Advertisement
Halin Girma
11
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb
_*Mierah’s dukkan_*
Advertisements
_*Mierah’s dukkan_*
_*Mierah’s dukkan_*
_(Palace of exotic scent and more)💯❤️_
_MD: is ur plug! Muna siyarda kaya kala2 kamar jaka da takalmi kamfanin lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers ‘yan yyi dominku da yaranku,Muna order kaya dga kasashe daban-daban,Muna siyarda da kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr suratti,Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria. Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi ku tuntube mu awannan nmbr kamar haka wa.me/07039773001 Muna turawa ko Ina afadin Nigeria da wasu kasashen ketare ngd_
***
A wani yanayi Maman ta dago, gabanta ya fadi ganin Abba a tsaye a kofar Zeenat na rakube a gefe kamar munafuka
“Dr, Sannu da zuwa.”
Advertisements
“Kinsan daga ina yarinyar nan take?”
Ya nuna Zeenat yana jin kamar ya rufe ta da duka.
“Aiken ta ne nan baya gidan Amarya me koko.” Tace bayan tasan ba hakan bane. Kwafa yayi cikin kada Kai yace
“Yaron da nace babu ita babu shi take zuwa suna haduwa a bayan layi, na fad’a miki na kuma bana son yaron domin ba yaron kirki bane, amma a bayan kunnenku.”
“Idan har ta dage ba zata ji magana ta ba, zata dinga fita suna haduwa a wani wajen ba da izini na ba ko na yan uwana, zan sallama masa sai tace ya turo,amma…”
Ya nuna ta da yatsa
“Idan har wani abu ya je ya dawo, kar ku kuka da kowa, ta kuka da kanku!”
Shiru Maman tayi taki cewa komai, haka Zeenat din da ya zaci zata bashi hakuri sai yaji tayi shiru
” Kin amince da Bashir din, kin yarda zaki aure shi?”
Daga kanta tayi da sauri babu kunya ba tsoron Allah, wani irin faduwa gaban Abban yayi, yaji tamkar zai fadi saboda wani jiri da ya nemi zubar dashi, be zaci haka daga gareta ba, sam ba tarbiyyar da yayi wa yaransa bace, sake maimaitawa yayi cikin danne abinda yake ji yace
” Kinji kin gani, kin Amince?”
” Dr ka bar maganar nan idan muka shiga ciki sai mu…” Dakatar da ita yayi da hannu, ya dakawa Zeenat din tsawa
” Ki bani amsa!”
” Eh Abba.” Tace tana nokewa idon ta fes tamkar an soye gyada
” Shikenan, shikenan.” Ya maimaita
” Kice dashi ya turo magabatansa, suzo wajen Yaya.”
Sai ya juya wajen Iman da tayi kamar ta bud’e kasa ta shige saboda kunyar abinda Zeenat din tayi yace
” Kema ki ce masa ya turo dan ba zan bata lokaci ba.”
Daga kanta tayi da sauri, ya wuce su yana jin wani irin tashin hankalin abinda Zeenat din tayi, tabbas laifin Hajara ne, ita ce bata tankwarata ba, bata nuna mata daidai da akasin haka ba, abinda ma ya lura Itace take son abin, ba zai yarda wani abu ya faru ba a dalilin hana ta auren Bashir din, dan yaran yanzu zasu iya komai akan soyayya, shiyasa kawai ya yanke shawarar aura mata shi din idan har ta kafe, da azo ana wallahi tallahi.
Abban na barin wajen itama Iman tayi saurin ficewa dan tasan sarai Mama zata huce akanta, tana juyo fad’an da take wa Zeenat din sama-sama, ta kara sauri ta zagaya ta baya ta shiga ta kitchen ta wuce dakin su kawai.
Tsawon kwanakin Abba bashi da walwala sam, ita kanta Mama ta kasa gane kansa, da ya shigo zai wuce dakin sa kawai sai kuma gobe, a da tayi tunanin fushin ba zai nisa ba, sai taga abin yana neman zarcewa, takanas ta same shi da maganar da ban hakuri amma sai ya share ta yama yi ficewar sa ya barta, haushin hakan ya sakata share shi itama ta san dole zai gama fushin sa ya dawo ko da Anyi auren yaji su kalou zai ajiye komai ya dawo, tasan ta fishi gaskiya shiyasa taki goyon bayan sa, dan tasan zugashi akayi dan an ga Zeenat din zata huta.
***Bayan tafiyar Muhammad basu yi magana da ita ba, sau biyu tana kiran number sa bata samun sa, hakan ya saka ta damu sosai, gashi tasan Abba zai sake mata magana akan abinda yace ta fad’a masan, gashi bata sameshi ba, tsoron ta daya Allah yasa ba guduwa yayi ba, dan har ga Allah zuciyar ta, ta yarda dashi. Har tana jin son sa na shigar ta, koman sa daban ne hatta maganar sa, ta kasa gane komai akansa musamman a fagen da zata ajiye shi, yanayin sa da koman sa yasha banban da shigar sa, tana bukatar sanin sa sosai kila ko bayan sunzo da iyayen sa an daidaita, a lokacin zata bijiro masa da tambaya akan sa, ko da ba komai ba, a kalla ya bata labarin wani abu da ya shafe shi.
Fitowa tayi falo ta zauna bayan ta gyarawa Gaji daki, maman su Maryam ce ta shigo, ta gaishe ta tana tashi ta kira mata Gaji, tare suka dawo da Gajin ta gaishe ta sannan suka soma hira akan abubuwa da dama. Ita dai Iman na zaune tana jin su tana duba wayar ta. Maganar Maryam suka shiga ya sakata d’agowa tace
“Umma Ya Maryam din ce bata da lafiya?”
“Wallahi Iman, wai har kwananta uku a asibiti amma basu fadawa kowa ba, bari tayi an sallameta dazu amma, shine nake tunanin wanda zai je mata ya dan taimaka mata ko na sati daya ne.”
“Allah sarki, Allah ya kara sauki.”
” Ko ke zaki je ne takwara?”
“Toh…” Tace har cikin ranta bata so ba
” Iman bata son mutane ai, zata iya zuwa kuwa? Maman su Maryam din tace tana murmushi
“Idan ta kamata ya zatayi?” Gaji tace
“Wai kar a takura ta dama.”
“Haba kinji wani zance, yar uwarta ce fa? Idan batayi mata ba wa zatayi wa?”
“Haka ne.”
“Zance Umma, ba komai ai.”
“Toh shikenan, anjima sai wani cikin samarin ya mik’a ki.”
“Ai ba sai anjima ba, yanzu zata shirya sai su wuce, ki shiga sai ki sanar da Maman tasu, idan yaso sai ta fadawa Ibrahim din duk da nasan babu abinda zaice.”
“Toh shikenan bari na shiga wajen nasu.” Ta tashi ta fita,ita kuma Iman ta wuce ciki ta dauko charger ta tazo ta fita.
A zaune ta tarar da Umman suna maganar da Mama, tana shiga tace
“Ki shirya zaki je gidan Maryam kiyi kwana biyu, Allah ya kara sauki.”
“Toh.” Tace ta wuce ciki, ta dauki wata karamar Jakarta, ta saka kayanta kala biyu sai undies da hisnul muslim, da dan abinda tasan zata bukata ta fito, bata ga su Maman a falo ba, sai ta nufi dakin ta rataye da jakar a kafadarta, ta kwankwasa kafin ta shiga
“Mama na fito.” Tace daga kofa, jakar ta dake kan gado ta dauko ta ciro dubu daya ta mik’a mata
“Sai kin dawo.”
Hannu biyu tasa ta karba mamaki na kamata, tayi godiya ta fito still tana jin kamar mafarki, magana me dadi daga Mama har da bata kudi? Akan me? Sam sai taji hankalin ta be kwanta ba, taji kamar ta koma ta tambaye ta dalilin action dinta amma babu hali.
Ita kadai ta dinga juya dubun har suka isa gidan Maryam din, ta fito rik’e da jakar ta shiga gidan. A falo ta tarar da ita da mijinta sai sister dinshi wata babba haka. Wani farin ciki ne ta gani a fuskar maryam din, ta tashi zaune tana mata sannu da zuwa.
Gaishe su ta fara yi suka amsa dukka sannan ta nufi wajen Maryam din tana mata ya jiki,
“D-D bari naje na kai Yaya gida tunda ga Maryam tazo.”
“Ok tam.” Tace
“Nagode sosai Anty Saliha, ku gaida gida.”
“Gida zaiji Maryam, Allah ya kara sauki ki kula da kanki sosai kinji? Ki dinga cin abinci sosai saboda kiyi saurin dawowa dai, Allah ya kawo wani rabo me albarka.”
” In Sha Allah zanci, nagode.” Tace a kunyace, sukayi sallama suka fita
” Sa mana key din a kofar.”
Tace wa Maryam din tana gyara zaman ta. Key din Maryam ta saka musu ta dawo ta zauna kusa da ita
“Ashe ke zaki zo, naji dadi da ba’a turo wata cikin yaran chan ba wallahi.”
“Wallahi, ya jikin naki? Naga kinyi fari sosai.”
” Toh ba dole ba, kin ga uban wahalar da nasha kuwa? Kai Iman aure- aure akwai wahala wallahi.”
” Sannu, Allah ya kara sauki.”
” Amin ya Allah.”
” Ya gida yasu Mama, Gaji da kowa da kowa?”
” Kowa lafiya lou, duk suna gaishe shi.”
” Ina amsawa, amma zasu zo su dubani ai ko?”
” Eh toh nasan zasu zo, dan baki ga ma fad’an da Umman tayi ba, kwana uku a asibiti baku fad’a ba.”
” Ina na sane, hankali na baya jikina, laifin D-D ne, shi ne be fad’a ba wallah. Anty Saliha ma baki ga fad’an da tayi ba.”
” Ai dole, wani abun kana bukatar Babba kusa da kai.”
“Aikuwa.”
” Allah ya kara sauki ya kiyaye gaba.”
” Amin addu’ar kenan.”
” Sai naji labari kuma, Ashe su Abba sun fara maganar ku, Umma tace min ma ke kamar su abba sun gama bincike akan shi har ma sun tabbatar da shi din zasu bawa, Umma tace bata taba ganin Abba ya damu da wani a cikin masu zuwa neman yayan gidan ba kamar yadda ya damu da wannan din, ko dai wani Babban kika samo mana ko wani basarake?”
Tace cikin zolaya
” Kai Ya Maryam, bafa kowa bane hasalima dai ba wani me kudi bane kawai dai inaga ko Abba ya gamsu da halayen sa ne.”
” Eh toh haka ma Umma tace, nima tsokanar ki nake, ke yanzu ka samu miji na gari me son ka me son farin cikin ka shine, ba yalwar arziki ba, da wani arzikin gwara rufin asiri.”
” Haka ne.”
” Allah ya kaimu lokavin, musha biki.”
Dariya tayi kawai dan ita jikinta a sanyaye yake da rashin jin sa har tsawon kwanaki hudu, ta damu sosai sosai har ta kan zauna tayi ta tuna moments din da sukayi tare, wani lokacin tayi murmushi ita kadai wani lokacin kuma ta ji kunya ta kamata.
_”I love you.”_ Kalmar da yadda ya fade ta take ta tunawa, har yadda lips dinsa suka hade waje daya yayin da yake furtawa, cikin muryar da take yawan yi mata amsa kuwwa a cikin kunnenta
“Dan Allah dafa min danwake, shi kawai nake sha’awa baki na babu dadi wallahi.”
Maryam ta katse mata tunanin da take, ajiye wayar ta tayi a gefen Maryam din, ta tashi zuwa kitchen din, minti kad’an ta leko
“Toh ai bansan Ina kayan naki suke ba.”
Tasowa Maryam din tayi, tazo ta dauko nata komai ta nuna mata sauran sannan ta dawo falon ta jona wa Iman din wayar ta a charge kusa da ita ta kunna tv ta koma ta zauna tana kalla, jefi jefi tana yiwa Iman din hira daga nan.
Wayar Iman din ce tai kara, alamar shigowar kira, tana daga kitchen din amma sai da ta ji gabanta ya fadi, saboda tsabar jiran kiransa har ringing tone ta chanja masa nashi shi kadai saboda da ya kira yadda zata fi saurin ganewa,
“Ana kiran ki Iman.” Maryam tace tana jawo wayar ta kalli screen din
“M ne yake kira, M M M waye Ma? Sirikin nawa?”
Tace tana murmushi, maimakon Iman din ta fito ta karba sai kawai ta cigaba da aikinta tana jin Maryam din na mata sababin zata katse, kamar ba kiran da take jira bane, amma kuma a kalla yanzu hankalin ta ya kwanta, tasan cewa da gaske be manta da ita ba. Sake kira akayi karo na biyu,
“Bana son wulakanci Iman, bari na daga kizo ki karba.”
Dagawa tayi ta saka a kunne
“Sweetheart.”
Ya furta cikin rada yana sauke ajiyar zuciya, da sauri Maryam tayi gyara murya tana cire wayar kafin ta mayar tace
“Yayarta ce maryam, tana kitchen ne.”
“Anty Maryam, Ina wuni?”
“Lafiya lou wallahi, ya aiki?”
“Alhamdulillah.”
“Dama tana kitchen ne, amma yanzu zata zo zata kira.”
“Owk nagode sosai.”
“Nima Nagode.” Ta katse kiran tana tashi, zuwa tayi kitchen din da daddage da d’aka mata duka a baya
“Dan wulakanci kina ji yana kira ko? Wannan irin hot guy din ba’a musu jan aji wallahi, kinji kuwa? Haka yake kashe ki da soyayya? Hmmm lallai yau ga wanda yafi D-D na.”
Banza Maryam din tayi mata tana murmushi, ta karbi wayar ta ajiye a gefe ta karasa kwashe danwaken ta zuba a flask ta zuba ruwan zafi akai ta rufe, ta soya man ta hada komai a babban tray ta dora Maryam din na tsaya a akanta tana mata hirar Moh din ita a dole sai taji wani abu daga iman din amma tayi mata fumfurus
“Mara lafiya ba’a cika son shi da yawan magana ba, muje na kai miki abincin falo.”
Dukan ta kara kai mata ta goce tana dariya, suka jero Maryam din na rik’e da bottle water ta ajiye mata komai a falon ta zuba mata sannan ta dauki jakarta tace
“Ina ne dakin?”
Da baki Maryam din ta nuna mata lokacin ta cika bakin ta da dan wake. Dakin ta nufa ta shige ta rufo kofa sannan ta cire hijab dinta ta ajiye a agefen gadon ta zauna tana kallon wayar, kunya da nauyin kiran sa take amma kuma tana bukatar kiran nasa, tayi missing dinsa da muryar sa gaba daya. Kiran nasa tayi tana tashi tsaye lokacin da ta soma ringing, be daga ba, amma kuma tana katsewa ya biyo kiran a take.
“Assalamu alaikum.” Tayi sallama wayar a hannun ta bata saka a kunne ba
“Wa alaykisalam.”
Ya amsa sai yayi shiru, itama shirun tayi tana saka abinda zata ce
“Shine baka kirani ba?” Ta samu kanta da fad’a ba tare da tayi tunani ba. Abinda dama yake son ji kenan, tayi missing dinsa in dai har tayi korafi akan rashin kiran, murmushi yayi wanda taji sautin sa ta cikin wayar
“Kinyi kewa ta kenan ko?”
“Um um.” Tace da sauri
“Kawai dai na kikkiraka bata shiga, kuma Abba ya bani sako shine kawai dama.”
“Ohh, sakon Abba ne yasa kika kira ni ba don kinyi kewa ta ba?”
Shiru tayi dan a zahirin gaskiya ba hakan bane, tana bukatar ji daga gareshi, tana bukatar comforting words dinsa, tana bukatar shi kawai ma in short.
“Ni kuma kinga nayi kewar ki, sosai sosai komai ma da nake anan din yinsa kawai nake ba don naso ba, kiyi hakuri kin kirani, ina wajen da dole na kashe waya, shiyasa har kika jini shiru haka.”
“Ok.” Tace a ba tare da tasan me zata ce ba
“Ya gida ya kowa da kowa?”
“Alhamdulillah, yasu Ammi? Ka samesu lafiya?”
“Lafiya lou, banje gida ba, yau nake shirin zuwa in sha Allah.”
“Ok tam, karka manta ka gaishe ta.”
“Ba zan manta ba, zance mata sirikarta na gaishe ta, zan kira sai na bata kuyi magana.”
” Um um ba zan iya ba.”
” Kunyar ta kike ji? Irin kunyar surkutan nan ko?” Ya kyalkyale da dariya
” Ni dai bance ba.”
” Ni kuma nace.”
” Uhum.”
” Wacece Maryam?”
” Yayata ce da akayi bikin su, nazo gidan ta bata da lafiya zan kwana biyu na dan taimaka mata.”
” Owk ayya, ki duba ta, Allah ya bata lafiya.”
” Amin zataji.”
” Baki fad’a min ba, me Abbanmu yace?”
” Na zata ba zaka tambaya ba ai?”
” Na isa? Ina sane kawai dai.”
” Dama cewa yayi, a turo.”
” Me!!! Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah! Kina nufin Abba yace na turo magabatana ayi magana? Kenan Abba ya yarda ya bani ke? Kai mAsha Allah, Alhamdulillah.”
” Wannan murnar haka.” Tace cikin mamaki
” Ba zaki gane ba, ba zaki gane ba Zahraah, Nagode sosai, Allah ya sakawa da Abba da alkhairi. Nagode nagode, wannan ranar ta shiga cikin ranaku masu matukar muhimmanci a tare dani, Alhamdulillah.”
” Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”
” Amin Zahra nah, Amin Amin. Bari kiga na tashi, banga ta zama ba a yau zanje na same su da maganar, in sha Allah a kwana daya zuwa biyu magabatana zasu zo, ayi komai a gama, Allah yasa Abba ya saka mana lokacin kankani, bansan irin farin cikin da zan ba, Alhamdulillah.”
” Uhum.” Tace dadi na kamata, a kalla ta samu wani da yake son ta sosai, irin soyayyar da ta rasa tun tana yar kankanuwar ta.
” Zan kiraki anjima, ki kula da kanki.”
” In Sha Allah. Ba-bye.”
Fadawa tayi saman gadon tana jin farin ciki matsananci
” Ya Allah ka sa ya zama alkhairi a rayuwa ta, Allah ka tabbatar mana da alkhairi.”
Ta furta tana jin kamar bata da saurin bakin ciki.
***Da karfin sa da kwarin guiwar sa ya isa masarautar su, wannan karon shigar da yasan Bubu yafi so yayi, shigar Manyan kaya da rawani, yayi masifar kyau ya fito a basaraken sa na ainihi, duk wanda yaci karo dasu sai sun kalle shi sun sake kallon sa, kai tsaye bangaren Aji ya nufa, domin wanchan karon be samu ganin Hajjan sa ba, shiyasa ya fara tachan dan tasan sai tayi korafi. Tana ganin shi kuwa ta hau murna, ta rasa in da zata sakashi, mace ce me jin mulki sosai domin mulkin a jinin ta yake dan har tafi Aji, amma kuma a duk abinda ya hada da muhammad bata hada shi da komai da kowa, da kanta take masa komai duk abinda yake so kuma shi take so ko da kuwa kowa ba zai goyi bayan sa ba.
Sai da ya gama mata shagwabar sa son ransa sannan ya gabatar mata maganar auren da yake so aje a nemar masa, murna a wajen ta kamar ta dauke shi ta goye haka taji, karshe ta dinga tsokanar sa da sauran idan amaryar tazo ya manta da ita, da tsohuwar zuma dai ake magani. Da haka ya wuce fada in da yasan zai samu Bubu wanda tuni labari ya riga ya kai masa, ya shirya yana dakon karasowar Muhammad din. Ganin sa ya saka Bubun farin ciki, musamman da ya ganshi cikin shiga irin ta gidan sarauta!
***Abba na zaune ya gama karatun alkur’ani me girma Maman ta shigo, ta zauna a gefen sa yayi kamar be ganta ba
“Dr wai fushin ne har yanzu? Be kamata ace abu irin wannan ya bata maka rai ba, yara hakuri ake dasu.”
Daga mata hannu yayi
“Bana son maganar nan, idan har ba zaki iya tankwara yarki ba, kuma ba zaki nuna mata dai-dai ba, shikenan, abinda kuke so kuka zaba zanyi muku.”
“Allah ya huci zuciyar ka, da anyi auren ma.in sha Allah zaka sauko, musamman idan kaga zaman nasu lafiya lou.”
“Allah ya taimaka.” Yace yana kokarin mikewa
“Dama magana nazo muyi, gida zanje.”
“Allah ya tsare hanya, ya kiyaya” yace kawai cikjn halin ko in kula
“Kwana uku zuwa sati nake son yi.”
“Duk yadda kika ga yayi miki.” Ya karasa ficewa. Kwafa tayi ta mike tana jin haushin sa. Ko me zaiyi ba zata hana Zeenat abinda take so ba, an wuce zamanin auren dole. Zai gaji dan kansa ya sakko.
GIPHY App Key not set. Please check settings