TAYI MIN KANKANTA 12

Advertisement

 

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 *TAYI MIN ƘANƘANTA*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*Zahra Surbajo*

*12*

Advertisements

A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito ya taka zuwa office Ι—in aminin nasa.

Da sallamarsa ya shiga office Ι—in cike da fara’a ya taso suka rungume juna,suna Ι—an dukan juna a baya,sannan suka koma kan doguwar kujera suka zauna.

Muhammad ne ya fara magana cikin yanayin damuwa”Abokina ina cikin damuwa fa,?”

“wacce irin damuwace wannan,?”abokin nasa ya buΖ™ata cike da kulawa.

Advertisements

“jibi daddy ze Ι—auramin aure da wata Ζ΄ar Ζ™anwarsa,na rasa inda zan tsoma raina”.

A razane ya miΖ™e tsaye yana ja da baya,take duk wani annurin fuskarsa ya kauce kamar wanda yacewa gobe ze mutu.

Cikin kakkausar murya yace”HAMMAD kana nufin alΖ™awarin auren Ζ΄arfillo daka lalatawa rayuwa yatashi a banza kenan?”

MiΖ™ewa muhamnad yayi ya Ζ™araso kusa da abokin nasa ya dafa kafaΙ—arsa yace”JAMEEL kafi kowa sanin irin son da nakewa Ζ΄arfillo,wallahi babu macen dana keso a zuciyata sama da ita,kullum jameel bana iya bacci sabida ita,wallahi akan Ζ΄arfillo zan iya Ι“ata ran kowa,sede itama wannan dazan auran akwai abun tausayi game da itan,kwatankwacin kaddarar data faΙ—awa Ζ΄arfillo itama hakanne,wallahi zan auri yarinyar ne,kodan jihadin da zanyi na auranta Allah ya kawomin Ζ΄arfillo na cikin sauΖ™i,pls jameel in baka fahimceni ba bame fahimtata”muhammad yayi maganar kamar zeyi kuka.

Waigowa jameel yayi,ya dubi hammad yace “b haka bane hammad ay kai mijin mace huΙ—une,bana de so ne sanadin auran da zakayi ka mance da Ζ΄arfillo shine yasa”

“har abada bazan mance da ita ba jameel,kuma zanci gaba da nemanta har se inda Ζ™arfina ya Ζ™are”Muhammad yafaΙ—i cike da tabbatarwa.

Jameel kwantar masa da hankali yaci gaba dayi akan auransa da zahra,inda yace ya daure yayiwa daddy biyayya hakanne zesa in ya kawo Ζ΄arfillo ya amince ya aureta.

Sosai Muhammad ya gamsu da shawarar aminin nasa,duka yakaiwa jameel yace yana dariya”wato jameel,da ace yadda kanka ke kawo wuta haka zuciyar ka take da nigeria batayi asarar soja ba,amma wai daga harbi Ι—aya a baya,sega resigning letter wallahi ka bada maza,ay gashi nan ka Ζ™are a kallewa mata al’aura,da wuri zaka makance”ya Ζ™arasa maganar yana dariya.

Duka jameel yakai masa yace”ay duk namijin da baya gudu baya tsawon rai,da asara gara gidadanci,taya na hango lahirar nasha da Ζ™yar zan bari a Ζ™arasa ni,kaima kaga zaka iya ne shiyasa baka fita ba”

“bazan taΙ“a barin aykin soja ba Jameel sede in ze shiga tsakanina da Ζ΄arfillo to tabbas zan fita”.

Haka de sukai tayiwa juna barkwanci,basu rabu ba se dare,agajiye muhamnad ya dawo gida,zuciyarshi fal farinciki kamar yaga Ζ΄arfillonsa.

To bari mu waiwaya bayaπŸ˜„

Kowa ta turo data se in ci gaba😎

Surbajo for life.

Leave your vote

-6 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

TAYI MIN KANKANTA 29

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *To sabon sauyi acikin tafiya,😊akwai sabon novels Ι—ina dazan…

RAYIMIN KANKANTA 23

Advertisement πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* Advertisements *23* Likitocine suka rufu akanta dan gano meke damunta,…

TAYI MIN KANKANTA 8

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *8* Advertisements A harabar gidan yayi parking,tun kan ya…

TAYI MIN KANKANTA 4

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *Hindatou Auwal,wannan shafi sadaukarwane agareki,bisa dogon nazari da kikeyi kamin…

TAYI MIN KANKANTA 19

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *19* Advertisements Cikin tsananin firgita jameel ya juyo yana kallon…

TAYI MIN KANKANTA 20

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *nace muku bana adding mutane a group,kuma bana tura novel…