TAKUN SAKA 18

Advertisement

 

*_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*

 *Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

*_Muna da haɗin_*

_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

_Muna Gyaran jiki_ 

_Na amare_ 

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_

_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

 _EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_

••••••••••••••••••••••••••••••••

*_Chapter Eighteen_*

…………..Tashin hankalin wannan magana yasa na yanke jiki na faɗi, dan ko sanda akai na Muhammad da sauƙi inada garkuwata Aliyu. Amma wannan ni kaɗai ce naketa ƙoƙarin kare kaina sai malam da Halilu da bansan miye manufarsa na bani kariyar ba. Kamar na Muhammad wannan ma malam yace sai a jira na haihu. Haka kuwa akai, na cigaba da rainon ciki Halilu nata hidima dani da ƴaƴa na. Abin na bani mamaki yana sakani a ruɗani., ya kuma bani tsoro Dan sam na kasa hango manufarsa a kan hakan har takai ALLAH ya saukeni lafiya na haifo ɗiyata mace a karon farko. Itama dai tunda ta diro duniya kowa ya shaida jinin Aliyu ce. Dan kamanni sak ta ɗebo nasa dana ƴan uwanta harma taso ta fisu ɗebo komai nashi, sai dai kawai dan ita mace ce. Bakin kowa ya mutu kam, dan ko tari ba’a sakeba akan batun na cigaba da shayar da ɗiyata da taci sunan mahaifiya Muhibbat. Bakowa bane da wannan aikin sai malam. Ya tabbatarmin da wasiyya ya cika shima. Mahaifina ne ya roƙesa dan ALLAH inhar ALLAH yasa na sami miji nai aure na haifi ɗiya mace duk rintsi yana son a saka mata suna Muhibbat sunan mahaifiyata. Sai ko gashi ALLAH yaja da ran malam ya cika wannan wasiya. Sakama Tanee sunan mahaifiyata shine abu na farko daya jawo mata baƙin jini itama a wajensu. Dan anata ƙananun magana Halilu ne kawai ke karewa. Haka dai sukayi suka gama har ƙura ta lafa. Bayan na yaye Tanee aka raba gadon ku, sai dai malam ya kirani gefe mukai maganar da kunyarsa bazata barni na bijire masa ba. Dan yamin hallaci irin wanda bai kamata ni na saka mishi da butulci ba.”

       “A wancan lokacin bayan na samesa ya fara da faɗin, (Asiya ke ɗin ɗiyace ɗaya tamkar da dubu. Kuma ɗiya kamar sauran ƴaƴa. Dan baki da banbanci da su kamar yanda wasu suke gani. Baki da laifin komai dan bakece kika aikata laifinba. Ita kanta mahaifiyarki ƙaddara ce ta afka mata har aka sameki. Kiyi haƙuri na ɗakko miki wannan zancen ne saboda abinda nake hangowa da zaije ya dawo game da zuri’arki da wannan dukiyar tasu. Nasan baki wuce aure ba. Dan haka manema yanzu zasu fito gareki tako ina. Sai dai bai zama lallai su kasance dan ALLAH zasuzo ba ko dansu riƙe waɗan nan marayun. Banason bayan babu raina ki shiga gararin rayuwa. Dan mahaifinki kafin yabar duniya yayi matuƙar nadama ya duƙufa neman gafarar ALLAH, ya duƙufa neman ilimin addini a wajena batare da kowa ya sani ba. Shiyyasa ya danƙa amanarki a gareni. Kuma insha ALLAHU zan yi iya bakin ƙoƙarina naga na tsare wannan amanar har zuwa sanda nima ta ALLAH zata kasance. Asiya babu wanda yafi cancanta ya adana dukiyar ƴaƴanki sai ke da kanki, amma dole sai da taimakon namiji. Ni kuma gashi ƙarfina ya ƙare, dan bani da isashshiyar lafiyar nima tun bayan rasuwar Zaki (da yake haka yake kiransa). Amma inata nazari har zuciyata ta yanke min wata shawara da nake fatan zata zama mafita agaremu baki ɗaya. Halilu ɗan uwane ga zaki, duk da halayyarsu ta banbanta. Amma shima idan kin lura ya jima da dawowa hankalinsa. Rasuwar ɗan uwansa kuma ta sake lausasar dashi ko mahaifiyarsu baya son yaji ta aibantaki. Shiyyasa nake ganin mizai haka ki amince ki auresa ku haɗu ku riƙe wannan amanar da ALLAH ya bar mana ta yaran nan da dukiyarsu har sanda zasu kai girma. Na tabbatar hakan zai sakaki nutsuwa da kwanciyar hankali Asiya. duk runtsi babu mai rabaki da ƴaƴanki kema kina gidan mijinki tare da su. Ko sake haihuwa kikai dai duk zasu zama da ga tsatson jini ɗaya ba zaki rarraba kan zuri’arki ba. Amma bawai dole bane fa. Na baki dama kije kiyi nazari daga nan har wata guda. Hukuncin da kikaji ya kwanta miki a rai sai kizo min da shi. ALLAH yayi miki albarka, yayama yaranki albarka. ya baku kariya a dukkan motsinku da numfashinku). Cikin kuka na amsa masa da amin”.

         “Tunda malam ya tafi ya barni ban huta ba dare da rana akan tunani da nazarin wannan tayi nasa nake. Na hanga na hango naga zancensa shine kawai mafita a gareni da ku kanku. Sai dai har cikin raina ina matuƙar tsoron abinda zaije ya dawo akan Halilu. Dan gaba ɗaya yanzu ba iya gane inda ya dosa nake ba kai tsaye. Ya riga yayma kansa lulluɓin biri da fatar kura. Ta wani gefe kuma ina kallon kima da darajar malam. ALLAH ne ya zaɓa min Aliyu matsayin miji shine ya zama sila kuma. Bai duba ni ɗin wacece ba, bai ƙyamaceni kamar yanda kowa ke ƙyamata ta ba. Ɗansa ya karɓeni da hannu biyu babu musu, ya nunamin dukkan soyayya da ƙauna. Ya bani farin ciki a ƙarƙashin igiyar aurensa. Koda suɓutar baki bai taɓa gorantamin akan asalina ba. Idan ma na faɗa ƙwaɓata yake ya nunamin ɓacin ransa. To nikan inba butulci ba mizai sa na bijirema zaɓinsa a karo na biyu. Ina ganin koda Halilu mutumin banza ne zanyi fatan dawo da shi hanya. Yanda mahaifinsa da ɗan uwansa basu ƙyamaceni ba shima bazan ƙyamacesa ba. Da waɗan nan kalolin tunanin na gama yankema kaina shawara, a ƙarshen watan da malam yazo ziyararmu tamkar yanda ya saba a kowane wata sai na nuna masa kawai na amince. Ya matuƙar nunamin farin cikinsa da jin daɗi. Yayta sakamin albarka da sakama ƴaƴana. Indai ta ƙaice muku zance da ga ƙarshe an ɗaura aurena da Halilu, auren da ya bama kowa mamaki, musamman da akaga Hajiya mama ko tari batai akansa ba balle asan bata so ko tana so. A farkon auren nan a kunyace nake da lamarin Halilu kota wane fanni, amma ina iya bakin ƙoƙarina na sauke haƙƙokinsa a kaina. Shima kuma yana bani kulawa da respecting ɗina. Hakama ƴaƴana ƙauna yake nuna muku tamkar mahaifinku. Hankalina ya sake kwanciya da shi, na saki jikina sosai tare da ɗaukar duka dukiyarmu na danƙa a hannunsa akan cewar sai kun girma za’a bama kowa nashi. Da farko ya nunamin bazai amsaba. Sai da naita roƙonsa da nuna masa muhimmancin zaman komai a hannunsa saɓanin ni mace. Da ga ƙarshe dai ya amsa da ƙyar. Sati biyu kacal da yin haka ALLAH yayma malam rasuwa. Ƙwarai da gaske na shiga ruɗani fiye da rasuwar mahaifina. Dan malam ya taka matukar rawar gani a rayuwata wadda baki bazai musalta ba. A wannan lokacin naje ƙauye rasuwar malam, duk da a ɗarare nake da kowa ban samu matsi kamar sanda ina rayuwa a ciki ba. Sai ma abin kallo da na zama ni da ƴaƴana saboda da kaina naja mota ta har can. Kwanan malam huɗu da rasuwa kakana ma ya rasu, mahaifin babana kenan. Ban wani ji tasa rasuwar ba. Dan da shi da babu a gareni duk ɗaya dai. Satina guda a kauye muka dawo tare da Halilu, inda tun shigowarmu na fara ganin sabbin al’amura da ga garesa da suka nema rikita mani tunani. Cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja. Hajiya mama ta dawo nan da zama, hakama matar Halilu da ƴaƴansa. Ya cireku da ga makarantar da kukeyi ya maidaku ta gwamnati, nima ya haramtamin tuƙa mota. Al’amarin ya matuƙar gigitani da sani a tashin hankali, amma saina daurema zuciyata saboda halaccin mutane biyu da nake tunawa a koda yaushe. Kawu na da mijina. Komai ya sauya da ga salonsa. duk wata cusgunawa ita Halilu da Hajiya mama kemin harma da matarsa da yaransa. Ku kanku baku da sukuni a gidan koda nayin wasa ne. Abubuwa da yawa kullum cikin gorantamin su yake, tare da neman komai gareni ta ƙarfi (uwa ta gari kenan, maimakon tace yana mata fyaɗe saita sirranta domin mutunta kanta😭). Ɗawainiyarku duk ta dawo hannuna. Komai baya mana ya bari. sai ma filin garden ɗinmu da Aliyu ya kashe kuɗi sosai yayisa saboda mutumne mai tsananin son furanni da ƴayan itatuwa Halilu ya bajesa ya kafa wancan ginin, part ɗinsa da matarsa, sai part ɗin hajiya mama. Bayan an kammala suka koma can da zamam babu ruwansu damu balle yaya mukaci, sai tarin masifa da hantara a garemu. Gidan da Aliyu ya sai min da kuɗin hayarsa na cigaba da ɗaukar nauyin karatunku, sai taimakon Sheikh Aliyu Maina abokinsa. Dan ya matuƙar taka rawar gani akan rayuwarmu shima. kullum nunamin yake nayi haƙuri na cigaba da rayuwa da Halilu har kukai girma dukiyarku ta dawo hannunku sannan na rabu da shi. Wannan yana cikin dalili na na karshe bayan tuna halacci da ƙauna da mahaifinku da Malam suka nunamin a rayuwa, yayinda kowa ya gujeni har ƙannen mahaifiyata. Shiyyasa kukaga ina cigaba da jure komai har kawo iyanzu da insha ALLAHU komai yazo ƙarshe, zamu bar musu gidan duk da kuwa haƙƙinmu ne. Dukiyarku kuma idan ma bai baku ba ku barsa da ALLAH kawai tunda ya rufa mana asiri bamu rasa ci ba balle sha da suturar sakawa. Fatana kar wannan labarin ya sakaku tunanin ɗaukar wani mataki akan hajiya mama da Halilu. Ku barsu ALLAH zai muku maganinsu ta hanyar da bakuyi zato ko tsammani ba. Dan banason ya cutarmin daku. Dan ALLAH na roƙeku ku barsu mu rabu lafiya salin alin”.

           Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, sai faman sharar hawaye kawai sukeyi. Hibbah ta fara miƙewa taje ta rungume Ummi, sai Yaya Ammar ma yaje ya haɗasu su biyun ya rungume. Hakan yasa suma sauran duka suka miƙe sukaje suka rungumesu baki ɗaya. Idan ka gansu dole ne su baka sha’awa, su baka tausayi, su kuma birgeka.

      Sun ɗau tsahon lokaci a haka kafin su koma su zauna suna mai kallon Umminsu cike da tausayinta da tsananin soyayyarta. Yayinda Hibbah duk ta fisu jin kewar mahaifinsu da ko cikinta baisan ya bari ba. Duk da kuwa yayi ƙwaɗayin a haifa masa ɗiya mace matuƙa ALLAH bai ƙaddara zai gani ba.

      “Ummin mu ai kece ZAKIN, SARAUNIYAR DUNIYA TA MATA”. Ammar ya faɗa cike da zolaya yana share hawaye. A tare suka sanya dariyar da basuyi niyya ba. Dan yanda Ammar ɗin ya faɗa yana salute na Ummi dole ne ya baka dariya.

      Duk yanda sukaso ɗakko maganar Ummi ta hanasu, sai ma ta shiga jansu da wata hirar cike da tsokana suna kwasar dariya. Gaba ɗaya sun shagala da batun fita aiki da makaranta, balle kuma breakfast ɗin da sukai zaman yi. Kafin su farga sai kiran sallar zuhur sukaji. Nanfa aka shiga jaje da sallami. Ummi kuwa ta dinga musu dariya wai yau itace gwamnatin da sukaima aiki ai.

         Suma dariyar sukeyi cike da nishaɗin ganinta cikin farin ciki, da ga karshe kowa yabi hanyar data dace wajen neman excuse a wajen aikinsa. Yaya Umar dama kasuwa ce baida matsala. Su Hibbah kuwa makaranta ce. Haka suka ƙarasa wannan yinin a tare, salla kawai ke fiddasu ƙofar gida har dare. Da za’a kwanta ma Hibbah ta maƙale tare da Ummi zata kwana. 

*_WASHE GARI_*

     Yau da sassafe duk sukai shirin fita aiki kasancewar jiya basu fita ba. Kamar yanda suka saba kullum yanzu suna ɗan fita da kayansu masu muhimmanci zuwa sabon gida saboda masu gidan yau ma sai da Yaya Muhammad da Yaya Abubakar suka ciccika booth ɗin mota sanan suka fice. Ammar kuna ya dauka Hibbah a mashin shima suka wuce makaranta. Yayinda suka bar Ummi na cigaba da haɗe musu abubuwansu masu muhimmanci da suka rage.

*________________*

     Kwanakin biki sun cigaba da gabatowa gab, dan yau gashi har an kawo lefen Hibbah gidan. Lefe ne na ƴar gata da ya bama kowa mamaki. Dan ƙiri-ƙiri yaran Abba suka shiga nuna hassadarsu da baƙin ciki. Ita kanta Hajiya mama da Momy tunma baƙin na nan suke yadda habaice-habaice dan zubarda mutunci. Ita dai Ummi komai batace ba. Dama ta gayyato ƙawayenta iyayen su Zahidah sai matan Sheikh Aliy su mama Jiddah😜 da suka amshi lefen. Dama hidimar tarbar baƙi duk da ga gidan Sheikh Aliyun aka yota. Komai sai gani su Hajiya mama sukai ana shigo da shi gidan. Ga makwafta sunyi hallaci duk sun shigo ana komai da su.

     Lefe kam yayi sai sam barka. dan Muhammad Shuraim ya kankaroma Hibbarmu  mutunci😂😉. Ita tanama makaranta sai da ta dawone taga akwatina da kayan su sweets biscuits da sauransu. Sosai abin ya bata mamaki har tana ƙorafin kamar hauka. Ita batason fariya. Ai basai ya nuna sunada shi ba.

         “Oh ni Ali, yau naga uwar kutsugu. Danma kin samu ya kankaro miki mutunci zaki mana iyayi a gida”. Ammar ya faɗa yana dalla mata harara. Itama harar ta dalla masa tana murguɗa baki. “To karya kankaro mutuncin mana. Wayace masa shi ake jira ya kankaro”.

       “Ni wlhy ina so da fatan ganin randa wanann bakin naki na akku  zai mutu murus auta.”

      “Ai bazaka gani ɗin ba kuwa Yaya Ammar.”

       “Hhhhh ALLAH dai ya kaimu ranar shiga labour room, kafin sannan ma nanda kwana goma sha bakwai kacal nasan ya gama mutuwa kodan rabuwa da ni da Ummi. Ayye mama ayye mama, mamaye iye, ayye mama labo labo, mamaye iye. Da aure yana raka aure, mamaye iye, dana biki mun tafi tare. Mamye iye, ko tuƙin tuwo ƙya koya, mamaye iya, har damun fura ƙya koya………”

      Kuka Hibbah ta fashe da shi da faɗin, “Ummi kin gansa ko. Wlhy nama fasa dan babu inda zanje to”.

     Da farko dariya Ummi da su Yaya Muhammad da suka shigo keyi, sai da sukaga abin nata da gaske ne sai kuma duk jikinsu yay sanyi. Dama su kansu dauriya kawai sukeyi. Dan tun shigowarsu sukaci karo da akwatinan sai zukatansu suka raunana. Suna matukar son Hibbah, gashi aure zai rabasu rana tsaka. Ita kanta Ummi wani lokacin har tambayar kanta take wai miyasa ma ta amince aima Hibbah aure yanzun ne. Itakam bataso a rabata da ɗiyarta. Zuciyarta kan gaya mata su waɗanda ƴayanta maza zasu auro fa? Da ta tuna hakan kuma sai tai shiru ta miƙa wuya.

     Ɗaki Ammar ya wuce yana sharar hawaye, dan dama komai da yakeyi dauriya ce kawai. Da gudu Hibbah ta tashi tabi bayansa ta rungumesa. Sai kawai suka fashe da kuka a tare. Duk yanda su Yaya Usman sukaso daurewa hakan ya gagara, suma sai gasu suna share ƙwallan a kaikaice.  Saurin barin falon Ummi tai, batasan yaya suka ƙare ba sai da ta fito bayan sallar isha’i ta samesu suna kallo ball Hibbah da Ammar na gaddama harda jefama juna filos tamkar basune suka gama shan kuka ba ɗazun.

       Washe gari bayan wucewar su Yaya Muhammad aiki aka miƙa kayan nasu auren gidajen matansu batare da sanin su Abba ba. Dan daga gidan Sheikh Aliy aka ɗauka. Hibbah ce kawai taje aka kai da ita ko ina. Dan haka ranar bataje makaranta ba. Sai da yamma liƙis ta shigo gidan a gajiye, ga ciwon kai. Sama-sama ta gaida Ummi ta shige ɗakinta acewarta zata watsa ruwa.

     Tana fitowa wankan ta tsinkayo muryar Ummi na kwala mata kira. 

          “Tanee! Tanee!!”  muryar Ummi dake ƙwala mata kira da ga falo ta cigaba da shiga kunnuwanta. Amsawa tai cikin saka kaya sauri-sauri sanann ta fito. Ganin Ummi zaune tare da Isma’il ya sata ƙalaro fara’ar dole ta yafama kanta. “Uhm su Yaya Isma’il ne yau a gidan namu? Yaushe a gari inji maƙi baƙo?”.

        Guntun murmushi ya saki dai-dai yana ɗagowa ya kalleta. “Auta nifa hausar nan taki cikin hausa na dulmiyar dani da yawa.”

         “Tofa, abinma ƴar zolayace kenan Yaya Isma’il. Ykk ya Abba da Dubai?”.

        “Abba yana lafiya. Nima kuma haka. Dubai kam tana can mun baro musu abinsu, mun dawo ƙasar gado”.

       Dariya Ummi da Hibbah sukai a lokaci guda. Yayinda Ummi ta ɗora da faɗin, “Yau kusan sati kenan inata jajen rashin dawowarka. Ga bikin ƴan uwanka nata matsowa ko faɗa maka ba ai ba”.

      “Biki kuma Ummi? Badai su Yaya Muhammad bane zasu angwance?”.

        “Aiko sune Isma’il, komai yazo ne a ƙurarren lokaci. Su duka huɗun ne insha ALLAH sai Tanee kuma”.

      A take alamar shock ta bayyana saman fuskar Isma’il har Ummi da Hibbah suka lura. Da sauri ya ce, “Ummi Muhibbat kike nufi kowa?”.

        “Eh ita kuwa Isma’il. Muma dai haka abin yazo mana tamkar haɓo”.

         Duk yanda yaso ɓoye ɗacin da ke tattare da muryarsa kasawa yay. “Ummi dama akwai maganar aure akan Muhibbat kenan?”.

          Ummi da yanayin Isma’il ɗin ya raba ma hankali biyu tace, “A’a Isma’il. Cikin kwanakin nan dai aka fara. Da yake kuma ALLAH yasa abin a kusa yake sai gashi har an kammala magana. Dan gaba ɗaya bikin yau saura kwana goma sha uku ne”.

           “A…ALLAH sarki, UBANGIJI ALLAH ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Ummi. Dama zan wuce ne nace bara na leƙoku. Inga bara inje zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan dawo. Ga tsarabarki nan ke da Muhibbat”.

           A yanda yake maganar ne ya saka wutar kan Ummi da Hibbah ɗaukewa. Sukai tsit a falon harya fice basu iya furta komai ba. Sai kallon juna da sukai suka kuma sake maida dubansu ga ƙofar tamkar zasuga Isma’il ɗin tsaye bai tafi ba.

         “Ummi kamarfa ransa ya ɓaci?”.

“Nima abinda ya bani mamaki kenan Tanee. Ko maganar aurenku ce ta ɓata ransa?”.

        “To Ummi mizai bata masa rai anan? Maybe dai akwai abinda ke damunsa daban ba wannan ba”. Hibbah ta ƙare maganar tana sakkowa da jawo ledar daya ce tasunce. Turarrukane a ciki da make-up box ƙarami mai ƙyau. Sai takalmi da jakka suma masu ƙyau kala biyu. Na Ummi da nata.

         Tana tsaka da ƙoɗa ƙyawun kayan Yaya Muhammad ya shigo. Ummi ce kawai ta samu damar masa sannu, Hibbah kam sam hankalinta baya wajensa. Sai da ya kai zaune yake faɗin, “Ummi lafiya kuwa? Miya faru da Isma’il?”.

          “Wlhy ban saniba Muhammad, nima man mamakin yanayin nasa ne ya sani zaman jugum nan.” (gaba daya ta kwashe yanda sukai ta bashi labari).

       “Tofa, anya kuwa Ummi Isma’il ba son Hibbah yake ba?”

    Da sauri Hibbah ta juyo ta kalli Yayan nata. “Yaya so kuma? Ni?”

       “Tabbas auta. Dama zuciyata ta jima tana rayamin Isma’il dan ke yake tare da mu. Dan take-takensa gaba ɗaya sun nuna akwai soyayyarki a zuciyarsa. Shiyyasa naso ace yana nan maganar nan ta taso na aurenkin nan. Koba komai ni hankalina ma zaifi kwanciya da Isma’il ɗin fiye da shi Shuraim ɗin nan. Duk da shima dai babu wani aibu tare da shi dan yau ɗin nanma sai da na sake samun bayanan binciken da na saka akaimin a kansa bayan waɗan can na baya”.

      Nannauyan numfashi Ummi taja, gaba ɗaya zuciyarta ta dagule. Dan harga ALLAH tana jin son Isma’il matsayin siriki a gareta. Sai dai kuma ƙaddara ta rigada ta riga fata. Dan babu ta yadda za’a gyara abinda tun farko aka ɓata. Shima harda laifinsa da bai fito ya nuna ba, a yanzu kuma basu da hurumin rusa maganar Shuraim inba so suke su kasance ƙananun mutane ba kuma.

     Ita dai Hibbah ko a jikinta. Tama cigaba da harkar gabanta ne dan kallon yaya take masa har cikin zuciya. 

