HALIN GIRMA 23

Advertisement

 

Halin Girma

      23

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*******

A hankali ya shiga bin ko ina na jikinta yana aika mata da sakonnin shi, kukan da take na taba shi, yana jin har cikin kansa, sai dai ba zai iya controlling kansa ba, abinda yake ji yafi karfin ikon sa, ba kuma zai iya tsere masa ba.

   Da fari ta dauka babu wani abu da zai mata sai son ganin ya rarrashe ta, amma daga baya sai taga abin yana chanja salo. Jikinta ne ya hau rawa ta ko ina, ta sauya akalar kukan nata zuwa magiya da rokon sa, baya jin ta, idan ma yaji ta baya tunanin zai iya yi mata abinda take so din.

   Juyo ta yayi ta zama a saman sa, ya sake hautsina ta zuwa kasansa , ya ajiye mata dukkan karfin sa, ji tayi kamar numfashin ta na janye wa daga jikin ta, ta dinga jansa tana kuka tana kiran sunan sa, yadda yake kissing dinta kamar mayaunwacin zaki ya sake tsorata ta,shi kansa jikin sa rawa yake,ga wani karfi da yake ji ya zo masa wanda be taba jin irin shi ba. Kayan jikin ta ya shiga janyewa yana wurgi dasu ta kowanne angle, har yayi nasarar rabata da komai. Idanun sa da suka rine sosai ya zuba mata yana kallon ta, wani abu yana kaiwa da komowa a tsakanin wuyansa.

Advertisements

“I’m so sorry.”

Ya furta mata da k’yar kafin ya shiga aiwatar da abinda yayi niyya.

   Sama sama yake jin ta, cikin muryar da ta shige ciki saboda kukan da ta sha,  kamar mafarki haka yake jin abun, juyowa yayi da k’yar ya dune ta, tana kwance agefen sa taci kuka har ta gode Allah. 

“Subhanallah!” 

Ya furta yana tashi, abinda ya faru ya shiga dawo masa akai, ya akayi haka? Bayan yayi ma kansa alkawarin zama so gentle, yadda yasan ba zai bata wahala sosai ba, what has gotten in to him? Me yayi mata?

  Rik’e ta yayi yana kokarin daidaita kansa ya samu damar kwantar mata da hankali

“I’m so sorry dan Allah, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, bansan me ya hau kai na ba, this is not me, bani bane ba.”

Bata da karfin da zata kwaci kanta, sai kawai ta lafe a jikin sa tana jan numfashi. Kanta ya dinga shafawa a hankali a hankali, yana jin wani irin son ta, na saka shigar sa. Idan har abinda kwakwalwar sa ta dawo mata dashi gaskiya ne, toh lallai sai yaci uban Lailah, dole ne yayi mata abinda ko a hanya ta hadu dashi ba zata nuna ta sanshi ba.

  Idonsa a rufe yana tariyo abinda ya faru, tabbas ya ganta a tsaye a kansa, lokacin da baccin da be san na menene ba dauke shi da sauri. Tunanin sa ne ya koma baya, zuwa sanda ya shigo ya tarar da juice akan table din da ake ajiye masa, a gajiya yace amma ya tsaya ya sha daga nan ne ya fara jin wani abu me karfin gask yana taso masa, sai wani irin bacci me nauyi da be taba jin irin sa ba.

“Desire pills?” 

Ya furta yana kokarin tashi, k’ara tayi mara sauti ya tuna tana jikin shi, yayi saurin komawa ya zauna yana sake gyara ta.

” I’m sorry.” 

Ya saka hannu ya goge mata hawayen da suke sauka a fuskar ta. Tsawon minti talatin yana a haka yana tunanin abubuwan da suka faru a daren, tabbas koma menene an shirya masa abu ne, be san ya akayi ya bada kafa ba, har aka yi galaba akansa. Tashi yayi bayan ya gyara mata kwanciya, ya shiga toilet ya gyara jikin sa, sannan ya fito, ya taimaka mata, ta tashi tana ciccijewa sai dai taki yarda su hada ido, ta hade fuska sosai a dole haushin sa take ji, haushi biyu ne suka hadu waje daya, ta kasa manta abinda ya faru farko da na karshen.

  Toilet din ta shiga sai taga ya biyo ta, ta dube shi tana tsaye gaban bathtub din, ta marairaice fuska, yi yayi kamar be ganta ba, ya rufe kofar ya karaso ya durkusa yana taba ruwan.

“Ka fita.” 

Ta fad’a muryar ta babu karfi, banza yayi kamar be ji ta ba, ya ciro towel a cikin jerin sabbin towels din dake jere a cikin wata drawer, sannan ya dauko brush da toothpaste ya saka mata a jiki ya ajiye a gefe ya hau nannade hannun rigar sa. Kamar ta rusa ihu haka taji, ta rasa yadda zatayi ta hanashi, bata ga alamar ma zai hanun ba, sai kawai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, bata san rashin kunyar namiji ta kai haka ba. Sai da ya gama abinda yayi niyya ya tabbatar yayi mata yadda zata ji dadin  jikin ta sannan ya kyale ta ya fito yana jawo mata kofar. 

   Kwanciya ta sake yi a cikin tub din ruwan na ratsa ta, gefe tana tuna abinda ya wakana tsakanin su. Murmushi tayi, duk kalaman sa na dawo mata daki daki, abu daya ne ya tsaya mata har take kokarin alakanta shi da abinda ya faru kafin nan, idan har shi din ba mutumin kirki bane, idan har wani abu ya faru tsakanin sa da Lailah, ba zai sha wahala wajen neman hanya ba.

   Saurin kawar da tunanin tayi kunyar kanta na kamata kamar yana wajen, da wanne idon zata koma wajensu Mamma ma wai tukunna, da wanne idon? Kwankwasa mata kofar yayi ganin ta dade, sai ta tashi tana karfafa jikin ta, ta dauro towel din bayan ta goge jikinta ta fito kanta a k’asa. Ajiyar zuciya taji ya sauke bayan ya kare mata kallo, hankalin sa yaki kwanciya tunanin sa ko yayi mata illa ne, sai yaga akasin haka, be sani ba ko duk cikin dauriyar da ya gane tana da ita bane. Lokacin sallah ake kira a cikin masallacin cikin Masarautar, daga jikin kofar ya tsaya be fita ba, yana kallon ta har ta gama ta saka doguwar jallabiyar sa daya ajiye mata a gefen gadon, murmushi yayi ya fice kansa sanye da farar hula da ake kira da tashi ka fiya naci ya dora doguwar riga irin wadda ya dauko mata.

   A sahun farko ya samu Kamal, daga liman sai shi, hakan ya bashi mamaki amma ya share, bayan an idar suka gaisa a tsattsaye ya fice yana son komawa ya ga halin da take ciki. Sun hadu da Bubu amma be masa magana ba, ya dai ce masa ya sameshi idan garin ya gama wayewa, sai dai yanayin fuskar Bubun ta saka shi tunanin akwai wani abu me girma.

   A saman sallayar ya tarar da ita, ta kwanta akan hannun ta ta mik’ar dashi, karasawa yayi ya daga ta, ya maida ta saman gadon yana zama a gefen ta. Rufe idon ta tayi da sauri jin ya matso da fuskar sa daidai saitin tata. Iska ya fitar me zafi, ya tashi ya kashe wutar dakin ta dawo ya hawo gadon ya kwanta.

“Me ya faru?” 

Yayi mata tambayar kai tsaye, yadda yayi sounding zaka gane daga muryar sa, maganar yake so suyi, shiru tayi bata ce komai ba, dan bata san me zata ce ba, tace masa ta same shi da wata a daki ko me? Ta yaya ma zata fara?

“A lokacin da kika zo dakin part din nan, wani ya shigo? Ko kinga wani a ciki?”

Nan din ma shiru ta sake yi masa, kasan zuciyar ta na ce mata kar ta yarda,kawai zai yi amfani da innocent dinta ne ya nuna mata kamar be san komai, daga gefe kuma wata zuciyar na ce mata ta fad’a masa watakila be sani ba, watakila so ake a hada su, tunda har yanxu bata san komai akan sa ba, ba zata iya dorar da wani abu ba balle har ta iya judging dinsa, kawai dai a matsayin ta na mutum me tunani , tana kyautata masa zato.

   Birkitota yayi da karfi muryar sa na fita da dan karfi akan dazu yace

“Tell me, me ya faru? Wani abu ya faru? Kin samu wata ko wani da kika zo? Wani ya fad’a miki wani abu ne? Me ya faru!”

Kuka ta samu kanta da fashewa da, ya tashi da sauri yana kunna wutar dakin, ya dawo ya tashe ta zaune suna fuskantar juna, zuwa lokacin ya ji yana neman loosing temper dinshi.

“Kalle ni, look at me! Menene? Me ya faru da ban sanshi ba? Tell me, waye yazo?

” Maimartaba ne yazo.”

” Maimartaba!?” Ya furta da dan karfi cikin yanayin dake nuna tsantsar mamakin sa

“Me yazo yi a part dina? Me yace? Me ya faru? Wani abu ne ya faru while i’m sleeping?”

” Eh.” Ta daga masa kai, tsugunawa yayi a wajen yana tattaro dukkan nutsuwar sa, gabansa na faduwa da abinda zata ce dan yasan ba karamin abu bane zai kawo Bubu part din sa.

” Believe me, bansan komai ba, kamar yadda babu alkalami akan me bacci, na rantse miki bansan me ya faru ba.”

Goge fuskar ta, tayi da hancin ta a jikin sa, ta dago tana kallon kasa tace

” Naga wata Laila a nan.” 

Ta nuna wajen da Lailan ta zauna

” Lailah!? “

“Eh.”

“Ehen, sai me?”

“Tana zaune a wajen tana kuka sosai, daga nan sai Maimartaba ya shigo, sannan ya tafi sai kuma wata mata ta shigo ta daga ta suka fita

   Abu ya hadiye me karfi, ya yi kokarin ganin be yi wani abu ba, a hankali yaji kamar ana masa rad’a

_Be calm Moh, be calm.”_

Kamar wanda aka saka abu aka bubbuge ma guiwa haka ya zube a wajen, zai tolerating komai amma banda fushin Bubu, shi za’a wa wannan kazafin? Abinda be taba tunani ko shaawar aikatawa ba, Zina? Shi Muhammad shi aka yiwa wannan sharrin? Saboda yayi kamar be san wani abu yana faruwa ba, shine har aka samu damar yi masa wannan kullin?

  Tana ankare da yadda ya shiga kaduwa, tana kuma ganin yadda Adam apple dinsa ke hawa da sauka tsakanin makogwaron sa, idon sa kadai zaka kalla ka tabbatar da ransa yayi masifar baci.

   Sai da yayi kusan minti goma be ce komai ba, ba dan bashi da abinda zai ce din ba, sai dan yadda mamakin Iman din ya hanashi komai, be zaci haka daga gareta ba, idan wata ce, ba zata iya daukar abinda ta gani ba, har ta tsaya jiran shi, ya ga kokarin ta sosai kuma ya jinjina mata, hakan ya kara mata matsayi a zuciyar sa. 

  Girgiza mata kai yayi yana kama hannun ta

“Kin yarda dani?”

” I don’t know.” Tace tsakanin ta da Allah

“Bansan yadda zan dauki abun na ajiye ba, all I know shine I’m hurt, more than yadda nayi tunanin I ll be.”

Folding hannun nata yayi a cikin nasa ya damke.

“I promise to make everything right, koma menene we will over come it, in sha Allah, together we will build tomorrow, I promise you that!”

Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, ko be ce ba, ko be ba ita zata gano komai, zata gane kafin ma ya gane, tana da kaifin tunani, sannan tana karantar komai kafin tayi judging din mutum. 

   Kwanciya tayi ganin suna zaune kowa da abinda yake tunani, ganin ta kwanta sai ya mike ya fita, ya nufi part din Ammi duk da lokacin garin ke karasa yin haske. Ya san tana zaune har lokacin tana azkar kamar yadda ta saba a ko da yaushe.

   Yadda ta ganshi ya shigo jikin ta, ya bata babu lafiya, katse abinda take tayi ta mike tana kallon sa har ya karaso

“Lafiya Babana?”

“Ina kwana Ammi?” Ya duk’a k’asa ya gaishe ta, kafin ya amsa mata tambayar ta

“Ba lafiya ba Ammi, yarinyar nan Laila tayi abinda zan nuna mata ko ni waye, ganin kamar ban san me take ba ya bata damar aikata abinda ta aikata wanda zai zame mata dana sani, dama chan Ammi kece kike hanani, saboda zumunci amma not anymore.”

“Me ya faru?!” 

“Bubu be sanar dake komai ba?”

“Be ba, me ya faru?”

Iyakar abinda ya sani ya sanar da ita, jikinta yayi sanyi, ta kuma san Bubu zai iya daukar kowanne mataki akan muhammad din, tun da be taba sanin wani abu daya danganci Laila din ba da shi, ita kawai da Muhamamd din ne suka sani sai Kilishi.

“Babu abinda zai faru, kai dai ka rike gaskiya, zatayi halin ta.”

“Shikenan, zanje naga Bubu, zanji me zaice.”

“Allah ya taimaka, zanyi magana dashi nima in sha Allah.”

Fita yayi ita kuma ta zauna a wajen tana hango abinda zai je ya dawo.

Kasancewar safiya ce, shiyasa ya shige kai tsaye wajen Bubun, a lokacin ya fito wajen shashen bayan sallah yana duba wasu littattafan sa. Sai dai yau ya kasa yin komai, tunda aka fito masa da littafan ya kasa taba ko guda daya, balle har ya karanta, abinda ya gani jiya yayi masifar girgiza shi, ya kada shi sosai, har yayi furucin da yake jin idan har Muhammad be wanke kansa a tsawon kwanaki biyar ba, ko da yana da gaskiya ya zama dole ya auri Lailah tun kafin maganar ta fito waje, a jita a ko ina.

