TAKUN SAKA 19

Advertisement

 *_Typing📲_*

*_Chapter Nineteen_*

………..Kamar yanda suka saka ɗaurin aure bayan sakkowa sallar juma’a su Ummi basu canja ba. Gida ya gama cika da dangin Momy da na Hajiya mama anata hidimar girki. Sai wasu tsiraru da ga abokan arziƙin Ummi na nan anguwa dana nesa.

Advertisements

        Anguna kam suna can a gidan da suka samu aro anan anguwar da abokansu. Sai dai tunda safe sun shigo sun gaida Umminsu. Tare da sake lallashin ƴar ƙanwarsu Hibbah da duk tabi ta takura kanta. Zazzaɓin nata yama sauka tunda safe amma duk ta zama wata kalar tausayi. Magana kaɗan sai ta kama hawaye. Ga ƙawayenta na secondary cike da ɗaki amma duk ta ƙi sakewa. Sai faman shaƙiyanci suke mata ta kasa maida murtani dan bakin ya mutu murus.

          Kusan sha ɗaya wata ƙawar Ummi ta shigo ta sata tashi dole tai wanka. Mai kwalliya ta shigo tai mata dai-dai misali dan da farko ma catai bataso sai da Ummi tai magana. Itama taci gayunta ɗas tamkar wata ƴar talatin. Dan sam Ummi bata da ƙiba, ALLAH yayi mata jiki mai ƙyau, shiyyasa da yawan mutane idan akace itace ta haifa su Yaya Muhammad sukan musa, inba ka nutsu wajen kallon fuskarta ba sai ka ɗauka yayarsu ce kawai.

      Amarya Hibbah ta fito ras abinta, tamkar ka saceta ka gudu. Ƙawayenta nata tsokanarta akan gaskiya ya kamata a ɗauka hoto a turama ango. Banza tai musu dan ita sai ma yanzu ta tuna da wani ango. Tun jiya damuwarta kawai rabuwa da ahalinta batashi take ba. Ga shi tanajin kewar su Zahidah da babu dama suzo nan suma suna gidajen iyayensu.

      A ɓangaren amare su Ameera ma kowacce ta ɗau kwalliya ta gani kasheni, da ka gansu kaga amare kam dan anata zuba iyayi da gwalli. Su barin gidan ma ko’a jikinsu suke jinsa. Ga ƙawayensu sun zagayesu sai taɓara da zancen banza suke zubawa suna sheƙa dariya.

         Ƙarfe sha biyu da kusan kwata anguna suka shigo gidan cikin kwalliyar fararen shaddoji tas iri ɗaya. Hatta da Ammar irin kayan ya saka shima. Idan ba’a faɗa ba sai ka ɗauka shima angon ne. Guɗa mata da ke kai kawon girki a tsakar gida suka shiga musu. Kowa na yaba ƙyawun nasu da yima mahaifinsu addu’a da babu rabon ya ga wannan rana.

         Ummi da ƙawayenta na zaune a falo suka shigo. Tai sagade tana kallonsu idanunta na cika da ƙwalla. Tanaji a ranta inama ace Aliyu na raye wannan rana…… Durƙusawar da sukazo gabanta sukai duka ne ya katse tunaninta. Tasa hannu ta share ƙwallar da suka taru mata a ido tare da kai hannu ta dafa kan Yaya Usman da ke kusa da ita. Sai kawai ta fashe da kuka. Har rige-rigen matsawa suke gabanta kowa ya riƙe hannunta idanunsu na cikowa da ƙwallan suma. 

        Sosai abin ya birge mutane ya kuma basu tausayi. Ummi ta shiga kwarara musu addu’oi da sanya albarka ana amsawa da amin. Kafin a kira Hibbah itama mai hoto yay musu. Itama kanta sai da tai hawayen jin daɗin ganin ƴan uwanta kamar ka sacesu ka gudu dan ƙyawun da sukayi. Sai dai tanajin ɗacin kasancewar su Amlah matsayin matansu bayan su Zahidah.

      Suna tsaka da hotunan kira ya shigo wayar Hibba. Tayi ƙoƙarin sharewa aka sake kira. Yaya Muhammad dake kusa da ita ya ɗauka wayar ya duba. Ganin Shuraim ke kiran nata ne ya sashi hararta yana miƙa mata. “Auta bana son rashin ji fa. Maza kije da ga waje sai ki ɗaga”. 

