TAKUN SAAKA 13

Advertisement

  •  *_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*

Advertisements

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

 *Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

Advertisements

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawa nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki._

*_Muna da haɗin_*

_Turaren wutane_ 

_Humrh_ 

_Kulacham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Gyaran jiki_ 

_Na amare_ 

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

*_Da magungun nan mata_*

_Irin su kaza_ 

_Tantabara_

_Tsumi_

_Gumba_

_Zuma_

*_Duka akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

Wushishi road KADUNA

08067807620

09057713999

_________________________

*_Chapter Thirteen_*

…………Gaba ɗaya jin su Hibba ya ɗauke ɗaf a cikin kunnuwansu lokaci guda. Dukansu sun zuba masa ido tamkar waɗanda sukai gamo da wata baƙuwar hallita. Namiji ne tsayayye da za’a iya kiransa namijin gaske a kowacce irin nahiya ko ƙabila. Sanye yake cikin shadda oxblood da ta fidda ainahin kalar fatarsa mai sheƙi. Fuskarsa cike take da ƙasunba da wani madaidaicin gemu mai kama da na gayu irin na ustazan wanan ƙarnin (😳Bily🤐). 

       A kallo ɗaya zaka fahimci rashin son hayaniya daga garesa. Da alama kuma ba mutum bane mai yawan sakewar fuska a mu’amula ko a yanayi.

         Ganin sun shagala wajen kalon sa ya saki wani shegen murmushi yana ƙarasa takowa gaban Hibbah gab. Haka kawai takaici ya kama Hibbah da kallo guda tai masa ta ɗauke kanta tun ɗazun. Cikin ɓata fuska da yatsineta ta ce, “Malam lafiya? Tun ɗazun ka ke ta binmu sai kace wani mai gadin mu”.

          Murmushi ya kuma saki, jerarrun haƙoransa farare na bayyana. Ƙoƙarin saka ƙwayar idanunsa cikin nata yake, amma sai taƙi. Sai ma harara da ta sake zuba masa ta ɗauke kai. A hankali taja siririn tsakin da yasa Hafsat da Zahidah shurin ƙafarta da galla mata tagwayen mintsini.

          “ALLAH ya isa”. Ta faɗi tana hararsu bayan ta saki ƴar siririyar ƙarar data saka baƙon nasu ƙyalƙyalewa da wata dariyarsa da ke fita a nutse. Harara ta sake zuba masa zata bar wajen yay saurin shan gabanta.

         Haushi ya sake kama Hibba. A tsiwace tace, “Malam kana shigarmin hanci fa”

       “Ba malam ɗin bane ai. *_Muhammad Shuraim Aliyu_* ne. Idan kina son nabar shiga hancinki address da number kawai nake buƙata”.

       “Baka da man kai” ta faɗa tana raɓawa ta gefensa ta wuce batare da ya samu koda harar ba yanzun. Badan Zahidah da Hafsat sun so ba sukace masa (bye) suna bin bayanta. Motarsa yay azamar komawa ya cigaba da binsu duk da uban sauri da Hibbah ke zabgawa tamkar zataci da ka. Jitake a ranta da da akwai lungunan da zatabi ya kaita gidansu da shi zatabi dan taga ƙarshen naci. Sai dai kash, tun daga islamiyyar har zuwa gidansu layine ɗoɗar. 

        Itace ta fara shigewa gidansu, dan ata wannan hannun itace farko kafin su Hafsat. Dan haka mai mota Shuraim ya tsayar da su Zahidah. Dole suka tsaya dan baiyi kama da wanda za’a cigaba da yarfatawa ba. 

         “Kuyi haƙuri fa na takura muku, naga mahaɗi nane babu damar yin sakaci. Dan ALLAH miye sunan ƙawarku?.”

       Kallon juna Hafsat da Zahidah sukayi. Roƙonsu da ya sake yi ne ya saka Hafsat cewa, “Muhibbat! Aliyu Hamza”.

          “Masha ALLAH, nice name. Nan ne gidansu?”.

     A taƙaice suka bashi amsa da eh. Shima sai bai sake jan zancen ba yay musu godiya ya koma motarsa ya wuce.

           “Gaskiya Hibbah ƴar yawa ce, amma fa guy ɗin nan ya haɗu ALLAH. Yaci sunansa Muhammad Shuraim”. Zahidah ta faɗa tana lumshe ido.

       Hafsat tace, “Shiyyasa ai na faɗa masa sunanta. Waya gaya mata ana sakaci da irin waɗan nan gayun a wanan ƙarnin.”

        “Barta ai zamuyi maganinta. ALLAH dai yasa har a hallaya haka yake, da kuma zancen aure yazo mu raƙwashe. Dan zanso Hibbah ta auri guy ɗin nan kodan ta kere sa’a a cikin shaggun su Amlah ɗin gidansun can. Masu shegen kakkafi da son asani. Su adole suna hawa motoci. ALLAH idan suka ga guy ɗin nan sai sun haukace. Sai dai kuma ya musu nisa da na Hibbarmu ne”.

       “Insha ALLAH”. Cewar Hafsat tana ƙyalƙyala dariyar mugunta. dan harta hango idon ƴan gidan su Hibbah da kullum suke mata iyayi akan su sun waye, sun girmeta. Suna hawa motocin da Abbansu ya saya musu su ƴaƴan so banda Hibbah.

★_____________★____________★

            A ɓangaren Master kam tunda suka koma L.E street shida yaransa sukai luf abinsu tamkar basa ƙasar. Da wannan damar jami’an tsaro suka sami na barazanar cewar ya tsorata da harin da suka kai masa ne, ƙilama sun sami nasarar kashesa dan sun harbesa.

      A lokacin da yaga wannan rahoto ba ƙaramin dariya abin ya bashi ba ƙwarai da gaske, ya saki wani malalacin mmurmushi mai ƙunshe da ma’anoni masu yawan gaske da shi ya barma kansa saninsu. Har cikin ransa yana mamakin sai yaushe ne ƙasarmu ta gado zata canja ne? Ji dai shareriyar ƙarya da wanɗan da suke amsa sunan iyaye manyan ƙasa suka karkace suka gilla dan kawai su burge su kuma kankaro ma kansu girma.

       Yaransa kansu abin ya basu dariya. Har cikin ransu suna tausayin ranar da Master ɗinsu zai maida murtani ga waɗan nan mutanen. Inhar bai kaisu kwance ba tabbas sai ya sakasu kuka da hawayensu ko su ajiye aikin koda lokacin ritaya ɗinsu baiyi ba. 

                 Shi ba’a sakashi yin abu dole, dan haka baice uffanba sai ma sake lafewa da yay domin tabbatar da zancen nasu. Yayinda a gefe kuma idanunsa ƙur akan batun matar gwamna da hukumar sa’ido akan ta’annati da kayan gwamnati take bin cika har yanzun. Jira suke suyi wani sakaci ko kaɗanne ya sake bankaɗo wasu surukan nata ma duniya harma da su kansu…

____________★__★__★___________

           

           “K kuma lafiya kika shigo kina cikama mutane baki da iska?”. Ummi ta faɗa tana kallon Hibbah da dawowarta kenan da ga islamiyya.

      “Babu komai Ummi. ALLAH yunwa nake ji ne”.

           “Shi abincin da kika tafi da shi fa?”.

       “Ummi naci fa. Kawai wata yunwar dai nake sake ji”.

          “To ALLAH ya ƙyauta, sai kije ki fara yin wanka kiyi salla sannan kizo kici”. 

       “Ummi dan ALLAH ki barni in fara ci ni dai”.

     Komai Ummi bata sake ce mataba. Sai ma miƙewa tai ta shiga takawa a hankali domin zuwa ɗakinta tai salla. Dan har yanzu jikin nata bawai yayi ƙarfi yanda ya kamata bane. Abincin ma Yaya Usman ne ya yisa kafin su wuce tasu Islamiyyar.

     Sai da Hibbah taci tai nak da abinci sannan ta shige ɗakinta. Bata fito ba sai wajen 8:30 da tajiyo hayaniyar yayunta. Cike da ɗokin dawowar tasu ta fito. sai dai ganin harda Isma’il ya sata yin turus.

     Komai babu wanda ya ce mata a akan yanayin nata. Sai ma tsokanarta faɗa da Ammar ya shigayi. Amma sai bata tayashi sunyi ba. Masifa ma taketa faman yi a ranta na yanda yayun nata suka sakema Isma’il ɗin kai kace ɗan gidan ne. Shi kansa yanda yake komai kansa tsaye sai ka rantse gidansu ne. 