★★★

     Kwanaki uku Isma’il bai sake dawowa gidanba. Hakan duk sai yabi ya dami Ummi harta ɗauka waya ta kirasa akan tana son ganinsa. Baiko musa ba sai gashi yazo da hantsi. Lokacin su Hibbah duk sun fice sai ita kaɗai.

        Ummi tanada dabaru sosai na iya sarrafa mutum bisa ƙyaƙyƙyawar hanya. Shiyyasa ta tarbiyanci ƴaƴanta da tarbiya mai ƙyau da ke bama kowa mamaki da yaba ƙoƙarin ta. Duk da Isma’il yazo mata ransa a cinkushe cikin hikima da dabarun da ALLAH ya bata ta bi da shi da nasiha. Cikin ƙankanin lokaci sai gashi yayi laushi, ya kuma gane cewar laifinsa ne da yabar zancem a ransa bai furtaba.

      “Ummi nagode matuƙa da gaske. Kiyi haƙuri ban tashi da uwa ba shiyyasa abubuwa da yawa bana ganesu kai tsaye sai sun ƙure min. Idan kuma ba’an fahimtar dani bane haka zanta kallonsu a yanda na ɗauka. Bazan boye miki ba ina matuƙar jin daɗin kasancewa da ke. Kuma ina miki kallo ne irin na uwa wlhy. Shiyyasa kikaga ko yaushe ina nane da ke. ALLAH ya sanya albarka a auren Hibbah na haƙura. Amma tabbas ina sonta da ƙaunarta. Wasu kuma nagartattun halayenki ne da nata suka jani ga hakan abinda ban taɓa tsintar kaina a ciki ba. Amma dan ALLAH koda wataran inaso ki cigaba da tuna hakan. Kuma kamar yanda kika fahimtar dani wanann bazai zama ƙarshen zumincinmu ba. Zan cigaba da kasancewa da ku a koda yaushe tamkar da. Zanje na nema yan uwana su Yaya Muhammad mu cigaba da hidimar biki”.

        “Alhmdllh naji daɗin hakan Isma’il, ALLAH yay maka albarka. Kaima ALLAH ya baka wadda tafi Tanee ɗin”.

     Murmushi ya saki mai sanyi laɓɓansa na ɗan motsawa alamar amsawa. da ga haka ya saki jiki da Ummi suka cigaba da tattaunawa akan hidimar bikin. Bata ɓoye masa zancen barinsu gidan ba da planning ɗinsu akan rusa auren ƴaƴan Abba da yaranta. Shima kansa yaji daɗin haka. Ya kuma tabbatar mata zai bada muhimmiyar gudun mawa. Da ga haka yay mata sallama ya tafi.

*___________________________*

         Alhamdulillahi, akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, shirin biki kam da gaske ya ɗau harama. Dan kuwa baƙi harsun fara sauka a gidan musamman na ɓangaren momy matar Abba. Hakama dangin hajiya mama sun fara sauka. A ɓangaren Ummi ne dai babu ko kare da yazo har yanzu. Ko’a jikinta dan dama batasa rai ba. Mutanen arziƙi ma da zata tara anan a cewarta sun wadaceta.

           A ɓangaren amaren su Yaya Umar na ɓoye har sun jajje sunyi jere a sabon gidansu. yayinda suma anan su hajiya mama suna shirin zuwa suyi nasu jeren na ƴaƴansu a gidajen Hayar da Abban ya kama.

          Itama dai Hibbah kayan nata jeren har sun isa gidanta. Dan kuwa yayunta sun haɗa ƙarfi da ƙarfe da taimakon Isma’il sun mata kaya ƴan gaske na ƴar gata. Dan data ga kayan sai kawai ta fashe da kuka dan daɗi. Ita kanta Ummi da ta gani sai da ta koka a ɓoye. Musamman da ƴan jere suka dawo cike da farin cikin tarbar da suka samu da kuma ƙyawun gidan na Hibbah.

