’a dake…..kukan shagwab’a yasmeen tasaka harda dire dire…

Lumshe idanuwansa khaleel yyi”tun imaan na tatsitsiyarta Allah yajarabesa da masifar sonta”

     yarasa ta ina zai Fara?agun MAI NASSARA ko agun imaan d’in…..Hmmm baby gara kimun shiru Allah ko jikinki yagaya miki yanzun”da b’acin ran da yasmeen ta k’unsamu zanji koda naki??”

       tamkar khaleel yyi mgn”amma sai yatuna da sauran time”amma yyi mamakin jin kalaman MAI NASSARA!

       Kinga imaan kiyi shiru kinji ko?”zanje nataho miki da yasmeen d’in”cewar khaleel cikin rarrashi”

     Lah dama kasan gidansu yaya khaleel?”ah ah zantambaya miki ne”yauwa dan Allah kabani number d’in ka zankirakq naji idan kagano gidansu”

murmushin samun nassara khaleel yyi”sbd dama yanason yasami number d’in imaan”

yayinda mr Aliyu yamusu banza zuciyarsa na zafi”yana tuna shi yasmeen zata zab’i rabuwa dashi sbd wani banza”

Khaleel nagama saka mata number d’in”imaan tayi ficewarta sbd tayi fushi da yayan nata”

Amma abok…..kaga mlm indai zancenta ne banaso! shikenan anjima idan kahuce munyi mgn”

Atare suka fice sbd lokacin sallar la’asar yyi…

    ***************

Imaan na isowa gidansu tayi k’ok’ari saita kanta”ta shiga fuskarta da walwala”

Kasancewar alhamis ne su asma’u na gida”sunata wasa itada Ahmed atsakar gidan”

wacce suke haya atare tana wanki da goyon d’anta”ta amsa sallamar ta”tana binta da kallon tuhuma”

Umma ta fito tana cewa”.yasmeen sai yanzun ?ya imaan da jikin?Eh wlh umma da sauk’i sosai”

gobe ma bazanjeba sbd bamu aiki a office sai monday”(tayi k’arya tunda gobe bata zuwa)to Allah yakaimu”

ruwa ta zuba taje tayi wanka ,tazo tagabatar da sallar la’asar”

Umma tace”.akamiki abinci?”ah ah umma ak’oshe nake”

Umma ta zauna tana kallon yasmeen kafin tace”.kinga d’ahara da munafurci da saka ido”(wacce suke haya atare)wai jiya da dare sai cemun tayi wai kina ina?taga baki dawoba”saina sanar mata dalili”bud’e bakinta sai cewa tayi Hmmm Allah yakyauta”ke yanzun kin yarda da cewa k’anwarsa bbu lafiya”k’ilama hutawa yakeyi da y’ar taki….banbari takai karsheba”nakuwa yimata tas”damata nasihar ta kyautata zato”subahanallahi!!wlh umma ni shaidace akan yaya Aliyu mutumin kirkine”betab’a mun zancen banza ba”bantab’a ganinsa da matan banza ba”asalima be sakar ma mata fuska”amma dan kanta itada Allah “

Da wannan suka canza wata firar”saidai gaba d’aya yasmeen hankalinta nagun mr Aliyu”

ga tsoron k’in amsa wayar imaan datayi” 

tabbas tasan be kyautaba daya kori salim”amma aganinta hakan shine mafita subar aikin atare “tunda itace sanadin barinsa aiki”

Koda dare yasmeen saidai bacci barawo yasaceta”sbd tunanin data sakama ranta”aikuwa tadinga mafarkin mr Aliyu”

Ab’angaren mr Aliyu kuwa”4 pm yakoma gida”yasami imaan na zaune a parlour”tana ganinsa ta d’auke kanta”

murmushi yyi yazo yazauna agefenta,yakama hannun ta guda”ahankali yace”.haba y’ar amanata!

kinfi kowa sanin idan raina ab’ace yake banason adameni ko?

