WATA TAFIYAR 14

Advertisement

 🦚WATA TAFIYAR🦚

       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟

*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

Advertisements

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“🌍`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAID BOOK

                      

               14

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Advertisements

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

WANNA LITTAFIN NA KUƊI NE,IN KINSAN BAKI BIYA BA DAN ALLAH KAR KI KARANTA, KUMA KAR KI YI SHARIN PLEASE.

Wani sanyayyan ajiyar zuciya ta sauke, sakamakon ruwan sanyin da Talatu ta sheka mata,tun bata fahimtar waye a kanta ba har idon ta ya kammala buɗewa a kan Talatu dake tsaye a kanta ta na jifan ta da irin kallon zan iya cin naman ki ɗanye idan aka barni,ba tare da ta shirya ba ta ƙara jin saukan mari a fuska ta”tashi munafuka,wato har kin samu rahamar da har zaki Suma ko,to bari kiji ko suman ban baki damar yi ba”ta ƙarasa faɗa tana kwance mata hannu, 

Kuka kawai take yi wanda ko fitan kirki muryan ta ba yayi,gashi kwance hannun ma cikin mugunta ake mata,zafi take yi sosai saboda hannun a kumbure yake ɗan jinin ta ya koma ƙasa,dan ko da ta kwance hannun kasa ɗaga shi ta yi, saboda nauyin da ya mata,ga ƙafa ya kumbura ya rike mata,wanda ta ci tuntuɓe da shi,ko lura bata yi ba,dan tuni ma Kumban wurin ya ɗaga.

Kwanun data zuba mata abinci ta daura mata saman cinyan ta”oya ci abinci,dan ki na da sauran anfani,dan kina saka mana hannun a takardu,shi kenan aikin ki ya ƙare,sai mu turaki can kafin wannan mijin naki ya biyo bayan ki”

Cikin shakakkiyar muryan ta tace”Mama dan Allah ki fitar da ni a nan!! 

“Saboda me”

“Dan Allah ina jin tsoro,kuma kin ga wannan mutumin yana iya kashe ni,ko dazu da safe kan ki zo,kallo na yake da idanun shi masu wani kala,”

“Ohh ashe fa na manta ban muku introducing ɗin kanku ba,to Albishirinki,kin ga wannan” Ta nuna mutumin dake kwance,tana ƙyalƙyalewa da dariya”to shi ne mijinki,wanda kike tambaya,Mama wai ina mijina ne?to yanzun ga mijin naki kwance a gaban ki,sannan dan tsabar munafurci sai kuma ki ce kina jin tsoron shi, ai kuwa baki isa ba,kin ga gama cin abincin ci sai in gabatar da ku ma juna dan kowa yasan dan uwan shi, kin ga koda kun sheka lahira ba sai kun wahala wurin gane juna ba”

Kuka ne ya kwace mata”to ni me nawa a ciki!!me laifi na!! 

Cikin daga wannan katon muryar nata tace “kasancewar ki mahaukaciya wacce ba ta da wayau,kuma mata a gare shi,iyayenta talakawa masu son abin duniya,kin ga koda mun kashe ki,zamu iya cewa haukanki ne ya tashi kika fado daga gidan sama kika mutu,kin ga ba wani binciken da za a yi sai dai ace ƙaddara ne,kin ga shi kenan an wuce wurin”

“Me yasa zaku kashe shi sannan ku kashe ni? 

” Saboda kin ga tsirrin mu sannan mata a gareshi,shi kuma saboda dukiyar shi da kuma wani dalili,wanda be kamata ya kasance a raye ba,dan mugun wayau ne dashi,dan a tarin Dalolin daya tara duk ya saka hannu akan na matar da zai aura ne,sai sa hannun shi,dan dole  sai da saka hannun ki sai na shi,sannan ne zamu iya mai da komai namu”

“Yanxun duk saboda dukiya ake wannan,sannan zaku iya kisa, to shi baku tsaron ƴan uwan shi? 

Dariya ta sheke da shi,tana dima mata tafi a cinya, wanda sai da ta yi ƙara” Kin cika tambaya, kin san me yasa nake baki amsa? 

Da sauri ta gargiza kai,tana matse idon ta yayin da hawayen ciki ya zubo saman kumatun ta. 

“Saboda nasan ba zaki bar nan a raye ba,kin ga wannan mijin naki mai kama da gawa?ke tukunna kin ma San waye shi kuwa?kinsan irin Dalolin daya tara a rayuwar shi,ga kuma wanda aka tafi aka bar masu,ko da yake ba zaki gane komai ba, to asalin ma wanda ke son ya ga bayan shi,ya kashe shi shine YAYAN SHI WANDA SUKE UWA ƊAYA UBA ƊAYA,duk yafi kowa zakewa,sai Kawunnan su,”

Mutuwar zaune ta yi,dan ita ko a littattafan Hausa, da fina-finai Hausa bata taɓa jin in da yaya uwa daya uba daya, yaso ganin bayan kanin shi ba,sai dai ko ƴan uba ne. 