     Bata wani jimaba tai musu sai da safe ta shige, ta barsu a falon suna kallon ball suna hira da cin abinci. Ummi ma tunda ta leƙo suka gaisa da Isma’il ɗin ta koma ciki abinta. Dan haka Hibbah bata san sanda Isma’il yabar gidan ba. 

         Washe gari dai an tafi islamiyya babu fushi. Sai dai kuma damuwar ƴan sandan can da ke damunta har yanzu ya sakata komawa wata silent kwana biyun nan. Ko magana ma bata cika sakin jiki tayi ba. Sannan har yanzu bata sake hawa computer ba. Dama wayarta tunda ta dawo take a kashe taƙi ta kunna.

      Yau ma suna fara tafiya a kan hanyarsu ta zuwa islamiyya ta fahimci ana binsu a baya. Wani takaici ne ya turnuƙe ta dan tsaf ta gane guy ɗin jiya ne da tun a ƙofar gate ta watsar da lamarinsa. Ba kuma ta sake tunawa da shi ba sai yanzu da taga motarsa. Sam Zahidah da Hafsat su basu lura da shi ba. Hakan yasa Hibbah fuskewa batace komai ba har suka shige cikin islamiyya.

        Ƙarfe biyar suka ta shi yau ma tamkar kowane weekend. Da ga nan kuma sai wani satin. Gaba ɗaya ta sake watsar da lamarin wani Shuraim. Amma a mamakinta sai gashi ta sake ganin yana biye da su har gida. Kamar da safe yanzu ma bai yunƙurin fitowa ba. A yanzu kam su Zahidah sun ganshi. Koda sukaima Hibbah magana sai tai musu tsaki ma.

        Ƙyaleta sukai ganin shima bai fito a motar ba.

      ★★

    Duk yanda Hibbah taso watsar da lamarin Shuraim sai hakan bai yuwu ba yau. Dan lokaci-lokaci yakan faɗo mata a rai. Sai dai takan ja tsaki da murguɗa baki tamkar tana a gabansa. Har takai abinda takeyi ɗin ya bama Ummi haushi ta balbaleta da faɗa har su Yaya Muhammad suka shigo.

      Sune suka bama Ummin haƙuri da fara tambayar Hibbah cikin lallashi ko wani abu ke damunta ne?. Sam batasan wani boye-ɓoye ba. Musamman ma awajen yayunta da suke da matukar shaƙuwa da juna. Kanta tsaye ta shiga basu labarin abinda takema tsakin.

        “Woow, ƴar Tanee ɗin Ummi anyi saurayi Congratulations. Yau ɗaya a tarihi dole na rubuta na ajiye na haɗa da shagalin barbaje kolin fati na musamman a gidan nan nayi suriki a matsayina na yaya mai lasisin cin gadon Muhibbat Aliyu Hamza (Tanee)”. Ammar ya faɗa yana tafa hannaye cike da tsokana. Filo Yaya Abubakar ya ɗauka ya jefe sa da shi. Dariya gaba ɗayansu suka kwashe da shi saboda yanda Ammar ya baje a ƙasa da bata fuska alamar yaji zafi..

       Hibbah kam dariya sosai take masa harda faɗowa saman kujera. Ta saka yatsun hannunta a kunne tana masa gwalo kamar yanda yara keyi. Filon da aka jefesa da shi ya ɗauka zai jefo mata ta tashi da gudu tai hanyar ɗakinta.

       “Ummi kanta sai da tai dariya. Cikin dariyar ne ta ce, “ALLAH dai ya shirye ku, kai da Tanee ɗin bansan wanda yafi wani shashanci ba. Ni tashi ka ɗakkomin magunguna na a ɗaki tunda ita ta gudu nasan ba sake dawowa zatai ba kuma”.

       Amsawa Ammar yayi da to yana mikewa ya nufi ɗakin Ummin. A dai-dai kuma wanann lokacin Abba da hajiya mama da wasu tsoffin maza biyu suka shigo falon da sallama.

       Da ga Ummi har yaranta da mamaki suke kallonsu, musamman ma Abba da basusan ya dawo gidan ba. Tsoffin kuma Ummi ce kawai ta sansu. Da ƙyar ta iya buɗe baki cikin ƙarfin hali ta ce, “Kawu sannunku da zuwa”. 

