TAKUN SAAKA 9

Advertisement

*_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_MG’s SKINCARE_*

*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*💃🏻

*_To maza kuzo ga mg’s skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*

Advertisements

*_mg’s skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*💃🏻💃🏻

*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne a gareku💃🏻_*

*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi💃🏻_*

*_Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za’a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*

_Duk zaku tabbatar da hakanne ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari💃🏻😍🥰_.

Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call 

08064532391

Instagram: glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

Location:kaduna buh we deliver Nationwide

Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift

 _*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_

____________________

*_Chapter Nine_*

………….Tunda jami’an suka dawo da labarin rashin nasara zukatan manyansu yay matuƙar ƙunci. Awanni ƙalilan suka rage musu da ga umarnin gidan gwamnati. Cikarsu babu Master a hannunsu kuwa yana nufin sun gaza a idanun al’ummar jiharsu da ƙasa baki ɗaya. Hakama ga gwamna da muƙarrabansa.

        A gefe ga gidajen jaridu da duk wata kafar yaɗa labarai sun baza kunnuwa da idanun domin ganin yanda awanni ashirin da huɗu zasu cika tare da wannan ɓarawo a hannunsu ko saɓanin hakan. 

       Waɗan nan tunane-tunanen nasu yasa su shirya zaman meeting na gaggawa.

        Dukkan wani babba mai alhakin faɗa aji ya hallara a ɗakin da meeting ɗin zai gudana. Sai wanda ya jagoranci jami’an da suka dawo yanzun nan da shirin kamo Master da yaransa..

         Kowa ka kalla a ɗakin meeting ɗin kasan yaci ya ƙoshi, dan babu wasu kamannin wahala tare da su. Da’ace ƙasace mai ƙyaƙyƙyawan tsari sun cancanci yin ritaya duk su koma gefe a kawo matasa masu jini a jika da basirarsu ke aiki da kaifin ƙwaƙwalwa a zuba a madadinsu. Su kuma su zama dattijai masu bada shawara wa ƙasa ta bayan fage matsayinsu na iyayen ƙasa. Sai dai sam a wannan ƙasar tamu ba haka bane ba. Anyi sakacin barin matasan da ke da basirar zuwa da salonsu na ƙuruciya wajen kawoma ƙasa cigaba zama ƴan ta’adda, dukkan tarin basirarnan tasu da ƙuruciya ta koma aiki ne ƙarƙashin aikata laifuka. Iyayenmu da gwagwarmayar rayuwa da raunin shekaru sukaima yawa sun zama sune masu riƙe da madafun iko wajen zartarwa da hukuntarwa. A duk lokacin da ƙasa tai sakacin rashin amfani da basirar matasa da ƙuruciyarsu wajen aikata alkairi, to lallai shaiɗanu zasuyi amfani da basira da ƙuruciyar waɗanan matasan wajen kafa tantin ta’addancin da zai ruguza ƙasa.

      A ƙasarmu ta gado iyayenmu sune ƴan siyasarmu, sune masu riƙe da madafun iko na mulkin gargajiya da na siyasa, sune riƙe da hukumomin ladabtar da masu laifi, sune riƙe da manyan kuɗaɗe na kasuwanci, sune riƙe da makarantun da ake bamu ilimi, sune.. Sune… Sune komai. 

      Babu wata hanya ko ƙofa da suka barma matasan wajen nuna bajintarsu da ƙwazon da ALLAH ya haliccesu da shi. Kallonmu suke masu yawan wauta, masu shashanci, masu ƙuruciya, masu rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da su. Masu… Masu… Ta ko ina. Amfaninmu kawai mu cigaba da zama a ƙasa har sai lokacinmu yayi. To yaushene lokacin namu zaiyi? Shin sai muma mun kai irin shekarunsu mu danne na ƙasa da mu kenan?. indai har a haka za’a cigaba da tafiya lallai da alamar ƙasar tamu bazata taɓa zama mai sauyawa ba ko samun ci gaba. Domin anyi sakacin ajiye lokaci an ɗauki rauni.

     Shi kuma lokaci a duk sanda aka gaza amfani da shi ta hanyar da ya dace wucewa yakeyi yabar mai shi da cizon yatsa da dana sani. A lokacin kuma daka buƙaci gyarawa sai ya kufce maka dan kayi sakaci wajen sarrafashi a sanda ya dace. To ya kamata manyan ƙasarmu su fahimci MATASANMU sune LOKACINMU. Cigaba da sakacin ƙinyin amfani da baiwarsu akan lokaci na nufin baragurbi amsarsu su su amfana da wannan damar wajen maidasu masu ruguza ƙasar da ku kuke ganin kunata ginawa. Sanda zakuyi ƙoƙarin son tarosu kuma sunyi nisan da bazasuji kiranku ba sam.