“Anya kuwa iyayen su daya kuwa?ko dai a kwai wani zunubi ne daya aikata ma shi”

“Kwarai kuwa iyayen su ɗaya,dan babu tantama akan haka, kuma shi mijin naki yana iya sadaukar da komai na shi domin ɗan uwan shi, sai da fa a kwai abin da be kamata ya ji bane,,shi ne aka samu akasi ya ji, da kuma wanda bai kamata ya gani ba,shi yasa”

“Mama ina iyayen su,sannan akwai wata rigima ne a tsakanin su dama”

Tabe baki ta yi “wama yasan me ya faru da ZAMIR family,ohho,su karan kansu ba su san inda iyayensu suke ba,kuma ba wani gaba a tsakanin su face soyayya,,ke a taice shi mijin naki shi kaɗai ya san sirrin komai, kuma shi ne mabuɗin komai,domin shi ne kaɗai yasan hanyar da za a bi a yi WATA TAFIYAR domin bankado abin ake ɓoye,kin ga ke nan ba yanda za ayi a yi WATA TAFIYAR ba tare da shi ba, shi yasa kawai suke so su ga bayan sa kafin nan,”

“Amma.. 

Kafin takai ƙarshen tambayar da zata sake jeho mata, ta ji sau kan wani uban tsawa a kanta” Kina hauka ne da zaki sani gaba da tambayoyi,kodin kin ga ina baki amsa,to ki rike duk wani tambayar da Kike da shi har zuwa lokacin da zaku haɗu da mijin ki a lahira,dan ya fini sanin amsar komai,kin ga sai ya amsa maki,oya dauki abinci ki ci “

Ta matukar tsorata,amma kuma duk yanda takai ga son ɗaga hannunta  ta kasa,saboda ji take ya riƙe mata.

Cikin rawar murya tace”na kasa ɗaga hannun,ya riƙe”

“Kaɗan ma kika gani,dan nan gaba wuyan ki ne zai riƙe” Kwanun ta dauka da chokali,idan ta ciko shi dam da shinkafa sai ta tura mata a baki,wanda kafin ta gama taunawa ta haɗiye ta kuma  ciko wani ta tura mata ko da bata buɗe baki ba to sai ta matse mata fuska ta kara tura mata,gabaɗaya ji ta yi tana niman mutuwa,dan abincin a kirji ya tsaya mata bai sauka ba,tunda kan wani ya sauka an daura wani,”zan mutu Mama ruwa,ki bani ruwa in sha!! 

“Ba zan baki ruwa ba har sai kin gama ci” Ai kuwa sai da taga da gaske tana iya mutuwa mata a wurin,sannan ta bata ruwan ta sha,wanda ko bayan shan ruwan sai da ta wahala kafin abincin ya sauka. 

Karasa kwance ta tayi “munafuka to tashi in kai ki ga mijin ki”

“A’a ni ba zan je ba,dan Allah kar ki kai ni wurin shi” ta faɗa tana ƙara mannewa jikin kujera tana kuka. 

Tabe baki ta yi “me yasa,bayan ke kika tambaye ni shi”

“Tsoron shi nake ji,ki taimaki rayuwa ta,ki min rai,zan mutu”

Da karfi da yaji ta jawo ta kamar wata kayan wanki tana janta a ƙasa har zuwa gaban gadon sannan ta daga ta tsaye “ai sai kin kalle shi”

Hannu tasa da ƙarfi da  duke ƙarfen gadon,nan take kuwa sai gashi ya buɗe ido yana kallon su,da sauri ta kauda kai tana zuba ihu,saboda Allah ya gani waɗannan idanun matsifar tsoro suke bata,domin wani irin ƙwayar ido ne da shi,wanda tunda take bata taba ganin mutum da irin shi ba,saboda shi wurin da yake baƙi,to na shi Brown  color ne,kuma irin me fitar da wani walwali a ciki,yanda kasan idon ya tara ruwa,saboda wani irin maikon da idon ke yi,gashi ƙwayar farin tar yake,ita bata taba ganin ido haka ba,har balle akan namiji,shi yasa abin ke matukar bata tsoro,ga uban suman dake jikin shi, dan tsabar  yawan suman da fuskan shi ya tara ba ta ko iya faras da ainihin kamannin fuskan shi,dan suman sajen shi,dana gemu duk sun lulluɓe mai fuska, wanda ko bakin shi ba a gani,sai dan ƙaramin jan labban shi(Lip)gana kan shi wanda ya sauko mai har wuya,ya kwanta dan tsabar yawa,wanda kallon daya zaka mai ka fahimci cewa shi din asalin Bafillace ne na gasken gasken kuwa,amma kasancewar shi a haka shima kallo data zaka mai ka sanya shi cikin jerin mahaukata. 

Ido ya zuba masu,dariya ta yi “yauwa dan gari,kalle ta da kyau yanda zaka gane ta koda kunje can,”

Ƙara dago kan Asma’u ta yi”oya ke ma kalle shi, kin ga wannan to shine mijinki ZABIHULLAH ZAMIR,dan haka ki rike sunan a kan ki, 

 Kai kuma wannan ce matar ka ASMA’U EL HABIB,kai ma ka rike sunan ta” ai kuwa kamar yasan mai ta faɗa sai kuwa gashi ya tsurawa Asma’u rikitattun idanun shi, 

Ita ma dan juyowa ta yi dan san ganin ko ya daina kallon su,ai kuwa cikin rashin sa’a in ji ta fa,sai gashi idan ta ya fada cikin na shi,wanda sabar rikicewa yasa sai da ta ji sau kan mari a fuskar ta wanda sai da ta yi ihu sannan ta dawo haiyacinta ta fahimci ashe fitsari tama Talatu a ƙafa,ai kuwa babu imani ta shiga kirban ta tana fika mata mari,shi kuwa mai da idanun shi yayi ya rufe.

Sai da ta gama jibganta sannan ta fita a dakin ta barta kwance a wurin ko motsin kirki bata iyawa. 

 Da daddare misalin sha biyun dare.

Wannan karan dukkan su suka zo harda uncle Tahir,anan suka samu Talatu,yayin da Asma’u ke saman kujera amma ba a daure ba,dan gaba ɗaya a galabaice take,

Gaisuwa suka yi,sannan kai tsaye suka tsaya a bakin gadon da yake kwace,cikin dariyar mugunta Haris ya ce”hello little brother,dama ina son in faɗa maka yau ne fa,ko in ce yanzun ne fa,kaga da zaran ta saka mana hannun ai shikenan,ni dai sakon da zan baka shine idan kaje can in ka haɗu da su ABU kace su yafe min kaji dan uwan na,dan haka juyo ka kalle yanda zan fara sheke matar ka “juyo da fuskan shi yayi setin Asma’u,uncle Tahir ne yace” Ina fatan kazo da takardar Nasir “

“Eh nazo da shi,yana hannun yaya Ahmad”

“To ya isa haka Haris,kuzo muyi abinda ya kamata mu wuce,ku kyale wannnan dan kunsan shi ai bamu  gama da shi ba,dan shi kaɗai yasan in da ya ɓoye asalin dokiyar,dan wannan da muke hauka a kanshi, kashi ishirin ne bisa dari,,dan haka da sauran aikin shi,ita dai wannan mu fara gamawa da nata aikin tukunna” Cewar uncle Ahmad. 

In da Asma’u take zaune suka nufa da takarda a hannun Uncle Ahmad din,yayin da su kuma fuskokin su ke ɗauke da murmushin farin ciki.

A gaban ta suka tsaya yayin da uncle Ahmad ya Daura mata takardan saman Cinyanta har da bairo”saka hannu “

Dago galabaitattun idanunta ta yi tana kare masu kallo,sannan ta mai da kallon ta izuwa ga Zabihullah wanda fuskan shi dai na fuskantar inda suke amma idanun shi a lunshe suke,lallai in da ranka kasha kallo,Yaya da kuma kawunne duk suna so su ga bayan shi,to me ya ji wanda be kama ya ji ba,me kuma ya gani wanda ya caccanci barin duniyar gaba ɗaya. 

Haris ne ya daka mata uban tsawa, wanda ba shiri ya dawo da ita hankalin ta”dalla Malama ki sama mutane hannu kin tsaya ki ba ta mana lokaci”

“Ba zan sa hannun ba” kalmar da ta girgiza kowa a wurin kenan. 

Mutuwar tsaye suka yi suna mata kallon mamaki, dan abun da basu zata bane,Mama Talatu ne cikin zafin rai zata kai mata duka uncle Ahmad ya dakatar da ita,”me yasa ba za kisa hannu ba”

Kai tsaye tana kallon idanun su tace”saboda nasan ina saka hannu zaku kashe ni,amma idan ban saka ba dole ku barni a raye saboda kuna  bukatar saka hannu na”

Wani irin mari Haris ya koda mata wanda sai da ta yi ihu,dan ji ta yi gaba ɗaya idonta ya rufe,”ke har kin isa ki kiyin abin da muka saki yi? 

Kara dago runannun idanunta tayi wanda  nan take jini ya kwanta a cikin daya, 

“Ko da zaku kashe ni,ku yi gunduwa-gunduwa da namana ba zan taba saka hannu a wannan takardar ba,balle kuci dukiyar da ba ku kuka tara shi ba, ba kuma hakkin ku ba ne”

Dariya uncle Tahir yayi,yana taɓa hannu “da kyau yarinya,amma ina so ki sani,in ba zamu iya kashe ki ba,amma dai ai zamu iya kashe wannan tsohuwar ta gida ko,wacce yanzun haka take kwance tana bacci,kin ga abu yazo gidan sauki,sai  mu sata a baccin da babu tashi gaba ɗaya,ta yanda data falka sai dai ta ganta  a lahira,dan haka zabi ya rage naki,ko saka hannu, ko kuma tsohuwa!!! ya karasa fada da ƙarfi. 

“Nanne!! Ta ambata sunan da matukar rawar baki…

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like