Advertisement
ππππππππ
*TAYI MIN ΖANΖANTA*
ππππππππ
*Zahra Surbajo*
*Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu lafiya,Allah kazaunar da kowa agidan auranta lafiya,Ameen*
Advertisements
*15*
Da asuba,da kanshi ya tasheta yabata jallabiyarsa tasa tayi rolling da rawaninsa tayi sallah,sannan ta koma bacci bayan ta cire masa rigar tasa,
Bata farka ba se tara na safe,tuni hammad yayi wankansa ya kimtsa,jin motsin da yayine yasa yazo ya sameta a zaune ta farka,rigarta take ΖoΖarin sawa amma zafin da gun Ζ΄unar jiya ke mata yasa ta kasa sawa sabida rigar bata kai jallabiyar daya bata faΙi ba.
Da sauri ya Ζaraso gurinta,Ιago ido tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kai,
Zama yayi kusa da ita har jikinsu na gogar juna,waigowa tayi asanyaye ta kalleshi shima ita yake kallo,hannu yasa ya zagayota dashi ya kamo rigar yasa mata,sunkuyar da kai tayi ta runtse ido sabida zafin da taji,a hankali yace”sorry,”gyaΙa kai tayi sannan ta miΖe,ta fice daga Ιakin,yabi bayanta da kallo,yana haΙiye wani miyau.
Advertisements
Se da ta fice ne kuma kunyar ta faΙo mata,to tacewa mummy agurin wa ta kwana,kasa Ζarasawa cikin falon tayi ta tsaya tana wasi-wasi.
Hammad ne ya fito zashi gaida iyayen nasa,anan yaci karo da ita tsaye tana tunani,Ζarasowa yayi inda take,yace”ke lafiyarki Ζalau kuwa,tsayuwar me kikeyi anan?”
A raunane ta Ιago idonta ta dibeshi tana hawaye tace”kunya nakeji suji na kwana agurinka”
Murmushi yayi sannan yace “sabida kin kwana da kwarto ko?”
Da sauri ta girgiza kanta tana faΙin “Allah ya tsaremin miji da zama kwarto,ni mijina ba kwarto bane,aniyarka ta bika”sam ita ta mance ma matsayinsa agunta take wannan batun.
Be kulata ba hannu yasa yaja hannunta suka nufi falon,itako tirjewa take tana kuka tana “wallahi bazaa ganmu atare ba,nide kasakeni ka tafi kai kaΙai”a haka suka shigo falon,inda mutanen gidan ke zaune a dinning suna karyawa,Ιurarin da zahra kewa Hammad Ιinne ya dawo da hankalinsu kansu,
Shiko Hammad be saketa ba seda suka shigo falon,ay tana ganinta gaban su mummy,da sauri ta Ιoye abayanshi,duk yadda Hammad ya kauce itama da gudu zata koma gurin,sosai abun yaba su daddy dariya,a hankali daddy yace “rakata Ιaki mana muhammad,ka tsaida ita anan”
Murmushi yayi sannan yaja hannunta zuwa Ιakin nasu se Ιoyewa take agefensa.
Seda ya kaita sannan ya dawo gun mahaifan nasa,tsugunawa yayi ya gaishesu sannan yaja kujera ya zauna,
“Angama shirya komai na gidan da zaku zauna,anjima mummynka zasu kaita gidan,ka kwantar da hankalinka”daddy ya faΙi yana murmushi.
Sosai kunya ta kama Hammad,ya sosa Ζeya yana murmushi yace”daddy ay ko anan Ιinma zamu iya zama”
“kuci gaba da mana rashin kunya a cikin gida ko?”daddy ya buΖata.
Shuru Muhammad yayi dan se yanzu yagano ma manufar daddyn.
Haka yayi break fast duk a tsarge,yana gamawa ya miΖe ya bar falon.
Shiryawa yayi ya fice zuwa gun amininsa Jameel,kasancewar yana hutu be koma bakin aykiba.
Surayya ce tasamu zahra a Ιaki tayi wanka ta kimtsa cikin wata atamfa ja da milk me golden tayi kyau matuΖa.
Tana shiga ta fara mata tsiya,”kaga amaryar yaya,me bin angonta Ιaki”duka zahra takai mata tana faΙin”zanko haΙaki dashi,bari muhaΙu”
“ayya yarinya kwantar da hankalinki yau zaa kaiki gidanshi seku dena satar hanya”ta Ζarasa maganar tana tuntsira dariya,
Zahra de ba baka se kunne,seda su mummy sika bar falon sannan taje tayi breakfast Ιinta.
Da magriba su mummy da Ζawayenta guda biyu suka kai zahra gidan auranta daya gaji da haΙuwa,se kuka take wurjanjan ita bazata zauna ba,
Surayya aka baro agurinta azuwan in Hammad yazo yasa direba yakawota gida.
Hammad ko suna can shida jameel yana Ζara kwantar mai da hankali,akan auran nasa da zahra,tare da bashi tabbacin insha Allahu zasi ga Ζ΄arfillonsa,
Sai da ishai daddy ya kirashi awaya ya shaida masa tun Ιazu ankai masa matarsa gida.
Jameel ne yasa shi yayi wanka ya kimtsa awata sabuwar shadda ta jameel Ιin,sannan,suka fito domin yamasa rakiya,kaji da madara suka siya sannan suka Ζaraso gidan.
Jameel besan me yasa ba amma lokaci zuwa lokaci gabansa na yawan faΙuwa,a haka suka Ζaraso gidan.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings