TAYI MIN KANKANTA 21

Advertisement

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *TAYI MIN ƘANƘANTA*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*Zahra Surbajo*

*21*

Advertisements

Tsawon kwanaki biyu da farkawar hammad aka sallameshi sabida jikin nashi yayi sauΖ™i.

Sede zahra ita bata jin daΙ—in yanayin yayan nata,sabida gaba Ι—aya kunyarta yakeji baya son su haΙ—a ido.

Jameel ne ya Ι—aukosu a asibitin ya kawo su gida sannan yatafi da zummar gobe ze dawo.

Suna shiga cikin falon zahra taja hannunshi zuwa Ι—akinshi,sede ita abun da bata gane ba koya suka haΙ—a ido kuka yake ta rasa gane kan lamarin.

Ɗakinshi ta kaishi,sannan ta juya ta koma nata Ι—akin domin tayi wanka.

Advertisements

Bayan duk sunyi wanka sun kimtsa ne taje Ι—akinshi tasameshi zaune ya rafka uban tagumi,zame hannayensa tayi sannan ta zauna akan Ζ™afafunsa,hannayenta tasa ta sakalo  wuyansa tace cikin shagwaΙ“a”yayana wai kode bakaji sauΖ™in bane?”

Kallonta yayi da hawaye cike da idanunsa yace”Naji sauΖ™i mana”

“to me yasa kake kuka?”tasake masa tambaya.

“tausayin kaina nake shiyasa”

‘to ka kwantar da hankalinka ay ina tare da kai yayana”

“kin min alΖ™awarin duk sauyin yanayi bazaki gujeni ba?”ya tambayeta cikin marairaicewa.

Dariya tayi ta faΙ—a jikinshi tace”yayana kenan to ni da na aureka dan ina sonka to ina zani,ay muna tare har abada”.

Sosai ya tattaro natsuwarshi yace,”to shi soja me ulcer meyasa bazaki yafe masa ba?”

ay kamar wacce ya mintsina,zimbur ta miΖ™e daga kan cinyar tashi,hawaye na bin idonta,tace”ay wannan baΖ™in karen har abada ba yafiya tsakanina dashi,ni yaya don Allah kar ka sake min maganarshi”ta Ζ™arasa maganar cikin kuka.

Janyo ta yayi jiki ba Ζ™wari ta faΙ—a jikinshi sannan ta saki kuka me sauti gwanin ban tausayi.

rarrashinta ya shiga yi yana Ι—an bubbuga bayanta gamida hura mata iska a kunne.

Sannu a hankali tayi shuru ta dena kukan,suna nan zaune aka kawo musu abinci daga gurin mummy.

Zubo musu zahra tayi suka ci suka Ζ™oshi,sannan kowa ya nufi Ι—akinshi domin gudanar da ibada.

Hammad zafin da zuciyarshi ke masa yafi gaban tunani,ya rasa ta ina ze Ι“ullowa zahra ya shaida mata shine wanda yay mata fyaΙ—e,tsoron ta tsaneshi yakeji,shiyasa damuwar tai masa yawa.

Haka suka kwana kowa a Ι—akinshi,hammad yadda yaga rana haka yaga dare ba tare da ya runtsa ba.

Gari na waye ba,yayi wanka ya kimtsa sannan ya fice a gidan batare da ya mata sallama ba ya nufi gurin jameel dan yazo ya warware masa damuwarsa.

Muje zuwa

Surbajo for life.

Leave your vote

-3 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

TAYI MIN KANKANTA 7

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *7* Advertisements *Bayan shekara Ι—aya* “Modibbo Ι—iyata zata mutu…

TAYI MIN KANKANTA 38

Advertisement  πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *SHIMFIƊAR AURENA,na fara posting free page,wanda zanyi daga Ι—aya zuwa…

TAYI MIN KANKANTA 15

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu…

TAYI MIN KANKANTA 35

Advertisement   πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *TAYI MIN ƘANƘANTA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *Zahra Surbajo* *TAYI MIN ƘANƘANTA bana kuΙ—i bane,SHIMFIƊAR AURENA shine na…