    Farin ne kawai yace, “Uhumm”. Ɗaya kam bai tanka ba. Sai dai bin su Yaya Muhammad da yake da kallo tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa.

         Yaya Muhammad da ya lura da kallon ƙurullar da kuma yanayin da Ummi ta shiga tamkar na ruɗani ya saka shi fara gaishesu. Haka yasa suma sauran ƙannensa fara gaisuwar. 

     Amsa musu sukai suna cigaba da kallonsu. Yayinda hajiya mama keta faman ƙyaɓe baki. Abba kam sai wani harare-harare yakeyi. 

         Ummi tai ƙasa da kai cike da ladabi ta hau gaishesu itama. Basu wani amsa mata da ƙyau ba. Sai ma baƙin tsohon ne a kausashe ya ce, “Uh lallai Asiya an samu guri kam tabbas. Ga manyan sojoji kuma a gefe masu tare miki faɗa. Dama irin wanan ai ake gudu akan auren masu asali irin naki. Saboda shi hali naso yakeyi har jikokin bayan-baya. Gashi ko mun gani yau da idanun mu”.

       Idanu Ummi ta lumshe a hankali kanta a ƙasa. Wasu zafafan hawaye suka silalo saman kumatunta. Sai dai cikin dabara ta kai hannu ta share dan kar ƴaƴanta su gani. Cikin dauriya da juriyar da kowa ya santa da shi ta ɗago murmushi a saman fuskarta. “Kawu ina fatan kunzo lafiya?”. Ta faɗa domin son kauda wancam zancen da ya fara.

      Sai dai sam bataci nasara ba. Dan kuwa hajiya mama ce ta amshe da faɗin, “Ni ko zan faɗa maka hali naso yake Hannafi, dan kuwa gashi nan a zuri’a ta. Wlhy badan jinin ɗan inna (babansu Hibbah) na yawo jikin waɗan man yaran ba da tuni na daɗe da sallama su, babu wanda ya cuceni sai malam da ya ƙarrafa wannan auren da har na mutu bazan taɓa daina kuka da ALLAH wadai a kansa ba. Wai fa kuga waɗan nan sanƙama-sanƙaman yaran ne babu mai ko neman aure. Kuma uwarsu ta zuba musu ido saboda ita ɗin bata hanyar…….”

        “Waɗan nan kuma fa? Da ga ina?”. Cewar Ammar da ya fito da ga ɗakin Ummi yaci karo da abinda bai bari ba. Furucinsa kuma ne ya katse zancen da Hajiya mama ta ɗakko tiryan-tiryan.

      Babu wanda ya bashi amsa. Sai zuba masa ido da tsoffin sukai tare da Abba. Baki ya buɗe zai sake magana Ummi ta girgiza masa kanta. Kansa ya ɗauke kawai tare da durƙusawa gabanta ya na ajiye ɗan basket ɗin da magungunan nata ke a ciki. Ɓalla mata ya shigayi yana miƙa mata tare da saka mata ruwa akan baki.

     Wani uban salllami farin tsohon nan ya shiga jerawa yana tafa hannaye. “Kai mizan gani haka ni Ballo (Bello😂). Wannan wane irin kafurcine kuma haka Hasiya?. Wannan ƙurmisheshen gardin ɗan ke baki ruwa a baki kuma?. A to lallai zancen Hannafi gaskiya ne. Da alama ma ke kinfi uwar taki iya shege”.

      A fusace Yaya Umar ya miƙe zai bar falon. Abba ya katsesa a gadarance da faɗin, “To mara mutunci da baiyi gadon arziki ba sai ka tsaya dan zuwan nakune ai”.

        Ido Yaya Umar ya rimtse da ƙarfi yana dunƙule hannunsa. 

     “Kai fitsararre, idan shi ka rainashi ai mu ka ɗaga mana ƙafa kodan rashin saninmu da kai ko.”

     Ƙafa Yaya Umar ya ɗaga zai cigaba da tafiya wasu hawaye masu zafin gaske na gangaroma kumatunsa.

      “Dawo ka zauna”. Umarni da ga Ummi ya hanashi ajiye kafar da ya ɗaga ɗin.

