TAKUN SAAKA 16

Advertisement

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

Advertisements

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_Chapter Sixteen_*

………Da sauri ta dafe kanta da ya sara mata da ƙarfi. Cikin ɗacin murya da zafin da takeji a zuciyarta tace, “Wai nikam mina muku ne na laifi? Dan ALLAH kubar rayuwata ta cigaba da tafiya a yanda take karku sakamin ahali a masifa. Wancan karon kunce dan na bibiyi wanine. Wannan karon kuma mina aikata zaku kawoni nan?”.

            “Duk bani da amsoshin tambayoyin nan naki. Aikina kawai shine ɗakkoki na kawoki nan wajen. Gashi kuma na cika. Amma idan muka shiga da ga ciki harma abinda baki tambaya ba za’a baki amsarsa na sani”.

          A fusace Hibbah ta dubesa zatai magana aka katseta……

      “Gaskiya ya faɗa miki, bashi da amsar da zai baki. Dan haka bismilla ɗiya ta”. Dattijon wancan karon da aka kaita office ɗinsa ya faɗa dai-dai yana ƙarasowa inda suke. Dan tun shigowar taxi ɗin cikin station ɗin yake kallonsu ta window. A fahimtar da yay mata na tsiwa da rashin tsoro da kafiya ya sashi yanke shawarar sakkowa da kansa ƙila tafi jin shakkarsa ta shiga.

     Sai dai kuma ina. Shima a fusace ta kallesa wasu hawaye masu zafi suna sakko mata. Ganin tana motsa  laɓɓanta alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. “Nan ba muhallin da ya dace ki cigaba da cewa komai bane ɗiyata. Ina mai tabbatar miki wannan kiran yasha ban-ban dana farko. Dan kai tsaye ke zai taimaka bamuba Muhibbat. Bakomai yasa nace hakaba sai ƴan uwanki dake gab da shiga haɗari”.

       “Ƴan uwa na?!”.  

Hibbah ta faɗa ƙirjinta na wani harbawa. Uffan jami’in dattijo A.G baice ba ya juya zuwa office ɗinsa. Da sauri tabi bayansa har tana haɗawa da ɗan gudu. Dan ba ƙaramin hargitsa tunaninta maganarsa ta ƙarshe tayi ba. Duk da yanajin tana binsa da gudu bai tsaya ba sai da ya isa har office ɗinsa. Kusan a tare suka shiga da Hibbah. Tai saurin zuwa gabansa ta durƙusa.

       “Uncle dan ALLAH karku cutarmin da ƴan uwa. Ku daina tursasani yi muku abu ta hanyar yimin barazana da su. Kunsan kuwa mi kuka nema haddasama rayuwata a wancan karon? Saura kaɗan na rasa Ummi na, gatana ni da yayuna. Farin cikinmu madubin rayuwarmu. Miyasa kuke son saka alkairi da sharri? Miyasa kuke son yin amfani da ni saboda ku haskaka kanku ma duniya? Miyasa ku ke……..”

        “Ya isa ɗiyata. Duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba a wannan gaɓar. Yanda kiɗan ya sauya itama rawar zata sauya ne dole. Inason ki nutsu ki bani dukkan hankalinki nan, domin haɗa hannu wajen tabbatar ma mutanenmu abinda suke ganin bazai yuwu ba saboda rauni da ƙarancin shekaru da suke kallo kai tsaye”.

       “Ni bazan nutsu ba, bazan taɓa nutsuwa ba dan ku taurarine masu wutsiya. Dan ALLAH ku daina saka rayuwata data ahalina cikin *_TAKUN SAƘAR KU_* da bawan ALLAHn nan. Bani da alaƙa da komai nasa kamar yanda kuma bani da alaƙa da ku. Indai harkar computer ce na barta har abada duk da kuwa itace burina, itace mafarki na, itace zummata, itace kaifina. Amma saboda cigaba da rayuwar ahalina cikin salama na tattarata na ajiye. Na manta kaina cikin waɗanda suka iya koda kunnata. Please na roƙeku ku barmin rayuwa data ahali su huta. Ku barni naji da damuwar cikin gidanmu ita kaɗai ta isheni”.

