Advertisement
ππππππππ *TAYI MIN ΖANΖANTA*
ππππππππ
*Zahra Surbajo*
*19*
Advertisements
Cikin tsananin firgita jameel ya juyo yana kallon Hammad,kamin yayi wani abu hammad ya cakumoshi ya bugasa da jikin bango,ya fara kai masa duka yana fadin.
“macuci azzalumi,Allah ya toni asirinka,dama kaine ka haike mata,shine yanzu kazagayo zaka Ιora,kabani mamaki”yaci gaba da kai masa duka.
Tsananin mamaki ne yasa jameel kasa furta komai,yakuma kasa kwace kansa a hannun hammad Ιin.
Zahra cikin zafin nama tayi kanshi tana faΙin”yaya me yayi maka ka Ζyaleshi,ina ruwanka dashi,”tana jan rigar hammad Ιin.
Advertisements
A fusace ya juyo kamar mayunwacin zaki ya kife ta da wani wawan mari,take yanke tasaki fitsari,sakamakom taurarin da ta gani na gilmawa a idonta.
“munafuka,ke har kina da bakin magana,shiyasa kika Ζi faΙin wanda ya maidake garejin ashe wannan munafukinne,to wlh ba agidana zakuyi bariki ba sede awani gidan”
Jameel tunda hammad ya koma kan zahra ya zame jikinshi ya fice agidan ko ganin gabanshi bayayi sabida tsananin Ιacin rai.
Hammad rasa abunyi yayi kawai shigewa cikin gidan yayi ya barta kwance agurin tana kuka.
A falo ya zauna yana huci kamar zaki.
Jiki asanyaye zahra ta miΖe ta nufi cikin falon,yana ganinta ya Ιauke kai.
DurΖusawa tayi agabanshi tana kuka,cikin kukan tace”jameel ba fasiΖi bane yaya,hasalima hannuna be taΙa riΖewa ba se yau,shima nice nayi kuskuren rungumeshi,nasan shine agarinmu falgore,inda ya nemi taimakon girko abinci sabida wani abokinsa dake fama da cutar ulcer,na rabu da jameel ne ranar da Ζ΄an taadda suka zo garinmi suka kashemin innata,inda na haΙu da abokin jameel Ιin sojan me ulcer daya keta mutuncina ana ruwan sama acikim wata bukka dana shiga domin ceto rayuwata,har baΖin mugun yace min jameel Ιin ya mutu,Allah ya isa tsakanina da kai soja me ulcer bazan taΙa yafe maka ba mugu azzalumi,baΖin kare wanda baze shiga aljannah ba”ta Ζarasa maganar cikin matsanancin kuka.
Hammad wanda yayi tsit kamar ruwa yacishi,jin abinda zahra ke faΙi,wasu hawayene masu zafi suka zubo afuskarsa,zuciyarshi ce tai masa nauyi,da Ζyar yace.
“kina nufin kece Ζ΄arfillo?”
“Nice yaya,hala ya baka labari na”
Wata ajiyar zuciya yaja sannan ya yanke jiki ya faΙi agurin ba numfashi,wani farin kumfa na fitowa abakinsa kamar yasha guba.
A gigice zahra tayi kanshi tana kiran sunansa tana girgizashi amma ina ko motsi baya yi.
Da gudu tayi gurin me gadi,ta kirashi koda yazo yaga halin dayake ciki,wayarshi ya ciro ya kira daddy kasancewar yana da numbarshi,baa jima ba,daddy ya iso da tawagarsa hankali atashe aka Ιauki hammad zuwa asibiti rai a hannun Allah zahra se kuka takeyi kamar ranta ze fita,dan gani take hammad dinta ya mutu.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings