TAKUN SAAKA 12

Advertisement

 *_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*

Advertisements

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_Chapter Twelve_*

…………..Oho su bama su san sunai ba. Dan koda suka fice a gidan babu wanda yay koda ambatar sunansu Abba ne balle su nuna sun damu da al’amarinsu. Asibiti suka nufa kansu tsaye. Inda sukai tozali da sanyin idaniyarsu da ke zaman jiran isowarsu. 

Advertisements

        Cike da ɗunbin farin ciki duk suka baibayeta kowa na jera mata tambayoyi game da jikinta da yanda takeji kuma. Komai bata iya ce musuba. Sai murmushi da take musu hannun Hibbah da Ammar a cikin nata tana kallon ciwukan jikin Ammar din. Da sauri ya ce,

        “Karki damu Ummi naji sauƙi. Kema ALLAH ya baki lafiya ki cigaba da mana tuwon dawarnan naki da bama son ci”.

      A tare suka kyaƙyale da dariya, Murmushin Ummi ma ya sake faɗaɗa ta kai hannu ta shafa fuskarsa. Hannun Hibbah ta kamo ta maida saman tata fuskar. “Ummi nice auta ni zaki shafama fuska ba wannan garjejen mutumin ba”.

     Ranƙwashi Ammar ya bata akai. Ta dafe kan da sauri tana sakin karamar ƙara. Ammar ya mike da ga inda yake zaune yana mata gwalo.

       “Yaya Umar ka ganshi ko?”.

Harar Ammar Yaya Umar yayi. “Kai wai miyasa baka rabo da zalunci ne. Ko wannan rankwashin da kake mata ma ya hana girma ai taita zama kamar ƴar cilikowa tana addabar mutane da ɗaukar magana”.

       Dariya duk suka tuntsure da shi baki ɗaya. Ransu fes da farin cikin tashin Umminsu. gashi doctor ma ya sanar musu nan da kwana uku zasu sallameta taje gida ta cigaba da shan magunguna. Dan dama irin aikin nata mai sauƙi ne inhar an dace da yinsa bisa nasara.

         Su suka taimakawa Ummin ta tashi suka jingina mata filo. a tare suka haɗu su duka suka ringa bata abinci duk da Hibbah na isarsu da rigima da rinto. Dan a layi aka dinga bi har Ummi tai musu nuni data ƙoshi. Sai da tasha maganinta sannan sukai mata sallama domin tafiya wajen aiki aka bar mata Hibba da Ammar. Dan su sai ƙura ta lafa zasu koma school musamman ma Hibbah.

       Kafin su wuce sun biya office ɗin doctor daya bukaci ganinsu. Bayan sun sake gaisuwa da shi da nuna jin daɗinsu akan nasarar jikin na Ummi ya shiga musu bayani akan wani bawan ALLAH yazo ya biya kuɗin aikin Ummi ɗin duka. Dan haka zai dawo musu da nasu kuɗaɗen insha ALLAH.

      Cikin mamaki suke tambyarsa wanene hakan?. Ya sanar musu shima dai bai sani ba kai tsaye. Dan ansha irin wannan taimakon batare da sunsan ainahin wanene ba. Amma kuma bayan hakan ma wani ma ya sake bada kaso ɗaya bisa uku na kuɗin aikin harma ya shiga ya duba Ummi. shima kuma dama yakanyi hakan a wasu lokutan. Yasan kuma zasu gansa suma kafin a sallami Ummi ɗin dan ya fahimci a yau kawai kamar har sabo ya shiga tsakaninsa da Ummi ɗin.

      Sosai abubuwan suka basu mamaki, amma sai suka watsar da mamakin sukacema doctor a maida musu kuɗin su da kansu insha ALLAH zasu biya kuɗin aikin mahaifiyar tasu basa buƙatar kowa. Cikin nasiha ya nuna musu hakan ba daidai bane. Sam babu ƙyau maida alkairi baya musamman irin wannan. Suma bawai sun biya bane domin sunga sun gaza. 

      Dole suka hakura suka amsa tare da yin addu’a ga masu biyan. Da ga haka suka fito domin nufar wajen aikinsu……..

_________________________________

            A ɓangaren yaran master kam, tun suna zuba idon zaman jiran dawowarsa har suka fidda rai. Dan sun fahimci dai yayi nisan kiwo. Badan sun so ba dole suka tashi sukai shirin barci duk suka kwanta kowa ransa da addu’ar ALLAH ya dawo musu da shi lafiya.

      Sukan damu idan yay fitar dare. Saboda sunsan shi sam bayasan yawon dare. Ko su duk aikin da zai sakasu inhar magrib tayi ya haƙura kenan. Sai ko idan ya zama dolen dole. Amma da anyi sallar isha’i basa ƙara fita sai ta lalura.

      Koda suka tashi sallar asuba ma basuji motsinsa ba, haka sukai alwala suka fita, dan sunsan duk inda massallacin da ya tadasu yake zasu ganosa a layin insha ALLAH. Sai ga shi fitowar tasu ma ta sakasu fahimtar a ina suke. Ashe bayan layin gidan da suka baro jiya ne. Har cikin ransu suna jinjinama boss ɗinsu, saboda matuƙar wayonsa da basirar iya takun rayuwa. Komai babu wanda ya faɗa suka adana a zukatansu har sukaje salla suka dawo. Sanin yace ƙarfe bakwai da rabi zasu bar gidan yasa basu kwanta ba suka tattare abinda suka ɓata.

         Suna tsaka da kimtsawar ne kusan 6:43 sai gashi ya dawo. Kallon mamakin ta inda ya shigo suka shiga masa. Dan sudai basuji alamar buɗe ƙofar gidan ba. Hasalima sakata suka saka mata ta ciki, dole ne sai yayi musu knocking sunzo sun buɗe masa.

       Sarai ya fahimci ma’anar kallon da suke masa, amma sai ya basar abinsa. Hakan yasa suka shiga gaishesa da masa barka da dawowa bayan Musbahu ya tashi ya amshi bag ɗin hannunsa. 

            Hannu kawai ya ɗaga musu, kafin ya fara magana a taƙaice yana nuna bag ɗin da ya shigo da ita, “Gaba ɗayanku zakuyi amfani da kayan cikinta ne, dan a wannan gaɓar magana ake ta kuɗin baƙine ango ya kawo ku kwana anan”. 

         Cikin girmamawa suka shiga amsa masa suna murmushi. Yayinda shi kuma yay shigewarsa ciki. Zaidu ne ya fara kwashewa da dariya yana faɗin, “Abokan ango waye angon to a cikinku?”.

        Salis ya nuna kansa yana wani buɗe hannaye irin eh😉😂. Hararsa Habib yay da taɓe baki. “Banza. Kana ɗan yahoo ubanwa zai baka ƴarsa, wataran shima ka yashe masa asusunsa”.

      Sanin boss na gidan ya sakasu fara dariya suna tarewa da hannu. Salis da ke harar Habib ya ce, “Da yake ma talle bataima audi gori duk tafiyar ɗaya ce. Ta wani fanninma gwara ni. Kuma tunda kace haka kwanan nan zakaji na zama ango ɗan baƙin ciki yahoo boy”.

         Duka Habib ya kaima Salis ɗin ya kauce yana masa gwalo. Rabi’u yace, “Kai kai ku tsaya kuji. Ni fa da boss yay maganar ɗaurin auren nan sai naji inama irin shine za’a ɗaurama auren. ALLAH na ƙagu naga mai tsaurin idon da zatai wuff da master”.

        Dungure masa ƙeya Musbahu yayi da saurin cewa, “Wanan saɓon naka banajin zai tabbata a gidan nan. Inko ya tabbata to lallai sai mun yashe asusun tsohonta tas inaga abiya sadaki da kuɗin auren nata”. 

