HALIN GIRMA 14

Advertisement

 Halin Girma

    14

_*Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

Advertisements

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

Advertisements

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*

*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

*_Muna da haɗin_*

_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

_Muna Gyaran jiki_ 

_Na amare_ 

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_

_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_

••••••••••

*****

Azahar sosai ya tashi, ya mike yana salati, daga curtains din dakin yayi yana mamakin tsawon lokacin da ya dauka yana baccin, wayar sa dake saman gadon ya dawo ya dauka ya bud’e ta, misscalls ya gani ya duba sannan ya ajiye ya fito zuwa falo in da yatar da abincin sa a jere cikin manyan warmers sai kuma wani dan basket da aka rufe shi da jan kyalle me kyau dake dauke da hoton heart, matsawa yayi gabansa yana kallo,

“Menene wannan?” Yayi maganar yana rik’e kugun sa da sauri wani bafade ya shigo, ya rissina yace

“Sako ne daga shashen Kilishi, inji gimbiya Laila.”

“Laila?” Ya furta cike da mamaki

“Yaushe ta zo?”

“Tun da safe, lokacin baka nan.”

“Dauke shi a kai sashen Ammi, ace ta ajiye.”

Sake dukawa yayi cikin girmamawa yace

“An gama ranka ya dade.”

Juyawa yayi ya koma ciki, yayi wanka sannan ya shirya yana tunanin dawowar Laila a irin wannan lokacin da yasan suna tsakiyar karatu ne. Fitowa yayi ya tsattsakuri abincin ya fita wajen ammi dan be samu ganin ta da safe ba.

A gabanta ya tarar da sakon nasa, ta bishi da kallo sannan ta kalli kwandon da yake na Kaba. Sai da ya zauna ya gaishe ta sannan ya saka aka miko masa basket din

“Ammi kinga ko? Menene ma’anar haka?”

“Ni kaina nayi mamaki, amma kuma kasan dama hakan zata faru idan har ta samu labarin auren ka.”

” Bana son wata matsala gaskiya, zan aika da sako wajen Kilishin dan ba zan dauki rainin hankali ba.”

” Ka rabu dasu, karka yarda su bata maka rai har kayi tunanin biye musu, ka cigaba da addu’a nima kuma ina tayaka mahaifin ka ma,.ba zasu taba samun nasarar abinda suke so ba.”

” Shikenan Ammi, dan Allah aje a kona basket din nan dan bana son ko ganin sa.”

” Shikenan, ka cigaba da walwalar ka karka yarda makiyinka ya gane weakness dinka.”

” In Sha Allah Ammi.”

” Allah yayi maka albarka.”

” Amin.” Ya amsa yana jin tamkar dawowar Laila akwai wani babban dalili

” Yawwa na kira Fatima akan lefen ka, zata hada komai in sha Allah, idan yaso sai su tafi ita da kai da wata dai cikin su, Takawa ma yace shi zaiyi komai, amma duk da haka Fulani tace yayi nasa itama zatayi nata mu ma nan sai muyi namu.”

“Wayyo ni dan gata.” Yace yana murmushi

“Ammi gatan kar yayi min yawa ai.”

“Ba zai ba, Allah yasa ayi damu kawai, amma dole sirikata taga gata.”

“Uhm.. Allah sa idan tazo karta kwace min wajena.”

” Dole ne ai, kasan dai yadda nake son ya mace ko?”

” Shikenan sunana sorry wallahi.”

Dariya Ammi ta saka

” Aikam ka shirya tun yanzu.”

” Shikenan, Muhammad kana ji? Kayi hakuri da duk abinda zaka gani.” 

Ya fad’a cikin yanayin kalar tausayi, dariya sosai ya bawa Ammi tayi sosai, kallon ta ya dinga yi cikin tsantsar son ta, yana son Ammi da duk wasu halayenta, babu abinda yake so irin yaga tana farin ciki sosai, hakan yake sashi jin zai iya komai dan ganin ya faranta mata, ya dawwamar da farin ciki a kan fsukar ta, hakan kuma ba zai yiwu ba sai dole yaki karbar muradin Bubu, dole ya hakura da mulkin ko da yana so, saboda farin cikin Ammin Sa!

***Satin Mama daya cif a Katsina, ranar da zasu dawo ranar Bashir ya iske su a chan da dalleliyar mota da sha tara ta arziki, murna wajen Mama da Zeenat ba’a magana aka dinga turashi gida gida na dangi dan aga irin mijin da zeenatun ta samo, aikuwa nan da nan magana ta karade ko ina cikin family din Maman, anan wasu da yawa suka samu labarin bikin Zeenat din wanda aka saka wata daya kachal bayan Bashir din ya tabbatar musu da zaiyi komai basa bukatar komai hatta da kayan gida duk shi zai zuba, hakan ya sake fasawa Mama kai ta dinga hura hanci a lallai zeenatun ta ta dallo miji na kere sa’a, tausayi da farin cikin halin da ta tabbata Iman zata shiga idan har ta auri fakirin nan take, gashi dai su kam Allah yayi musu gam da katar dan yadda aka dinga maganar Bashir din a dangi kadai ya ishi Mama tutiya da alfahari.

   A motar ya kwaso su Zeenat na gaba gida na tashi cikin taken soyayya Mama da Marwan na baya har Kano, Zeenat ji take kamar tafi kowa sa’a a duniya dan da gaske take jin wani irin son Bashir din na ratsa ta.

   Sanda suka isa gida magriba tayi saboda basu taho da wuri ba yana faman zaga dangi, alwala aka kawo masa ruwa yayi, ya zauna Zeenat din ta shiga ta fito suka dasa sabuwar hira irin ta yaushe rabo. Cikin hirar ne yake fad’a mata lefe in sha Allah za’a kawo cikin upper week, zai sanar mata da ranar sai ta fadawa Mama, hakan yayi mata dadi har tana hasashen uban kayan da za’a kawo mata dan taga Bashir din me bajin ta ne sosai.

  Ranta fes ta koma ciki bayan ya tafi, ta labartawa Maman lokacin Matar Abba Musa ta shigo wajen Maman yi mata sannu da zuwa. 

“Haba ni nayi mamakin da aka ce manyan mutane ne suka zo neman aure gidan nan na tabbata dama wajen Zeenat ne, yarinya kakarki ta yanke saka wallahi.”

Tace tana dariya, murmushi mama tayi

” Kice manyan mutane ne suka zo? Bani labari Binta.”

” Ai Maman Habib baki gani ba, wallahi manyan mutane ne kamar ma daga wata babbar masarauta, yadda naga mazan gidan nan sun rikice kadai zaka gane ba kananun mutane bane, na zata ma na Iman ne ashe na Zeenatu ne, Baban Walid be min bayanin da zan gane ba kinsan wajen lokaci daya suka zo dukka.”

” Aikuwa sune, kai kice dai manyan mutane ne, masarauta fa? Kai masha ALLAH abu yayi kyau wallahi.”

” Ai Maman Habib ba karamin dace Zeenat tayi ba wallahi, Allah dai ya kaimu bikin nasan za’a ga lefe na ban mamaki.”

” Bari kawaii, sai muzo mu tanadi kyautar girma da zamu fita kunya, na gode da kika sanar dani dan Dr ba lallai ya fad’a min ba muna yar tsama dashi.”

” Ai haka suke, basa fadar cikin su wallahi, itama kuma Gajin ba zaka ji daga bakin ta ba tunda komai suna fad’a mata ai.”

Tabe baki Mama tayi

” Ai ni baki sani ba, so akayi a yi min bakin ciki.”

Sai ta rage murya

” So akayi fa a hana Zeenat auren Bashir din nan, kuma ina kyautata zaton akwai saka hannun Gajin a ciki, toh in ba haka ba yadda Dr ya rikice akan maganar lokaci daya zaki gane zugashi akayi.”

Kama baki Matar Abba Musa tayi

” Allah? Tab ashe an so yi miki tsakiyar da ba ruwa.”

” Ke dai bari, shiyasa na tsaya kai da fata, kinsan mutane basa son ka cigaba ko aga danka ya cigaba ko zai huta.”

” Zahiri, toh Allah ya kyauta, ban yi zaton hakan daga gareta ba.”

” Ai ba laifin ta bane, itama yadda aka dora ta haka zata tafi akai.”

