Advertisement
Halin Girma
18
Hafsat Rano
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK๐๐พ_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK๐๐พ_*
Advertisements
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK๐๐พ_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK๐๐พ_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Shigowa Mamma tayi, ta same ta a tsaye ta ma rasa abinda zatayi. Hannun ta, ta kama ta zaunar da ita, ta bud’e jakar da suka zo da ita ta ciro turare me dadin kamshi na daban ta fesa mata, ta duba fuskar ta sannan tace
Advertisements
“Ki kwantar da hankalin ki dan Allah,bari na duba kayan da yan matan nan suka kawo, ba za’a rasa alkyabba ba. “
Fita tayi sai gata ta dawo tare da daya daga cikin yan matan, ta russuna har k’asa ta gaida Iman din da gabatar da kanta da sunan ta Ummimi sannan ta matsa daga gefe,
” Tashi ta taimaka miki ta saka miki. “
Mamma tace tana murmushi, wani banbarakwai Iman taji, ta tashi cikin sanyin jiki yarinyar ta hau saka mata alkyabbar cikin k’warewa. Ji take tamkar mafarki, kamar zata farka taga komai yana yadda take. Har ta gama gyara mata, ta kawo sauran kayan ta sassaka mata ta fito sosai a gimbiyar ta mamaki be bar ta ba.
Khadija da Zahra ne suka shigo, kusan sa’annin Iman din ne a family, doki ya saka su zuwa suka Iman din suma su bawa idon su abinci, suna shigowa dakin suka ganta cikin shigar da tayi masifar mata kyau, shigar alfarma.
Hoto Zahra ta ciro waya ta hau daukar ta, kala kala har da videos dan dole ne yau followersa dinta na Instagram su kara kiyayarta.
Kiran ta ya sake yi dan da gaske ya matsu ya ganta, irin matsuwar ba don idon sirikai ba, da dumbin jama’a da sai dai kawai ta ganshi a duk ma in da take.
Mamma ce ta dakatar da hotunan haka, tace suyi mata rakiya zuwa in da Muhammad din yake, ko tace Yarima Muhammad dan sunan kam be chanchanci a dinga fadar sa haka nan kai tsaye ba.
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, haka ta tashi tana turo baki. Tare suka fito da biyu daga cikin hadiman yan matan nan, suna daga bayan ta suna take mata baya, domin da gaske Ammi tayi musu gargadi akan surukarta ta, su kula da ita da komai nata
Suna zuwa daf da seat room din suka soma jin hayaniyar maza,amma ba irin hayaniyar da zaka ji ba irin ta wasu mazan marasa aji da tsari. Hayaniya ce ta nuna farin cikin su da taya murna cikin ilimi da wayewa. Ji tayi kamar ta koma da baya, dan yadda ta tsani taro na maza har ya zama tana ciki, bata san kalar kunyar da zata sha ba, dan da alama dukkan su masu surutu ne. Bata dai ji muryar uban gayyar ba, ta kamo addu’a ta soma yi har ta samu nutswar ta
“Iman.” Ya kirata yana karasowa wajen, tare suke da Habib da abokin sa Sadeeq. Murmushi tayi masa
“Uncle Khalil, ashe kazo.”
Murmushin yak’e ya maida mata, ya tuna da warning din da Moh ya kada masa, duk da yayi kokari matuka be saba ka’ida ba, yanzu ma dole ce ta sakashi zuwa tun da dai ba zai ki zuwa daurin auren Zeenat ba.
“Nazo Iman, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya.”
“Amin.”
Ta amsa a ciki tana jin babu dadi, lokaci daya yanayin sa ya sauya, yayi saurin barin wajen yana yin gaba, suka gaisa da Sadeeq da Ya Habib sannan suka wuce zuwa in da zasu.
Sallama Ummimi tayi daga kofar, ta sanar da zuwan Iman din kamar yadda yake a tsarin masarauta, murmushi Moh yayi me aji, ya mike da kansa yana hararar su Ja’afar
“Amaryata tazo dan Allah muna bukatar privacy.”
Dariya suka kwashe gaba daya, ya hade rai da gaske ba da wasa ba,su ka hau tsokanar sa amma yayi fumfurus yace wallahi sai sun fita. Musaddik ne yace
“Ai ka bari ta shigo mu gaisa ko? Sai mu fita daga baya.”
Da kai ya amsa ya koma ya zauna yana jin rawanin da ke kansa ya soma gundurar sa. Shigowa sukayi bayan sun saka Iman din a tsakiya, idanun ta da tayi kokarin saukar dasu k’asa sosai suka shiga cikin nasa, da sauri ta dauke idon ta, ta zauna su Zahra suka sakata a tsakiya. Gaishe su sukayi suma suka amsa sannan suka gaisa da Iman din da take amsa musu ciki ciki dan ji take kamar ace fit ta fice saboda tsoro.
“Capt. Lets snap please.”
Wani abokin sa Gbenga yace yana kallon sa
“Ok sir.” Yace yana tashi, taimaka mata Zahra tayi, ta isa wajen da yake a tsaye, daga gefen sa ta tsaya, sai taji kamar ana saka abu ana bubbuge mata kafafunta. Hannun ta taji yana laluba ta cikin babbar rigarsa, ta daga kai da nufin kallon sa, shima a lokacin kallon ta yake, Ja’afar yayi sauri ya dauki scene din, hoton yayi masifar kyau, duk suka hau yabawa.
Masifaffiyar kunyar da take ji ta hanata sakewa sam, duk da haka an dauki hotunan sosai sun fita, banda camera man suma wayoyin su duk babu na banza.
Wani irin laushi hannun sa da yake cikin nata taji,ta tuna kullum cikin safar hannu yake zuwa mata, duk sanda zata ganshi hannun sa da kafar sa, na sakaye, sai yanzu ta gani dalilin nasa na yin hakan.
Mammatsa mata hannun ya dinga yi, ya hanata sakat ya sakata a wani irin yanayi me wuyar fassarawa, gashi ya saka shi cikin rigar yadda ba wani wanda zai lura, sai da aka gama hotunan tas sannan suka fita suka barsu da nufin idan sun gama gaisawa sai su fito a shiga cikin gidajen ayi sauran hotunan a cewar Musaddik.
Kamar me jiran kiris kuwa, suna gama ficewa ya saka dukkan karfin sa, yayi hugging dinta kamkam yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
“Alhamdulillah.” Ya furta yana murmushi
“Mrs Muhammad Ahmad Santuraki.”
Ya rada mata a kunnenta, ture shi tayi tana turo bakin ta gaba, ya tsaya yana kallon ta dan be taba sanin ta iya shagwaba ba sai yanzu
“Me yasa kayi haka?”
Tace cikin dan daga murya ita a dole ya bata mata rai, riko ta yayi da sauri ya dora hannun sa akan lips dinsa yace
“Shssh… Ba’a dagawa miji murya babu kyau.”
Kokarin ture shin ta cigaba da yi amma sam ya hanata damar hakan, sai ma sake manne ta da yayi sosai da jikin sa suna shakar kamshin juna. Luf tayi ta daina motsawa kowa na sauraron bugun zuciyar dan uwan sa. Wajen minti daya suna a haka kafin ya saketa yana jan ta suka zauna a saman kujerar, ya rik’e hannayen ta yana kallon cikin idanunta
“I promise you ba abinda kike tunani bane, zan miki bayanin komai amma ba yanzu ba, yau ranar farin ciki ce, let’s not discuss duk wani abu da be shafi ranar ba kinji matata? “
Turo bakin ta sake yi, ya saka hannu ya shafa yana murmushi
” I love that. ” Saurin rufe fuskar ta tayi kunya na kamata
” Itama kunyar duk ina so, komai ma ni so nake kinji? Amma dai ki ajiye mana zuwa sanda zamu tare a gidan mu, ko nawa ne zan biya na siya. Bana so a samu matsala dan zai iya yin abinda ban shirya ba. “
Da sauri ta gyara bakin ta, ta kuma gyara zama tana matsawa kadan, matsowa yayi ta sake matsawa ya sake matsowa kafin ta samu damar sake matsawa ya saka hannu ya tokare ta, ya matso da fuskar sa daf da tata, tayi saurin runtse idon ta tana jin kamar zata saki fitsari. Light kiss taji yayi mata a saman idonta dake a rufe.
A hankali ta bud’e idon ta, tayi saurin rufewa ganin yadda nasa ya sauya sosai.
” Amm.. amm muje kaga su Mamma da yan uwan mummy, sai Gaji da sauran yan uwan Abba ko? “
” Hmm. ” Yace yana jan ajiyar zuciya
” Tohm bari na kira Musaddik yazo. “
Tashi yayi tsaye, ita kuma ta dukar da kanta k’asa, murmushi ta samu kanta da yi, tayi saurin katse shi ta sake saukar da kanta dan kar ya gani.
Dawowa su Musaddik sukayi, su Zahra da aka samu sabbin samari suka shiga ciki don sanar da shigowar su Mubamamd din.
Ta bangaren Gaji aka fara, akayi hotuna sosai da kowa da kowa, sannan aka dawo in da su Mamma suke nan ma akayi musu, sai sauran mstan gidan da jikoki da sauran yan uwa da abokan arziki har ma da makwafta da suka shigo ganin kwaf.
***Yadda Zeenat ta koma zaka rantse tayi shekara tana jinya, gyaran gashin ma da aka yi duk ya hargitse kamar ba’a yi ba, ta tada aljanu yafi kala biyar duk da muryoyi kala kala akan suns gargadin in dai aka sake aka kai ta gidan sai sun kashe ta.
Ko da Mama ta kira Abba ta fad’a masa cewa yayi karya ne, ya kashe kiran dan yana cikin mutane ne, amma kuma sai ya dinga jin babu dadi yana kuma tausayawa Zeenat din sosai, amma ya zai yi? Su suka jawa kansu duk da ba irin muna musu da be yi ba.
Kayan kitchen su Aunty Maimuna suka dauka, suka kira Bashir din dan ba ma a samu damar zuwa an yi jeren kitchen din ba. Cewa yayi zai aiko a tafi dasu, ba’a dade ba kuwa sai ga wani saurayi yazo a golf irin ta hayar nan, dole suka saka Habib bin bayan su da wasu kayan bayan ya dauko yar kurkura dan yawan kayan kadai sun isa a yiwa wasu amaren biyu amfani dasu bayan Zeenatun.
Sanda suka shigo unguwar gaban kowa ya hau faduwa, basu gama shiga masifa ba sai da suka ga kofar gidan da aka tsaida, katuwar kwatar dake kwance a kofar gidan ce ta fara tsorata su. Haka suka daure suka fito ya bud’e musu gidan suka shiga.
Babban tashin hankali sanda suka shiga gidan suka tarar da kayan da suke gidan da Bashir din yace ya saka mata kaya kar ayi komai, su kansu kujerun bayan yadda aka daina yayin su, ba set bane dan babu three seater ko kankantar falon ya hanata shiga ko kuma ba’a yi da ita ba oho.
Sanda suka shiga kitchen din sai da suka kusa kurma ihu, kwatan kwatan abinda Maman ta siya ba zai shiga kitchen din ba. Babu wanda yake wa wani magana a cikin su, suka saka abinda zai iya shiga kitchen din da ko kitchen cabinets babu, sauran na amfanin suka saka mata a cikin sip dan wannan ba za’a kirashi da wardrobe ba sai da sip๐ข๐ ragowar kayan suka juya dasu cike da tunanin yadda za’a kare da Mama. Babu maganar uban kayan turaren wutar da ta siya wajen hadaddiyar me turaren wutar nan*yerwa incense and more.*
Shigowar su kenan suka tarar ana ta hotuna da Iman, jiki a sanyaye suka wuce bangaren Maman suna taraddadin yadda za’a kwashe. Mama ma jin ance sun dawo ta yi zumbur ta tashi, sai dai tun kan su gama zama ta san da matsala.
Aunty Maimuna ce ta jata daki tayi mata bayanin komai sai ragowar kayan da tace an loda su a motar Aunty Muhibba dan kar a shigo dasu saboda yan saka ido.
A k’asa dirshan ta zauna, ta cire dan kwalin ta da take jin yayi mata nauyin gaske saboda yadda kanta ke masifar sarawa
“Amma Bashir ya cuce mu, ya cuci rayuwata, yanxu dan Allah wannan abun kunya da me yayi kama? Na shiga uku.”
Ta jefar da hannun ta gefe,
“Be kyauta ba gaskiya, ha’inci ne wannan kuma, sam be kyauta ba.”
Aunty Maimuna dake kokarin bata baki ta fad’a duk babu dadi
” Allah ya isa ban yafe ba wallahi,shege macuci. “
“Kiyi hakuri Yaya Hajara, cuta dai Bashir ya riga yayi mana ita sai dai muyi hakuri, mu lallaba a kai ta idan yaso daga baya idan hankalin kowa ya dauke sai musan abinda ya kamata. “
Wani kallo tayi mata, kamar ma ta rufe ta da duka take ji
” Sai bayan an kai ta ya gark’ama mata ciki sannan ne kike tunanin zai rabu da ita? “
” A ah Yaya, kinga wai ai dai yanzu daga daure aure yau ai ba za’a ce ya saketa ba, kinga hakan ai kema zai iya baki matsala da Dr. “
” Matsala ta nawa kuma? Ni yanzu ya riga ya fita daga kaina, ta yata kawai nake, dole na bata farin ciki ko ta halin Kaka. “
Shiru kawai Aunty Maimuna tayi dan ba kuma tasan yadda zatayi ta bawa Maman hakuri ba. Aunty Muhibba ce ta shigo, tace maman ta tashi ta gyara jikinta Iman da mijinta zasu shigo. Kamar ta danna ma Aunty Muhibban ashar taji dan dai akwai kunya tsakanin su kasancewar ta matar babban wansu, dole ta tashi ta wanko fuskar ta a bathroom ta shafa mai da yar hoda ta saka kwalli sannan ta fito.
***A zaune take ta tankwashe kafar ta akan dan carpet din da yake jikin gadon dakin, ranta a bace yake tun bayan da ta samu labarin auren da Yarima Muhammad zai, taso ta tada hankalin ta amma Kilishi ta hanata, yanzu gashi tana ji tana gani an daura.
“Laila!”
Ta kira sunanta tana daga zaune a gefen makeken gadon ta, da ido ta kalle ta ba tare da ta amsa ba, ta mike tsaye. Sanye take da doguwar gown ja, sai gashin ta da yake a tattare a waje daya da yasha gyara na musamman.
“Yaushe zaki koma?” Ta ta da tambayar bayan tasan amsar da zata bata. Da ido ta sake dubanta, ranta na sake baci tace
“Na dawo kenan.”
Da sauri ta mike daga gishingid’ar da tayi, ta dauka zata ce mata soon zata koma kamar yadda take bata amsa a ko da yaushe idan tayi mata maganar komawar.
“Kinsan me kike cewa? Ba zaki koma ba? Me yasa?”
“Ba zan koma ba har sai na samu cikar burina. Ni ce na chanchanta da zama a wajen da aka bawa yar talakawa, wadda bata da komai da kowa. Yarima nawa ne ni kadai babu kuma wanda ya isa ya dakatar dani.”
“Har ni?” Tace tana zaro ido cikin mamaki
“Duk wanda yayi kokarin shiga hanya ta, ko waye kuwa, ko da Bubu ne!”
Tsam kilishi tayi a in da take tsaye ta kasa cewa komai. Tana son Laila tamkar yadda take son Kamal,sai da tafi son Kamal ya gaji ubansa akan yadda ita Lailan take so. Sai dai idan taga da gaske Kamal ba zai samu sarautar ba, toh zatayi duk yadda zatayi ta samu Laila ta shiga rayuwar Muhammad din.
Juyawa Lailan tayi cikin takun ta na isa, ta bar dakin. Da kallo Kilishi ta bita ta girgiza kai
“Ba zan taba barin ki da tsarin ki ba har sai na ga da gaske plan dina ba zai yiwu ba, wanda bani da shakku, Kamal shine zai gaji ubansa a ranar da suka shirya bawa dan gatan dan nasu. Maimartaba da kansa zai yi fushi dashi, fushi irin wanda be taba yi ba!”
Dariya ta saki ta koma ta zauna tana harda kafarta, indai tana numfashi Muhammad ba zai taba sarauta ba wannan alkawari ne da tayi wa kanta.
****
A gajiya Bubu ya dawo, shiyasa be samu ganin kowa ba ya shige turakarsa. Tun da wuri Ammi ta shirya tana jiran sa dama,aiko yana dawowa ta tafi dan tana so su karasa maganar da ya fara yi mata ranar basu samu damar gamawa ba
Har ta karaso ta zauna be bar kallon ta ba, babu wani babban chanji akan sanin da yayi mata a dah da nayi yanzu, jikin ta me kyau ne zaka rantse bata ajiye garkamemen saurayi kamar Muhammad din ba.
“Barka da zuwa gimbiya a fad’ar Ahmadu.”
Yayi mata kirarin da ya saba mata tun zamanin kuruciyar su. Dariya tayi ta zauna tana dora tray din da ta shigo dashi a saman table.
“Sannu da zuwa, kun sha gajiya. An rabu da taro lafiya da kowa?”
“Lafiya Alhamdulillah, Takawa yayi matukar kokari sai dai muci Allah ya saka masa da alkhairi.”
“Ai dama yace shine uba, kuma shine kuma kaka, mu yan kallo ne kawai.”
Murmushi Bubu yayi yace
“Gaskiya kam ga zahiri nan mun gani ai.”
“Allah ya basu zaman lafiya, har na matsu su tawo nan wallahi.”
Hannu ya kai saman hancin ta ya lakace mata fuska yace
“Ko kunya, dan farin.”
“Kuma dan auta ba.”
Sai suka saka dariya a tare.
“Allah dai ya basu zaman lafiya da zuria dayyiba, kwanan nan zaki ga yan duguiw duguiw suna yawo a tsakiyar masarautar nan, lokacin na dawo gida nima na huta kamar Aji, kinga sai kawai na dinga kallon su ina jin dadi.”
” Allahu ya sa, Allah ya nuna mana. “
” Amin. ” Yace yana hasaso lokacin idan da rai da lafiya
” Ka gama yanke shawarar nad’in ranar juma’a din? “
” Haka muka tsara da Aji kuma na sanar da Takawa shima yayi na’am da hakan. “
” Kana ganin babu matsala? “
Rik’e ta yayi a jikin sa, yasan me take tsoro take gudu kuma
” Babu komai in sha Allah, babu abinda zai faru. “
” Aikin sa fa? “
” Ajiye shi zai kinga ba zai yiwu a hada ba ai. “
” Amma… “
” Ki tayashi da addu’a har ma dani din ma, idan ban ajiye mulkin nan ba hankali na ba zai taba kwanciya ba. “
” Allah ya nuna mana, Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya. “
” Yawwa ko kefa, addu’ar kenan. “
#Rano๐
*_ZAFAFA BIYAR 2022๐ฅ_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*๐๐
Dโaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*๐๐๐
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*๐๐
09134848107
GIPHY App Key not set. Please check settings