TAKUN SAAKA 8

Advertisement

 *_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*

Advertisements

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_MG’s SKINCARE_*

Advertisements

*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*💃🏻

*_To maza kuzo ga mg’s skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*

*_mg’s skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*💃🏻💃🏻

*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne a gareku💃🏻_*

*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi💃🏻_*

*_Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za’a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*

_Duk zaku tabbatar da hakanne ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari💃🏻😍🥰_.

Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call 

08064532391

Instagram: glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

Location:kaduna buh we deliver Nationwide

Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift

 _*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_

*___________________________*

*_Chapter Eight_*

………..Wani wawan tsaki ya ja tare da kai hannu kan Wadrobe ɗin dake a jikin bangon ɗakin ya danna wani maɓalli. A take ta zuge kanta, ɓoyayyar ƙofar sirri da ke a jikin bangon ta bayyana. 

        Cikin sauri suka shiga shigewa mamaki fal ransu, dan ko su da ke tare da shi tsahon shekaru basu taɓa sanin da ƙofar ba. Bama batun ƙofa kawai ba, ko fuskarsa ta ainahi har yanzun basu sani ba. Yanda yake zuwama duniya da mabanbanta fuskoki suma haka yake zuwa musu, duk da kuwa akwai alaƙa tsakaninsa da wasu a cikinsu ta zuminci.

        Shi mutum ne mai aiki da matuƙar taka tsan-tsan a kowane ɓangare, shiyyasa yay dogon zangon da har yanzu an kasa cimmasa a duk tarkuna da ake ɗana masa, dan kota ina idanunsa a buɗe suke, hakama kunnuwansa. Sai da duk suka gama fita yana kallon jami’an tsaron da ke shigowa cikin gidan da sanɗa ta cikin tab ɗin dake a hannunsa. “Humm” ya faɗa yana rufe tab ɗin, shima yabi bayan yaran nasa tare da maida ƙofar a yanda take kamar babu.

           Koda ya fito bai tankasu ba, sai wasu ƙananun fitilu masu azabar haske daya fiddo a aljihun wandonsa  ya shiga kunnasu yana mika musu, A take ko ina ya gauraye da haske har suna iya ganin gabansu. Sam babu ruwa ko datti a ciki, hanyace ɗoɗar da basusan iyakarta ba, domin dama can ba’a yisa dan ruwa ya wuce ba. Sukam dai ɗunbin tsoro da mamakin Master ɗin nasu tuni ya gama kashesu a tsaye. Tun fitowarsu a ɗakin da suka tsinci kansu a cikin doguwar hanyar ruwa komai ya kuma kwance musu game da shi. Sagade sukai suna kallon ikon ALLAH da sake tsorata da al’amarinsa. Lallai sun sake yarda da gaskiyar zantukan mutane da ke kiransa *Hatsabibi shu’umi*.

          “Zakuje ne ko zaku tsaya kallo na?”. 

        Sautin furicinsa ya maido da hankalinsu jikinsu kusan a tare lokaci guda.

       Da sauri suka haɗa baki wajen faɗin, “Sorry Master!”. 

★★★

            Jami’an tsaron da suka iso anguwar bisa jagorancin Hibbah da ke basu haske ta hanyar waya kuwa tun kafin su iso gidan suka ajiye motocinsu can farkon layin suka ƙaraso da ƙafa. Mai-gadi da dama yake zaman jiran tsammani kamar yanda Master yay masa bayani ana yin knocking gate ɗin ya tashi ya buɗe bayan ya ƙara ƙarar redio ɗinsa da yake ji.

       Jami’in da ya fara isowa wajen cikin son nuna basaja ya bama mai-gadi hannu yana murmushi. Babu musu shima mai gadin ya bashi hannu sukai musabaha cikin nuna ƙaulanin rashin sani.

        “Sai dai gashi ban waye kaba bawan ALLAH. Kuma su alhaji basu sanarmin wani baƙo zaizo nan ba”. Mai-gadi ya faɗa lokacin da yake sakin hannun jami’i da yazo a suffar basaja.

            Jami’in da furucin mai-gadi ya ɗan tsaya masa a rai ya ce, “Kana nufin masu gidan basa nan kenan?”.