     Duk yanda sukaso matse dariyarsu hakan ta gagara, tuni suka shiga ƙyalƙyalewa harda masu faɗowa ƙasa da ga kujera. Khalid ne ya fara farga da Master da tun dariyarsu ta farko ya fito. Tsaye yake a jikin ƙofar ya harɗe ƙafafu da hannayensa a ƙirji kawai ya zuba musu idanu. Da sauri Khalid ya zunguri Rabi’u da ke kusa da shi, babu shiri shima ya gimtse tasa dariya yana zungurin Zaid. Shima Zaid da sauri ya haɗiye tasa yana mintsinin kafar Idris da ke kusa da shi. Musbahu da shima idonsa ya kai yay azamar haɗiye tasa yana rarrafawa zai ɓoye bayan kujera. Habib da Salis da basusan anayi ba kam sai ƙara tuntsurawa suke. Salis yace, “Ni why bana tunanin boss zai wani iya soyayya, dan ita tayi yamma shi yayi gabas. Inagama sai munyi karo-karo wajen badashi sadak……”

     Da sauri Musbahu ya rufe masa baki. Hannu Salis ya shiga bige masa yana ƙoƙarin yin magana idonsa ya sauka akan Master da har yanzun yake tsaye yana jinsu. Dan ya wani lumshe idanu tamkar wani mai yin barci a wajen.

     Babu shiri Salis ya ture Musbahu gefe ya miƙe da gudu ya afka bedroom. Ganin haka suma duk sai suka shiga rufa masa baya. Wani silent numfashi master yaja yana buɗe idanunsa akan ƙofar ɗakin da suka shigan harda rufo ƙofa. Uffan bai ceba ya juya ya koma cikin ɗakinsa.

         Koda suka kammala shirin cikin ɗanyun shaddoji iri ɗaya kalar sararin samaniya suka fito, kasa haɗa ido da shi sukayi. Sai satar kallonsa sukeyi ta ƙasan ido, yayinda dariya ke cin ransu a ƙasan zuciya dan shi tashi shigar ta irin marasa jin direbobin nan ce yayi. Da alama da kansa zai tukasu a mota kenan tsabar iya taku. Gaba yay batare da yayi magana ba duk suka rufa masa baya suna ƙoƙarin gimtse dariyarsu.

         Motar bus da zata iya kwashesu ce a waje a fake master nata faman gogewa kai kace driver ɗinne na gaskiya irin wanda suke zuba iya shege a tafa zuwa agege da maraban jos. Dan facemark ɗin dake fuskarsa bata da maraba da ta direbobin da ke tsaka da cin duniya da allura.

          Da kansa ya buɗe musu motar yana harararsu dan ganin kallon da suke masa a munafunce suna murmushi. Sai da suka gama shiga ya rufe yana zagayawa mazaunin driver bayan ya dagama matasan dake zaune a wajen mai shayi anata fira akan abinda ya faru jiya na mayar gwamna hannu. Sai zabga gaddama suke kowa na kare abin son sa. Wasu Master, wasu jami’an tsaro, wasu matar gwamna ɗin. Yayinda wasu ke faman zuba ashariya kai kace faɗa ne ya tashi.

       Murmushi ya saki yana shigewa a motar saboda jin furicin wani da ke faɗin, “Suma jami’an tsaron lusarai ne da zasu zauna mutum ɗaya ya gagaresu. Kawai dai sunyi niyyar barin shegenne kafin suyi ma rayuwarsa walmakalifatu” 

     “To ka sani ko aljanine?”.

Wani ya bashi amsa dai-dai master na reverse da motar. Hannu suka ɗago musu wasu na faɗin ALLAH ya sanya alkairi. Dan sun yarda su ɗaurin auren za’aje😂😝.

            Lallai maganar yaran master gaskiya ne. Wannan gida yaji kayan ƙawa da more rayuwa. Shi kansa yana matuƙar son gidan. Dan a cikinsa ne kawai yafi sakewa sosai. Sanann anan ne kawai yake zama da yaransa. Amma duk sauran gidajen ba kullum yake kwana tare da su ba sai yaso.

*_BAYAN KWANAKI UKU_*

           Alhamdulillahi jikin Ummi yayi ƙyau sosai, dan tattali iya tattali take samu da ga iyalanta sanyin idaniyarta. Yayinda wasu a cikin ƴan uwa ke tururwar zuwa dubata da jiki.

      Hibba ce take kwana tare da ita, su kuma su yaya Muhammad da sun taso aiki anan suke tarewa har sai 11 suke wucewa gida. Har zuwa yanzun Abba bai dawo ba da ga tafiyar da yay randa akaima Ummi ai. Itama hajiya mama taɗan lafa da fitinarta saboda ƙafarta data motsa, duk da dai su su yaya Abubakar ɗin sunsan wani abun suke ƙullawa basu nuna sun damu ba.

         Junaid ma ya dawo gida bayan kwana biyu da yayi a asibiti. Sai dai kuma tunda ya dawo ɗin ko ƙeyarsa basu gani ba, sai sauran ƴammatan gidan marasa kunya. Su kuma ko kallo basu ishesu ba. Dan a cikinsu wai sonsu su Yaya Abubakar ɗin sukeyi.

         Tuni shaƙuwa ta shiga tsakanin Ummi da mutum nan da ya biya kuɗin aikinta kaso ɗaya bisa uku. Dan kamar yanda yaranta ke jurar zuwa kullum safiya dubata haka shima yake zuwa dubata duk safiya. Da rana kuma ya aiko da abinci a kawo mata. Da dare idan ya tashi kasuwa ya shigo da fruits ya sake gaisheta sannan ya wuce. Haka zataita saka masa albarka da masa fatan alkairi akan kasuwancinsa da ya sanar mata yanayi, tare da ma mahaifiyarsa da yace ta rasu addu’a, da mahaifinsa da ke raye.

        Addu’ar da take masa ke sakashi jin daɗi. Da kuma yanda su Yaya Umar suka sake da shi sosai tamkar shima ɗan uwansu ne. Hibbah ce dai da ga gaisuwa bata sake kulashi dan dama ita haka take tana da wahalar sabo duk da rawar kanta. Idan kaga ta sake to tare take da Umminta ko yayunta. Su kaɗaine takema yanda taso.

  

            Yau ma suna tsaka da tattare kaya dan an sallamesu Ummi zataje ta cigaba da shan magani a gida yay sallama. Sai da Ummi ta amsa da bashi izinin shigowa sanann ya shigo. Hibbah da ke haɗa kayan ko ɗagowa batai ba balle ta nuna tasan da zamansa. Shima kallo ɗaya yay mata ya dauke kansa. Dan har cikin ransa kallon miskila yake mata tunda ba yarda take tai magana a gabansa ba. Ko surutu take da ya shigo take gimtse bakinta.

     Cike da girmamawa ya gaida Ummi da tambayar ta yaya jikinta?. Fuskarta faɗaɗe da murmushi tace, “Alhmdllh yaro na. Ykk ya Abban naka shima?”.

       “Lafiya lau ya ke Ummi, yana ma gaisheki da baki haƙurin rashin zuwansa saboda shima yana ɗan fama da ƙafa ne”.

        “ALLAH sarki babu damuwa ai. ALLAH shima ya bashi lafiya yasa kaffara ne. Yaya iyali ko babu kaima kamar ƴan uwan naka?”.

        Murmushi yayi yana duƙar da kansa ƙasa da kai hannu ya shafi wuyansa zuwa ƙeya. “Ku mana addu’a dai Ummi, ALLAH ya bamu nagari”.

        “To amin. Amma ni bansan mi kukema hange-hangen ba sam. Mutum bazai yi aure da ƙuruciyarsa ba kamar yanda iyayenmu sukai mana sai ya gama tsofewa. Ni ban sani ba ko tsoron matan kuke ji ne wai?”.

         Murmushin sa ne ya sake faɗaɗa sosai yana faɗin, “Ummi tsoro kuma? Kawai dai matan ne sai a hankali, sai ka dage wajen zaƙulo mai tarbiyya gudun dana sani”.

         “Da kuma wanan dan wanan. ALLAH ya baku na gari to”.

     “Amin Ummi mun gode”.

Yay maganar yana duban Hibbah. Da sauri tace, “Ina yini”. Yanda tai ɗin ma harya so bashi dariya. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Autar mu ykk ya ƙoƙarin kula mana da Ummi?”.

       A ranta tace, (Kaji ɗan iya). A fili kam sai tace, “Alhmdllhi Yaya Isma’il. Ya Abba?”.

        “Abba yana lafiya, yana ma gaishe ki”.

     Murmushi kawai tai batare da ta sake cewa komai ba. Shima sai ya mike kawai yana faɗin, “Ummi bara naje waje idan kun gama shiryawa sai mu wuce”.

      Zaram Hibbah tace, “Ai ga Yaya Ammar nan zaizo ya maidamu gida a motar Yaya Muhammad. Dama kaje abinka mun gode”.

          Ɗan kallonta yayi na wasu sakanni. “Oh auta, kodai bakison naima Ummi rakkiya na samu lada ne?”.

       Baki ta tura gaba ta dauke kanta batare data amsashi ba.

        Ummi tai murmushi da faɗin, “Kaga manta da ita Isma’il. Tunda kazo ka kaimu kawai shi Ammar ɗin bara na kirasa basai ya amso motarba ma”.

     Godiya yay mata yana ficewa. Hibbah kuma ta hau ƙunkunin ita batason motarsa ya cika shishshigi. Ummi na jinta amma tai mata banza. Sai ma ƙoƙarin kiran Ammar da takeyi a waya akan ya dawo basai ya amso motar ba ga Isma’il yazo.

         Badan Hibbah taso ba Isma’il ya kaisu har gida. Sai dai bai shigaba iyakarsa waje ya juya duk da Ummi tace ya shiga. Haƙuri ya bata akan yana sauri ne zai koma kasuwa. 

      Albarka sosai Ummi ta saka masa. Hakama Ammar yayta masa godiya. Hibbah kam dama tuni ta shigewarta cikin gida. Sai Ammar ne ya kama Ummi suka shiga cikin suma. Babu motsin kowa a gidan da alama yaran duk sun fice. Hajiya mama kuma maybe tana barci ko kallon nata na masifa dan bata gajiya da sanya ido a television, shiyyasa jikokin nata har tsiya suke mata akan hakan.

           Ko mintuna ashirin basuyi da shigowa ba maƙwafta suka fara shigowa ƙara yima Ummi sannu. Ciki harda Zahidah da Hafsat tare da iyayensu. Sune suka taimakawa Hibbah wajen gyara gidan tsaf. Suka kuma daura girki. A kitchen ɗinne suka sami damar mata tambayar abinda ya faru ranar game da tafiya da ita da ƴan sanda sukayi.

      Duk da aminanta ne tun ƙuruciya sai bata faɗa musu komai ba yanda ya faru saboda tuno gargaɗi da akai mata akan idan ta fitar da zancen za’a saka mata ƴan uwa a tarko. Ta dai basu labarin iya abinda zata iya. Sosai sukaji takaici har cikin ransu. Nan fa suka shiga labarin rauni da hukumomin tsaron ƙasar nan suke da shi.

       Zahidah tace,  “A kullum ca ake ana aiki amma babu alamar hakan a ƙasa. Shin laifin gwamnati ne ko na jami’an tsaron?.”

       Cikin taɓe baki Hibbah ta amshe da faɗin, “Kema dai ƙya faɗa Zahidah. Ita kullum gwamnati tana faɗar kuɗaɗe da take warewa domin harkar tsaro. Amma su jami’an tsaron kullum ca suke basu da kayan aiki isassu. To wai kuɗinne ba’a warewa? Kokuwa jami’anne basa saye? kasa kuɗin suke a tebir kowa ya dauka kasonsa?”.

       Da tsantsar takaici Hafsat tace, “Duk ma yanda sukeyi ɗin ai akwai ranar tonon asiri. Ranar da babu wani gacci ko mayafi da ya isa lulluɓe tsiyar da aka shuka aka binne. Ranar da za’ai walƙiya muga kowa da ayyukansa”.

     A tare Zahidah da Hibbah sukace, (Insha allahu kuwa).

      Haka dai suka cigaba da tattauna abubuwa da dama har suka kammala girkin suka sake gyara Kitchen ɗin. Koda suka fito ɗakin Hibbah suka wuce dan har yanzu ƴan dubiya nata shigowa. Sai dai bayan maigadi ko karen da ke a cikin gidan har yanzu bai leƙo ba. Dama kuma basuje asibitinba. A cewarsu ai ba’a sanar musu bata da lafiya ba.