” Eh kuma gaskiya, tunda kinga ai bata cika saka ido akan al’amuran mu ba.”

” Shine, koma waye kansa yayi wa, aure kam babu fashi.”

” Assalamu alaikum.”

 Iman tayi sallama ta shigo, gimtse fuska Maman tayi,ta gaishe su matar Abba musa ta amsa a sake tana tsokanar ta da amarya amarya, murmushin yake kawai tayi tana satar kallon yanayin fsukar Maman, zuwa tayi ta fad’a mata anjima zata tafi wajen dangin Mamanta amma ganin Matar Abba Musa ya saka ta fasa ta wuce kawai daki ta karasa hade koman ta waje daya.

  Bayan tafiyar Matar Abba Musa ne ta fito ta samu Maman a kitchen tana rarrabe kayan da tazo dasu dangin su kuka kubewa da daddawa waje daya

“Mama dama yau zan tafi gidan su Mamana.”

Tsayawa da abinda tayi, tayi ta kalle ta a mamakance tace

“Yau? Yaushe aka yanke  maganar tafiyar taki ban sani?”

“Dama tun ranar da na dawo daga gidan Ya Maryam Abba yayi min maganar.”

“Toh! Shi zai kaiki kenan? Ko turowa za’a yi kije? Ko da yake mutanen da basu damu dake ba yaushe zasu turo? Wannan din ma nasan dan Dr yayi magana ne.”

“A ah tare da Abban zamu je.”

“Kutmar Uba!” Da sauri Iman din ta ja baya dan yadda ta ga Maman ta birkice lokaci daya

” Ni za’a yiwa munafurci? Wato yace zai ganki saboda yaga tsohuwar matar sa ko? Dan an raina min wayo an maida ni wata sakarai. “

” Dama… “

” Dallah rufe min baki, wato gani shashasha an dauko raino an bani shine yanzu za’a nuna min bariki ko? Toh wallahi ba zata sabu ba wallahi kinji na rantse, ko ya barki ki tafi ke kadai ko ya hada ki da wani cikin yan uwansa ko Hafiz ne ma. “

Shiru Iman tayi kamar ruwa ya cinye ta, tana jin sababin da Maman take kanta na kasa ita dai bata ce komai ba,me zata ce ma?

” Bari yazo naji abinda yasa zai munafurce ni wallahi, bayan duk kokaarin da nayi wajen rik’e ki amma sam yanzu baya gani, dan kawai yar matsala ta ratsa tsakanin mu shikenan sai ya rufe ni. “

” Uwata zo ki wuce, kije waje kina da bako. ” Abba da yazo a lokacin yace yana kallon Maman, sum sum Iman ta fice kafin Abban ya dubi Maman cikin bacin rai yace

” Kin bani mamaki Hajara, ban zaci haka daga gareki ba.”

” Dama ai haka ne, duk abinda mutum yayi ba gani za’a yi ba musamman aka ce da ba naka bane, amma ai Allah ya gani. “

” Bakya tsoron Allah kuwa in dai haka ne, har kece zaki ce Allah yana gani? Kina tsoron haduwar ku kuwa? Bayan wahalar da kika bawa yarinyar nan har kina da bakin magana? “

” Wahala? Ita tace maka na bata wahala kenan ? Oh shine ka shirya zaka kaita wajen uwarta kenan bayan na gama cin wahalar ta, duk abinda nayi baka gani ba. “

” Kiki tsoron Allah, na gano duk irin rikon da kika yi wa Ummi, kinci amanata kin ha’ince ni, Ashe ke din fuska biyu ce dake ban taba sani ba.”

” Da yake yanzu hankalin ka ya koma wajen tsohuwar matar ko, ko nace tsohuwar karu… “

 A wani irin bacin rai ya daga hannu zai Kai mata mari, fasawa yayi yaji kamar an rik’e  hannun zuciyar sa na tafasa, ba ya cikin mazan da zasu daki matar su,baya kuma fatan hakan duk da irin yadda Maman ta bata mishi rai.

“Dukana zakayi Ibrahim? Dukana? Akan na fadi gaskiya, waya san auren da kukayi na gaske ne ko kuwa? Tunda mu dai babu wanda ya shaida, shine zaka dauki hannu ka dake ni akanta ko?”