    Aji ya samu da maganar a lokacin dan ji yayi yana neman faduwa k’asa, sai dai yadda yayi tunanin maganar zata taba Aji sai yaga akasin haka, yana zaune kem fuskar sa bata chanja ba ko kad’an, har sai da Bubun ya kasa daurewa ya tambayi Aji dalilin da be ji abun ba, murmushi yayi yace.

“Ahmadu kenan, da Muhammad da Laila su dukkan su nawa ne, ni na haifi iyayensu na kuma san kowa a cikin su, na san abinda kowa zai aikata da wanda ba zai aikata ba, duk da yanzu ance baa shaidar mutum, amma ni zan shaidi Muhamamd ko aina ne, lallai akwai wani al’amari bayan abinda kai din ka gani.”

“Amma kuma komai ya nuna, a yadda na ganshi naga Lailan, bani da hujjar kare shi ko yarda dashi, idan har nayi haka sai naga kamar banyi wa Yaya adalci ba, mutane zasu ce ko dan babu shi. “

” Duk abinda zakayi karka tuna mutane dan dama su baa raba su da abin fad’a, kayi gaskiya kawai. “

” Toh ta yaya zan yarda da Muhamamd be aikata ba? Da wacce hujja zan yarda dashi? “

” Ka bashi lokaci, ya kare kansa, idan har ya amsa laifin sa shikenan, idan kuma ya kawo hujja gamsasshiya toh.”

” Idan har muhammad ya kasa kawo hujjar bai aikata abinda ni da mahaifiyar Laila muke tunanin ya aikata ba, nayi alkawarin aura masa ita a tsakanin kwanaki hudu! “

  Dawowa yayi daga tunanin yadda suka kwashe da Aji yayi, ya bata rai sosai sanda Moh ya dire a gabansa, cikin girmamawa ya gaishe shi, amma sai yaki amsawa, ya kausasa murya yace

” Ban kiraka nan dan ka gaishe ni na amsa ba, ban kuma kiraka nan dan muyi doguwar magana ba, me ya faru tsakanin ka da Lailah? “

” Babu komai Bubu. ” Yace kai tsaye dan dama ya riga ya shiryawa tambayar

” Babu komai? “

” Eh babu, duk abinda ka gani sharri ne, bansan komai akai ba. “

” Waye shaidar ka? ” 

” ALLAH! ” 

Ya fad’a kai tsaye, shiru Bubu yayi, ya dauki wani lokaci kafin yace

” Ka dauki alaka ta da kai ta d’a da mahaifi ka ajiye a gefe, ka kalle ni a matsayin alkali da aka kawo min kara ka, na baka nan da kwana hudu ka kawo min kwakkwarar hujja, idan har kwana hudu ya wuce babu komai, nayi maka alkawarin aura maka Laila! “

” Aure?!!! “

” Aure, tashi ka bani waje.”

Jikin sa a sanyaye ya tashi, ya fice cikin sauri sauri ya nufi part din Lailan, yana tafiya yana huci, ji yake kamar ya dauko bindiga ya harbe ta, mutanen da suka fara fitowa wanda suka kasance masu aikace aikace a tsakanin parts din suka hau mamakin ganin Moh a irin lokacin shi kadai babu wani tare dashi. Be same ta a bangaren nata ba, tana bangaren Kilishi,juyawa yayi zuwa bangaren Kilishi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi musu.

     Sai da ya kusa zuwa sai kuma zuciyar sa tace yaje yayi musu me? Yafi karfin haka, ba girman sa bane, dan haka sai kawai ya koma nasa part din yana lissafin kwanaki hudun da Bubu yace, yasan zai iya yin komai ba kuma sai karya alkawarin sa ba, idan kwanakin suka cika bashi da wata hujja. Abu na karshe da zai iya shine auren Lailah, gwara ya hakura da komai akan ya aure ta. 

    Bacci ya sameta tanayi, baccin da yasan na wahala ne, duk tausayin ta ya kamashi, shi da yaso ta huta sosai kafin ta fara sanin komai amma sai gashi daga shigowar ta gidan ta fara da karo da abinda yafi komai muni. Peacefully take baccin,fiye da wanda tayi jiya, a kalla yanzu ta samu kwanciyar hankali bayan ta sanar masa da abinda yake damun ta, yasan tayi dauriya sosai.

   Kissing goshin ta yayi, ya gyara mata kwanciyar ya koma dayan side din ya kwanta da tunanin kwana hudu

Rano

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

HALIN GIRMA 24

Advertisement  Halin Girma       24 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…

HALIN GIRMA 21

Advertisement  Halin Girma       21 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…

HALIN GIRMA 22

Advertisement  Halin Girma       22 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…