       “Iyeee! A lallai Haƙilu kuna ganin jalalar rayuwa. Wato itace kawai mai sawa da hanawa akan ƴaƴan, bayan wahalar da kaci na kula da su tsahon shekaru. Tabbas Hasiya kinyi asara kekam. 

        Da sauri Ammar ya ɗago ya kallesa. Ya miƙe tare da nuna Kawu Bello da ɗan yatsa cikin kaushi da ɗaci yace, “Kai kaine kai asara tsohon banza ɗan tasha”.

        A tare Hajiya mama da Abba da kawu Bello da kawu Hannafi suka zazzaro ido suna zabura. Ummi tai saurin fisgo hannun Ammar tare da daka masa tsawa. “Aliyu!!”.

          Cikin ficewar hayyaci ya fisge hannunta a cikin nasa da faɗin, “Haba Ummi, wai sai yau she ne zaki daina zama anacin kashi akanki a gidannan ne? Babu ruwana da alaƙarsu gareki. Na rantse da ALLAH idan tsoho bai gyara kalaman harshensa ba to kafin ya fita a falon nan zan datse harshen kuwa na jefar ƙasa”.

      Ɗimmm

Ummi ta sauke ma Ammar dundu. “Ammar kanada hankali kuwa? Miyasa kai bana faɗa maka kaji ne wai?. Kasan waɗan nan ɗin su wanene a wajena? To iyayena ne, ƙannen mahaifiyata ne, tamakar yanda Hajiya mama ta ke uwa a gareni itama. Ka shiga hankalinka kona saɓa maka kaji ko”.

      “Amma Umm…..”

Wani kallo da ta masa ya sakashi yin shiru ya haɗiye sauran maganar.

     Wata ƴar dariya Abba yayi da faɗin, “Kun gani ko? Hakafa gidan yake kullum kamar na ƴan tasha. Sun rainani basa ganin mutunci na bale na mama, bayan ma yaƙi nai da zuciyata wajen rufa mata asiri. To uwar tasu ma ba wai raga mata sukeyi ba. Dan haka na ɗakko ku nan dan ayita ta ƙare. Bazan iya cigaba da ciyar da ƙattan banza ba. Dan haka na yanke shawarar aura musu su Amlah, inba hakaba wataran yankan rago za’a samu sunmin a gidan nan. Ita kuma waccan fitsararriyar uwar ƴan janye-janyen jidalin da suke ɗaurama ƙugu a gidan tana zuba taɓara saboda ita ƴar ido ce Junaid zan aurawa. kunga shikenan anyi tuwona maina ko ba komai sun huta da gori ma asalin uwarsu.”

       “Wannan gaskiya ne Haƙilu. Ai kama taimaki rayuwarsu. Dan a zamanin nan kowa yaji tushen zancen ta ina zai basu ƴarsa. Balle ma ita da take ƴa mace. Bayan ma ka riga ka bata Junaidu ɗin ai wlhy da nayima Musa kamu ma”.

          Da sauri Abba ya ce, “Shi Musan sai yay haƙuri tunda na riga naima Junaid ɗin alƙawari dai. ALLAH ya bashi ta shi”.

       Yaya Muhammad da ya ƙule matuƙa da takaicinsu ya buɗe baki zai yi magana. Amma sai Ummi tai saurin girgiza masa kanta cikin gargaɗi. Kawai sai gani tai hawaye suna sakko masa tsabar zuciyarsa ta kai ƙololuwa a ɓaci.

         Ummi itace ke katange dukkan yunƙurinsu, sun rasa miyasa take hakan a gare su game da dangin mahaifin nasu. Abinda ma basu gane ba shine a yau. Shin ta amshi ballagazayen ƴaƴan gidan da ake iƙirarin an basu kenan matsayin matansu ko mi? Koda ace zasuyi haƙuri suyi mata biyayya bazasu taɓa amincewa a aurama Junaid Hibbah ba. Sai dai komi zai faru ya faru wlhy………..✍

*_Tofa masu karatu, yaya kenan? Wanene zai ci nasara tsakanin su Abba da su Yaya Muhammad? Ni kaina inason jin wace ƙaddarace baibaye da Ummi da ta fi bukatar haƙuri da cin kashin waɗan nan mutane haka?. Kumuje zuwa. muna gab da tsunduma cikin wasan gadan-gadan😉👎🏻_*

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* 

         

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like