Ji yayi kansa yana sarawa, be taba tunanin tashin hankalin mAman ya kai haka ba, juyawa yayi da nufin barin kitchen din amma sai yaji ta rik’e masa riga ta baya

“Wallahi ba zaka je wajen ta ba, wallahi ba zan yarda ba.”

Tsoro ne ya kamashi jin ta daga murya sosai, da sauri ya fizge rigar sa ya daga kafarsa wajen ficewa daga gidan ma gaba daya, ba zai biye mata ba, har a jisu a gidan abinda zai zamar masa abun kunya a wajen yan uwan sa .

  Shashen Gaji ya wuce da ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.

  Tana shiga Mama dake tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad’an ta fadi amma ta tsaya akan kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba 

“Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na gama cin wahalar ki.”

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman magana, 

” Lafiya Mama? Me tayi?”

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.

   Abinda Abba ya guda sai da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana kallo ta cigaba da haukanta.

***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin, karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a k’asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya saka shi samun relief. Tafiyar su Dubai ya saka basa waya sai dai chatting dan kar tayi saurin gano shi. Da zata tafi ya saka Musaddik kai mata dubu biyar a cikin envelope, sai da ya jinjina kudin kafin ya aika, kyautar sa ta farko kenan amma sai yake jin kunyar kai mata, tana bukatar manya manyan abubuwa a wajen sa amma akwai sauran lokaci.

   Tunawa da tayi da envelope din ya sakata cirota a cikin handbag dinta ta bud’e, murmushi tayi ganin kudi ne sai wani dan karamin note an rubuta I love you da shape din heart a k’asa. Sosai taji dadin kyautar tayi ta kallon note din tana jin dadi sosai. 

   Cigaba da rikewa tayi a hannun ta har zuwa sanda zasu sauka sannan ta maida cikin handbag dinta tana jin wani irin feeling, she’s nervous bata san wanne irin tarba zata samu ba. Tana ganin sanda Abba ya dauko waya bayan sun sauka yayi kira.

“Mun sauka.” Taji yace sai kuma yave

“Owk tura min number shi.”

Suna tsaye ya sake duba wayar, number aka turo ta text message ya ciro ta ya kira ya fad’a masa yadda zai gane su kafin ya kashe yana cewa

“Ummi muje gashi chan ma.”

Matse jakar hannun ta tayi, taja akwatin ta zuwa wajen wanda yake nufo su.

“Welcome Sir.”

 Yace cikin girmamawa, ba bahaushe bane jikin sa sanye da wasu uniform navy blue an saka number 5 a daidai aljihun.

“Thank you.”

Karbar kayan su yayi ya zuba a booth sannan ya budewa Abba gaban motar ya zauna ita kuma Iman ya bud’e mata baya sannan ya jasu suka fita daga airport din.  A daidai wani hotel suka tsaya Abba ya juyo bayan ya kalli Iman yace

“Zanzo da safe in sha Allah, ki gaishe su, idan kina bukatar wani abu ki kirani.”

“In Sha Allah Abba, Nagode sai da safe.”

“Allah ya kaimu.” Ya fice ya rufo kofar ya tsaya daga gefe yana kallo suka bar wajen.

   Ta cikin dark tinted glass din motar Iman take karewa garin kallo tana admiring ko ina musamman da dama magriba ta kawo kai dan wasu masallatan suna kokarin fara kiran sallah.

    A wani babban gida cikin jerin gidajen Babbar unguwar nan ta Maitama yayi horn, a hankali gate din ya shiga zugewa har ya karasa budewa gaba daya. A gefe daya yayi parking kafin ya gama daidaitawa wasu mata su uku da wasu maza biyu suka fito ta wata kofa suka nufo su dukkansu fuskar su dauke da farin ciki mara misaltuwa.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

HALIN GIRMA 20

Advertisement  Halin Girma       20 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…

HALIN GIRMA 21

Advertisement  Halin Girma       21 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…

HALIN GIRMA 25

Advertisement Halin Girma       25 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…

HALIN GIRMA 16

Advertisement  Halin Girma     16 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements *_ZAFAFA…