      Hibbah Amarya kuwa da su Zahidah amaren su Yaya Usman Ummi da Mama Jiddah ce ke gyaresu da ingantattun magungunan sanyi harda amaryar Yaya Umar. Sai ingantaccen tsumi da duk ta sami iliminsu da ga Sheikh Aliyn ta (karku manta masanin sirrin magunguna ne😹). Dan hatta maganin sanyin ma shine ya haɗama su Hibbah da kansa. Sai Haɗaɗɗun kayan gyaran fata na dilka da ƙamshi da Mama Maimoon uwargidan malam ke gyaresu da su itama. Ta ko ina Ummi dai ta zama ƴar kallo.

       Gaba ɗaya Hibbah ta tattara batun wasu ƴan sanda da wani master can😏 ta watsar, dan kasancewar su waje guda da su Hafsat ya mantar da ita komai. Iyakarsu susha shaftarsu, kowa idan nata angon ya kirata ta koma gefe tasha soyayya. To ita Hibbah ma bazatace soyayyar take sha ba, dan sam Shuraim bai cika damuwa da kiranta a waya ba. Yafi tura mata text massege na sonjin lafiyarta kai tsaye. Ita kuma jan aji yasa itama bata kiran nasa balle nuna damuwarta da hakan garesa. ko sau ɗaya ma bata taɓa ƙorafi ba.

        ★★★

   A yau laraba aka saka dukkan amaren a lalle. Dan kamar yanda aka saka su Ameerah da Hibbah anan gidansu, haka aka saka su Zahidah a nasu gidajen batare da duk wanda ke zagaye da su yasan su waye angunan ba. An dai san ana biki, hatta da Momy da Hajiya mama sunsani tunda anguwa ɗaya ne layi ɗaya. Sai dai basusan anguna ba basu kuma damu da sani ba tunda ba wani mu’amula mai karfi ce a tsakaninsu ba. Hasalima sun tsanesu saboda suna huɗɗa da Ummi. Ko gidan sukazo aka gamu da ƙyar suke amsa gaisuwarsu.

    Yau akai kamu da ya kayatar matuƙa anan harabar gidan. Dan ƙarya sosai momy ta nuna ma ƙawayenta data tara cike da gida da danginta. Sai dai kuma koda anguna sukazo fili bisa gayyatar da akai musu sai suka ƙare da bama autarsu kulawa ta musamman. Dan har liƙeta sukai da kuɗaɗe sanda masu kiɗan ƙwarya ke bugawa. Nanfa ƙananun magana suka fara tashi, zukatan su Ameerah fal baƙin ciki da takaici. ji suke wata muguwar tsanar Hibbah na sake shigarsu matuƙa, amma dai duk sun danne a zukata bisa huɗubar iyayensu akan shirinsu.

     Oho su Yaya Abubakar ma basusan sunai ba. Su dai kawai burinsu autarsu tayi farin ciki, tafi kuma kowa. Burin nasu kuwa ya cika. Dan ta haska haskawa mai tsayawa a rai duk da ango baizo ba danginsa sunzo ansha shagali da su.

     Washe gari kuma alhamis akai walima da hajiya mama ta ɗauki nauyi😝. Aka gayyato matan Sheikh Aliy sukai wa’azi, yayinda aka ci aka sha kowa yay ɗiff. Gab da magrib aka tashi. Su Ameerah kuma suka dasa nasu fatin su da kawayenau maza da mata a hotel. Babu ango ko ɗaya a wajen, dan su su Yaya Muhammad ma zuwa lokacin suna manne da Umminsu dake ta musu nasiha suna sharar hawaye tamkar ba gida ɗaya zasu cigaba da kasancewa ba. Hibbah kuwa kuka take iya iyawarta harda amai. Da ga ƙarshe kuma sai zazzaɓi ma ya rufe ta. Har sai da Isma’il da yazo kawo drinks da za’ai amfani da shi na ɗaurin aure ya kira family doctor ɗinsu yazo ya dubata. Ana mata allura yay tafiyarsa shi da doctor ɗin.

*_RANA BATA ƘARYA…….._*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😂.

*LALLAI YAU AKE TAKUN SAƘAA😖🐒*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like