TAYI MIN KANKANTA 13

Advertisement

 

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

  *AURE DA HAIHUWA*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*Zahra Surbajo*

Advertisements

*Page 13*

Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana hango ta nufo shi yataso da sauri yadan risina yace “barka da safiya hajiya,me kike da bukata?”amsawa tayi cikin sakin fuska tace”baba don Allah cefane nakeso kayomin,a wuse market,”

“To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki”

Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .

Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya ta dawo falo zaman jiran akawo mata cefanen.

Advertisements

Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai masa godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.

Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata tazo ta hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.

Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.

Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin Rayhan, shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai  toilet acikin dakin Nata, 

A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar doctor Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su hallara agabansa.

Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida adadi.Neman Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata shiga,wannan shine yakara daga hankalinta.

Ranar shiga kotun da safe Rayhan yaje kofar dakin na safna yace cikin dakewar murya.

“Ki bude kofa ki fito mu tafi kotu Dan yau alkali yabada mu hallara agabanshi ina jiranki a mota”yana kaiwa nan yayi fucewarsa abunsa

Safna jin maganar tayi kamar saukar Aradu,yau itace Rayhan yakai kara kotu?wannan wacce irin masiface.

Tunda ya fada tasan dagaske yakeyi,Dan karya bata daya daga cikin halayensa.

Jiki asanyaye ta janyo hijab tasaka,ta zura takalmi ta fito.bayan ta kulle dakinta.

A motar ta sameshi yana cika yana batsewa,ba me cewa shine Rayhan din ta me yawan murmushi.

A harabar kotun suka samu doctor Amina ma ta iso ita da maaikatan da suka gudanar da aykin.

Karasawa gunta Safna tayi suka gaisa,inda doctor Amina tace”Safna kinga kaddara ko?”

Hawaye ne suka gangaro daga idon Safna masu zafi sannan tace”doctor ina cikin tashin hankali”

Karasowar Rayhan gurin ne ya katse musu hirar,inda ya dakawa Safna tsawa da cewa “wuce mutafi”.ba musu tabishi abaya suka shiga cikin kotun.

Bayan kowa ya hallara ne me gabatar da kara yatashi ya gabatar da karar da Rayhan Hashim ya shigar agabanta,yana me kalubalantar doctor Amina,da sauya kwayoyin halittarsa Dana wani ta sawa matarsa,Wanda hakan ya janyo matarsa ta dauki ciki,yana me rokon kotu datasa matarsa ta zubar da cikin,kuma yanaso kotu me adalci da ta bi masa hakkinsa.

Bayan an gabatar da kara ne alkali ya bukaci ganin doctor Amina,jiki asanyaye ta karasa inda aka tanada domun tsayuwar Wanda ake tuhuma taje ta tsaya.

“Munaso ki gabatar mana da kanki”cewar alkali,

“Sunana Amina Galadima,likita,kuma mamallakiyar Asibitin Galadima special hospital”

“Kinji korafin da aka shigar akanki shin haka akayi koko kina da ja game da hakan?”alkali yasake jefo mata tambayar.

“Duk abinda aka fadi ranka ya Dade haka ne,sede ba nice da kaina na gudanar da aykinba, kuma kuskuren suna aka samu ta hanyar kamanceceniyar suna,ina me rokon kotu datai mana sassauci”.ta kwashe komai ta sanar da kotu gamida mika takaddu na bincike da kuma duk wani Abu daya shafi dashen tun kan ayi har zuwa bayan anyi,

Alkali ya bukaci maaikatan da suka gudanar da aykin dasu gabato gabansa,suma suka amsa sune suka yi,

Bayan dogon rubutu alkali yafara magana,”Bayan nazari da bincike,wainda ake tuhuma basu wahalar da sharia ba kotu ta gamsu da duk bayanan kowanne bangare,kuskurene babba suka aykata,Wanda dole ay musu hukunci,Na farko,kotu ta yankewa doctor Amina hukuncin biyan Tara ta dubu Dari,bisa laifin daukar maaikatan da suke sakaci da aykinsu,su kuma wainda suka aykata laifin,kotu na umartar da akaisu gidan gyaran hali na tsawon wata guda,ko zabin Tara,ta dubu goma goma”kotunce ta hargitse da surutu,kamin alkali ya tsawatar akai shuru, sannan yaci gaba

“Kotu na kira ga Rayhan da yayi hakuri bisa faruwar wannan Lamari,sabida kotu bazata sa Safna ta zubar da cikiba, Wanda aykata hakan zunubine,kuma shi wannan Abu daya faru,shima kuskuren ne babba, duba da tabbaci da aka samu daga bakunan maaikatan na cewa cikin an sameshi bada kwayoyin halittarka ba,kuma kamin ayi an tabbatar da bata da ciki,bayan anyi kuma baka kusanceta ba seda aka tabbatar da ta samu cikin,hakan ya tabbatar da cewa cikin jikinta ba naka bane,Dan haka kotu ta sallami wannan karar”

Gaba daya kotun ta kaure da hayaniya,Safna kuka take kamar ranta ze fita, wannan kaddara dame tai kama.

Haka ta mike tabi bayan Rayhan din daya fita afusace,

Sede kamin ta karaso tuni yaja motar sa yabar harabar gurin,Dan shi Sam ba haka yaso ba,so yayi asa safna ta zubar da cikin, sannan adaure doctor Amina, amma gaba daya ba hakan akayiba,

Hakanne yasa shi tunanin anya ma kuwa alkalin yasan aykinshi?

Muje zuwa

Surbajo for life.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

TAYI MIN KANKANTA 7

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *7* Advertisements *Bayan shekara Ι—aya* “Modibbo Ι—iyata zata mutu…

TAYI MIN KANKANTA 12

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *12* Advertisements A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito…

TAYI MIN KANKANTA 2

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *2* Advertisements  Gudu-gudu sauri-sauri Zahra’u ke tafiya zuwa gida,dan…

TAYI MIN KANKANTA 38

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *SHIMFIƊAR AURENA,na fara posting free page,wanda zanyi daga Ι—aya zuwa…

TAYI MIN KANKANTA 5

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *5* Ƙara shigewa jikinshi take,sabida sanyin da takeji,a hankali ya…