      Kanta kawai ta ɗaga masa. Tare da tashi tabi ta kitchen ɗinsu ta zagaya baya domin kiran Shuraim ɗin……

Advertisements

      “Yauwa A.G zamu iya magana yanzu na fito”.

    Muryar Abba ta saka Hibbah saurin dakatawa a ƴar barandar kitchen ɗin nasu. Abu biyu ne yaja hankalinta ga Abban. Na farko yanda yake tsaye a laɓe wajen tamkar wani tsohon munafuki, na biyu sunan A.G da taji ya ambata. Wanda inhar hasashenta yayi dai-dai sunan dattijon jami’in nan haka yake shima A.G. Maganar Abba ta sake katse tunaninta.

          “A.G nawa, kasan mutunuyar taka tana nan tana jira kazo ka saceni ni da duk masu hannu a ɗaurama yayunta aure da ƴaƴana.”

        Batajin mi ake faɗa da ga can, sai dai yanda Abba ya tuntsure da dariya ne ya saka zuciyarta tsargawa duk da batasan wane A.G ɗin ba. Abba ya ciga da faɗin, “Inaga zan fito yanzun nan kuwa insha ALLAH, dama munyi shirin wucewa wajen ɗaurin auren ne. To amma su zan barsu su wuce kai kuma mu haɗu a gidan hutuna muyi magana”.

       Gaba ɗaya jikin Hibbah rawa yake, tai saurin leka bayanta. Ganin hankalin yayunta da su Ummi duk yana kan yin hoton ya sata saurin jan ƙofar kitchen ɗin tayo waje. Bayan Abba da ya bar wajen tabi da sauri. Kasancewar da sanda yake tafiya saboda kafarsa da bata gama warkewa ba yasa Hibbah cin masa, sai dai a sace take binsa yanda bazai gane ba. Suna gab da fita ta ɓarauniyar ƙofar da ke bayan ɗakunan su Abba taci karo da hijjab ɗin wata mata dake alwala a fanfo. Dauka tai ta saka, tai saurin bin ta gate ta fice batare da an ganeta ba dan harda nikaf. Cikin sa’a ta cimma Abbah ta baya saboda harda gudu ta haɗa duk da tarin mutane dake shirin tafiya ɗaurin aure a ƙofar gidan nasu. Ganin Abban ya shiga wata baƙar mota dake fake a barauniyar ƙofar tasu itama tai azamar tare mai napep. 

        “Malam dan ALLAH motar can nakeso kabi, amma banason ya fahimci shi ɗin muke bi Please”.

        “Babu damuwa hajiya, amma kenan kuɗinki zasu kasance masu nauyi fa?”.

       Batare da tamaji abinda yace ba tace, “Babu damuwa muje”.

      Kasancewar mai napep da alama kwararren matuki ne ya dinga bin Abba abaya ta yanda bazai iya fahimta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso wata anguwa mai ƙarancin hayaniyar mutane. Da alama sabuwar anguwa ce, dan ga uncompleted buildings nan bar-katai. Sai dai kasancewar inda Abba ya faka motar a farko-fatkon anguwar ne sai ya zama wajen yayi ɗan rukunin gidajen da aka kammala. Tun a titin ta sauka. Ta dubi mai napep ɗin cikin raba hankalinta biyu. “Dan ALLAH ka jirani nan bazan jimaba zan fito. na maka alƙawarin ko nawa ka bukata zan baka”.

     Cikin farin ciki da tunanin yayi babban kamu yace, “Babu damuwa hajjaju a fito lafiya”.

      Gaba Hibba tai batare data amsashi ba. Ta bi ta bayan gidan inda take addu’a da fatan samun koda karamar hanya ce da zata shiga gidan. Dan Abba na shigewa aka rufe gate ɗin. Sam babu wani hanya data samu, dan haka tai azamar sake dawowa ta gaban gidan zuciyarta na ayyana mata wata dabara. Gate ɗin ta ƙwanƙwasa kaɗan tana waige-waigen bayanta da addu’ar dacewa. Batare da zaton anjita ba taji an buɗe gate ɗin. Tai saurin kallon wajen tana jan numfashi. “Barka da rana”. Ta faɗa cikin matukar kashe murya. 

     Kallon sama da ƙasa mai gadin yay mata, kafin yace wani abu tai azamar faɗin, “Ni baƙuwar Alhaji ce”.

         Maigadi yay ɗan shiru alamar tunani. kafin yace, “Amma hajjaju idan Alhaji zaiyi baƙuwa yakan sanar min, yanzu ko bai faɗa ba ya shige duk da naga kamar cikin sauri yake”.

       Cikin ƙara ƙasa da murya Hibba tace, “Ka bama kanka amsa kenan, saurin nasane yasa bai faɗa maka ba inaga. Amma bara na kira maka shi zai fi…..”

       Da sauri maigadi yace, “A’a hajiya bama sai anyi haka ba. Nasan inba da sanin Alhaji ba babu wani mahaluki kam da zaizo nan. Bismillah”.

     Ya kai karshen maganar yana matsawa ya bata hanya. Wani shegen ajiyar zuciya Hibba taja tana ƙoƙarin haɗiye busashen yawun da ya daskare mata a baki tana ƙoƙarin shigewa.

      “A fito lafiya hajjajuuu”.

Maigadin ya faɗa cike da shaƙiyanci.

★★★★

        A ɓangaren su Yaya Muhammad kam sun cigaba da hotonsu da tunanin Hibbah nacan na waya da Shuraim ne. Sunyi hotuna sosai da jama’ar da ke a sashen na Ummi kafin su fito domin tafiya massallaci karsu rasa salla. Kusan tare suka fito da gayyar su Kawu Hannafi da ƙannen Momy da yayunta. 

        Cikin tsari gayyar motocin ɗaurin aure suka bar anguwar batare da kowa ya farga babu Abba a tafiyar ba. Yayinda aka bar mata na cigaba da himar abinci da shagali a cikin gida. Sun isa massallacin juma’a gab da za’a fara khuɗuba. Kamar yanda aka tanadar musu gaba saboda za’a ɗaura aure duk aka basu hanya suka shige. Sai da suka nutsu waje guda Sheikh Aliy ya fara gabatar da khuɗuba mai taɓa zuciya akan kashe-kashen dake faruwa a ƙasar nan na zalunci. Tare da jan hankalin hukuma da gwamnati akan sake jajircewa. Hakama jama’ar gari ba zama zasuyi kallon gwamnati da hukumaba suma. Dolene a miƙe da addu’a kuma kowa ya zama jami’in sirri akan abinda bai gamsu da shi ba. Sosai khuɗuba tai tasiri a zukatan bayin ALLAH. Da ga haka aka fara gabatar da sallar Juma’a.

       Kasancewar mutane sun san da ɗaure-ɗauren aure bayan idar da salla babu wanda yay yunƙurin tafiya. Sai lokacin su kawu Bello suka fahimci babu Abba tare da su. Nan fa aka shiga tambayar juna, sai dai kowa yana cewa bai gansa ba maybe bai ƙaraso ba..

       Miƙewa ƙanin Momy yay ya fita a taron da zummar neman wayar Abba suji ko ina ya tsaya…..

★★★★★

         Addu’a Hibbah ke karantowa tana ƙara kutsa kanta cikin gidan da batasan kansa ba. Sai da ta ga ta bacema idon maigadin sanann ta ɗan dakata ta sauke numfashi. Haggu da damanta ta kalla ko zataga ƙofar shiga. Cikin sa’a idonta ya hango mata window. Da sauri ta nufi windown tana addu’ar ya kasance inda zata iya hango su Abba.

     A rufe windown take, dan haka tai gaba cikin takaici da fatan samun mafita a gaba. Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke saboda cin karo da ƙofar kitchen irin ta bayan nan. Ta kama handle ɗin ta murɗa a hankali cikin sa’a ta buɗe. Wani irin daɗi ne ya baibayeta kamar ta tashi sama. kitchen ne babba, komai na amfani akwai, da alama ma ana amfanin da shi, dan yanzu hakama ga alamun anyi girki a ciki. Gaba tai zuwa ga ainahin ƙofar kitchen ɗin ta cikin falo, tai saurin maida kanta baya saboda ganin Abba zaune tare da wani mutum a dining ɗin abinci jere tamkar masu shirya fati.

      “Ina fatan kukun nan taka ta fita ko?”.

      Mutum da ke tare da Abban ya faɗa. Ƴar dariya Abba yayi, cikin salon narke murya tamkar wanda ke gaban mace yace, “Karka damu nace taje waje ta zauna. Bakuma zata shigo ba sai na bata umarni kaima ka sani”.

      “Hakane baƙon ya faɗa yana sumbatar hannun Abban”.

    Wani irin mugun faɗuwa gaban Hibbah yay. Tai saurin kauda abinda zuciyarta ke bijiro mata ta sake maida hankali akansu.

       “A.G kasan a ƙage nake da son jin abinda ke bakinka, duk da kuwa kwana biyu ina tare da kewar harka saboda jiyya data cikuykuye rayuwata. Amma soon zan dawo, fatana a ɗaura auren nan yau cikamakin bukatuna su sake shiga tafin hannuna sannan na dawo. Kaima kasan banida wani buri da ya wuce dukiyar ƴaƴan Aliyu cigaba da kasancewa a hannuna. Hakan kuma naga bazata taɓa tabbata ba har sai na aura musu ƴaƴana, sannan na bisu ɗaya bayan ɗaya na halaka su. Dan duk wadda ta fara samun ciki a cikin ƴaƴana to mijinta ne zai fara baƙuntar lahira. Ko ƴaƴan nawa da mahaifiyata basu san da shirin nan nawa ba. Sai na gama da su kaf sannan na ɗinke bakin zaren *_TAKUN SAAƘA_* ta da Asiya. Wadda ubanta ne ya fara sarƙata akan mugun bugun da yay mini tun tana ƴar shekara goma sha ɗaya kacal a duniya.”

      Dariya A.G yayi da faɗin, “Baka da dama Gwarzo. Wato kai sam baka manta bashin gaba.”

       “Har abada kuwa A.G. Naso fanshewa akan budurcinta hakan ya gagara, abin takaici da baƙin ciki ta sake hawa kaina, aka aurama Yayana uwa ɗaya uba ɗaya shi ya mora bayan na ƙwallafa rai. Tazo ta katantane komai, duk hanyar dana ɓullo akan wasoson dukiyarsa sai tabi ta toshe ta hanyar fargar da shi. Shiyyasa yanzu daya mutu bayan ya tara musu na shirya hawa kan dukiyar, sai dai nafison nacita a gaɓar da Asiya zatafi jin ciwo da raɗaɗi, kamar yanda na ɗauki tsahon shekaru ina jin ciwo da raɗaɗin abubuwa masu yawa a kanta. Wannan dalilin ya sani yin dakon shekaru goma sha tara ina haƙurin cigaba da juyata tana haɓaka har zuwa yanzu da wasan zai fara. Sai na ɗan-ɗana-ma Asiya azabar ciwon mutuwar ƴaƴanta ɗaya bayan ɗaya a tafin hannunta”.

       “Anya kuwa hakan ta kasance Gwarzo? Dan wannan ƙaramar ƴar tata ta fi sauran yaran tsaurin ido da rashin tsoro. Shiyyasa nake ganin wautarka na canja ɗanka da zai aureta zuwa wani daban, duk da nasan wanda ka canja ɗin yafi ɗanka kwaƙwalwa da wayo da hatsabibanci. Kagafa shekararta sha takwas kacal amma take da dabarar ƙulla agreement da ƴan sanda akan a ƙwamusheka ranar aurensu domin yayunta su kuɓuta daga auren ƴaƴan naka. Ina jimaka tsoron wannan yarinyar fiye da kowa cikin ƴaƴan matarka. Koda yake nasan Master bazai taɓa yarda da mace ba”

        “Humm kai kasan tun randa ka bani labarin nan da mamakin yarinyar nan nake kwana nake tashi a raina. Yanzu haka fa tana can tana jiran ku tattareni kenan fa?. Batasan kai ɗin mutumina bane.”

     Atare suka kwashe da dariya. Yayinda Hibbah dake makale tana saurarensu ta daskare a tsaye, dan zuwa yanzu ta gama fahimtar dattijon jami’in nan ne dai A.G da ya sakata bibiyar Master…….

     Maganar Abba ta katse tunaninta.