      Yanda ta haɗe hannaye tana roƙonsa hawaye na kwarara a kumatunta duk sai tausayinta mai tsanani ya kamashi. Idanunsa suka kaɗa sukai jajur. Kansa ya shiga girgiza mata yana ƙoƙarin kamo hannayenta dake haɗe har yanzu waje guda alamar rokonsa🙏🏻. Sai dai yana kawo hannu ita tai azamar jan nata baya. 

        Da sauri yace, “Shike nan naji zan barki ki tafi. Amma ki tabbatar Tabbas kinada alaƙa da Master Muhibbat, saboda wannnan ɗin kasarki ce, kuma a ƙasar taki yake aikata dukkan ɓarnarsa. Sannan rayuwar yayunki da mamanki na cikin haɗari a hannun ƙanin mahaifinku da shi wanda kike ganin baki da alaƙar komi da shi. 1Mu kaɗai ne kawai kuma zamu iya cetosu tare da ke kanki. Zakuma muyi hakanne kawai idan kin amince kin yarda zaki cigaba da mana aiki akan mutumin nan Master. Idan kuma bazakiyi ba zaki iya tafiya kawai”.

       Shiru Hibbah tai tana kallonsa. Kallo mai cike da ma’anoni da yawa da ita kanta ko ca’akai ta fassarasu bazata iya ba. Kansa ya jinjina mata alamar tabbatarwa.

      Sosai zuciyar Hibbah ke ƙara wani irin lugude, babu abinda ke mata kai kawo a zuciya sai batun auren yayunta da ƴaƴan Abba. Dama har cikin ranta tanaji akwai manufa, amma batasan miyasa Ummi ta amince ba bayan kuma ta sanar mata yayun nata nada waɗanda suke so. Wani tunani da yazo mata daban a cikin rai ya sakata kai hannu kawai taja kujera ta zauna tana share hawayenta da suka kasa tsayawa. Shima sai ya sauke ajiyar zuciya da takawa wajen kujerar zamansa ta office ɗin ya zauna yana fiskantarta.

          “Miyasa sai ni kaɗai ce zan muku aikin? Bayan nasan akwai mutane da yawa masana kuma jajirtattu akan wannan harkar, waɗanda idan a gabansu nake ni ɗin bakomai bace, bansan kuma komaiba?”.

           “Tunani mai ƙyau Muhibbat. Tambayarki na da matuƙar muhummanci kuma ta birgeni. Har cikin raina na sake yarda zaki iya domin kina da kaifin ƙwaƙwalwa. Kafin kiyi mana wancan aikin tunanina irin nasune, ina kallon raunin mace matuƙa nima. Ko a cikin hukumar nan aka bama mace aiki raina kan ɓaci naga babu abinda zata iya. Amma sai ke kika ruguza dukan wannan tunanin nawa a waccan ranar, dan kinyi abinda ƙwararru da yawa suka kasa matsayinki na mace mai ƙarancin shekaru kuma ɗaliba da iya ƙasarta kawai ta samu ilimin kimiya da fasaha. Na zauna nayi dogon nazarin da yasa na fahimci irinku ba’a sakaci da al’amarinku, dan da irinku ƙasashen turawa suka cigaba a nasu ƙasashen da suke birgemu a yau. Muhibbat na miki alƙawarin wannan aikin ƙashin kanki zakiyi. wanda dole duniya tasan da zamanki bayan kammaluwar komai insha ALLAHU. Inason barinma bayana alkairi bayan na ajiye aiki, kuma kece wanan alkairin da nake fatan bari insha ALLAH. Da kuma wanan damar zakiyi amfani kema wajen ceto ahalinki da sake darajasu cikinƴan uwanku, ki wanke baƙin fentin da ƙanin mahaifinku da kakarku sukai muku wanka da shi. Da wanan damar zaki canja masu irin tunanina game da ɗiya mace”

               Murmushi Hibbah ta saki wanda ita kaɗai tasan ma’anar kayanta. Ta ɗan muskuta zamanta da faɗin, “Na amince zan muku aiki, sai dai ku sani hakan ba yana nufin idan baku sami nasarar kamashi ba zan cigaba da dawowa nan wajen. Zan muku abinda kuke buƙata ko ba’a sami nasara ba nima zaku kuɓutarmin da ahalina”.

         “Tabbas mun amince, harma da wata gagarumar ƙyauta da zaki samu inhar yazo hannun namu.”

          “Yallaɓai na bar muku ƙyautar basai kun bani ba. abinda kawai nakeso shine ranar auren yayuna ana gab da halartar ɗaurin aure ku kama Abba ku ɓoye min har sai an kammala ɗaura auren yayuna da matan da suke so da kwanaki biyu. Abu na ƙarshe kuma inason amin cikakken bincike akan Muhammad Shuraim da Abba ya iya hana ɗansa ya yarda na auresa duk da zaɓin Ummi na ne shi”.

       “Duk mun amince da sharaɗinki”.

Murmushi Hibbah ta saki a karo na biyu. “Inhar ya kasance Muhammad Shuraim bashi da wani aibu a rayuwarsa zan auresa na rayu da shi matsayin miji kodan son da Ummi na da Yayuna ke masa. Zanbi duk hanyar da zanbi na ganin ya ɗaukeni zuwa ƙasar China yin karatuna akan ilimin kimiya da fasaha. Ni kuma a wannan lokacin zan muku aiki. Ko wanene wanan master ɗin nayi alkawarin insha ALLAH sai na zama sanadin da zaku kamashi a tafin hannunku. Dan haka na baku dama kafin kwanakin aurenmu 60 da aka saka nasan wanene Muhammad Shuraim ciki da bai. A samama ahalina waje na musamman da zasu rayu a lokacin da zan fara farautar MASTER. Dan ko ƙwarzane bana son ya samu koda farcinan hannunsu”.

           Wani irin tattausan murmushi dattijo A.G ya saki, yayma Hibbah jinjina. “Tun a ranar farko da kikazo nan na tabbatar zaki iya a cikin idanunki, tabbas zaki iya. Kuma insha ALLAH dukkanin bukatunki zasu biya Muhibbat, daga ƙarshe ƙyautar dana ambata zata kasance biya miki kuɗaɗen tafiya ƙasar China ko wata ƙasa daban yin karatunki. Abinda kawai zakiyi shine neman yardar mijinki”.

          A take wani irin farin ciki ya baibaye Hibbah. Ta ɗaga hannu tana addu’ar godiya ga UBANGIJI da fatan nasara akan alƙawarinta. 

      Shiko dattijo A.G na tayata da amin. Sai da ta sauke hannayenta sannan ya tura mata takarda da pen.

     Ki rubutamin dukkan sunayen ƴan gidanku da duk wanda kike tunanin kawo tangarɗa akan auren yayunki anan”.

         Takardar ta jawo gabanta tana wani irin dariyar ƙeta. Dan babu wanda take hangowa a idanunta sai Hajiya Mama da su Kawu Hannafi. Bayan ta gama zana masa ya bata wata bag dake ɗauke da tarin files da suka shafi Master. Ya ɗora da gargaɗinta akan muhimmancin riƙe musu sirrinsu. 

          “Dukkan abinda zaki buƙata da ya shafesa na tanadar miki anan, dole ne sai kin fara shiga kansa, kinyi irin tunaninsa. Ke mace ce, kuma ƙaramar yarinya. Inaji a jikina kafin ya ganoki ko ya farga da ke kin kammala aikin nan insha ALLAH. Kisa a ranki ALLAH na tare da ke, kuma duk inda kika shiga akwai jami’an dana tanada zasu dinga bibiyarki ke da ƴan uwanki domin baku kariya.”

       Kai kawai Hibbah ta jinjina masa. Da ga haka ta fito mai taxi ɗin da ya kawota station ɗin ya sake ɗaukarta domin maidata gida.

★★

           Kamar yanda Hibbah tai fata koda ta shigo gidan nasu bata sami kowa a falo ba, yayunta babu wanda ya shigo, Ummi kuma tana ɗakinta. Ɗaki ta wuce ta adana bag ɗin da tazo da ita sannan ta fito ta sanarma Ummi ta dawo.

       Sosai Ummi ke binta da kallon mamaki ganin tanata washe haƙora kamar ba itace ta fita da ɓacin ran zancen aurensu ba. Komai Ummi batace mata ba akan walwalar tata. Sai ma ce mata da tai idan ta gama taje tai mata list na kayan kwalliya da kayan underwears.

        Cike da zumuɗi Hibbah ta fice dan tasan na kayan lefen yayunta ne da za’a haɗa a gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra’uff Maina. A gurgije tai wanka ta kimtsa kanta. Ko abinci bata nema ba duk da yunwa da ciwon kan da ke damunta har yanzun, tai zaman rubuta list ɗin bayan ta kunna wayarta ta shiga WhatsApp ɗinta tana bugar cikin Hafsat da Zahidah akan kalo da sayis ɗinsu.

      Cikin awa ɗaya ta kammala komai ta fito ɗauke da takardar. Kai tsaye ɗakin Ummi takai ta ajiye sannan ta fito wajen yayunta suka cigaba da hira. Su kansu sunyi mamakin ganin yanda taketa faman walwala tamkar yanda suka santa tun fil’azal. Sai dai komai basuce mata ba suma.

*________________________*

      Kwana uku da faruwar haka Muhammad Shuraim yazo gidan su Hibbah a karon farko. Ya sami ƙyaƙyƙyawar tarba da ga wajen su Yaya Umar, inda aka saukesa ƙaramin falonsu da Dadynsu kan sauke baƙi kafin rasuwarsa. 

          Da farko Hibbah catai ita bata gayyatarsa, dan haka bazataje ba. Sai da Ummi tai mata jan ido sanann ta zumbula hijjab ta fita ɗauke da karamin tire da aka ɗora ruwa.

       Tunda ta shigo da sallama ya kafeta da idanunsa manya da ke neman rikitata. Tiren ta ajiye saman Centre table ɗin falon tana harararsa da kumbura fuska. 

      “Malam lafiya?”.

Ta faɗa cike da tsiwa.

       Kansa ya ɗan girgiza kawai yana lumshe idanunsa dake a kanta ya sake buɗewa. “Ina tausayin bakin nan naki saboda tsiwansa, amma babu komai lokaci kaɗan ya rage ya daina”. 

     Baki ta taɓe da kaiwa zaune cikin kujera tana faɗin, “Karka ɗauka maganin da kaima iyayena suka yarda da kai lokaci guda nima ya cini. Wasu dalilai ne kawai sukasa na yarda da aurenka badan kayi dai-dai da ra’ayin mijin da naima kaina buri ba”.

          “A hakanma na gode. Na kuma sake tabbatar da cewa nazo inda ya dace neman aure. Dan biyayyar da kikai ga iyayenki kawai cikakkiyar amsace akan nagartaciyar tarbiyyar da kika samu da ga garesu mai inganci.”

        “Humm” kawai Hibbah ta faɗa batare da tace komai ba.