    Bawai munason fiddo da gazawarku bane ma duniya ko goyon bayan laifukan matasa. Muna buƙatar ku duba ku kuma fahimci sai da matasa ƙasa ke iya samun ci gaba. Basu dama kuma shike nufin daƙile dama a hannun masu ɗorasu bisa bigiren ta’addanci. Kun cancanci kuma muyi alfahari da ku, dan kun bamu gudunmawa ta musamman bayan kasancewarku iyaye a garemu. 

       Bayan ƙarin bayani da suka samu a bakin jami’in da suka fita bibiyar Master zukatansu sun ƙara ɗaci. Ɗakin yayi shiru kowa na nazari da tunani a cikin zuciyarsa. Ɗaya da ga cikinsu da zuciyarsa ke raya masa wani abu ya nema izinin yin magana.

          “Bismillah, an baka dama. Ya kamata kowa ya faɗi abinda ke bakinsa ko hakan zai bamu wani haske da ga kullewar da kawunanmu sukayi.” Ogan nasu ya faɗa cike da taraddadi.

         Kansa ya jinjina da faɗin, “Thanks you sir. Dama wani tunanine yakemin yawo a zuciya game da ita wannan yarinyar datai mana aikin. Shin baƙwa tunanin shine ya tsara duk hakan kasancewarsa shu’umin mutum kuwa?. Al’amarin da matuƙar mamaki ta yanda ta bibiyesa cikin sauƙi. Idan har dama ba shirinsa bane ta yaya akai ta jefa masa abunda ta samu damar bibiyarsa?”.

       Da sauri wanda ke a kusa da shi ya ashe da faɗin, “Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba. Tabbas da alamar akwai lauje cikin naɗi game da wannan al’amarin. Nasan za’a iya samun mai ƙwazo da kaifin basirarta, amma yanda al’amarin ya faru da ƙanƙantar shekarunta sai nake ganin kawai shiri ne na musamman akai. Dan bana hangen tana da wani ƙyaƙyƙyawan tunanin da har zuciyarta zata bata damar aikata hakan. Banda shirme da shiririta mi yaran yanzun suka iya? musamman ma ita da ta kasance MACE”. Ya ƙare maganar cikin jin zafi sosai.

          Wanda ya gana da Hibbah dake ta faman buga pen a kan laɓɓansa yana kallonsu da nazarin maganganunsu yay murmushi. “Wannan tunanin namu na ganin yaranmu bazasu iya komai ba wajen taka rawar gani ke maida ƙasarmu da mu baya a koda yaushe. Da hakan kuma suke samun damar yin amfani da basirar tasu a gurɓatacciyar hanya. Tabbas ita ɗin MACE ce kuma ƙaramar yarinya, amma kallonta da rauni na *ɗiya mace* shine babban kuskuren mu. Banace inada tabbacin bata da alaƙa da shi ba, dan shi shu’umin mutum ne hatsabibi da zai iya aikata duk ma abinda bamuyi tunaninsa ba ko munyi. Sai dai banason mu kasa fahimtar cewar itama duk da kasancewar tata MACE zata iya taka wata rawar gani a harkar tsaro da duk wani sha’ani na rayuwa duk da raunin da ALLAH yay mata. Shawarata anan itace mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya”.

        Sake maida hankalinsu sukai garesa domin sonjin ƙarshen zancen.

      Ya gyara abin maganar gabansa yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. “Ma’anar mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya shine muyi amfani da wannan yarinyar ta hanyar riƙeta a jikinmu ta zame mana ma’aikaciyar sirri. Ta wannan hanyar zamu amfanu da alkairinta da kaifin basirarta. Mu kuma saka mata ido wajen gano shin akwai alaƙar da zuciyarmu take zargin tsakaninta da shi ko babu?”.

          “Yes! Wannan shawarar taka tayi matuƙa *A.G*”. Ogansu ya faɗa yana tafa masa. Hakanne yasa suma sauran tafa masa duk da wasunsu batai musu ba sam. Dansu babu abinda zukatansu ke ayyana musu sai ganin babu abinda Hibbah zata iya matsayinta na ɗiya MACE mai kuma ƙarancin shekaru.

          Sun cigaba da tattaunawa har zuwa wani lokaci, kafin ogan nasu ya bada damar shigo da Hibbah.

           Hibbah da damuwar ahalinta kecin ranta ta shigo fuskarta a cinkushe babu ko ɗigon walwala. Babu abinda zuciyarta tafi bukata a yanzu kamar tozali da Ummi da yayunta dan tabbatar da babu abinda ya faru da su. Zama tai a kujerar da aka nuna mata bayan ta gaishesu ranta fal jin haushinsu, musamman mutumin ɗazun da tun shigowarta da shi ta fara haɗa ido yana mata murmushi.

          Bayan sun gama nazartarta da ƙare mata kallo ogan nasu yay gyaran muryar da ta saka Hibbah ɗago manyan idanun ta kallesa. Ganin yanda ya kafeta da nasane ya sata sake maida kanta ta duƙar tana wasa da yatsun hannunta.

       “Muhibbat Aliyu Hamza!”.

Ya kirayi sunanta murya babu alamar wasa. Hakanne ya saka gabanta faɗuwa, ta sake ɗagowa tana amsa masa da rawar murya. “Na’am yallaɓai”.

        “Miye alaƙarki da Master!?”.

  “Master kuma yallaɓai? Ni ban sanshi ba”.

       “Kin tabbatar?”.

Kanta ta jinjina masa.

     “Taya za’ai mu yarda baki da alaƙa da shi?. Bayan tsahon shekaru biyu kenan kowace hukuma ta jami’an tsaro farautarsa suke, amma sun gaza koda ganin farcen yatsansa. Sai gashi ke a cikin kwana ɗaya rak kin haresa akan dai-dai?”.

        “Ni wlhy yallaɓai bansanshi ba, bakuma ni da wata alaƙa da shi ko sanin wanene shi. Na aikata duk abinda kukaga nayi ne saboda wasa da rayukan mutane da sukeyi ta hanyar power rider amma badan wani dalili ba”.

       “Okay, mu ɗauka hakanne kamar yanda kika faɗa ɗin. Yanzu wane tunani kikeyi game da makomar ahalinki?”.

        Saurin ɗagowa tai tana kallonsa idanunta cike da ƙwalla. Muryarta na rawa tace, “Amma yallaɓai naga na muku aikin da kuka buƙata dan na tabbata kun kamasa. Kuma kun tabbatar min hakan shine fansar ahalina ai”.

        “Eh tabbas haka muka faɗa, sai dai kuma ba’a samu nasara ba kamar yanda mukai tunanin za’a samu. Rashin samun nasarar kuma na nufin shigar ahalinki a haɗari ta fuska biyu. Na farko mu jami’an tsaro ba zamu barsu ba har sai wancan hatsabibin yazo hannunmu. Hakan shine zai wankeki a garemu mu tabbatar baki da alaƙa da shi, ahalinki kuma su kuɓuta. Na biyu dole ne mu baki kariya yanzun dan tabbas zaki zama abin farautarsa kema dan bazai barki ba tunda kin karya masa tarihi. Dolene kowane motsinki dana ahalinki su kasance a tare damu. Idan kin amince ki cike wannan. Kokuma kiyi tafiyarki amma babu ruwanmu da abinda zai samu ahalinki. Zakuma mu fitar da bayanan sune ke aikata laifukan da muka nuna miki ɗazun da mabanbanta fuskoki. Kinga za’a kamasu a kaisu kotu, da ga ƙarshe a yanke musu hukuncin kisa bayan duniya ta sansu matsayin ƴan ta’adda”

           Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Hibbah. Idanunta suka ciko da hawaye ta shiga girgiza musu kai laɓɓanta na rawa. “Dan ALLAH yallaɓai karkuyimin haka. Wlhy bani da alaƙa da mutumin nan sam, iya gaskiyata na sanar muku.”

           “Ta hanyar shigowa kiyi aikin sirri da mu ne kawai zai tabbatar mana da hakan, ahalinki kuma su kuɓuta da ga garesa da mu kammu. Gashi ki cike waɗan nan takardun idan har kin amince”.

         Da ƙarfi Hibbah ta rumtse idanunta. Wani irin zafi da ɗaci na sauka mata cikin zuciya. Karan farko na rayuwarta da taji tsiwa batai mata rana ba. Tanajin tsana mai yawan gaske akan mutumin da batasan wanene shi ba. Yayinda gefe na zuciyar tata ke jin haushin waɗan nan jami’ai da ke son yin amfani da damar da ALLAH ya basu ta hanyar amfani da ita. Wani gefen kuma na haske mata ahalinta cikin bala’i mai muni da idan har ta zama sanadin shigarsu cikinsa har gaban abada bazata taɓa yafema kanta ba. A take wani irin kangarewa da bushewar zuciya suka saukar mata. Batare da yin wani dogon nazari ba wautar ƙuruciya ta fisgeta da zuciya wajen ɗaukar pen ta hau cike takardun da ɓarin jiki, batare data duba mi suka ƙunsa ba..

       Fusatar tata ta basu matuƙar mamaki da al’ajabi. Sai dai zukatansu na ayyana musu tanayin komai ne domin ahalinta. Dan fahimtar sune rauninta ya sakasu yin amfani da su wajen tursasata. Aiko sunci nasara, dan ta cike takardun kamar yanda suka buƙata. Ta kuma saka hannu bisa takardar contract ɗin zatai musu aikin sirri har sai sun kama Master. Su kuma bazasu saki wancan bayanan ƙaryar da suka shirya ba domin mata ɗaurin talala saboda ƙarancin shekarunta.

         Sun mata bayanai sosai da zata iya fahimta. Tare da bata date ɗin da zata fara amsar horo na musamman a ɓoye. Da ga ƙarshe sukai mata dogon gargaɗi akan riƙe dukkan abinda suka tattauna matsayin sirri. Dan inhar ta fitar tamkar ta bayyana ƴan uwanta ma duniya ne matsayin ƴan ta’adda. Daga haka suka sallameta.

        Fitowar Hibbah da aka haɗa da jami’ai biyu zasu mata rakkiya zuwa gida yayi dai-dai da isowar Yaya Abubakar da Yaya Muhammad station ɗin. Tana ƙyalla ido a kansu ta kwasa da gudu garesu. Jikin Yaya Abubakar dake gaba ta faɗa tare da fashewa da kuka.

        Shima rungumeta yay yana mai rintse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Yaya Muhammad ya ƙaraso garesu da sassarfa shima. Dafa kanta da yayine ya sata barin jikin Yaya Abubakar ta rungumeshi shima. Cikin son danne nasa ɓacin ran ya saki murmushi yana ɗagota da shafa kanta. Hannu yasa ya shiga share mata hawaye. “Kukan ya isa haka nan, ba gamu tare da ke ba”. Ya ƙare maganar da sake sakar mata murmushi mai kwantar da hankali.

       Yaya Abubakar da shima ke ƙoƙarin ganin ya shanye tasa da muwar ya ce, “Bara naje zanyi magana da su”.

     Da sauri Hibbah ta riƙo hannunsa tana girgiza kanta. Cikin sanyin da basu santa da shi ba ta ce, “Yaya karka je. Ka barsu kawai babu abinda sukai min”.

            “Karki damu, ba wani abu bane yanzu zan fito”. Yay maganar da zare hannunsa cikin nata yana shafa kanta. Kama hannunta Yaya Muhammad yay shima ya buɗe mota ya sakata, tare da ɗaukar goran ruwa ya miƙa mata. “Sha ruwa ki wanke fuskarki ina zuwa”.

    Hibbah na ƙoƙarin dakatar da shi bai jira cewarta ba ya nufi cikin station ɗin shima. Jitai kamar ta fasa ihu, dan gani take kamar shigar tasu na nufi jami’an zasu riƙesu su sanarma duniyar ƴan ta’adda ɗinne su.

         Ganin an shafe kusan mintuna a shirin tai yunƙurin bin bayansu, sai dai tana buɗe motar suna fitowa kowannensu ransa a ɓace. Ta sauke ajiyar zuciya da yin sagade tai tana kallonsu har suka ƙaraso. Yaya Muhammad ya sake kama hannunta ya sata a motar sannan ya zagaya ya shiga shima. Yayinda Yaya Abubakar ya zauna mazaunin driver.

          

      Suna fara tafiya kiran Ammar ya shigo wayar Yaya Muhammad. Kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga ɗin. Da ga can Ammar ya fara magana cikin ɗacin murya. “Yaya kazo gida dan ALLAH akwai matsala. Hajiya mama da Abba na nan sun taru akan Ummi harda Junaid. Nayi magana kuma ta dakatar dani. Wlhy zanma Haƙilu (Abba) dukan mutuwa sai dai Ummi ta tsinemin. Har wannan shegiyar tsohuwar ba raga mata zanba dan mahaifina ta haifa ba ni ba.”

        “Ammar!!”

Yaya Muhammad ya kirayi sunansa a tsawace jin zai yanke kiran shima jikinsa na matuƙar rawar ɓacin rai.