       “Tabbas basa nan mai-gida. Yau kwanansu tara kenan da komawa can ƙasar da suke zaune ai”.

         Wani kallon kama rainamin hankali jami’in yay masa, amma sai ya saki murmushi da maida hannayensa baya yanama ƴan uwansa alamar su taho ba tare da yasan mai-gadin na lure da shi ba.

      Baki mai-gadi ya buɗe zai sake magana sauran jami’an suka iso suma. Bindiga wanda ya fara zuwa ya nuna masa tare da turasa cikin gidan duk suma suka shishshigo. Duk rarrabuwa sukai a kowace kusurwa ta gidan suka fara shiga da sanɗa, wanda ya fara zuwan kuma na tare da mai-gadi da zuciyarsa ke cike da tsoron kar dai ƙaryarsu ta ƙare yau, dan shi duk tunaninsa su Master na’a cikin gidan suma tunda bai sanar masa shirinsa ba bayan aikin da zaiyi kawai. Duk da ya yarda da hatsabibancin uban gidan nasu amma dolene akwai ɓacin rana. Da alama kuma idan har ta ƙwaɓe yau da shi zata fara ruftawa. To amma insha ALLAH zaiyi ƙoƙarin ganin ya bi duk abinda Master ya faɗa masa yanda ya kamata.

            Sai da jami’in nan ya tabbatar abokan aikinsa sun gama zagaye gidan sannan ya tasa ƙeyar mai-gadi shima suka nufi ciki. Ƙofar shiga da suka fahimci a rufe take suka bashi umarnin buɗewa. Amma sai ya nuna musu sam bai san password ɗin ba shi.

         Jikinsa jami’in ya fara laluba, ya ciro waya nokia da tasha ɗaurin ƙyauraye da salataf. Wayar ya jujjuya a hannunsa yana ƙare mata kallo fuska a yatsine, kafin ya maida dubansa garesa yana sake gyara zaman bindigar da ya ɗora masa a saman kai. 

       “Nasan dai kanada number ɗin mai-gidan, maza ka kirashi yanzun nan ya faɗa maka password ɗin komu ɓalla ƙofar a yanda muka gadama.”

       Babu wani nuna damuwa ko ɗar mai-gadi ya amsa wayar ya shiga laluben Number. Dailing yayi kansa tsaye, sai dai harta tsinke ba’a ɗaga ba. Ya sake kira a karo  na biyu, sai da taje gab da tsinkewa aka ɗaga cikin muryar isa. Cikin girmamawa mai-gadi yay gaisuwa, sannan ya ɗara da bayanin cewar jami’an tsaro ne sukazo gidan suna buƙatar password na ƙofa wai zasuyi bincike, bai san mi suke nema ba. Carab jami’in ya amshe wayar yasa a kunnensa bayan ya kalla no. Ɗin da mai-gadin ya kira ya tabbatar da ta ƙetare ce.

           “Jami’an tsaro kuma? Rabi’u!. To mu miya haɗa gidanmu da jami’an tsaro?”.

      “Bincikenmu ne ya nuna mana wannan gidan na masu laifine Alhaji. Bazamu tabbatar da ba haka bane ba sai mun shiga mun duba kuma. Dan haka muna jiran mabuɗin sirrin ƙofar da ga gareka kawai, kafin muyi magana ta gaba da kai idan har ya kama”.

      “Okay to babu damuwa yallaɓai”. Daga can aka faɗa tare da zayyano masa password ɗin. 

        

      A sakawa ɗaya kuwa ƙofar ta buɗe. kusan rabi a cikinsu suka shiga ciki akabar wasu a waje. Akan idon mai-gadi suka shiga hargitsa gidan tako ina. Sai dai abin mamaki babu wani alamun abun rashin gaskiya da sukayi gamo da shi. Cikin glass ɗin nan da computers ke ciki ɗazun yanzu babu shi, sai wasu ƙayatattun flowers masu ɗaukar hankali da ƙamshinsu ya cika falon.

        “Tabbas yarinyar nan ƙarya take mana. Ko tana ɗaya da ga cikinsu ne yawo da hankalinmu kawai take son yi”. Ɗaya daga cikin jami’an ya faɗa a hasale.

               “Sam banajin hakan a raina, akwai dai wani ɓoyayyen abunda bamu sani ba. Karku manta shiɗin mutum ne mai matuƙar wayo da dabaru kala-kala. Tabbas ya fahimci ana bibiyarsa ne ya bada ƙafa. Kokuma yayi amfani da wanann location ɗin domin sakamu zargi.”

        “Nima zuciyata tafi rayamin hakan yallaɓai”. Wani ma ya sake faɗa cikin jin zafi.

        “Karku samu damuwa. ai rana 99 da tara na ɓarawo, ɗaya tak na mai kaya. Inhar kere na yawo, zabo na yawo watarana dole a gamu. Tunda yace shi hatsabibi ne ya samu dai-dai da shi kuwa. Zamu bar wasu a gidan nan har sai mun tabbatar da gaskiyar babu wani abun zargi a cikinsa”.

      Duk sun amsa da girmamawa. Shi dai mai-gadi kallonsu kawai yake yana kwasar dariya a zuciyarsa. Koda suka fito harabar gidan sun tsara wanɗanda za’a bari, wanda zasu koma kuma suka nufi hanyar barin gidan. Karaf idon ɗaya ya sauka akan bag dake rataye acan ƙarshen gate ɗin gidan ta waje. Saurin zuwa yay ya ɗakko yana nuna musu. Commander ɗin operation ɗin nasu ya amsa yana zazzage jakkar cikin kulawa gudun kar a saka musu bom a ciki.

    Agogon Hibbah ne ya fara faɗowa tare da takarda mai ɗauke da sunansa akoda yaushe da facemark. Sai ɗan gajeren rubutu a bayan takardar.

        *_“Bibiyata na nufin ƙare rayuwarku a wahala. Inhar bani naso kusan niɗin wanene ba, bazaku taɓa ganoni da kanku ba har abada insha ALLAHU rabbi. Dan haka ku daina azabtar da kanku wajen bibiyata komai yana da lokacinsa”_*

         _Master👌🏼_

    Wani wawan tsaki jami’in daya gama karanta takardar yaja. Ya cije leɓensa na ƙasa da ƙarfi, cikin alwashi yace, “Ni kuma na maka alƙawarin da wannan hannun nawa zan kamaka, sannan na maka horo mai tsananin gaske wanda sai ka gwammaci mutuwarka da rayuwarka shaiɗani”. 

         Suma sauran zukatansu na matukar ƙuna suka ɗauki nasu alwashin…..

___________★★★__________

          Yaya Abubakar ya shiga tashin hankali matuƙa lokacin da yake isowa cikin makarantar su Hibbah yaji abinda ya faru a bakin Ammar da Zahidah. Tare da samun ƙarin bayani a bakunan wasu ɗaliban.

      Da taimakon wani malamin su Hibbah ya shiga Computers room nasu yay bincike a computer ɗin da ta gudanar da binciken. Sai dai kuma ta saka security, shiga yay gwada passwords kala-kala yayi wanda yasan tana amfani da su a gida ko zata iya amfani da su. Sai dai sam babu wanda ya buɗe. Cike da ɓacin rai ya mike yana bugar desk ɗin cikin ƙunar zuciya. Lalubo wayarsa da ke ring a aljihu yayi. Yaya Muhammad ne, ɗagawa yay sukai yar magana ya yanke. Wani abokinsa ya kira kasancewar shi jami’i ne a hukumar ƴan sandan ta farin kaya. Ya tabbatar shine kawai zai iya bincika masa idan Hibbah na hukumar tasu. Bayan ya ɗaga ko gaisuwar kirki ba suyi ba ya sanar masa bukatarsa. A take jami’in ya tabbatar masa lallai Hibbah na’a headquarters ɗin tasu dan yaji ƙishin-ƙishin ɗin zancen yanzu a bakin wani ogansu cewar akwai yarinya da ke da alƙa da case ɗin na jiya.

