SULTAAN 9-10

Advertisement

 

👑 *S U L T A A N*

Mss Flower🌸

*FITATTU HUƊU🔥*

Advertisements

_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_

*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

           *9-10*

Advertisements

*ZEENA POV*

Kafin ya janye hannunsa ya koma kan gado ya kwanta bayan ya yi folding hannunsa a ƙirji tare da lumshe kyawawan idanunsa masu ɗauke da wani irin ruwa narai-narai kuma lumsassu, ajiyar zuciya na sauke tare da saka hannu na ɗan yi tapping ɗinsa na ce “ka tashi ka ci abinci” ya ware idanunsa a kaina tamkar mai nazarta ta sai kuma ya yamutsa baki tare da maida idonsa ya rufe

“Tun da ba za ka ci ba, bari na maida anjima na kawo maka” na faɗa ina miƙewa tare da nufar ƙofa, jin taku a bayana ya sa na waiwaya da sauri, tsaye na gansa ya ƙura min kyawawan idanunsa suna wani fidda wani irin sheƙi, yana mamular bakinsa tamkar wanda ke shan sweet, ganinsa tsaye da ƙafafunsa ga shi ingarman namiji sai ƙwaƙwalwata ta shiga tunanin to wace irin cuta ce ke damunsa shi kuwa, take zuciyata ta raya min wataƙil hauka yake, wani tsoro ya kamani na yi saurin kallon fuskarsa amma yanda na gansa so innocent sai jikina ya yi sanyi, ban ce mai komai ba na yi waje shi ma sai ya biyo ni a baya, ɗakin da na sauka na shiga yana biye da ni, ina zama shi ma ya samu waje ya zauna yana kallona tare da wasa da hannunsa, ɗaurin kayana na kwance na shiga shirya su a drawer da ke maƙale jikin bango, lokaci-lokaci ina kallonsa har na kammala, bayan na gama miƙewa na yi yana biye da ni har kitchen, na ɗora ruwan zafin wankansa sannan na ɗunɗuma porridge ɗin da na yi na zubo a kwano, parlor na zauna yana gefena sannan na ɗibo na kai bakinsa,kauda kansa gefe ya yi alamun ba zai amsa ba, hakan ya sa na shiga sha abuna don ni dai wata muguwar yunwa nake ji, ƙuri ya yi yana kallona tare da bin wooden spoon ɗin hannuna zuwa bakina da ido, sai na ga kamar so yake na ba shi, hakan ya sa na kai bakinsa, caraf ya amshe, lumshe idonsa ya yi alamun ya yi masa daɗi, ɗan murmushi na yi na kuma ɗebowa na ba shi, sai ya amsa, ganin zai sha ɗin sai na janyo ɗayan kwanon da na zubo a ciki na miƙa masa, bai amsa ba sai ƙuri da ya yi yana kallon kwanon,hannuna da fuskata tamkar bai fahimci me nake nufi ba, ganin yana nufin ba zai sha da kansa ba ya saka na shiga ba shi, idan ya sha Ni ma sai na sha, haka muka ƙare kwanon sannan ya daina amsa a ɗayan alamun ya ƙoshi. Jingina ya yi da gadon karar ɗakin yana kallon yanda nake sha har sai da na tsargu, ban shanye ba na nufi kitchen na ajiye kwanukan. 

Misalin bakwai na dare na kwaso masa ruwan zafin da suka tafasa na kai ƙaton ɗakin wankansa wanda aka tanadi wani kwami ko rami zan ce tamkar swimming pool, bayan na haɗa masa ruwa mai ɗumi na dubesa tare da cewa “ka je ka yi wanka” 

