Advertisement
πππππππ
*TAYI MIN ΖANΖANTA*
ππππππππ
*Zahra surbajo*
*banida lafiya ne,kuma ga mara lafiyan danake kulawa da ita,shiyasa abubuwan suka chushemin,pls asamu a addua,Allah ya bamu lafiya*
Advertisements
*16*
A harabar gidan sukayi parking a gurin da aka tanada domin hakan.
Fitowa sukayi fuskokinsu ba yabo ba fallasa,suka nufi cikin gidan.
Sallama Hammad yayi afalon amma baa ansa ba,hakanne yasa ya fahimci tana Ιaki.
Advertisements
“zauna mana ka tsaya kamar baΖo,bari inje in kirata ku gaisa”Hammad yace yana ΖoΖarin haurawa benen.
Zama jameel yayi a sanyaye shi ya rasa meke damunsa da yasa yanayinsa ya sauya.
A gefen gado ya sameta zaune,ta lulluΙe fuskarta da jikinta da mayafi,ko baa faΙi ba kuka takeyi.
Sallamarsa ce tasa ta Ιago dara daran idanuwanta ta dubeshi suna tsiyayar da hawaye,
Tausayinta ne ya kama Hammad,a hankali ya Ζarasa kusa da ita ya zauna,ya sa hannu ya dafo kafaΙarta yace a sanyaye.
“kince kina sona ke ba auran dole aka miki ba,to kuma se gashi se kuka kike kamar wacce aka yanka,ko kin dena son nawa ne?”
murmushi tayi sannan ta girgiza masa kai,
“to tunda ba haka bane share hawayenki kizo muje falo gun babban aminina ku gaisa tare muke dashi”
Share hawayen tayi sannan ta miΖe shi kuma yayi gaba,da sauri ta Ζarasa jikinshi ta ruΖo hannunsa ta kwantar da kanta a gefenshi.
Hammad bece komai ba ya buΙe Ιakin sika nufi falon.a hankali.
Jameel tunda suka jero sosai suka burgeshi,yaji dama ace da Ζ΄arfillo yaga aminin nasa dase yafi jin daΙi.
Kujerar dake kallon ta jameel Ιin suka zauna fuskarta a rufe da mayafi.
“A gaskiya ba abinda zamu cewa Allah sede godiya,daya kawomu lokacin da aminina ya fita akasuwa”cewar jameel yana murmushi.
Dariya Hammad yayi sannan yace”zakuma mu Ζara godewa Allah in ya nuna mana ranar da kaima zaka bar kasuwar”gaba Ιaya suka tuntsure da dariya.
Ita de zahra ba dan kar ta gasgata kunnenta ba da se tace tasan muryar nan da jimawa,amma seta kauda tunanin hakan.
Sosai jameel yay musu faΙa da tunasarwa kan suji tsoron Allah inda aΖarshe yace”kuma shi aure ibada ne kowacce ibada abar tambaya ce agurin Allah kaji tsoronsa,kar son da kakewa waccan yarinyar yasa ka cutar da wannan,wallahi Allah baze barka ba”.
A sanyaye Hammad yace”insha Allahu son waccan baze cutar da wannan da komai ba,zan kula”
MiΖewa jameel yayi yana duba agogo,yace yana kallon zahra data rufe fuska da mayafi”Amarya me rowar fuska,gashi har zan tafi banga kamannin amaryar ba”
Da sauri hammad ya kamo mayafin nata yana dariya yace”tuba muke ina zaa yima rowar fuska ay dole ka ganta,”ya Ζarasa buΙe masa mayafin data rufe fuskar.
runtse idonta tayi tana dariya,wanda ya bayyana wushiryarta da lotsawar kumatunta,fess ya ganeta dan duk tsayin zamani da sauyin yanayi,jameel baze kasa tino kamannin Ζ΄arfillo ba.
Sosai gabanshi ya faΙi tsoro ya mamaye zuciyarshi,tambayoyi fall cikinsa,amma a bayyane cewa yayi “masha Allah,daddy gaskiya ya gwangwajeka,to Allah bada zaman lfy bari in Ζarasa gida”yana faΙin haka be jira amsarshi ba yayi sauri ya bar gurin gudun kar ta buΙe idon ta ganshi.
Rakoshi Hammad yayi yaga tafiyarsa sannan yakoma cikin gidan,zuciyarshi cike da damuwa ganin abokin nasa duk abirkice yayin barinsa gidan nasu.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings