SULTAAN 2

Advertisement

 

👑 *S U L T A A N*

Mss Flower🌸

*FITATTU HUƊU🔥*

Advertisements

_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_

*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

           *02*

Advertisements

Zai tarwatsa musu ahalinsu. Hadarin da ke ta haɗuwa ne ya yi baƙiƙirin ga samaniya ta fara rugugi ya saka shi hanzarin miƙewa yana cewa “bari zan je na taho da Amma, da Abbu”

Ko kafin ya isa gidan uban gidan nasu wanda tazarar ba ta fi minti uku ba an kece da ruwan sama tamkar an karkata bakin kogi, da hanzarinsa ya ƙarasa gidan yana tsoron ka da ruwan ya sauka jikin Ammansa don sosai take fama da ciwon sanyi (pneumonia). Turus ya yi ganin mahaifin nasa da amininsa mahaifin nasa wanda shima ya kasance bawa ne suna faskaren itace, yanda ruwa ke sauka kamar da bakin ƙwarya ba lallai ba ne ma ka iya buɗe idonka na minti biyar tsaye a ciki ba, amma sarar iccen suke ruwa na dukansu, da hanzari ya ƙarasa tare da janye su suka samu wajen fakewa, bai ce da su ƙala ba ya koma cikin ruwan ya ɗauki gatarin ya shiga faskare, yana cikin faskaren idonsa ya sauka kan Ubangidansu da ke tsaye cikin harabar ɗakinsa ya harɗe hannu a ƙirji yana dubansa, inkiya ya yi mai da hannu alamun ya je hakan ya saka ya ajiye gatarin ya nufi wajen, ko kafin ya isa ya shige ciki. Tsane kayansa ya yi ya shiga bakinsa ɗauke da sallama 

“Wa ya ba ka izinin karɓar aikin da ba a saka ba?” Cewar Ubangidansa cike da gadara. 

Bai ɗago kansa ba, bai kuma ce ƙala ba, hakan ya kuma harzuƙa Uban gidan nasu ya ce “ba da kai nake magana ba!” 

Amma da ke shayar da yaronsu ɗan kimanin shekara ɗaya da wata shida nono ta yi maza ta ce “Ka amsa masa”, jin muryar Ammansa ne ya sanya ya ɗan ɗago kansa fuskarsa har ta yi ja alamun ransa ya ɓaci, “Afuwan” ya furta cikin muryarsa da ko da yaushe in ya yi magana tamkar an masa dole. 

“Ka bari zan ji da shi” cewar Uwargidan idanunta kan Sultaan da kansa ke ƙasa. 

Gyaɗa kai ya yi ya miƙe ya shige ɗaki. Cikin kallon ƙasƙanci ta dubi Amma ta ce “kar na ji kukan Na’im, idan ya yi kuka kema ki kuka da kanki” ta ce tana yamutsa fuska tamkar wadda ta ga kashi, maida dubanta ta yi ga Sultaan ta ce “biyo ni” 

Kwance ya taddata kan makeken gadonta ta cire rigar da ta suturta jikinta sai ta ciki, wani irin shu’umin kallo take bin sa da shi kafin ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce “me ya sa kake da taurin kai Sultaan, gasar _Lelu_ ta kusa ga shi kasawa ta bayyana ƙarara tare da mahaifinka, ba za ka so ka ceto ahalinka ba daga tarwatsewa da ƙangin bautar da ya fi na yau?”

A hankali ya ɗago kansa ya zuba mata shanyayyun idanunsa masu kama da yana jin bacci, karo na farko da ya yi mata kallon tsaf, shekarunta zasu haura na sa da a ƙalla ashirin, amma tun lokacin da girma ya fara kama shi ta saka masa ƙahon zuƙa. 

Nadiya ta lumshe idonta tare da kauda kanta daga dubansa, zuciyarta ta tsananta bugawa tamkar za ta faɗo, wani irin so take masa tun yana ƙarami, ta nuna masa a ɓoye har ta bayyana a fili amma a kodayaushe nunawa yake bai fahimci inda ta dosa ba, yaron wani fitinannen taurin kai gare shi, ga izzar masifa kamar ba bawansu ba, ga shi da kafiya tamkar antaru. Saukowa ta yi daga gadon cikin kwarkwasa ta iso wajensa tare da dafa kafaɗarsa ta ce “a karo na ƙarshe zan kuma ba ka dama, ka amince da ni, na tseratar da ku a ranar _Lelu_ ka bijire min kuma sai na tabbatar da na jefa ka a halaka, wanne zaɓinka, yi nazari cikin daƙiƙa biyu” ta ce tana hura masa iskar bakinta a fuskarsa sannan ta wuce ta zauna a gado tana kallonsa, zuciyarta cike da kwaɗayin matashin mai kwarjini da tsananin kyawu. 

Cikin takun ƙasaita ya ƙarasa har inda take, ido cikin ido a karon farko ya dubeta ya saki ɗan murmushin gefen baki, har zai yi magana sai ya fasa ya cije jajayen leɓensa murmushin bai yanke ba ya fice. 

Amma na ganinsa ta miƙe tana cewa “murmushin me kake Sultaan?” A tsorace, ta sani sarai murmushi ko dariyarsa sai in ta yi mugun ɓaci

Girgiza kai ya yi, ya amshi yaron hannunta da ke bacci ya maida shi wajen mahaifiyarsa sannan ya fito ya ja hannunta, sai da ya ƙarasa faskaren don ruwan sun ɗan tsagaita sannan ya ja hannun mahaifan nasa suka wuce. Bayan sun isa gida sun yi sallah, rumfar gashi ya nufa ya shiga aikin naman da ya kamo sannan ya ɗaure bayan ya gama ya sagala kan wuta. 

Zaune ya tadda iyayensa kan tabarma cikin ɗakinsu, Halime na gefe idanunta sun yi ja, kallo guda ya yi musu wani irin sanyi ya shigesa,damuwa da tsoro fal sun bayyana a fuskokinsu, a hankali ya samu waje ya zauna kansa a ƙasa. 

Abbu ya nisa ya ce “ba na jin daɗin jikina, gani nake nasara ba tawa ba ce a wannan karon, ba mutuwa nake tsoro ba, ina tsoron halin da za ku kasance in na tafi” 

Wani irin kuka Halime ta fashe da shi haka ma Amma ta kama, rintse ido Sultaan ya yi yana mai jin sautin kukansu tamkar ana ɗiga masa ruwan dalma a zuciya, wani irin sarawa kansa ke yi, can ya daka wa Halime tsawa wadda ta sauka kamar saukar aradu ya ce “yi min shiru! Kukan me zaku yi ina numfashi” 

Ya ɗaga idanunsa da suka sauya launi ya dubi Abbu ya ce “Ni zan karɓa maka gasar _Lelu_” 

Wani irin kiɗima suka yi a tare duk suka zabura musamman Amma ta ce “me ka ce?”

Ya runtse idanunsa ya ce “e ni zan yi gasar _Lelu_” …

*🔥FITATTU HUƊU🔥*

      

*👑SULTAAN* # Nml grp ~N~ 300 vip ~N~ 500 via 1401611541 Access bank, shaidar biyanki ta wannan numbern 08167888934

*Mss Flower🌸*

TSINTACCIYA

Nimcyluv

Baƙar fata

Autar manya

DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo

Gaba ɗaya 800

Via 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

*Mss Flower🌸 08167888934* For more information😇

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like