WATA TAFIYAR 15

Advertisement

 🦚WATA TAFIYAR🦚

       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟

*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

Advertisements

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“🌍`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAID BOOK

                      

               15

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Advertisements

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

WANNA LITTAFIN NA KUƊI NE,IN KINSAN BAKI BIYA BA DAN ALLAH KAR KI KARANTA, KUMA KAR KI YI SHARIN PLEASE.

“Nanne!! Ta ambaci sunan da matukar rawar baki. 

” Ke muke jira Mahaukaciya,wato har kina tunanin zaki iya mana wasa da hankali,to ko waɗanda suka fiki munyi dasu bare ke wawuya”

Ita dai shiru ta yi kawai tana kallon su,tabbas tasan cewa idan ta saka hannu a takardan nan to tamkar ta yankar ma kanta ne tikitin zuwa lahira,haka kuma idan taki shima tamkar ta bada rayuwar mace mafi soyuwa ne a gare ta,Nanne!to yanzun ina mafita tana buƙatar yin tunani,sai dai kuma yanzun ba lokacin tunani ba ne lokacin yanke hukunci ne. 

Kamar Almara,sai ji suka yi ta ce “ai kuwa dakun taimake ni,dama na daɗe da sanin Nanne ba ƙaunata take yi ba,dan Allah idan kun tashi haɗawa ku hada da kawunnai na,ciki har da wanda ya bada aure na,ɗan in da zan samu damar barin wurin nan, to da kai  tsaye gidan Ɗan Nanne za ni in musu kisan gilla,tunda da sanin su aka kawo ni nan”

Wani irin gigitaccen mari uncle Tahir ya koda mata,wanda sai da baki da hanci  ta suka fashe,wanda nan take jini ya ɓalle har diga ya ke,gaba ɗaya ji ta yi idanunta sun soye zuciyarta ta bushe,domin ta tabbatar in bata biyo musu ta bayan gida ba suna iya karar da ahalin ta. 

“Ke wace irin mahaukaciya ce, Kakar taki zaki kashe, wacce ta rene ki? 

Daga jajayen idanunta ta yi,tana watsa masu wani irin kallo” To me marabina da ku iye!! “Ta faɗa da daga murya. 

Sannan ta ci gaba” Ku ɗan Yayan ku kuke so ku kashe saboda abin duniya da wani dalili naku,amma har kuna da bakin kiran na da mahaukaciya,ai sai dai ku hada ku kira mu da suna mahaukata,kunga ke nan ni daku ba maraba, har ma gara ni tunda faɗa kawai na yi,tunda ba barin nan zan yi ba,dan haka ba zan saka hannun ba,sai dai ku yi duk abin da zaku yi “

Idan ransu yayi dubu to aba ce  yake,cikin fushi  uncle Ahmad ya fara magana har bakin sa na fitar da kunfar bala’i “wannan wace irin yarinya ka dauko mana haka Haris,bayan sai da na ce ka yi bincike sosai akan ta, ka  ce ka yi,to yanzun kalle abin da ka jawo mana,”

Shima cikin fushi yake ba shi amsa”uncle ai ba laifina ba ne,tunda sai da kai ma  ka ga yarinyar kace ta yi, to me yasa tun farko da kasan haka ne baka ce a canza wata ba,shi ne yanzu zaka ɗaura min laifi”

Tsaki su uncle Tahir suka yi, yayin da suka juya suka bar ɗakin cikin bacin rai, haka shima uncle Ahmad bin bayan su yayi yana ci gaba da matsifa,

Juyo wa yayi kanta kamar zai man gare ta “wallahi zamu dawo gode,idan kin isa kar ki sa hannu,za ki ga yanda zan yi dake” Fauu ya juya ya fita yayin da Mama Talatu tabi bayan shi tana kiran sunan shi. 

Ajiyar zuciya ta sauke,tana fashewa da kuka.

Nanne!!dan Allah ki gafarta min nasan nafada ba dai-dai ba akan ki!maganar gaskiya ke mace ce mai zuciyar zinari wacce ba a ko’ina ake samun irin ki ba,kin nuna min soyayya irin wacce na rasa,haka kuma kin reneni cike da soyayya irin wacce ƴa ke buƙata a wurin uwa ta gari,ina fata ki yafe min aduk lokacin da kika ji irin tsauraran kalaman dana faɗa akan ki!! ina fatan aduk lokacin da kuka samu labarin mutuwa ta ku iya jurewa,

sosai daran ranar ta yi kuka irin wacce ba ta taɓa yi ba,ga sanyin dakin,ga azabar raɗaɗin da ciyukan ta ke mata,dan irin dukan da tasha wurin Mama Talatu da kuma irin marukan da tasha dazun,shi ya haifar mata da wani irin matsananciyar zazzabi da ciyon kai wanda ko daga yatsa  ba ta iya yi,kamar yanda bata yi bacci ba ta kwana kuka da kiran sunan  Nanne,da Baba Mudassir,haka shima bai yi barci ba yana kallon ta,sai gab da Asuba ta samu wani wahalallan barci ya dauke ta. 

Ranar sai ƙarfe goman safe Mama  Talatu ta kawo mata abin kari, 

Ganin ta a kwace tana barci ne yasa ta zuba mata duka a baya “iyee!samun wuri lellai abin ki na kyau,wato ki ɓata ma mutane rai sannan ke ki zo ki shimfide kina barci ko,to  tashi maza tunda ba wurin hutu aka kawo ki ba” Ta karasa fada tana zuba mata wani dukan,sai dai fa ga mamakin ta ko motsi yarinyar bata yi ba, gani hakanne ya ƙara hassalata ta birkitota da ƙarfi,sai dai fa abin da ta gani ne ya bala’i daga mata hankali,harma ya kusa sa zuciyar ta ta buga saboda tsoro,dan ta tabbatar da idan wani abu yasamu daya daga cikin su ta shiga uku,dan ƙila su iya kashe ta ma akan haka, dan ba karamin buri suke da shi ba akan su,ƙara kallon Asma’u ta yi wacce ke kwance a ƙasa reram idanun ta sunyi fari kai sun kafe ko motsi bata yi. 

Na shiga uku ta furta a fili,ya zama dole in kira yallabai in shaida mai abin da ke faruwa, 

Cikin sauri ta dauki  waya ta shiga kiran lambar shi,sai dai yana ta Ring ba a ɗauka ba,hakan ne yasa ta mai da akalan kiran kan uncle Tahir, wanda bugu biyu ya daga, kasancewar sun san kansu yasa yana ɗagawa yace”ya aka yi ne? 

“Ranka ya daɗe akwai fa babban matsala!!

” Wani irin matsala? 

Sai da tayi ɗan shiru  saboda fargaba kafin ta ce “ina ga yarinyar nan fa ta mutu”

Wani irin ihu da ya mata a kunne  sai da ta cire wayar a kunne”ki na hauka ne Talatu! Yarinyar da muka bari jiya shine yanzun zaki ce min ta mutu!!to in ta mutu to ki tabbatar da ke ma kin mutu!sha shashar mata kawai ga ni nan zuwa!”dif  ya kashe wayar. 

Number Haris ya kira,yana dagawa cikin fushi da tashin hankali ya ce “kana ina ne? 

” Uncle ina Abuja “

“God! Yaushe har ka tafi Abuja da safen nan? 

Bata fuska yayi” Uncle tun ƙarfe bakwai fa na wuce,yanzun kuma goma ma ta yi,amma lafiya kuwa na ji muryar ka wani irin? 

Tsaki ya ja cikin takaici “yanzun wannan wawuyar matar ta kira ni wai yarinyar da muka bari jiya ta mutu”

Cikin sauri ya tashi zaune  har yana ture yarinyar dake kwance a jikin shi,”me? 

“Ni dai ba wannan ba,na kira number yaya Ahmad bai ɗauka ba,ka turamin number Sultan kawai sai mu je tare ya duba ta”

“To Uncle,ni ma gani nan dawowa” Number ya tura ma shi,sannan kuma ya turama Sultan din bayanin koma da gidan da zasu haɗu da uncle. 

Yama riga uncle Tahir din isa kofar gidan,sai dai bai shiga ba,saboda shima yasan masu gadi ba zasu bari ya karasa ciki ba,yana nan tsaye sai ga shi ya iso.

“Yauwa Sultan mu shiga” Buɗe masu Get aka yi suka shiga,shi dai kawai da kallo ya ke bin gidan,har zuwa cikin dakin ta,wanda aikin Uncle din ne ya bada umarni da ta kawo ta dakin ta,dan gudun matsala,kwantar da ita tayi a kan gado bayan ta mata wanka ta canja za mata kaya,munafuka har da turare ta fesa mata,wai dan kar Sultan din ya zargi komai,sai dai fa ta manta duk yanda ta yi sai ya nuna,kasancewar fatar jikin Asma’u mai haske ne,duk da ba fara ɓace, amma duk yanda ka dan matse mata hannu to sai wurin yayi ja,to balle irin uban dukan da tasha a kwana biyu nan,hakan ne ya haddasa mata kumburin jiki,wurin duk yayi ja-ja ya kumbura haka ma fuskanta.

Su na shiga da sauri ya karasa wurin ta,nan take ya shiga duba ta cikin kwarewa,sai da ya ɗauki wasu yan mintuna kafin ya dago ya kalle uncle “wahala ne ya jawo mata dogon suna,wanda idan ta ci gaba da shiga irin wannan yanayin zuciyar ta tana iya bugawa,kasancewar  tana harbawa fiye da kima duk bayan wasu dakiku,haka kuma duk bayan dakikun takan rage harbawa shi ma fiye da kima,wato ta kanyi sanyi,hakan kuma na iya haifar da bugawar ta ako wani lokaci kenan,saboda idan ta tashi bugawa to zata halba ne da karfin gaske,wanda hakan ne ba a so”

“To yanzun ya za ayi? 

“Eh to akwai wasu alluran da nake buƙata in mata, kuma ban da su sai dai in je in siyo in dawo”

“To ba damuwa” Nan ya ciro kudi masu yawa ya bashi,amsa yayi ya fita da sauri.

“Yallabai kayi haƙuri,wallahi kuskure aka kasu,nima shigowa ta kenan na ganta haka”

Cikin tsawa da matsifa ya katse ta”imin shiru shashasha! Bancin irin uban kudin da muke biyan ki shine baki kula! To in ba zaki iya ba sai mu samu wata,kuma mu munce ki dake ta ne?to daga yau sai yau karma ki sake daure ta in ta farfaɗo aka komar da ita dakin,kar ki sake daure ta ko dukan ta,illa iyaka ki  saka mata ido sosai mu kuma za muji da sauran,dan sai ta gommace kiɗa da karatu tunda haka ta zaɓa!! 

“Dan Allah yallabai ka rufamin Asiri,wallahi da aikin nan na dogara, kuma na yi alkawarin duk zan kiyaye abin da ka ce”

“Da yafi miki, sannan in wannan likitan yazo ki tsaka mashi ido dan bana son asamu kuskure, dan kinsan ba shi ke mana aiki ba,shi Dr Bala baya gari, dan haka ki kiyaye”

“To ranka ya daɗe” Juyawa yayi ya fita zuwa falo,, T.V ya kunna yana kallo. 

Bai jima ba sai gashi ya dawo da Leda a hannun shi ya shigo, 

“yauwa Sultan shiga kawai suna ciki, in ka gama sai kazo mu wuce”

“To uncle” Hau rawa yayi har dakin,bai kula Talatu dake zaune ba,tana jimamin yau saura kaɗan ta rasa rayuwar ta,dan ta tabbatar da in dai har ta yarda ya kore ta ya canza wata,to bawai yana nufin kora ba ne,A’a yana nufin kashewa ne,dan ta tabbatar da kashe ta za suyi saboda taga sirrin su,kai ita kan ɗan ba ƙara. 