Turo baki tayi tana kukan shagwab’a tace”.nidai idan kanaso na hak’ura kadawo da anty yasmeen”

shikenan zan dawo da ita bbu komai karki damu”yauwa yayana nakaina”tafad’a tana rungumesa”

yaya muje na had’a maka ruwan wanka tunda anty yasmeen batanan”

Ah ah kiyi zamanki zan je na had’a da kaina”yana fad’in hakan yatashi ya wuce sashensa”

gaba d’aya da dare mr Aliyu daya kwanta bacci”tunanin yasmeen dank’are aransa”sai yadinga alak’anta hakan da sabone kawai da shak’uwa da yyi da ita”da har zai kirata sai kuma yafasa…

Washe gari daya tashi da kansa yahad’a ruwan wanka yafito da kayansa”duk sai yaji wani iri”daba yasmeen ce tafito masa ba”tunawa yyi jiya tace”.yau yasaka manyan kaya tunda Friday ne”

Atake yasaka sabuwar farar shadda”wacce taji aikin zare bak’i”yakawo hula da takalmi da agogo bak’ak’e yasaka”yanata zuba fitinan nan k’amshi”

yyi kyau tamkar ango”atsatstsaye yyi break fast yafita”

Anty amarya da zakiyya na zaune ya wuce”ji zakiyya tayi inama ace mr Aliyu mijinta ne…..ita kanta anty amarya taji kwad’ayin yazama surukinta…lol

koda ya isa office gaba d’aya sai yaji bbu dad’i da bbu yasmeen”

Tunawa yyi idan yana aiki”tadinga mishi sannu da kamishi ruwa”idan yagaji ta amshi loptop tamasa typing”

itace goge can ,share can”amma yau saiyaga cleaners d’in kamar basuyiwa office d’in komaiba”

Dukda har yanzun haushinta yakeji”gashi wannan saurayin yanaso yaje yyi mgn dashi kafin asakeshi”

yana nan har 1:pm tayi “yarufe office d’in yatafi masjeed”

Ana tasowa masjeed yayiwa mani driver waya yazo yasameshi a Inda yake”

mani na isowa mr Aliyu yace”.gidansu yarinyar nan yasmeen zaka kaini”

dato ya amsa yana shiga driver sit”mr Aliyu ya zauna aback sit”suka d’auki hanyar anguwarsu yasmeen”

yasmeen kuwa bayan ta gama kalacin safe”ta wanke kayanta masu datti”dukda wankin tana yine tana tunanin mr Aliyu harta idar”

wanka taje tayi”bayan ta fito tayi sallar azahar”kafin suci abincin rana”

ta shirya cikin doguwar riga areviant gwont wacce mr Aliyu yasiya mata”

wayarta da babu caji ta d’auka tana kallon mama tace”.zanje gidansu fatima nasaka caji(k’awarta dake mak’wabtaka)

Dakin kai kidawo gida yasmeen”dato ta amsa tayane kanta da mayafin ta fice”

Tana k’okarin fitowa dg k’ofar gidansu”saiga sanusi (d’an baffa d’ahiru)

da sauri yasmeen ta Ida fitowa”yana binta da wani mayen kallo yana lashe lips d’in sa”

Ina wuni?”

yace”.Hmmm!bbu shakka yasmeen”da gske ashe a maganar d’ahara ko?”gashi kin canza,jikinki yyi kyau kuwai luwai alamar ana hawanki”

Kina aiki a MAI NASSARA INTERPRISES ko?kina samun kud’i “kuma shi d’an iskan CEO d’in yana nemanki ko?”amma ni kin nuna bakya sona”to wlh ta k’arfin tsiya zanje dake nima na huta dake…

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un!!yasmeen tafad’a cikin b’acin rai”haba yaya sanusi “wace irin banzar mgn ce kakeyi haka?

niba y’ar iska bace”dakai da wanda yasanar maka duk nabarku da Allah”kuma insha Allah bazan tab’a auren marar tarbiyya irinkaba…tana fad’in hakan ta juya da nufin ta wuce”

Sanusi yyi saurin finciko hannunta ya d’auke ta da wani gigitaccen marin da stars suka mata shawagi a cikin ido…..hakan yafaru akan idon mr Aliyu da suke abayansu suna k’okarin yin parking”tun kafin mani driver yagama parking mr Aliyu yaturo k’ofar da k’arfi yafito cikin fushi”yanufi gurinsu gadan gadan yana huci……โœ๏ธ

Comments kawai guys ko wane team afito akafta ko k’unsamu update๐Ÿคช

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAU DA GOBE 37&38

Advertisement  ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ   ๐ŸŒนYAU DA GOBE ๐ŸŒน ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ Story & writing by mmn farees ๐Ÿ…ฟ๏ธ37&38 ,,,,,, Agajiye yadawo…