            Sai dare samarin na Ummi suka dawo. zuwa lokacin sashen tsit da ga Ummi sai Hibbah kawai. Hibbah ma tayi barci a kujera dan akwai gajiyar asibiti tare da ita. Sai sautin kiɗa dake tashi da ga sashen momynsu Junaid da hayaniyar ƴammatanta. Da alama wani fati sukeyi, duk da dai shan kiɗa a gidan ba sabon abu bane ba dama.

          Sannu Ummi tai musu. Yayinda suka zagayeta kowa nason jin yaya karfin jikinta?. Cike da jin daɗi da fara’a take amsa musu. Kafin tace suje suci abinci kar yayi sanyi. Ammar zai tada Hibbah Ummi ta hanashi.

        “ALLAH ka tada ita sai naci gidanku, ka barmin yarinya ta huta ta gaji wlhy, dan tamace kanta ke ciwo”.

              “ALLAH yasa gaskiya ne Ummi. Ni naga a kwanaki ukun nan wani sabon hankali take ji da shi. Ko ciwonki ne ya sata nutsuwa oho”. Ammar ya faɗa yana dariya.

     Suma su Yaya Muhammad duk murmushi sukayi suna nufar dining.

★★★

      

         Har washe gari babu wanda yazo ya duba Ummi a cikinsu hajiya Mama. Abba dama bai dawoba har yanzun. Ummi ko a fuska bata nuna ta damuba. Haka suma su Yaya Abubakar babu wanda yace uffan akan hakan. Sai ma tarkata Hibbah sukai ta wuce islamiyya tun safe kasancewar yau ɗin weekend ce akwai tahfiz da take zuwa dama har suma kansu.

        Badan taso zuwan ba ta tafi harda ƙwallanta dan taga abokin hamayyarta Ammar yau bazai je ba. Da yake a kafane babu nisa ita kaɗai ta fita. Sai da ta fitane taci karo da Hafsat da Zahidah sun taho biyo mata dama. Gaisawa sukai da tambayar jikin Ummi sannan suka wuce islamiyyar.

       Islamiyya ce babba matuƙa. Dan tun da ga ƴan shekara uku har zuwa saba’in duk zasu iya karatu a cikinta. sai dai su yara da ga shekara uku zuwa ashirin da biyar suna zuwa ne tun safe har yamma. Daga ashin da shidda zuwa har tsoffi suna zuwa bayan sallar azhar har magriba, kuma iya weekend ne kawai. Dan haka su su Yaya Muhammad sai karfe biyu zasuje. Itace dai da Ammar dama ke tafiya tun safe. Ammar kuma yau akwai abinda zaiyi shiyyasa bazai je ba.

        Kamar kowanne sati yau ma sun ɗauki darasi daban-daban har zuwa ƙarfe biyar na yamma da aka tashe su. A ƙafa suka taho Zahidah da Hafsat nata hira banda Hibbah. A yanda suka lura gaba ɗaya ta zama wata shiru-shiru. Kafin faruwar wannan al’amarin a kowane sati sukaje islamiyya sai ta addabi kowa a ajin ko ta takalo faɗa. Su kansu malam sun buga har sun bari, dan mafi yawancin lokaci ƙoƙarin ta ne ke cetonta akan wani tsiyar idan ta tafka.

        Cike da jin haushi Hibbah ta ja tsoki tana tsayawa cak da ga tafiyar da sukeyi. Kallonta Zahidah da Hafsat sukai cikin alamun sonjin lafiya?. Bata tanka musu ba, sai kallonta da ta maida kan motar da ke bin bayansu ta gefen titi tunda suka fito Islamiyyar. Suma su Hafsar ɗin sun lura tun ɗazun, sai dai basu kawo a ransu mai motar su yake bi ba. Musamman da ya kasance ya ɗan basu tazara.

           Domin tabbatar da su ɗin yake bi a bayyane yay fakin dai-dai inda Hibbah da ta cika tai fam da takaicinsa take.

       Cikin takun nutsuwa da cikar haiba ga ma’abocin kallo ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tarin kamala ya sanyo kafarsa ƙasa dai-dai yana buɗe ƙofar motar mai baƙin gilashi (tinted glass). Wani shegen ƙamshin turarensa ne ya daki hancunansu tare da sallamar da ke fita cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai tarin nutsuwa da sanyi……………..✍

        

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* 

            

    

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like