Advertisement
ππππππππ
*TAYI MIN ΖANΖANTA*
ππππππππ
*Zahra Surbajo*
*nace muku bana adding mutane a group,kuma bana tura novel pc,amma kunki fahimta,kuma in ba’a baku amsa ba kuji haushi,nace muku banayin Ιaya daga cikin wa’innan,groups Ιina akwai admins da yawa,sannan wasu groups Ιin akwai link yana zagayawa,zaku iya bin ta hannun su ku shiga,nagode*
Advertisements
*20*
Wasa-wasa tsawon sati guda kenan,likitoci na tsaye kan hammad amma ko alamun farkowa bashi da ita,
Hankalin iyayensa dana zahra yayi matuΖar tashi,ko kaΙan basu cikim natsuwa.
Duk yadda mummy tayi da zahra kam ta koma gida Ζi tayi,ko wanka bata zuwa gidan tayo sede tayi a asibitin akawo mata kaya ta sauya.
Koda su daddy suka tambayeta me ya haddasa masa ciwon,ce musu tayi faΙa sukayi da abokinsa jameel,sosai su daddy sukayi mamakin afkuwar hakan a tsakaninsu,
Advertisements
Daddy jameel ya nema a waya,dan jin abinda ya haΙasu,cikin girmamawa jameel yace”daddy wannan saΙanine yashigo da rashin fahimta,da taimakon shaiΙan,kar ku sa kanku aciki mu mukayi faΙanmu kuma da kanmu zamu shirya”ya faΙi cikin girmamawa.
“to amma jameel ga fa shi abokin naka a asibiti rai a hannun Allah,tun ranar da kukayi faΙan yake a sume a asibiti,baka ganin akwai buΖatar mu shigo ciki dan Ιinke Ιatakar da ta shigo tsakaninku?”
“Daddy bansan bashi da lafiya ba,amma zanzo in dubashi bana garine nima tun ranar ina lagos,”jameel ya faΙi cike da tausayawa abokin nasa,tabbas yasan hammad farin sani,masoyinshi ne na haΖiΖa,dole ze shiga wani hali aduk ranar daya gano gaskiya,duk yadda yaso yayi fushi da hammad Ιin baze iya ba.sabida shima yana matuΖar Ζaunarsa,kuma ko shine hakan ta faru abinda zeyi kenan.
A cikin sati na biyu ne hammad ya farka gaba Ιaya ya rame yayi baΖi ya fice hayyacinshi.yazama abun tausayi.
A hankali ya kai dubansa gefen da zahra take tsaye tana share hawaye,a hankali ya miΖa mata hannu alamun tazo gunshi,ba musu ta taka a hankali ta isa gareshi.
Janyota yayi batare daya ji kunyar su mummy ba ya haΙeta da Ζirjinshi ya rungumeta yana hawaye.
Su mummy ficewa sukayi daga Ιakin,sabida ya basu kunya.Ιago kanta tayi a Ζirjinshi tana share masa hawayen tace cikin shagwaΙa”yaya kayi haΖuri karkayi fushi damu,don Allah ka samu lafiya banason ganinka baka da lfy”ta Ζarasa maganar cikin kuka.
Ζara rungumeta yayi ajikinshi yana ci gaba da zubar da hawayen,ya kasa magana.tsawo mintuna talatin ya kwashe rungume da ita,turo Ζofar da akayine da sallama yasa yakai dubansa gun me shigowar,
jameel ne.
Wata matsananciyar kunya ce ta kama hammad,maida kansa yayi ya kwanta,sannan ya lumshe idonsa ya juya baya.
Sosai jameel ya karanci aminin nasa,yasan kunyarshi ce tasa yayi hakan dan haka ajiye kayan hannunsa yayi sannan ya Ζarasa gunshi.
Cakumo rigarsa yayi yace”Ιan iska mara mutunci,har da wani dukana rannan,to wlh baka daki banza ba zuwa nayi in rama”yana kaiwa nan shima ya shiga kirΙarsa,ta yadda yasan baze cutar dashi ba.
A galabaice Hammad ya buΙe idonsa,ya haΙa hannayensa gida biyu hawaye na bin idonsa,alamun tuba ga jameel Ιin.
Shima jameel Ιin hawaye yakeyi,da zafin nama ya janyo hammad Ιin jikinshi ya rungumeshi,shima rungumeshi yayi dukansu hawaye sukeyi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings