MATAR UBA 37

Advertisement

 πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

     *MATAR UBA*

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

Advertisements

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

CHAPTER 37

πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š

Mc yace “To Allah Yasa lafiya,tunda Wanda ake taron don su sun watse ina ganin ai gara mu tashi muma,kashe kid’an akayi sai surutai kake ji kowa na fad’an Albarkacin bakin sa.

Sunyi sa’a su Hashim Basu tafi ba,babu Wanda ya tsaya magana suka lodo a mota, hashim ke jaan motar, a guje ya fizgi motar suka bar haraban hall d’in.

Advertisements

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

………….”farees yanzu shi Alhaji khamal d’in ne yace maka haka?” 

“Eh wallahi yace min ya Kira ka baka d’aga ba,ya Kira number faysal da Asiyah duk baku d’auka ba,sai ya Kira ni, ya fad’a min Wannan mumunar Labarin”

Hashim yace “Yanzu yana ina?”

“Yana gida don yace min har sun shirya wajen zuwa dinner d’in,sai aka kirashi aka Sanar dashi”

Asiyah tace “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un Shikenan mun mutu”

Hashim yace “Asiyah ki kwantar da hankalin babu abinda zai same mu kinji”

Kai tsaye gidan su Yesmin sukayi, da sauri suka fito Kai tsaye suka shiga cikin gidan, Khamal da Nana sai Aunty Rukayya suna tsaye sai safa da marwa suke, suna ganin sun shigo a tare sukace “Alhamdulillah dukkan ku Kuna Nan ko?”

Murya na rawa Safiyya Tace “Yanzu da gaske mummy ta gudu?”

Nana tace “Eh bata asibiti Kuma an nema ta ba a ganta ba,Ashe tun da safe ta bar asibitin”

Diyya Tace “Amma ta yaya? How comes ta gudu,me polisawan sukeyi har suka Bari ta gudu”

Khamal yace “Tayi outsmarting d’in su ne ta samu ta gudu sanan ta rubuta wannan wasikar ta ajiye”

Hashim ne yayi saurin sa hannu ta karb’a, ya Fara karanta shi a bayyane kamar haka.

“Na fad’a Muku babu Wanda zai iya kamani, Kun d’auka wasa nake ko to gashi na fito,Kuma yanzu Haka ina farautar ku, Nana daga kanki zan fara yanda Kika ci amanata Sai na kwakule Miki Ido na cinye,ke Kuma Rukayya Sai na yanka ki gunduwa gunduwa har ki mutu, Safiyya ke ‘yatace Kuma gudan jina nace kisa a ranki cewar maza goma zan d’auki hayar su,su Miki fyad’e har sai kin mutu, faysal da farees naku Mai sauki ne Zan sa a kashe min kune kawaii sabida laifin naku Mai saukine, Yesmin ke Kuma hukunci ki shine a gaban idon ki Zan sa a kashe min iyayen ki, Hashim  Kai Kuma da Asiyah hmm bazan fad’a ba sai dai mun had’u daga yau zuwa gobe duk Zaku kwana a makabarta.”

Hashim yace “Wannan ai shirmen banza ce babu abinda zata iyayi,Kuma insha Allah sai an Kama ta” ya nufi hanyar fita khamal ya tare shi ya nuna Masa wuri Zama ma’ana ka zauna,zama yayi Yana huci dukkanin su hankalin su yayi matukar  tashi, Asiyah tunda aka karanta wasikar idanun ta suka bushe ta kasa kukan ma gaba ki d’aya.

Fadeelah sai kiran Hashim take, ganin  yanda ta damu ya koma gefe ya mata bayani Kuma ta fahimta sannan yace ta bawa mutanen da suka tara hakuri hakan kuwa akayi.

WASHE GARI

………. A zaune suka kwana duk cikin su Babu Wanda ya rintsa, sai sallar asuba ne kad’ai ta tada su bayan sun idar suka dawo suka zauna, Yan matan ne suka samu suka lallab’a suka had’o musu tea suka sa cikin su,don duk cikin su babu wanda zai iya cin abincin.

Wai shin ina Baraka??

……. Baraka tunda ta baro asibitin, Kai tsaye gidan ta, ta nufa a zaton ta zata ga Asiyah da Safiyya, dariyar mugunta tayi tace “Yan iska Ashe dai Kuna tsoro na, da ku zauna a gidan Mana kuga yanda zanyi daku”

‘dakinta ta shiga ta ‘debo makudan Kud’i ta fito waje, ta Mika wa mai gadi wasu bandir biyu Tace “kaje na sallme ka”

Zaiyi magana ta daka Masa tsawa, “ka fice min a gida”

Jiki na rawa ya fita ko kayan sa bai d’auka ba, a gidan nata ta kwana duk da cewar ita ma ta kasa baccin ga kafarta da yake ta zogi karaya tafi wata ‘daya amma yaki warkewa, da asuba ta fita, ta tari Keke napep sai da suka bar cikin gari ta umurce shi da ya tsaya, Kud’i Mai yawa ta Mika mishi, tana d’ingisawa har ta Shiga jeji, ta d’auki tsawon Mintuna talatin Kan ta nufi wata karamar bukka irin gaisuwar su ta matsafa ta Masa, ya amsa bayan ta zauna ta juye masa dukkanin kud’ad’en da suke cikin Jakar da ta ratayo,wata iriyar dariya yayi, yace “me kike bukata ayi miki?”

Nan ta kwashe cin amanar da akayi mata ta fad’a Masa ya girgiza kai yace

“Na ji matsalar ki idan na fahimce ki fansa Kika son d’auka ko?”

“Eh fansa nake so,mafi munin fansa”

Ya kyalkyale da Dariya Mai tsoratar wa yace an gama,wasu gari kulli biyu ya Mika mata yace wannan, ki yi wanna dashi wannan Kuma ki watsa musu a jikin su idan suka Shaka Shikenan kin gama dasu”

Murmushi tayi tace “Nagode Nagode”

Tsawa ya daka mata yace “Kin San bana son godiya idan kina so ki gode min kin sab irin godiyar da nake so”

Murmushi tayi tace “Hakane barin shuga daga ciki” 

Cikin bukar ta shiga ta tub’e tsirara haihuwar ta ta kwanta a Kan Yar karamar gadon dake d’akin,boka na shiga dake dama zani kawaii ya d’aura ya kwance ya fad’a mata, Baraka duk da bata jin dad’in abun Amma ta dage wajen bashin had’in kai  a tunanin ta idan yaji dad’in ta aikin zaifi tasiri.

Ya d’auki tsawon awa d’aya Yana Abu d’aya idan ya gaji sai ya huta ya Kuma d’aura daga inda ya tsaya,ya samu na banza ai Dole, sai dai ya gamsu sannan ya kyale ta, kayanta ta Maida ta tashin ta fita, tunda ta hau Kan titi Bata samu abin Hawa ba tayi tafiyar awa d’aya har ta Fara shiga cikin gari wani Keke napep ta hanga tana Masa magana baiji ba, dake yana ta gefen Titin ne ganin in bata karasa  gunsa ba zai iya tafiya, da saurin ta hau Kan titi bata lura ba Ashe akwai babban Mota Daf irin Wanda ake da shanu a cikin yayi kanta jaan kafarta take amma ina har motar yayi kanta ,Mai motar yayi kokarin kacewa amma ya kasa.

Ihu take tana neman agaji Amma babu mai taimakon ta ganin ihun bazai anfane ta da komai ba ta fara ambaton “La’ila ha illahu, Muhammadar rasul…….” Sai karsa passs kamar an fasa ledan pure water, Motar kanta yabi sannan wannan karar,karar fashewan Kan Baraka ne.

Mai motar kuwa ganin babu wanda ya ganshi yasa Kai sai ma kara gudu yayi bai tsaya ba, mutanen da suke fita suna Shiga gari ne suka taru akan ta ana neman mafita ta yanda za a samu Yan uwanta,wani mutumi ne yasa hannu a jakar ta ya d’auko wayar ta anyi sa’a babu password a wayar ,Ya Shiga bin cike, last call d’in ta My Daughter ya gani yayi dialling yaji ba Kati sai ya sa number a wayar sa duka biyu ta d’auka yace “Akwai wata mata da ta yi hatsari” ya kwatanta mata inda akayi hatsariin mikewa tayi ta tsaya tace “Ya kamannin matar yake?”

“Ai bazaiyu na kwatanta miki ba,sabida fuskar ta duk ya dagargaje, hatta jikin ta duk a manne yake da kwalta sai an kankare namarta”

Katse wayar tayi takwala ihu, tana amabaton suna Allah,da gudu su Hashim suka Shiga d’akin da suke suna tambayar su Mai ya Faru, Asiyah m, Diyya da Yesmin Basu amsar tambayar sabida su Kan su Basu San dalilin kukan nata ba, cikin muryar kuka take cewa “Shikenan Shikenan ta mutu mamana ta mutu”

A tare suka ce “A ina?”

Ta musu kwatancen inda aka fad’a mata ,Basu tsaya ‘bata lokaci ba,suka Shiga mota suka nufi inda akayi hatsariin tun daga nesa suke hango taron mutane,hakanne ya tabbatar musu da a gun akayi hatsariin.

Safiyya Ce ta fara fita da gudu ta ture mutanen dake kawaye da gun, tana ganin gawar duk da bata iya ganin fuskar ta Amma ta shaida kayan jikinta ta da zoben da ke hannun gawar ta Baraka ce ihu take tana Kiran “wayyo Mummy, Mummy Kinga abinda Kika jawo wa kanki,kin cuci Kanki kin cuce ni,wayyo ina Zan sa kaina bani da uwa bani da uba.”

Duk Wanda suke gun sun tausaya mata, Nana da Safiyya, Diyya da Asiya da Kuma Yesmin duk Saida suka yi kuka sabida mutuwar Baraka yin Allah ne sannnan ta mutu a wulakance Dole a tausaya mata.

Da kyar a ka d’aga Safiyya a ka zaunar da ita a mota, Asiya ce ta zauna tana rarrashin ta, ambulance aka Kira suka Zo suka kankari gawar dole suka bar sauran naman da suka makale a Kan kwalta.

Ba amfanin Kai ta asibiti don hakaw a tsakar gidan ta aka ajiye musu gawar, ruwa aka yayyafa mata sabida bazaiyu a mata wanka ba, kwakwata Hashim, khamal, farees da Faysal sai Kuma mutum biyu da suka Zo da ambulance d’inne suka sallace ta,duk Yan unguwar da zaran sunji itace ta mutu sai su tir da halin ta da yi mataw fatan Allah Kara mata azabar kabari,bayan sun sallace aka kaita makabarta, Shikenan su Baraka an tafi sai munzo. Wata shari’ar sai a lahira.

Allah ubangiji kasa muyi kyakkyawar karshe ameen.

Safiyya ta dad’e tana jimamin uwa uwace ko da ace a bola take kwana, dole Safiyya taji zafin mutuwar mahaifiyar ta, Asiyah da Safiyya sun Zama marayu gaba da baya.

Bayan Watanni Biyu

Safiyya da Asiyah sun Kika tamkar Khamal da Nana ne suka haife su duk abinda suke so ake yi musu,duk kadarorin da Baraka ta bari duk aka Saida aka sa musu Kud’in a account, Hashim da Diyya Kuma sun tare a gidan su da ya gina musu flats biyu ne komai iri d’aya.

A tare suka yi paper,sannan sukayi jamb duk su ukun suka samu admission Gombe State University.

A yaune aka d’aura auren

Asiyah da Hashim

Yesmin da Faisal

Safiyya da Farees

Allah ya basu zaman lafiya ameen.

Bayan an d’aura aure khamal ya koma zariya dashi da matar sa don gudun karta Kara afkawa kuskuren da tayi a baya.

Karshen MATAR UBA

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah

A yaune na kawo karshen labarin MATAR UBA,Wanda labarin ya farune dagaske,duk da cewar na Kara wasu abubuwan Kuma na rage wasu,don ya Nishadantar daku,wannan labarin izinace ga mata masu mugun hali irin na Baraka,kunji yanda tayi mugun karshe.

Ya Allah Ina rokon ka, duk abinda na fad’a dai dai ka bani Ladar sa idan Kuma nayi kuskure Ya Allah ya yafe mana gaba ki d’aya.

Ina rokon Allah ya yafe min dukkan kurakuran da nai a wannan labarin nawa na *MATAR UBA*

Ina rokon Allah da ya isar min da sakona inda nake da bukatar ya isa dan *MATAN UBA* su fahimci illar kishi da Kuma son zuciya

Fadeelah Yakub (Milhaart) ke muku fatan Alkairi.

Ubangiji Allah ya gyara zukatan mu da aikata khairan.

Mu had’u a littafina na gaba Mai suna DANGIN UBANA,yazo Muku da sallo na daban Ku kasance tare dani Kar ku bari a baku Labari.

Taku a kullum Milhat ✍️

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MATAR UBA 2

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦        _(A True Life Story_ )…

MATAR UBA 35

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*  …

MATAR UBA 13

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA* 🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ  _(‘Kungiya d’aya tamkar da…

MATAR UBA 1

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦              *MATAR UBA*  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦        _(A True Life Story_…

MATAR UBA 18

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦      *MATAR UBA* πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Daga Alkalamin ✍️               *Milly*  …

MATAR UBA 5

Advertisement  πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦           *MATAR UBA*   _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________ *MATAR UBA*  Labarine…