      Shuraim ya murmusa batare da ya nuna damuwa da yanayin nata ba. “Kamar yanda na faɗa miki sunana Muhammad Shuraim Aliyu. A garin nan aka haifeni, anan na tashi, anan na girma, anan nai karatun addini dana boko har zuwa secondary. Kafin na ƙetare wajen ƙasar nayo karatun jami’a har zuwa matakin degree na biyu. A yanzu haka ina akan haɗa degree na na uku tare da harkar kasuwanci tamkar yanda na taso na gani anayi a gidan mu. Abinda ban faɗa miki ba bayan wannan kuma na baki damar yin bincike a kaina dan ki sani. Ƙwarai da gaske naji daɗi matuƙa na samunki musamman da ya kasance ban zaci hakan ba. Abinda zance kawai kiyi haƙuri banyi kamar yanda samarin wannan zamanin keyiba na fara shimfiɗa soyayya kafin aure. Ni sam hakan ba ra’ayina bane ba, shiyyasa tun farko ban taɓa zuwa ƙofar gidanku ba kai tsaye sai dai bibiyarki kawai. A randa kuma iyayena sukazo domin neman izinin zuwa zance gunki sai akace anma bani ke, dan ƙa’idarku ku ba’a barinku dama yin zance. Nagode ƙwarai da gaske Muhibbat. Ina fatan zaki amsheni da hannu biyu batare da tunanin nayi miki kutse cikin rayuwarki ba?”.

       Har ga ALLAH kalamansa sun sanyaya ranta. Taji matuƙar kinarsa da girmansa. Sai dai maganarsa ta kusan ƙarshe-ƙarshe akan ba’a barinsu zance ta tsaya mata arai. ta kuma sake tabbatar mata akwai abinda Abba ke ƙullawa game da auren nata da Shuraim, wanda shima da alama baida masaniya akai. 

         Numfashi taja tare da duƙar da kanta ƙasa, dan a karon farko taji kunyarsa da nauyinsa ta lulluɓe ta. Cikin sanyin muryar da batasan tana da ita ba tace, “ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”.

      “Amin ya ALLAH”  ya faɗa yana murmushi dan ya fahimci dukkan abin cewar data shigo da shi falon ya gudu.

    Ba wata hira mai tsayi sukai ba, sai ɗan guntun tarihinta itama data bashi sukai sallama ya tafi itama ta shige ciki. Dama ALLAH-ALLAH take ya wuce ta tafi ga aikin da ke gabanta akan files ɗin da dattijon jami’i ya bata (kamar yanda ta raɗa masa suna😂). Dan tun randa ya bata washe gari ta kwashe Computer ɗinta da ga falo ta maida cikin bedroom. Koda Ummi ta tambayeta dalili sai tace babu komai zata ajiyesu ne dan ta daina amfani da su sai nan gaba.

     Ummi ta gamsu da bayaninta ɗari bisa ɗari. Sai dai abinda bata sani ba tuni Hibbah ta haɗa kayan a ɗakinta harma ta fara aiki akan abinda aka sakata. Ta samu bayanai na laifukan da Master ya aikata kashi-kashi, sai flash drive guda uku dake ɗauke da wasu rubuce-rubucensa na yanar gozo, da fuskokin da yake amfani da su. Abinda ta yanke na farko shine zaman yin nazari da kutse na musamman akan facemasks da yake amfani da su. Haka kawai taji a ranta tana son samo ainahin fuskarsa ta ainahi da take kallo a matakin farko na aikinta. Zatayi hakanne ta wasu hanyoyi da take ganin zasu taimaketa duk da ko farcensa baya bari a gani rufesa yake. Sai duka handles ɗinsa na yanar gizo da ya taɓa amfani da su ta hanyar tura saƙo. Da nambobin waya da yay kira dasu masu tsananin tsaro.

     Yanzu gaba ɗaya lokacinta da hankalinta duk sun koma akan binciken Master da ayyukansa. Ta matuƙar maida kanta busy batare da kowa ya sani ba. Sai da safe ne idan Yayunta suka ga idanunta duk a kumbure suyita tambayarta miya hanata barci?. Takance karatune na exam da zasu fara. Tanason ta dage ne saboda shirye-shiryen exam ɗin zai haɗe mata da hidimar biki.