Tsaye ya yi yana kallon bakina da ke motsi alamun sam bai fuskanci inda zancena ya nufa ba, na ja doguwar ajiyar zuciya a raina ina cewa lallai wannan shi ne aiki mutum sai ka ce wani jinjiri, cire masa kayan jikinsa na shiga yi ya rage daga shi sai ɗan ƙaramin farin yadi da ya naɗe D ɗinsa, ga mamakina kai tsaye sai ya wuce wajen kwamin ya shiga, ya ɗan ɗauki mintina kafin ya fito ruwa na bin sa yaro-yaro yayin da yadin da ya naɗe D ɗinsa ya jiƙe sharkaf da ruwa hakan ya kuma bayyana girman surarsa. Da sauri na naɗesa cikin towel sannan na ja hannunsa zuwa ɗakinsa, da hannuna na shafa masa mai sannan na buɗe drawer sa, kusan dukka kayan sababbi ne, wasu farare masu taushin gaske na ɗauko masa sannan na ajiye masa kan gado na fita, bayan mintina kamar biyar na koma sai na tarar da kayan yanda na bar su, yayin da shima yake yanda na bar shi, sauke numfashi na yi sannan na yaye bargon da ya ƙudundune na shiga saka masa kaya, ko kafin na gama ya shiga lumshe idanuwansa alamun bacci yake ji, bayan na gama na gyatta wajen sai na kwantar da shi na zauna gefensa ina shafa lallausar sumar kansa, na shiga rera masa waƙa don baccin ya kwashesa Ni ma na samu na fice daga ɗakin, babu jimawa bacci ya yi awon gaba da shi, hakan ya sa Ni ma na miƙe na fice daga ɗakin. 

Nawa ɗakin na koma sai dai bacci sam ya gagara ɗaukata hakan ya sa na sauko daga ɗan gadon na fita waje don ganewa idona masarautar da kyau, garin ya yi haske sosai dalilin farin wata, ga wani sassanyan sanyi ake mai saka nishaɗi da shauƙi a zuciyar mutum, na yi tafiya mai nisan gaske kafin na samu wani dakali na zauna ina buga ƙafafuna da suke ɗan ciwo, kaina sunkuye yayin da baƙin gashin kaina mai mugun walwali ya zuba ya rufen fuska, ɓuruntu na fara ji daga ɗan nesa hakan ya sa da sauri na ɗaga idona na kalli wajen, wata ƙatuwar gafiya na gani, hakan ya sa na miƙe da sauri na fara yin gaba ina waiwayenta, gaf na ji na bige da wani abu, wata irin ƙara na saki dalilin tsoratar da na yi sai kuma na ga gafiyar ta yo wajena da mugun gudu, wata ƙarar na saki jikina ya ɗauki rawa,hannu na ji a bayana wanda ya kuma tsoratani sai na saki wani ihun, rufe min baki aka yi da sauri, tare da riƙe ni cikin wani faffaɗan hannu, kusan sakan goma sannan na buɗe idona da na rintse, hasken farin watan ne ya haska min kyakyawar fuskarsa, lumshe idona na yi sannan na kuma buɗewa ina jin wani irin sassanyan ƙamshi na fita daga jikinsa, kallon kallo muka shiga yi ido cikin ido kafin na janye idona ina daidaita nutsuwata. Ɗan murmushi ya yi ya ce “tsoronki ya yi yawa” 

Ɗan turo baki na yi na sauke kaina ƙasa, hannu ya saka ya ɗago kaina ya ce “ke mutum ce?” 

Da mamakin tambayarsa nake kallonsa kafin na janye idona na murguɗa baki na ce “a’a aljana ce” 

“Ban taɓa ganin abu me kyau kamarki ba  tsawon rayuwata” ya ce 

“Uhm!” Na ce ina ƙoƙarin tafiya. Da sauri ya riƙo waist ɗina yana min wani irin kallo ya ce “I’m Prince Wahid” 

“Zeena!” Na ce ina sauke idona don ban san shi ɗin Prince ba ne sai yanzu da ya faɗa

Ya ja wata ajiyar zuciya ya ce “You are new here, right?” 

*Nml 300, Vip 500, 1401611541, Access bank, Fatima Lawal Sa’id, 08167888934*

“E!” Na ce a sanyaye

“A ina kike aiki?” Ya tambaya

“Wajen wani Prince mara lafiya” na ce a sanyaye 

Taɓe baki ya ɗan yi sai kuma ya yi murmushi tare da cewa “we will meet again!” Ya ƙare yana rufa min bargon da ya rufa ya wuce. 

Da ido na bi sa da kallo ina mamakin kirkinsa kafin na ja ajiyar zuciya ina rufa bargon sosai a jikina da ke fidda wani irin ni’imtaccen ƙamshi mai masifar daɗi…

*🔥FITATTU HUƊU🔥*

      

*👑SULTAAN* # Nml grp ~N~ 300 vip ~N~ 500 via 1401611541 Access bank, shaidar biyanki ta wannan numbern 08167888934

*Mss Flower🌸*

TSINTACCIYA

Nimcyluv

Baƙar fata

Autar manya

DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo

Gaba ɗaya 800

Via 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

*Mss Flower🌸 08167888934* For more information😇

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like