  “Karka damu ita na gama da lamarinta kaima ka sani. Shi wanann yaron dana kawo ya canji Junaidu dan ya aureta kamar yanda ka faɗa yafi Junaid hatsabibanci kaima ka sani, sannan a tafin hannunmu yake a kuma gaɓar da muke more ƙuruciyarsa. Ana gama ɗaura auren zanbi shawararka na biya mata kuɗin karatun tafiya China kamar yanda take buri, da wanann damar zanyi amfani na ɓadda rayuwarta. Dan rashin nata ne zai fara karya rayuwarsu saboda tsananin son da suke mata matsiyatan sai kace ƴar gwal. Ku kuma da ya ɓaddata zaku amfani da wannan damar ne ku fito ku nunama duniya shi wannan Master ɗin da kuke nema ruwa a jallone ya sace ta. Kaga shikenan babu mai zargin Halilu Hamza gwarzo kenan ko”.

    Ya kare maganar da shaƙiyancin da ya sakasu sake kecewa da dariya. Jikin Hibbah ne ya kama rawa. Tai saurin kai hannu ta toshe bakinta jin kuka zai kufce mata. Dai dai nan A.G ke faɗin, “Gaskiya mun iya maida mutane wawaye. Kowa ya saki baki kullum muna aikin tukuru na son kamo Master, basu san shi kansa Master ɗin mune muka ƙirƙiresa ba. Yana gama tattare mana kuɗaɗen shima zamu ɓaddashi a doron ƙasar baki ɗaya, mu kuma cigaba da amfani da rigar jami’an tsaro wajen tsula tsiyarmu. Yayinda duk wanda ya fito da niyyar aikin gaskiya mu ɓadda banza, dan mu ba gyaran kasarne gabanmu ba. Wanda suke gaba damu kuma mu cigaba da kwantar musu kai muna nuna mun fisu san ƙasar da cigabanta, da tabbatar musu aiki muke tuƙuru. Kaga mun toshe ko ina kenan”.

      Dariya suka kuma kwashewa da shi, har sai da kira ya shigo wayar Abba sanann suka tsagaita. Ya miƙe yana faɗin, “Alhaji Alu ne ke kira, ina kyautata zaton suna wajen ɗaurin aure tashi muje dan nasan ana gab da ɗaurawa kar ayi babu mu.”

     Da sauri A.G ya riƙo hannun Abba cikin marairaicewa yake faɗin, “Gaskiya ina da bukata, shine ma dalilin da yasa na kiraka nan. Ka barsu kawai su ɗaura tunda ko baka akwai masu amsa da bayarwa, ni kuma ka ragemin zafi anan. Dan kwana biyun nan matasan ma da muke ɗan samu mu taushe wa’azin malaman nan ya fara tasiri a ransu gudunmu sukeyi shegun.” Abba ya buɗe baki zaiyi magana A.G ya sake marairaice masa da rungumosa jikinsa cike da salon shaiɗanci da bushewar zuciya irin ta masu fasadi da rashin tsoron ALLAH a ban ƙasa😭. (Wa’iyazubillah. ALLAH mun tuba ka yafemu🙏🏻😭😭). 

(Ya ALLAH ka gafarta mana badan halinmu ba, ka kare mana zuri’armu da mazanmu da ƴan uwanmu da matasan al’ummar musulmi baki ɗaya😭🙏🏻. Abba ɗan homo, A.G ɗan homo, da ire-irensu abokan ƙazantarsu da yawa dake lullube da rigunan mutunci suna cin dunduniyar al’umma da addini. Kuga dai A.G, ya shige cikin jami’an tsaronmu jajirtattu yana tsula tsiyarsa ta hanyar ruguza shirye-shiryensu batare da sun sani ba. Shin kamar yanda ya faɗa Master yaronsa ne? Su Master kema aiki?. Mu cigaba da kasancewa a cin TAKUN SAAƘA domin jin yaya take ne?)

       

        Gaba ɗaya jikin Hibbah rawa yake yi, ta shiga tafiya da baya-baya zuciyarta na tsitstsinkewa tamkar zata faɗo waje. Wani irin duhu-duhu idanunta suka farayi, abinda takeji a labari shine yau a zahirin rayuwa take gani ga ƙanin mahaifinta da idan aka tsaga jininsa za’a ga nata a ciki. Innalillahi wa inna-ilaihirraji’u. (Dole ne kafin a daura auren nan tayi wani abu) wannan tunanin ya sakata zabura ta fito a guje. Kotakan maigadi dake zaune yana sauraren redio bataiba ta buɗe gate ta fice. Saurin miƙewa yay yana tambayarta lafiya?. Ina batama san yanai ba. Yay saurin bin bayanta wajen, sai dai kafinma ya leƙo ta kusa kaiwa titi inda take tsammanin mai napep ɗin nan na jiranta.

       Waige-waige ta shigayi dan babu mai napep babu alamarsa. Cikin hakki da rawar jiki ta ciro wayarta dake maƙale cikin zani ta hau laluben wayar Yaya Muhammad. Harta katse bai ɗaga ba. Ta sake kira nan ma bai ɗaga ba. Ta maida akalar kiran nata kan Yaya Abubakar tana fassewa da kuka. Sai dai shima harta katse bai ɗaga ɗin ba. 

        “Yaya ku ɗaga dan ALLAH”. Ta faɗa a kiɗime tana zubewa ƙasa da sakin wani kuka mai ban tausayi. Tunanin kiran Ammar ne yazo mata a zuciya. Cikin sa’a kuwa ya ɗaga a bugu biyu, sai dai batajinsa sosai sai tsananin hayaniyar ƴan ɗaurin aure. Da ga can shima sai faman faɗin, “Hello! hello! Auta bana jinki wlhy, ki yi haƙuri zan kiraki za’a fara ɗaura auren ne”. 

    Kafin tace wani abu ya yanke wayar ƙit. Daga wayar tai zata dasa da kasa sai kuma ta fasa. Tai azamar yage niƙaf ɗin fuskarta ta jefar da tunanin fara gudu tabar cikin anguwar kozata sami abun hawa. Inda rabo sai ta isa massalacin kafin a fara ɗaura auren.

         

      ★★

   Matashin saurayin da ke can baya kaɗan da Hibbah cikin wata farar mota ya gyara zaman abinda ke kunnensa, cike da girmamawa yace, “Boss ta fito. da alama abin hawa kuma take nema, tunda na kaɗa mai napep ɗin da ya kawotan”.

      Bansan amsar da aka bashi ba da ga can, ya dai gyaɗa kansa cikin ƙara bama wanda yake maganar da shi girma, tamkar yana gabansa ya sake faɗin. “Yes Master. Insha ALLAH”. Da ga haka yay ma motar key tare da harbata kan titin ya nufi Hibbah da ke tsaka da tattare hijjabi da alama gudun da ta yankema zuciyarta shawara take shiryamawa. 

         Sai dai jin tamkar tahowar mota a bayanta ya sata sauri juyowa ga titin tana ƙoƙarin yin alamar tsaidawa. Bai tsaya ba sai da ya ɗan gota ta sannan ya dawo da baya. Yana tsayawa ko tunanin taga waye bataiba ta buɗe murfin ta shiga baya. “Bawan ALLAH dan ALLAH babban masallacin juma’a na Sheikh Aliy Maina zaka kaini, ka taimakeni kayi sauri na roƙeka dan ALLAH.”

        Jin shiru bai amsata ba bai kuma tada motar ba ya sakata cigaba da magana cikin tsumar jiki da ƙaguwa. “Malam dan ALLAH ka taimakeni, wannan ita kaɗaice damar da nake da ita ta ƙuɓutar da ƴan uwana da ni kaina. Tana kufcewa mun faɗa gararin rayuwa”.

        Yanzun ma komai bai ceba. Sai handkerchief ɗin da ke saman cinyarsa ya ɗauka ya jefa mata a kan fuska. Hannu tasa ta kaɗe handkerchief ɗin da faɗin, “Malam wane irin wulaƙanci ne haka? Minene wannan ka………”

      Ta kasa ƙarasa abinda take shirin faɗa ɗin saboda duhu da ya mamaye ganinta baki ɗaya. Tai ƙoƙarin fisgo numfashin da ke san kufce mata tana kai hannu bisa ƙofar da laluben neman sa’ar buɗewa. Sai dai ina abinda ke jikin handkerchief ɗin ya gama tasiri a cikin jikinta, tai baya jikin kujerar yaraf tamkar wadda aka zarema rai. 

         Sassanyan numfashi Habib ya sauke yana mai ƙoƙarin hana kansa yimata kallon ƙurulla ta cikin mirror ɗin gaban motar ko dan kima da darajar wanda ya sakashi ɗakkotan. Ya ɗan murmusa yana ma motar key tare da harbata kan titi…………✍

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like