      Duk sun gamsu da bayanin nata, dan haka sukai mata nasiha kawai akan ta ringa sassautawa tana barci dan karta saka kanta a matsala. Insha ALLAH zataci.

★★★★★

          A lokacin da Hibbah keta kaikawo akan ƙoƙarin yin kutse cikin lamarin Master a gidansu shirye-shiryen biki ake tuƙuru ta fanin su Hajiya Mama da Abba da ke faman jiyyar ƙafarsa da hannu. Shiri suke na bikin ƴaƴan gata ta kowanne fanni. Dan hatta da gidajen da su Yaya Muhammad zasu zauna da amare Abba duk ya saka abokinsa ya nema musu haya, ya kuma biya kuɗin hayar da kudinsa acewarsa zai biya na farko daga haka su cigaba da biya.

       Komai dake faruwa Ummi na kallo. Sai dai ta maida kanta makauniyar ƙarfi da yaji bata taɓa nuna alamar tana fahimta ba. Sai ma faman nata shirye-shiryen da takeyi ita da Sheikh Aliyu Maina da iyalansa itama. Dan a yanzu haka ma anata shirin miƙa akwatunan lefen auren su Yaya Muhammad da suka haɗama kansu da kansu zuwa gidan amarensu. Gidansu kuma na gab da kammaluwa sai sam barka da fatan alkairi.  

       *______________________________*

     

          Kwanakin biki sun cigaba da turawa, shirye-shiye na ƙara faɗaɗa a kowanne ɓangare. Sai dai kuma a ɓangaren Hibbah ita hankalinta a tashe yake matuƙa bisa dalilai biyu. Na farko shine har yanzu bata sake ji da ga jami’an tsaro ba, musamman akan binciken da sukace zasu mata game da Muhammad Shuraim da zuwa yanzu shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakaninsu. Dan tun daga waccan ranar duk bayan kwana biyu sai yazo gidansu. Bawata hira sukeba mai yawa, mafi yawanci ma akan karatu ne dan tafi sakin jiki da shi. 

        Na biyu ganin yanda su Abba ke shirye-shiryen auren duk da yana kwance har yanzu yana fama da ƙafa sai yake ɗaga mata hankali take ganin tamkar tarkon data ɗana musu domin kuɓutar da yayunta bamai yuwuwa bane a garesu. Cikin ɓacin rai yau ta tattara dukanin kayan da A.G ya bata ta maida a bag ɗin. Dama addu’a taketa faman yi ALLAH yasa Ummi ta fita zuwa gidan malam da taji tana faɗa zata.

      Tana samu yayunta suka fita, Ummi ma ta fita gidan malam ɗin tare da su sai itama ta samu ta siɗaɗa ta fice da addu’ar ALLAH yasa har taje ta dawo Ummi bata dawo gidan ba.

         Tana shirin shiga napep aka dakatar da ita. Tai saurin juyowa a rikice jin an ambaci sunanta. Kallon sama zuwa ƙasa taima matashin saurayin da batasan daga ina ya fito ba. Shima batare da wani damuwar kallon da take masanba ya miƙa mata ƙaramar jakkar hannunsa.

      “Babu buƙatar ki sake komawa can. Zaki sami dukkan bayanan da kike buƙata anan. Akwai waya yace zai kiraki tanan zakuyi magana. Kiyi komai da kula”.

      Batare da ya jira cewarta ba ya juya ya barta tsaye galala da jikka a hannu tana binsa da kallo. Takaici da haushi yasa mai napep jan napep ɗinsa yabar wajen yana masifar an bata masa lokaci.

       Itama Hibbah juyawa tai ta koma gida jiki da sauri…………..✍

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like