        Tuni Ammar ya riga ya katse kiran baima jisa ba. Yaya Abubakar da duk yaji komai ya ƙara ƙarfin gudun motar, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu a ƙofar gidan. Tun a waje yay fakin, gaba ɗayansu suka fita da sauri zuwa ciki. Dan tun da ga waje suna jiyo kururuwa da ihun Hajiya Mama da Momy.

         A harmutse suka iske gidan. Ammar da Junaid na kwasar uban dambe. Sai dai duk da kasancewar Junaid yaya ga Ammar hakan bai hana Ammar hayewa saman ruwan cikinsa yana duka ba tamkar ALLAH ya aikosa. Mahaifiyar Ammar ɗin da suke kira Momy taje ceton ɗanta Ammar ya bata mahangurɓa a muƙamuƙi. Tuni ta koma gefe jikinta na matuƙar rawa. 

         Abba da hajiya mama kuwa tuni suna a wani lungu maƙale dan su ne Ammar ya fara fafara Junaid ɗin ya maresa. Shine faɗan ya juye a tsakaninsu. Da ga cikin lungun Hajiya Mama keta fama kwaɗa ihu da kururuwar Ammar zai kashe mata jika. Yayinda Abba ke a rikice ga tsoro, yana son zuwa ɗakko waya ya kira ƴan sanda yana tsoron fita Ammar da ya juye musu kamar wani mayunwacin zaki ya gansa ya dawo kansa.

      Ummi ce kawai akan Ammar tana ƙoƙarin janyesa tana kuka amma ta kasa, dan gaba ɗaya ya juye mata tamkar ba Ammar ɗinta ba. Ya koma ainahin sunansa na ALIYU ZAKI.

          

      Kuka Hibba ta fashe da shi ganin yanda Yaya Ammar kema Junaid dukan mutuwa. Sai jini ke fita ta hancinsa da baki amma yaƙi sakinsa. Da ƙyar Yaya Muhammad da Yaya Abubakar suka iya haɗuwa wajen ɗagasa da ga kan Junaid ɗin. A hakanma sai famar turjewa yake yana nuna Junaid cikin gargaɗi.

           “Duk iskanci da kukejin kun iya da rashin mutunci muma mun iyasa. Ba tsoronku bane yasa muke barinku kuna taka mana mahaifiya yanda kuka gadama. Son yin biyayya a gareta da ga taka mana birkin da take na barinku kawai ke dakatar damu. Amma idan har kun isa wani ya sake nuna nata ɗan yatsa a gidan nan ya gani in ban karya shi ba na tauna ƙashin. Wlhy hatta waccan annamimiyar tsohuwar bazan bari ba, sai na ida ƙille ƙafafun nata ta koma gurguwa ta gaske…….”

         Kuka sosai Ummi keyi tana kiran sunan Ammar amma yaƙi yin shiru. Su Yaya Muhammad suka turashi sashen nasu da ƙyar suma rayukansu duk a jagule.

       A dai-dai wannan lokacin ɗaya da ga cikin ƴammatan gidan ta dawo. Horn tayi mai ƙarfi kamar yanda suka saba. Da sauri mai-gadi dake maƙale yana kallon duk abinda ke faruwa da ga windown ɗakinsa shima ya fito  domin buɗe mata gate ɗin. Sai dai shima har cikin ransa yaji matuƙar daɗin dukan nan da Ammar yayma Junaid. Dan duk wani cin zarfi da akema mahaifiyar su Ammar ɗin a gidan akan idonsu ne tun da ƙuruciya.

       A guje Ameera ta danno motarta cikin gidan kamar yanda ta saba. Sai dai hango su Abba akan Junaid da ke kwance kamar ya mutu ya sata saurin taka birki tamkar ba’a cikin gida ta ke ba. Fitowa tai da sauri. Ta zaro idanu sosai cikin ƙaraji na rashin tarbiyya take tambayar miya samu Junaid ɗin?.

           Abba yay saurin ɗago Junaid ɗin da numfashinsa ke fita da ƙyar yana faɗin, “Kinga maza buɗe mana motarki mu kaisa asibiti shine mafi muhimmanci yanzu. Sauran bayani ƙyaji da ga baya dan anzo gabar da yaƙin duniya na uku zai fara tashi a gidan nan.”

       Zata ƙara magana Hajiya mama ta katseta a tsawace. Baki ta murguɗa mata da yin fari da idanu sannan ta nufi motar tata Abba da mai-gadi biye da ita ɗauke da Junaid da gaba ɗaya jini yayma fuskarsa faca-faca………..✍

    *TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* 

            

    

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like