     Yanke wayar kawai yayi batare da sun ƙarasa maganar tasu ba, ya kira Yaya Muhammad yana sanar masa a inda zasu haɗu yanzun nan……

__________________________

           Master da yaransa kam bayan ƴar tafiyar da sukayi ta cikin hanyar kwata sai gasu sun ɓilla ta wani ƙaramin gida. Gidane ginanne mai ƙyau na dai-dai mai matsakaicin ƙarfi. Yanda yake bin ko ina cike da nazari haka suma suke kallon gidan. Bayan kamar mintuna biyu ya gyara tsaiwarsa sosai yana fuskantarsu. Binsu ya gamayi da kallo ɗaya bayan ɗaya batare da su suna kallon ko ƙwayar idonsa ba. Tabbas sun jima suna kwaɗayin ganin fuskarsa, amma sam yaƙi basu damar hakan koda da kuskure.. 

           _Gyaran muryar da yay ne ya katse tunaninsu. Ya sake gyara tsaiwarsa yana tura hannayensa duka cikin aljihun wandonsa. Muryarsa a kausashe da tabbatar musu da fushinsa ya fara magana cike da nutsuwa da ƙasaitar sa,

          “Yau mun tsallake rijiya da baya, amma wataran saboda sakacinku tabbas bazamu tsallake ba. A kullum ina faɗa muku duk sanda zakuyi aiki, ku ringa yinsa da *_ƘWAƘWALWA  DA ZUCIYA_* a haɗe. Dan duk lokacin da ɗan adam yay amfani da ƙwaƙwalwa kawai wajenin aikata muhimman abubuwa to ya tabbatar zai kasance mai yawan shiga ruɗani da tafiya yana dawowa baya saboda wani ya fika kaifin basirar. Idan ko da zuciya kaɗai ka dogara wajen ginin muhimman abubuwa, kasani nasararka ragaggiyace saboda zuciya abinda ke mata daɗi kawai take ayyanawa da buƙatar ya kasance mata. Bai kuma zama lallai ka kasance cikin jin daɗi da farin ciki ba a kowanne daƙiƙa na rayuwarka. Dan wani lokacin hanyar jin daɗi wahala ce, wata hanyar wahalar kuma jin daɗi ce. Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe, idan ba hakaba ni ɗin nan da kaina zan bada ƙafar da za’a kama duk wanda ya cigaba da sakaci a cikinku. Ba kuma zan taɓa kuɓutar da shi ba har sai ya jigata yasan muhimmancin bama kasan kariyar yin aiki cikin tsantseni. Duk wanda ya haremu ya sokemu akan dai-dai kuma na jinjinama ƙwaƙwalwarsa da kaifin tunani. Sai dai na baku awa goma kacal ku ganomin koshi ɗin ɗan gidan uban wanene. Dan sai ya amshi hukunci dai-dai da iyawarsa!”_.

        “Insha ALLAHU zamu kiyaye sir. Muna kuma neman afuwa daga gareka”. Suka faɗa a tare cike da girmamawa a garesa. Yayinda Habib da yasan komai ya farune ta sanadinsa yay ƙasa da kansa bayan ya sake matsowa gabansa. “Ka gafarceni Master, dan wannan tabbas sakaci na ne. Amma wlhy sam bansan ta yaya akai hakan ta kasance ba. Sannan koda muka dawo kuma ban fargaba.”

       Hannu kawai ya ɗaga masa batare da yayi magana ba. Sai kuma ya nufi ƙofar fita da ga gidan baki ɗaya. Da kallo duk suka bisa har ya isa ƙofar ya buɗe sannan ya juyo yana kallonsu shima.

      “Zan sake maimaita muku awa goma kacal, na samu cikakken labarin akan ko shiɗin wanene!……” Daga haka ya ida ficewa baki ɗaya.

         A tare suka sauke ajiyar zuciya. Sun tabbatar a salon da yay maganar babu wasa a cikinta, dama can kuma ba wasan ya ke musu ba ballema su ɗauketa wasa. Suma kuma har cikin ransu suna bukatar sanin wanene wanda yay musu wannan tarkon da suka tsallake rijiya da baya?……….✍

           *_Gadai jami’an tsaro basu sami nasarar aikin Hibbah ba, ga kuma Master ya bada awanni goma domin binciko wanda ya haresu, hibbah dai kuma itace ta kai harin da babu niyyar dalilin da su suke kallo. To yaya zata kasance kenan tsakanin Muhibbat Aliyu Hamza da Jami’an ƴan sanda da Master kenan?🤔. TAKUN SAAƘA wasa farin girki👎🏻_*

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

    

       

      

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like