Cikin ƙwarewar shi yake kula da ita,Allurai ya mata,sai da ya tabbatar da ta farfado tana gane abu,sannan ya juyo wurin Talatu”ko zaki iya kawo mata abu mai dan ruwa-ruwa, saboda akwai Alluran da zan mata kuma yanzun,dan Allah ki yi sauri dan ana jira nane”

Kamar zata ce wani abu,amma ganin yanda ya bata rai ne yasa kawai ta tashi ta fita,yana ganin fitarta da sauri ya ciro wani dan gundun fefa daga Aljihun shi ya ce “gashi imaza ki ɓoye,in kin samu dama ki karanta”

Kamar ba zata amsa ba,amma ganin yanda hannun shi ke rawa,da kuma yanda yake kallon kofa ne yasa ta amsa,ta tura cikin riga,tana fito da hannu uncle Tahir na shigowa,

ɗan kare masu kallo yaye kamar mai nazari,dan a falo ya haɗu da Talatu shine yake tambayar kome ya sauko da ita,, tana faɗa mashi shine ya shigo da sauri dan shi mutum ne mara yarda. 

Ganin hakan ne yasa Sultan din ƙara haɗa fuska ya shiga kara mata ruwa,koda aka kawo   shayin,da kyar ta iya sha, sannan ya mata ɗayan Alluran ya kuma ba Talatu magunguna,sannan suka fita gidan da uncle. 

Sai ƙarfe uku ruwan ya ƙare wanda cikin waɗannan awoyin maimakon ace ta samu isasshen barci sai ta kasa,da ta fara bai wuce mintina biyar zuwa goma zata farka a firgice,hakan ne ma yasa kawai ta hakura da baccin,ruwan na ƙarewa ta dauke ta ta mai da ita wannan Underground din,sai dai wannan karon sai da ta rufe mata fuska da bakin kyalle dan karta gane hanya,kuma a yana yin tafiya kaɗai ta fahimce ba hanyar da ta bi ba ne wancan ranar, har cikin wani daki ta kaita sannan ta buɗe mata ido,sai dai fa abin mamaki wannan dakin ba irin wancan ba ne,kuma tare aka ƙara haɗa su,wato ita da shi, sai dai shi har yanzun a kwance yake saman irin wannan gadon dare da belet,tana tura ta dakin ta fita ta kullo masu ƙofar, wanda ya kasance da Na’urori yake amfani,dan gaba ɗaya ƙofofin wurin da Na’ura da kuma number suke buɗewa da kullewa,shi yasa in baka sani ba ba daman fita kuma ba daman shiga. 

Ajiyar zuciya ta sauke ganin idon shi a kulle kamar yawancin lokaci,

daya daga cikin kujerun ta jawo ta zauna,a hankali ta warware takardar da wannan likitan ya bata,wanda ta ciro daga cikin rigar ta,abin da takardar ta ƙunsa kuwa shine,(ko ta halilin yaya ki ɗaure duk wani kalan azabar da zasu miki, kar ki kuskura ki saka hannu,sannan daga ƙarshe ki bi duk ta kowani hanyan da zaki bi domin ganin kun bar wannan gidan ke da Zabihullah  nan da ƙwanaki huɗu,in ba haka ba a kwana na huɗu zasu kashe ki su aura mashi wata,wacce za ta saka masu hannun,yanzun haka harsun fara niman auren yarinyar,wannan ne tsarin su, dan haka  ki gaggauta).

“Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun!! Nan da kwana huɗu,to ta yaya zan yi in fita daga wannan ramin,ga waɗannan mahaukatan kofofin,sannan ya zan yi da wannan mutumin,ya Allah ka samar min mafita”

Tashi ta yi daga zaune, kai tsaye wurin gadon da yake kwance ta nufa,tsayawa ta yi a kan shi tana ƙare mai kallo,can kuma a hankali ta buɗe baki ta kira sunan shi”ZAMIR ka tashi mu yi magana “tamkar ya ji mai ta ce, sai kuwa gashi ya buɗe idanun shi tar a kanta,wanda hakan ne yasa da sauri ta matsa baya..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like